fbpx
Wednesday, January 8, 2025
30.1 C
Abuja

Cutar Kai by Aysha Bagudo – Complete

~TRUE LIFE STORY~

Free page

*AYSHA A BAGUDO*

WATTPAD @HAUESH

bismillahirrahmanirrahim

EGYPT

*Reehab*  unguwa ce dake    cikin   babban  birnin   kasar  cairo , unguwa  ce  data  tattare kan   manya  attajiran  masu   kudi , zagaye  da had’ad’dun  gidaje  masu kyau  da  tsari  kamar yadda   gidan 
muhammad  realwan  yake   d’aya  daga  cikin jerin   gidajen unguwar   .

    Babban  katanfarin fili ne  wanda  aka gina madaidaicin   gidajen  sama    guda uku  a cikinsa   mai  hawa ɗay d’ay,   tun  daga  bakin  get  din  gidan  har  zuwa  babban   parlou’n  gidajen ciki  zaka fahimce  yadda  had’uwar gidan  yake ,  babban parlou’n  ne  wanda ya kunshi  duk  wani nau’i  abubuwa na  more  rayuwa da qawata  muhalli  , idan mutun yana   parlou’n   zai ɗauka  a wata  duniyar yake  ba’a wannan  duniyar tamu yake  ba.”

makakeken tv bango  ne  manne da bango kowani   parlour dake  cikin  gidan,  ga wani  katon  wutan lantarki  a saman parlou’n   mai  jere da   fitilu  masu matukar haske   riras ,ga masuburbud’an  sanyi , ga  makaken  dining table  zagaye  da kujeru na alfarma  ,  yayinda parlou’n  yake  zagaye   da  fararen  kujeru  masu ratsin  baki ajiki   , banda  kitchen   da   bayi  kwaya daya  tal da  landury ,  babu  d’aki  ko  daya a cikin parlou’n  .”

yayinda sama gidajen  ke  ɗauke   da dakuna  guda  biyu  da parlour d’aya  Alhaji  realwan ya gina wannan katafarin gidan ne  saboda  ya’yansa Aliyu da samir da shi kansa idan ya kawowa kasar ziyara    , yadda   tsarin    ginin   Samir   yake   haka  na     Aliyu   yake babu  wani  bambamci , komai iri  ɗaya  aka zuba acikinsa  “.

Wata  matashiya  mace ce   raku’be a akan kujera  a  matukar  tsorace take a parlou’n  saboda girmansa,   ta  takure jikinta guri  ɗaya  saboda duhun  parlou’n  ga yunwa  dake  tattare daita , tun   jiya da suka sauka  a kasar  bata  ci wani  wadataccen abinci ba   ,tunanin  yadda tahowarsu   ta wakana  take  , tun  da suka shiga jirgi  yake  cicccin magani  wanda a idanun iyayenta  ba haka ya nuna  ba, cikin sakin fuska  da  farinciki  suka rabu  da  iyayensu , jirgin na  gama  mikewa a sararin  samaniya ta nemi  murmushin  dake kwance akan  fuskarsa ta rasa, fuskar  ta dawo tamkar hadari ko ta wani mayunwacin zaki ,a hankali ta  d’aura  kanta a kafad’ansa  ta ɗan  d’aga idanunta kaɗan  ta  kalleshi ,  bai  motsa ba , hasalima wani  bangaren  yake kallo  yana  danne danne a wayarsa   tamkar babu wata halitta  atare dashi ,a hankali  hancinta ya dinga  zuko mata dad’ad’d’an   kamshin turaren   jikinsa dake gauraye da kamshin skin dinsa  , a natse  ta sauke  numfashi kamshinsa  na sake mata  dadi  ,duk wannan shiru  da  yayi  a lokacin  tasan  zuciyarsa cike  take fal  da jin haushinta  ..”

