Munsamu labarin rasuwar Barista Sadik Gaya Wanda yake da’ne agurin Sanata Kabiru Gaya.
Sadik gaya ya rasune a babban birnin tarayya a safiyar Talata 14 ga watan Satumbar 2022 kuma anyi janaizarsa a yammacin ranar a birnin tarayya Abuja.
Mahaifinsa Sanata Kabiru Gaya wand yake babban Dan siyasa a jihar Kano kuma Dan majalisar dattawan kasar yasamu sakon ta’aziyya daga manyan yan siyasan jahar Kano da ma qasa baki daya Wanda Gwamnan jahar Kano yakasance daya daga cikinsu.
Marigayi Sadik Gaya yayi karatun lauya a jami’ar Ahmadu Bello da ke Zariya ya kuma yi digiri na biyu a jami’ar Wales dake birnin Landan.
Marigayin yakasance lauya da hukumar kula da dukiyoyi wato AMCON dake Abuja kuma ya mutu ya bar mata daya da yara guda biyu.
Hussaini Ambo Indabawa me magana da yawun Sanata Kabiru Gaya ya sanar da hakan ga manema labarai a jahar Kano.