Dole ne iya turancinka Saboda shi zai sa iyayen ka su san cewa ba matsiyaci suka haifa ba- inji Maryam Labarina
Daga dandali.com.ng
Ya zama dole ka iya turanci kasancewar shi yare mafi rinjaye, sannan iya shi zai tabbatar ma iyayen ka ba matsiyaci suka haifa ba-inji Maryam Labarina
An samu wannan bayanin ne a Shafin jarumar na Tiktok inda take maida ma masu tsangwamar ta kan yawan turancin ta Martani.
Read Also: Jaruma Maryam Labarina Taba da Hakuri Akan Maganar da Tayi.
Amma kuma bayan bayyanar bidiyon da tayi wannan bayani a kafafen sada zumunta, jarumar ta sha Zagi tare da Allah wadai kan wannan maganar ta ta, inda daga baya kuma aka ga tana bayar da haƙuri.
Dandalin.com.ng ya dauko muku bayani da ta yi a wani faifan bidiyo da ta saki wanda tace ” Jama’a suyi haƙuri fushi yasa tayi waɗancan kalamai kuma martani ne take yiwa wani mabiyin ta da yayi mata comment din da bata ji daɗinsa ba” wato dai ba da daukakin Jama’a take ba kamar yanda sukayi zato.