Jin  bai  yi magana ba har  lokacin yasa taki  buɗe  idanunta  , tayi lamo  tana cigaba da  shakar kamshinsa  a haka  bata san  lokacin da bacci ya ɗauketa   kanta na kan kafad’ansa ba.

ji  kanta  ya  bugu da kujera  yasa  tayi firgigib tare da  bude idanunta  da sauri ta furta  “oooooo  ta dafe gefen  kanta  tana kallonsa , ko kallon inda take  bai  yi ba , bama zakace  shine  yayi muguntar  ba,   Allah Allah  ya  dinga  yi  su isa dan  baya  sonta  a kusa dashi  ,yayinda  bangarenta kuwa    babu  abinda  tafi  qauna da muradi  kamar kusancinsu  tare  ..”

Suna  sauka a kasar cairo  motar campanie dana escout dinsa  na  tsaye    zaman jiran  karasowarsu , kai tsaye  Aliyu Muhammed  realwan  ya wuceta ,
cikin sauri itama ta gyara zaman handbag d’inta   ta  biyo bayansa dan  tasan ba karamin aikinsa ya barta agurin ba  , escout dinsa na hangosa suka hanzarta k’arasowa inda yake cikin girmamawa tare da buɗe masa  gidan bayan ,ya shiga ya zauna yana gyara zaman rigar suit din  jikinsa , cikin hanzari itama ta shiga  inda taga an buɗe masa  ta zauna gabanta na faduwa   ,
gama saka jakunkunan kayansu ke da wuya  direba yaja motar  suka bar gurin  escout dinsa na biye da motar da yake ciki a baya  .

Koda  suka  iso  gidan ko’ina  a gyara  yake  tsab   kasancewar Companie   club  ɗinsa  man United  sun san   dawowarsa  dan haka suka  sanarwar    masu  aikin  gyara gida  ,
tsayawa   tayi  a  parloun gidan , shi  kuma cike da kuzari  ya hayewarsa  sama , ganin haka  yasa  ta biyo bayansa  da sauri tana shiga d’akin da ta gani a bude  wayarsa  ta  ɗauki qara  ,hannunsa rike da kugunsa  ya  k’arasa  jikin window  ya  zuge  labule window  yana kallon  haraban  gidan, maganar  minti  goma yayi  yace “gani  nan zuwa   ya  maida wayarsa  cikin aljihun  wandonsa  ya juyo inda take tsaye  “fitar min a d’aki ” ya furta a fusace .

   jiki  a  sanyaye  ta fito ta  tsaya  daga bakin kofar  d’akin  ya  fito ya kulle ya sauko  zuwa  parloun bayansa  ta  biyo ta tsaya, tana  tsaye  mai gadi  ya  shigo da manya  jakunkunansu  ya  juya  ta  kasa  zama  tana kallonsa ya kashe wutan gidan  gabadaya  sannan ya fita   tare da kulle  kofar parloun  bai dawo gidan  ba  sai  tsakar dare  lokacin  tuni  bacci yayi  awon gaba daita akan doguwar   kujera   .

idanunshi  ya  tsura mata  cike da takaicin ganin yadda take bacci  ya balain  bata masa  rai  ya  shiga kitchen ya  buɗe    fridge ya  d’auko  roban ruwa mai  sanyi  ya  fito ya tsaya  akanta ya shiga tsiyaya  mata  tun daga tsakiyar  kanta har sansar jikinta    ta farka a matukar   firgice , yana  ganin ta buɗe  idanunta  ya ɗauke idanunshi akanta  tare da cilla mata  roban ruwan da yayi saura  ajikinta  ya  haura  step ,da sauri  ta mike ta  biyo bayansa  tana masa magana  yayi mata banza , bakin gado ta samu  ta  zauna tana kallon  jikinta dake jike ,   ta  zabga  tagumi   tana kallonsa  ya  buɗe  bakar jakarsa  ya fito da takeway  ,  snaks da  cake  ne  aciki sai driks   ya  zauna kan doguwar  kujera ya mike kafafunsa  ya cinye tasssss  ya da’ura  driks akai  sannan  ya mike ya shiga  bayi ya watsa ruwa  ya fito , haka suka kwana  batare da yayi mata magana  ba ko damuwa da bata abinci ba   .”

