Friday, September 12, 2025
26.1 C
Abuja

3MTT Programme zai sa matasa da yawa su samu aikin yi inji minista

MINISTAN Yaɗa Labarai da Wayar da Kai, Alhaji Mohammed Idris, ya bayyana cewa gwamnatin Tinubu ta shirya tsaf don samar da ayyukan yi miliyan uku ga matasan Nijeriya ta hanyar Shirin 3MTT.

Ministan ya bayyana hakan ne a Abuja ranar Litinin a Taron Matasa ‘Yan Sandan Nijeriya mai taken “Inganta Ƙimar Matasan Nijeriya don Tsaron Ƙasa.”

Ministan, wanda ya samu wakilcin Darakta Janar na hukumar gidan rediyon Muryar Nijeriya (VoN), Malam Jibrin Baba Ndace, ya ce shirin na 3MTT, wanda Ma’aikatar Sadarwa ke jagoranta, wani shiri ne na ilimi da ƙwarewar da za su inganta iyawa da ƙimar matasa a harkar tsaron ƙasa.

Join 3MTT alts here

Ya ce: “Shirin 3MTT tabbaci ne na burin Shugaba Tinubu na samar da cigaban matasa a cikin dabarun cigaban ƙasa baki ɗaya. Domin samar da kyakkyawan tsari don cimma wannan, gwamnatin tana kuma ba da fifiko ga tattalin arzikin matasan Nijeriya, wajen gina ƙasa mai tsaro da wadata.”

Idris ya ce kafa Asusun Ba Da Lamuni na Ilimi na Nijeriya (NELFUND), wanda a halin yanzu yake bayar da lamuni da tallafin kuɗi ga ɗaliban Nijeriya, yana ɗaya daga cikin manyan tsare-tsare a ƙarƙashin Shirin Sabunta Fata na Shugaba Tinubu, da nufin yin tasiri sosai kan neman ilimi na matasa.

A yayin da yake magana kan tsadar sufuri a ƙasar nan, ministan ya ce Shugaban Ƙasa ya ɓullo da shirin CNG don amfani da isasshiyar iskar gas da ƙasar ke da ita wajen rage farashin sufuri da kusan kashi 70.

Ministan ya kuma jaddada buƙatar da ke akwai ta matasa su yi koyi da kyawawan ɗabi’un da suka dace domin su taka rawar su a harkar tsaron ƙasa.

Sai dai ministan ya gargaɗi matasa kan illolin da yaɗa labaran ƙarya ke da shi ga tsaron ƙasa, yana mai cewa wannan muguwar ɗabi’a amfani da ‘yancin faɗin albarkacin baki, wanda gwamnati mai ci yanzu ta amince da shi, ta hanyar da ba ta dace ba ne.

Ya ce: “Inda aka ba da yawa, ana sa ran da yawa. Dole ne mu yarda cewa yaɗa labaran ƙarya ya haɗu da babbar barazana ga tsaron ƙasa, wadda ta haɗa da tada hankali, rashin zaman lafiya, laifuffuka na ƙasa da ƙasa, ta’addanci, fashi da makami, tsattsauran ra’ayi, da munanan ayyukan da ake yaɗawa ta hanyar intanet.”

Hot this week

SEC States That Meme Coins Are Not Securities

On Thursday, the Securities and Exchange Commission (SEC) made...

“NDLEA Destroys 25 Tons of Illicit Drugs in Kogi: A Major Blow to Drug Trafficking”

A Landmark OperationIn a significant move to combat drug...

Tinubu Dismisses NYU VP, Empowers UNIABUJA VC: Leadership Changes in Nigerian Universities

President Bola Ahmed Tinubu has made some bold leadership...

NAHCON Chairman Welcomes NCPC Executive Secretary at Hajj House

In a move aimed at strengthening interfaith cooperation, the...

El-Rufai Joins the Battle: Accuses Ribadu of “Amnesia” in Naja’atu Muhammad Feud

The ongoing war of words between National Security Adviser...

Topics

Eniola Badmus Reaffirms Her Support for President Tinubu, Sparking Reactions

Eniola Badmus, a well-known actress and Special Assistant for...

Rapper Jeriq Explains Why He Has Never Been in a Relationship

Nigerian rapper Jeremiah Chukwuebuka Ani, widely known as Jeriq,...

Album Releases: Ruger and Joeboy Face Off in a Supremacy Battle

The Nigerian music scene is buzzing with excitement and...

“Famous singer NBA YoungBoy has been released from prison.”

Popular American singer Kentrell DeSean Gaulden, better known as...

“My kind of wealth cannot be achieved through investment,” Davido proudly declared.

Nigerian Afrobeats singer David Adeleke, widely known as Davido,...

“I backed Tinubu, but the hardship is becoming unbearable,” said Cynthia Morgan.

Nigerian singer Cynthia Morgan, now known as Madrina, has...
spot_img

Related Articles

Popular Categories

spot_imgspot_img