fbpx
Wednesday, January 8, 2025
30.1 C
Abuja

Bongel by Zee Yabour

Bismillaahir rahmanir raheem
Da sunan Allah mai rahama mai jin kai’

SHAFI NA D’AYA

GGC KABOMO

Yara ne mata manya da k’anana duka sanye da uniform na makaranta, kowa da abunda yake yi, wasu na wasanni, wasu na cin abinci wanda ke nuni da lokaci ne na break, Yanayin yaran zai tabbatar maka iyayen su ba masu hali bane, makaranta ce ta gwamnati wacce ana jeka ka dawo kuma akwai b’angaren yan’ kwana.

Budurwa ce yar’ kimanin shekaru 17 da haihuwa zaune a aji ita kad’ai, littafi a gabanta tana bitar karatu, “Bongel sarkin boko, wai bakya gajiya da karatu” Cewar Asiya da shigowar ta kenan, itama ba zata gaza shekaru 17 da haihuwa ba, Ta d’ago kai ta kalle ta tace “Hmm Asiya kenan, wannan shine matakin k’arshe na sakandire wanda ya kamata nayi k’ok’arin ganin na fita da sakamako mai kyau, haka karatun nan shine gatana, shi zanyi na taimaki iyayena, basu da buri da ya wuce ganin na samu ilimi mai zurfi, saboda shi na baro ahalina” Asiya ta jinjina kai da cewa “Allah ya bada nasara”, “Amin” Ta amsa, ta juya ta cigaba da karatun, Asiya ta zauna kusa da ita, itama tana d’auko nata littafin.

“Sannu Baffa, Allah ya tashi kafad’un ka” Dattijuwar mata wacce ba zata gaza shekaru arba’in ba ta fad’a da k’arasawa da hawaye, Wanda aka kira da Bappa kansa ya girgiza yace “Ko bayan raina kada a cire Bongel makaranta ita kad’ai Allah ya bani ikon sawa makaranta, Dan Allah ku cika mun burin nan nawa na ganin tayi ilimi mai zurfi”, “Baffa In Shaa Allahu kana tare damu, zaka tashi ka cigaba da rayuwarka”, Kansa ya girgiza ba tare da ya sake cewa komai ba,

Bongel komai yau sukuku take yin sa, duty d’inta na ranar kawai tayi sa ne, ta fito hostel, Tun shigarta aji bata cewa kowa komai ba, dama ita ba gwanar surutu ba ce, sai dai shirun yau yasha bambam dana kallo, Ta rasa dalilin da yasa bata jin dad’in ranta, ga gabanta dake yawan fad’uwa.

Hot this week

Kazar Kwanci By Rufaida Omar

Kazar Kwanci By Rufaida Omar *1)*  " Mairamu! Mairamu!!" Matar dake zaune...

KAZAMAR AMARYA Na Rahama Kabir Mrs Msg

KAZAMAR AMARYA Na Rahama Kabir Mrs Msg Rahma Kabir:...

RUGUNTUSUMI Book 2 Compelet

RUGUNTSUMI Book 2 part 1 Rubuta labari Abdul’aziz Sani Madakin Gini Ɗaukar Nauyi Mansur...

GUDUN KADDARA NA HUGUMA BOOK 2

GUDUN KADDARA NA HUGUMA BOOK 2            ".............ya fada soyayya?,yana...

Gudun Kaddara na Huguma Book 1

Gudun Kaddara na Huguma Book 1 🏃🏽‍♀️ GUDUN ƘADDARA🏃🏽‍♀️ H U...

Topics

Honeywell Reloaded: Flour Mills of Nigeria Revives Its Iconic Brand

Flour Mills of Nigeria Plc (FMN), the leading food...

Fintech in Nigeria: Breaking Barriers and Driving Inclusion

Nigeria’s fintech industry continues to break barriers, driving financial...

Nigeria to Host Africa’s Largest Tech Expo

In a major boost to its tech credentials, Nigeria...

Edtech Revolution: Nigerian Startups Transforming Education

Nigeria’s edtech sector is witnessing unprecedented growth, with startups...

Telegram Sees A Rise In User Data Sharing With Law Enforcement

Recently published information from the messaging platform Telegram indicates...

BMW’s Latest User Interface Displays Widgets on the Windshield at CES 2025.

BMW is completely overhauling its in-car user interface, beginning...

Lagos Tech Summit Focuses on AI and Blockchain

The annual Lagos Tech Summit returned in 2025 with...
spot_img

Related Articles

Popular Categories

spot_imgspot_img