Saturday, September 13, 2025
22.1 C
Abuja

Da yiwuwar masu amfani da shafin mu na X zasu fara biyan kudi duk wata: Elon Musk

Da yiwuwar masu amfani da shafin mu na X zasu fara biyan kudi duk wata: Elon Musk

Elon Musk
Shafin X ya gudanar da sauye-sauye da dama a kwanakin baya ciki har da sauya masa suna.

Ina Tunanin duk masu amfani da shafin mu na X su fara biyan kudi duk wata: Elon Musk

Musk ya bayyana haka ne a lokacin da yake tattaunawa da Firaiministan Isra’ila bayan firaiministan ya yi tambaya kan yadda Musk zai magance yadda ake amfani da shafukan bogi wurin tunzura kiyayyar Yahudawa.

Shugaban kamfanin X wanda aka fi sani da Twitter a baya Elon Musk ya bayyana cewa akwai yiwuwar duka masu amfani da shafin su rinka biyan wasu ‘yan kudade a duk wata.

Musk ya bayyana haka ne a a ranar Litinin a lokacin da yake tattaunawa da Firaiministan Isra’ila Benjamin Netanyahu bayan firaiministan ya yi tambaya kan yadda Musk zai magance yadda ake amfani da shafukan bogi wurin tunzura kiyayyar Yahudawa.

Daga nan ne Musk ya ba shi amsa inda ya ce kamfanin zuwa gaba na son a fara biyan kudade kadan kafin a rinka amfani da shi.

Babban dan kasuwan mamallakin kamfanin SpaceX da Tesla ya gudanar da sauye-sauye da dama tun bayan da ya karbi jagorancin Twitter inda ya sayi kamfanin kan sama da dala biliyan 44 a Oktobar bara.

Musk ya kori dubban ma’aikatan kamfanin da kuma fito da wani sabon tsarin biyan kudi, da kuma mayar da wasu shafuka wadanda aka dakatar kamar na tsohon shugaban Amurka Donald Trump.

A watan Yuli, Musk ya bayyanan cewa shafin na X ya rasa rabin kudin shigar da yake samu ta hanyar tallace-tallace.

Akwai shafukan bogi wadanda akasarinsu kwamfuta ke kirkiro su da kuma gudanar da su a maimakon bil adama a shafin na X, inda ake amfani da su wurin aika sakonni na siyasa ko kuma na nuna wariyar launin fata.

Hot this week

DeepSeek’s AI Breakthrough: China Has An Edge – But It Won’t Last Forever

In recent weeks, a significant event in the world...

DeepSeek Says It Could Make A Possible Profit Of 545%

DeepSeek, a Chinese artificial intelligence startup, recently made headlines...

Opera Introduces A Powerful AI Helper That Works Directly Inside The Browser.

Opera, the well-known web browser company, has recently introduced...

As Skype Closes, Its Legacy Is Providing End-to-End Encryption For Everyone

On the evening of March 5, 2012, a significant...

This Is How People In America Really Feel About Self-Driving Cars

A recent survey conducted by AAA reveals that a...

Topics

Eniola Badmus Reaffirms Her Support for President Tinubu, Sparking Reactions

Eniola Badmus, a well-known actress and Special Assistant for...

Rapper Jeriq Explains Why He Has Never Been in a Relationship

Nigerian rapper Jeremiah Chukwuebuka Ani, widely known as Jeriq,...

Album Releases: Ruger and Joeboy Face Off in a Supremacy Battle

The Nigerian music scene is buzzing with excitement and...

“Famous singer NBA YoungBoy has been released from prison.”

Popular American singer Kentrell DeSean Gaulden, better known as...

“My kind of wealth cannot be achieved through investment,” Davido proudly declared.

Nigerian Afrobeats singer David Adeleke, widely known as Davido,...

“I backed Tinubu, but the hardship is becoming unbearable,” said Cynthia Morgan.

Nigerian singer Cynthia Morgan, now known as Madrina, has...
spot_img

Related Articles

Popular Categories

spot_imgspot_img