fbpx
Wednesday, January 8, 2025
30.1 C
Abuja

Innocent Girl Na Nameerah and Nainarh

Innocent Girl Na Nameerah and Nainarh

بسم الله الرحمن الرحيم

Ep. One.

Shigowa suka yi ganin yadda aka taru yasa ta ce.

“Dan Allah menene yake faruwa ne?.”

Kallonta guard ɗin ya yi yayi gaba abin sa, suna shiga compound ɗin gidan ƙara waro idanu tayi ganin jama’ar har sunfi na waje yawa har suka ƙaraso gabansa wani mutumine wanda aƙalla zaikai 65yrs ɗin ta kalleshi bakinta narawa ta ce.

“Your Excellency ko bakai bane ba president of Nijeriya ba.”

Kamo hannunta ya yi ya ce, “Ni ne Aneeserh.”

Da mamaki ta ce “A’ina kasan sunana please and Menene waɗannan mutanen suke yi a gidan mu?.”

Kallon ta ya yi cike da tausayawa ya ce. “Aneeserh kinsan duk abin da ya faru da mutum Allah ya riga da ya rubutashi a cikin littafinsa, kuma ba’a gujewa ƙaddara saboda haka inason kizama mai ɗaukan ƙaddarar data zomiki mai kyau ko akasin haka.”

Shiru tayi dan ita batasan ma’anar waɗannan maganganun dayake ba kamar antsikareta ta ce.

“Yawwa bari naje nagasu Abba suncemin yau zasu dawo.”

Gaba tayi dan shiga gidan tana zuwa entrance ɗin parlour’n su taga anjere mutane har uku akwance kowanne ansaka masa likkafani anrufe kamar gawa. Jikinta ne yahau rawa saboda Allah ya zuba mata tsoro tayi cikin gidan da gudu tana cewa.

“Abba!! Ummi!! Yaya!!.”

Kowa na gidan kuka yake domin duk rashin imaninka sai kaji tausayinta.

Haka ta gama bincike gidan amma bataga familynta ba hakan yasa ta fito lokacin His Excellency yazo ƙofar entrance ɗin tana fitowa ya riƙeta cikin rawar baki ta ce.

“Ka sakeni waje zanje naduba naga su Yaya Farooq basu dawoba kuma sunce idan nadawo daga makaranta zanga sun dawo.”

Hawayen fuskarsa ya goge sannan ya ce “Kinga Abbanki da umminki can akwance an rufesu.”

Buɗe dara daran idanunta ta yi, sai kuma ta tafi kan gawwakin ta tsuguna a hankali kuma ta buɗe likkafanin ɗaya daga cikin su, wata ƙara ta saki cikin tashin hankali take faɗin.

“Abba! Abba!! ka tashi, menene ya sameka Abba ka daina wannan wasan kaji bana so.”

Kowa na wurin kuka yake, ta ƙara buɗe ɗayar gawar inda tayi arba da Umminta sosai jikin ta yayi weak dan ganin abun take kamar mafarki cikin mutuwar zuciya dakuma rauni ta sake buɗe ɗayar, jikinta banda rawa babu abin da yake yi take faɗin.

“Yaya Farooq! Ummi!! Abba ku tashi please ku daina irin wannan wasan please banaso zan mutu, kutashi kunji…”

His Excellency ne ya ƙari so wajen ta, ya ɗago ta yana faɗin.

“Ki nutsu Aneeserh kinji.”

Riƙe shi tayi gam bakinta na rawa ta ce.

“Your Excellency please kacewa Abba na ya tashi kaji kacewa Yaya Farooq su daina wannan wasan Ummi ta tashi wayyo Allah.”

Ganin yadda ta rikice yasa ya rungumeta jikin sa yana shafa kanta yake faɗin.

“Aneeserh kiyi haƙuri kinji amma Abbanki, Umminki, your brother Farooq sun rigamu gidan gaskiya kiyi haƙuri kiyi musu Addu’a kawai kinji…”

Jin kusan two minutes amma babu respons yasa ya ɗagota kafin yayi magana ya ganta aƙasa jikake timm, cikin tashin hankali ya tsuguna kanta ya ɗa go ta, da aka kira guards dan kaita Asibitin.


