Fati *3
Faaatimaa……
Fati Fatima autar Mata, araina babu Yake Har kullum
Fati… Ni Fatima autar Mata, a raina babu yakai Har kullum
Fati ni ke nakaso yan Mata
A guna kin wuce sauran Mata
Mafarki na Fatima Idan na kwanta
Natsuwa babu Sai Idan na ganta
Ako yaushe Sai inji ina kewarta
Shiyasa bani so tanai min Nisa
Fati……….. Autar Mata
Kai na zaba, samari kuyo haquri
Na Sanya ka cikin rai, na baka wuri
Da ka nemi ka ganni, za na zo da wuri
Cikin rayuwa ta ka wuce gishiri
Ni Fati, zanyi Wa Mata kuri
Masoyina, ya wuce kanwar lasa
….. Autar Mata
Darajar suna
Assalin suna
Martabar suna…… Fatima
Ko iyayena
Kai suke qauna
Suga aure na dakai angama
Ya Allah ya kaimu ga wannan rana
Ta aure na da Fatima shi na kosa
Fati……. Autar Mata
Kyawun halinka su nake kuri
Kai kadai Ke Sanya zuciya sanyi
In Sanya ka murna bana Jin nauyi
Kafin in yi Maka ka riga ka yi
Ni Fati…. Kai na riqe ba sauyi
Ta ko ina, masoyi baida makusa
Fati….. Fatima autar Mata
A raina babu yakai Har kullum
Na shiga taro na Mata na duba na gani
Ke ce kika haska kowa fuskar ki ake gani
Mata dar dar suke, kin yi musu kwarjini
Don Kyawun kwlliyar ki ta kauda maqi gani
A halayya, Fatima bata da raini
A qaunar ta na yi nutso na nauso
Fati…. Ni Fatima autar Mata
A raina babu yakai Har kullum
Fati…. Fati…… Fati…. Fati……..