Ba kowa zai gane ba
Yanda ake Jin zugi
Indai Har so ya darsu
Ko Kuma yayi Maka Barna
Ni Kam so yayi mani Barna
Ya canja min suffa na
Ya mai San tamkar bare a cikin dangi na
Ya sauya lissafi na
Ya tauye min hakki na
Ya sa na baje sirri na
Sambatun soyayya shin menene Ke jawowa
Yaudara ce ko Kuma kula ku ban amsata
Amma wani sa’in zuciya ta ce Ke harbawa
Inna tuna cewa, a soyayya na yo bauta
Wasu Har sun canja mini kallona
Sun Kasa su Gano me Ke damuna
Ni Dai na San menene ciwo na
Magani nasa Allah daya ne gata na
Haaaaaaaaah……..
Heeeeeeyy…..
In na mutu Kaine sanadi
Sannan Kuma baka da madadi
Samun mace mai qaunar ka kamar ni ba lallai ba
Hanyar da ka nunan za nabi
A silar so nayi Maka ladabi
Amma haka Bai Sanya ka tuna ni ka fasa butulci ba
Menene soyayya in ba qarya ce ba
Menene soyayya in ba cuta ce ba
Menene soyayya in ba hadari ce ba
Na daina, na huta Har qarshen rayi na…..(sobbs)
Aaaaaaah……
Yaya za kayi da hakkin soyayya ta
Ka saba mini da so Kuma kayi min qeta
Ka barni alaqa ta fa ka yanke ta
Ka mamaye sashin zuciya ka canja ta
Ko wani laifi taima ni ban roqi ka yafe min ba
Domin na horu da soyayya ka sa ban saba ba
Yau kuka, gobe kuka, ni Dai ba zan jure ba
Tunda Allah na Nan, addu’a ce zata yi gadi na…