Bayanai daga Unguwar Kurna na nuna cewa akwai matsala a wannan ranar duk da dokar ta baci da aka sanya a jihar Kano inda gungun matasa suka fito suka fantsama a tituna
Wata mazauniyar unguwar ta shaida cewa “A Unguwar mu ta kurna akwai matsala gaskiya, bayan fadan daba sunyiwa DPO duka, yanzu kuma an tayar da zanga zanga. Harbe harbe ba kakkautawa” inji Nadiya
Yanzu haka dai ana ta ƙoƙarin shawo kan zanga-zangar da ta barke a wurare da dama na Kano ciki har da Na’ibawa, Dan Agundi zuwa Gidan Sarki