Ciwon idanu na Kiyi mini magani, nayi Miki godiya kinji masoyiyata
Ciwon idanu na Kayi mini magani, nayi maka godiya kaji masoyina
Amshi Kiran da nayi Miki Kiyi mini lamuni
Na makance idanu na basa gani
Na bi zafi Nabi sanyi Ke nike son gani
Inji sautinki kawai shi zai warkar dani
A rashin lafiya, da nayo kwanciya
Maganar gaskiya, kece magani na
Ciwon idanu na Kayi mini magani, nayi maka godiya kaji masoyina
Gani da batutuwa Don Ke nattanada
Gani da gurin zuwa in ba kya gida
Ke zan kawowa komai kika yo bida
Ba na mantuwa Zance in kin fada
Kiyi mini kwarjini, yanda Nike gani
A so Sam ba yani ko a abokaina
Banjin zugar qawaye a soyayya Kai na dauka
Ka share min hawaye ka sa na daina kuka
Indai ina a Raye Sam ba na barinka
Allahu ya kiyaye bani son waninka
Kaine Dai daya, a cikin zuciya
Mai saka ni dariya, sannu masoyi na
Ciwon idanu na Kiyi mini magani, nayi Miki godiya kinji masoyiyata
Zani zamanto uwa cikin zuri’arka
Zani zamo suruka gun mahaifiyarka
Ba ni barin damuwa ta iso gare ka
Babu jira dariya nayi shirin baka
Bani so Kayi fushi
Na dau alwashi
Ban barinka da qishi
In ka shigo gida na
Banso a mini Zance in ba naki ba
Banso a mini kyauta in ba naka ba
Zani rasa rai Idan aure ba a bani ba
Ban shirin zama da kowa in ba Kaine ba
Maganar gaskiya, a cikin zuciya
Kece Ke daya, ni na aadana
Haaaaaaaah………..
Hooooooooh……….