Har ranar bakwai batasan waye akan taba, suna uku kawai take kira wato “Abbanta, Umminta, sai kuma Yaya Farooq ɗinta.”

Yau ma kamar kullum Your Excellency ya shigo bakinsa ɗauke da sallama, zaune ya sameta ta rufe idanunta amma ba barci take yi ba, zama ya yi gefenta ya taɓa ta yana kiran Sunan ta.

“Aneeserh!!”

A firgice ta buɗe idanunta ta ce da shi.

“Ummina.”

Kallon ta ya yi sai kuma ya girgiza kai ya ce.

“Ba ita bace.”

Shiru tayi masa kusan five minutes sannan ya kuma cewa.

“Ya kamata ki daina wannan tunane tunanen Aneeserh kisani duk wanda ya mutu baya dawowa kiyi haƙuri, ki koma cikin mutane ki dawo rayuwarki kamar da, ki dinga yi musu Addu’a a duk lokacin da kikayi sallah kinji?.”

Kallon sa take amma kana ganinta kasan ba fahimtar abin da yake faɗa take yi ba, girgiza kai ya yi yana tuna sanda sukai sallama da iyayenta bayan sun taho ne aka kira aka ce sunyi hatsari kuma babu wanda ya yi rai a cikin su…

FOUR MONTHS AGO

Fitowarta kenan daga ɗakinta ya kalleta ya ce.

“Ke Aneeserh kiyi sauri idan ba haka ba wallahi zanyi tafiya ta na barki.”

Turo baki tayi tana ƙunƙuni ya kalleta ya ce.

“Kee!! Ni kike yiwa tsaki ?.”

Shiru tayi masa ya ƙara cewa, “Ba magana nake miki ba?.”

Daidai nan wani Babban mutum ya fito wanda aƙalla zai kai irin 60yrs ɗin nan sai kuma wata mata a bayansa wacce kamarsu ɗaya da Aneeserh fara ce tass kana ganinta kaga asalin bafulatana.

Ƙara sawa suka yi, ai kuwa ta fashe da kuka ta tafi wajensa ta ce.

“Abba kaga Yaya Farooq ko?.”

Hot this week

Kazar Kwanci By Rufaida Omar

Kazar Kwanci By Rufaida Omar *1)*  " Mairamu! Mairamu!!" Matar dake zaune...

KAZAMAR AMARYA Na Rahama Kabir Mrs Msg

KAZAMAR AMARYA Na Rahama Kabir Mrs Msg Rahma Kabir:...

RUGUNTUSUMI Book 2 Compelet

RUGUNTSUMI Book 2 part 1 Rubuta labari Abdul’aziz Sani Madakin Gini Ɗaukar Nauyi Mansur...

GUDUN KADDARA NA HUGUMA BOOK 2

GUDUN KADDARA NA HUGUMA BOOK 2            ".............ya fada soyayya?,yana...

Gudun Kaddara na Huguma Book 1

Gudun Kaddara na Huguma Book 1 🏃🏽‍♀️ GUDUN ƘADDARA🏃🏽‍♀️ H U...

Topics

Honeywell Reloaded: Flour Mills of Nigeria Revives Its Iconic Brand

Flour Mills of Nigeria Plc (FMN), the leading food...

Fintech in Nigeria: Breaking Barriers and Driving Inclusion

Nigeria’s fintech industry continues to break barriers, driving financial...

Nigeria to Host Africa’s Largest Tech Expo

In a major boost to its tech credentials, Nigeria...

Edtech Revolution: Nigerian Startups Transforming Education

Nigeria’s edtech sector is witnessing unprecedented growth, with startups...

Telegram Sees A Rise In User Data Sharing With Law Enforcement

Recently published information from the messaging platform Telegram indicates...

BMW’s Latest User Interface Displays Widgets on the Windshield at CES 2025.

BMW is completely overhauling its in-car user interface, beginning...

Lagos Tech Summit Focuses on AI and Blockchain

The annual Lagos Tech Summit returned in 2025 with...
spot_img

Related Articles

Popular Categories

spot_imgspot_img