To yau  ma  tun  safe daya bar  gidan  bai dawo ba har  gashi  shabiyu da rabi  na  dare  ta buga , tana  cikin wannan tunani   taji motsin shigowar  motarsa  ba’a fi  second  biyu  da shigowar  motarsa  ba taji  yana ƙoƙarin buɗe kofar  parlou’n naunayen ajiyar  zuciya  ta sauke   , haske   wayarsa   ne ya  gwauraye  parlou’n, idanunsa  ne  suka  sauka   akanta  takure guri  daya , a natse ta d’ago  kyawawan idanunta  ta sauke su akanshi   yana  tsaye kikam  kamar  wani soja rashin  wadataccen hasken  parloun  bai hanata  karewa kyawawar  fuskarshi kallon  tsab ba , ita ba dawowarsa   bace  abin daga  hankali da fad’uwar gaba  irin yadda gaba-daya siffarsa ta sauya  ,idanunsa  dake kanta  cike   suke da bala’i iri iri  ,fuskarsa nan nashi  tamkar ba’a taba saukar  da rahma  akanta ba , tana kallonsa ya nufi gurin  meter  yayi changeover   yana jan  tsaki ,  a  yadda   ta lura babu  abinda  ya tsani gani  kamarta   ..”   Ya waigo  bangaren da take  zaune  ,yayi  mata  kallon  second biyu   sannan   ya ɗauke idanunshi  akanta  yana  sake jan  tsaki ya  nufi sama    ya tsaya tare da  tura  hannu cikin aljihunsa  ya ciro key ya bude  kofar  d’akinsa  ya shiga   ya…

Hot this week

Kazar Kwanci By Rufaida Omar

Kazar Kwanci By Rufaida Omar *1)*  " Mairamu! Mairamu!!" Matar dake zaune...

KAZAMAR AMARYA Na Rahama Kabir Mrs Msg

KAZAMAR AMARYA Na Rahama Kabir Mrs Msg Rahma Kabir:...

RUGUNTUSUMI Book 2 Compelet

RUGUNTSUMI Book 2 part 1 Rubuta labari Abdul’aziz Sani Madakin Gini Ɗaukar Nauyi Mansur...

GUDUN KADDARA NA HUGUMA BOOK 2

GUDUN KADDARA NA HUGUMA BOOK 2            ".............ya fada soyayya?,yana...

Gudun Kaddara na Huguma Book 1

Gudun Kaddara na Huguma Book 1 🏃🏽‍♀️ GUDUN ƘADDARA🏃🏽‍♀️ H U...

Topics

Honeywell Reloaded: Flour Mills of Nigeria Revives Its Iconic Brand

Flour Mills of Nigeria Plc (FMN), the leading food...

Fintech in Nigeria: Breaking Barriers and Driving Inclusion

Nigeria’s fintech industry continues to break barriers, driving financial...

Nigeria to Host Africa’s Largest Tech Expo

In a major boost to its tech credentials, Nigeria...

Edtech Revolution: Nigerian Startups Transforming Education

Nigeria’s edtech sector is witnessing unprecedented growth, with startups...

Telegram Sees A Rise In User Data Sharing With Law Enforcement

Recently published information from the messaging platform Telegram indicates...

BMW’s Latest User Interface Displays Widgets on the Windshield at CES 2025.

BMW is completely overhauling its in-car user interface, beginning...

Lagos Tech Summit Focuses on AI and Blockchain

The annual Lagos Tech Summit returned in 2025 with...
spot_img

Related Articles

Popular Categories

spot_imgspot_img