fbpx
Monday, January 6, 2025
29.9 C
Abuja

Ana gudanar da zaben gwamnan Jihar Edo

Ana gudanar da zaben gwamnan Jihar Edo

‘Yan takara 17 ne waɗanda suka haɗa da maza 16 da mace ɗaya ke fafatawa a zaɓen domin neman maye gurbin gwamna mai ci a halin yanzu wato Godwin Obaseki.

Tun da safiyar yau dubban mutane suka fita zuwa rumfunan zaɓe a faɗin jihar domin kaɗa ƙuri’a a zaɓen gwamnan Jihar Edo da ke kudancin Nijeriya.

‘Yan takara 17 ne waɗanda suka haɗa da maza 16 da mace ɗaya ke fafatawa a zaɓen domin neman maye gurbin gwamna mai ci a halin yanzu wato Godwin Obaseki.

Sai dai daga cikin ‘yan takarar 17, mutum uku ne za a iya cewa za su fi fafatawa a tsakaninsu.

‘Yan takarar ukun waɗanda suka fi shahara sun haɗa da Asuerinme Ighodalo na Jam’iyyar PDP sai Monday Okpebholo na Jam’iyyar APC da kuma Olumide Osaigbovo Akpata na Jam’iyyar Labour Party.

A wannan zaɓen wanda ake gudanarwa a ƙananan hukumomi 18 na Jihar Edo, mutum miliyan 2.2 ne suka cancanta su jefa ƙuri’a, kamar yadda hukumar zaɓe ta ƙasa INEC ta tabbatar.

Rahotanni sun tabbatar da jibge jami’an tsaro masu ɗumbin yawa a jihar waɗanda suka haɗa da sojoji da ‘yan sanda da jami’an NSCDC musamman a Benin City babban birnin jihar.

Jami’an ‘yan sandan Nijeriya sun tabbatar da aika ‘yan sanda 35,000 jihar domin tabbatar da tsaro, haka kuma ‘yan sandan sun tabbatar da aika jirage marasa matuƙa da helikwafta da sauran kayayyakin aiki domin taimakawa a wurin tabbatar da tsaro a yayin zaɓen.

Hot this week

Wani Alkali yayi Alkawarin zai Biyawa Saurayi Sadakin Naira 100,000

Wani alkali yayi alkawarin zai biyawa Salele sadakin Naira...

Jimami: Rasuwar Dan Sanata Kabiru Gaya a garin Abuja

Munsamu labarin rasuwar Barista Sadik Gaya Wanda yake da'ne...

Topics

Foreign Direct Investment

Foreign Direct Investment (FDI) continues to be a crucial...

Intensified Crackdown on Oil Theft

Nigeria has ramped up its efforts to tackle oil...

Telecom Companies Warn of Service Cuts Due to Rising Costs

Telecom companies in Nigeria are raising alarms about potential...

Jeniks and Qatar’s $20 Billion Deal to Boost Africa’s Gas Wealth

Africa, home to over 620 trillion cubic feet of...

Nigeria Implements Landmark Low-Carbon Policy for Oil Licence Approvals

Nigeria has introduced a landmark policy requiring oil licence...

Do Virgins Always Bleed During Their First Intercourse?

One of the common myths regarding female virginity and...

Do Mermaids Really Exist? An Exploration of the Enigmatic Sea Creatures

For centuries, stories of mysterious, human-like beings living beneath...
spot_img

Related Articles

Popular Categories

spot_imgspot_img