Friday, September 12, 2025
23.1 C
Abuja

Amurika da Africa ta kudu zasu kara dankon dagantaka da girmama juna

Afirka ta Kudu na neman ‘girmama juna’ a dangantakarta da Amurka

Afirka ta Kudu ta jaddada ‘muhimmancin kyakkyawar alaka’ da ke tsakaninta da Amurka.

Afirka ta Kudu na neman “ci gaba da kulla alaka bayyananniya” da Amurka kan batutuwan yankuna “bisa doron girmama juna”, in ji Ministan Harkokin Waje Ronald Lamola.

Lamola ya bayyana haka a ranar Alhamis bayan kammala ziyarar da ya kai Amurka.

Ya isa Washington a makon da ya gabata a yayin da ake yada jita-jitar cewa jami’an diflomasiyyar Isra’ila na rokon ‘yan majalisar dokokin Amurka su tirsasa wa Afirka ta Kudu ta janye karar kisan kiyashi da ta kai Tel Aviv a Kotun Kasa da Kasa (ICJ).

Afirka ta Kudu ta kai Isra’ila kara Kotun kasa da Kasa saboda hare-haren kan mai uwa da wabi da take kaiwa Gaza da aka mamaye wanda ya yi sanadiyyar mutuwar mutum 41,200 tun watan Oktoban bara.

Lamola ya gana da manyan masu ruwa da tsaki a Washington, ciki har da kwamitin Majalisar Wakilai Kan Afirka, Kwamitin Bakaken Fata, Kungiyar ‘Yan Kasuwar Amurka da kungiyoyi masu zaman kansu.

‘Yarda da sabanin ra’ayi’

Ministan harkokin wajen ya jaddada muhimmancin cigaban sauyin da ake samu a alakar da ke tsakanin Afirka ta Kudu da Amurka, inda ya kuma zayyano fannonin da ake hada kai.

“Ana matsa wa gaba, za kuma a bi hanyoyin dorewar tasarin dangantakar siyasa a koyaushe,” in ji Lamola.

Da yake jawabi ga Babban Taron Shekara-Shekara Karo na 53 na ‘Yan Majalisar Dokoki Bakaken Fata a Washington a makon da ya gabata, Lamola ya bayyana cewa “Mu yi mu’amala duk da bambance-bambance amma kuma dole mu yarda ana iya saba wa juna.”

Ya ce “Ba za mu fada wa Amurka abinda za ta yi ko me muke tsammani ta fada mana mu yi ba.”

Hot this week

“Shehu Sani Warns: Ukraine to Lose Land to Russia, $500bn Minerals to US Amid War Fallout”

The ongoing war between Ukraine and Russia continues to...

Pope Francis’ Health: Doctor Says Pontiff ‘Not Out of Danger’ Amid Recovery

Pope Francis’ personal physician, Dr. Sergio Alfieri, has given...

Trump Sparks Controversy Over 14th Amendment, Claims Birthright Citizenship Was Never Meant for Immigrants

Trump Challenges Birthright Citizenship in New Executive Order President Donald...

Trump announces he will implement tariffs on products from the EU

U.S. President Donald Trump has once again emphasized his...

“America, China And The World As Trump Returns”

When Huge Fortune Is Involved There Is No Price...

Topics

Eniola Badmus Reaffirms Her Support for President Tinubu, Sparking Reactions

Eniola Badmus, a well-known actress and Special Assistant for...

Rapper Jeriq Explains Why He Has Never Been in a Relationship

Nigerian rapper Jeremiah Chukwuebuka Ani, widely known as Jeriq,...

Album Releases: Ruger and Joeboy Face Off in a Supremacy Battle

The Nigerian music scene is buzzing with excitement and...

“Famous singer NBA YoungBoy has been released from prison.”

Popular American singer Kentrell DeSean Gaulden, better known as...

“My kind of wealth cannot be achieved through investment,” Davido proudly declared.

Nigerian Afrobeats singer David Adeleke, widely known as Davido,...

“I backed Tinubu, but the hardship is becoming unbearable,” said Cynthia Morgan.

Nigerian singer Cynthia Morgan, now known as Madrina, has...
spot_img

Related Articles

Popular Categories

spot_imgspot_img