Sunday, September 14, 2025
23.1 C
Abuja

Isra’ila takai wani babban hari a makarantar MDD a Gaza ya kashe a kalla mutum 14

Isra’ila takai wani babban hari a makarantar MDD a Gaza ya kashe a kalla mutum 14

An dade ana gwabza fada a Gazakusan kwanaki 341. Abin baƙin ciki, mutane da yawa, musamman matada yara, sun ji rauni ko kuma sun rasa rayukansu. Kusan mutane 41,084 sun mutu, kuma kusan 95,029 sun ji rauni. Wasu da yawa, fiyeda 10,000, ana kyautata zaton sun makale a karkashin gine-ginen da suka fado.

1522 GMT — Wani hari ta sama da Isra’ila ta kai ya kashe akalla mutane 14, ciki har da yara biyu, a makarantar Majalisar Dinkin Duniya da ta zama matsugunin iyalan Falasdinawa da ke tsakiyar Gaza, in ji jami’an asibiti.

Jami’ai daga asibitin al-Awda da ke Nuseirat sun ce sun karbi gawarwakin mutane 10 da harin ya kashe, sannan an kai wasu mutum hudu da suka mutu asibitin shahidan al-Aqsa da ke Deir al Balah.

Jami’an asibitin sun ce akalla mace daya da yara biyu na daga cikin wadanda suka mutu, sannan akalla mutane 18 sun samu raunuka.

More updates👇

1348 GMT — Adadin wadanda suka mutu a Gaza sakamakon harin da Isra’ila ta kai ya karu zuwa 41,084

Harin da sojojin Isra’ila suka kai a Gaza ya yi sanadin mutuwar Falasdinawa akalla 41,084 tare da raunata 95,029 tun daga ranar 7 ga watan Oktoba, in ji ma’aikatar lafiya ta Falasdinu.

Akalla mutane 64 ne suka mutu a cikin sa’o’i 24 da suka gabata.

1256 GMT — Shugaban Iran ya caccaki Ƙasashen Yammacin duniya kan yakin Gaza da kuma goyon bayan Isra’ila

Shugaban kasar Iran Masoud Pezeshkian ya caccaki Kasashen Yammacin Duniya yana mai cewa Isra’ila na yin kisan kiyashi a yakin Gaza da kuma amfani da makaman Turai da Amurka wajen yin hakan.

Pezeshkian, wanda ya yi magana a Bagadaza a farkon ziyararsa ta farko a ketare tun bayan hawansa mulki, yana fatan karfafa alakar Tehran da Bagadaza a yayin da ake fama da rikici a yankin.

Hot this week

“Shehu Sani Warns: Ukraine to Lose Land to Russia, $500bn Minerals to US Amid War Fallout”

The ongoing war between Ukraine and Russia continues to...

Pope Francis’ Health: Doctor Says Pontiff ‘Not Out of Danger’ Amid Recovery

Pope Francis’ personal physician, Dr. Sergio Alfieri, has given...

Trump Sparks Controversy Over 14th Amendment, Claims Birthright Citizenship Was Never Meant for Immigrants

Trump Challenges Birthright Citizenship in New Executive Order President Donald...

Trump announces he will implement tariffs on products from the EU

U.S. President Donald Trump has once again emphasized his...

“America, China And The World As Trump Returns”

When Huge Fortune Is Involved There Is No Price...

Topics

Eniola Badmus Reaffirms Her Support for President Tinubu, Sparking Reactions

Eniola Badmus, a well-known actress and Special Assistant for...

Rapper Jeriq Explains Why He Has Never Been in a Relationship

Nigerian rapper Jeremiah Chukwuebuka Ani, widely known as Jeriq,...

Album Releases: Ruger and Joeboy Face Off in a Supremacy Battle

The Nigerian music scene is buzzing with excitement and...

“Famous singer NBA YoungBoy has been released from prison.”

Popular American singer Kentrell DeSean Gaulden, better known as...

“My kind of wealth cannot be achieved through investment,” Davido proudly declared.

Nigerian Afrobeats singer David Adeleke, widely known as Davido,...

“I backed Tinubu, but the hardship is becoming unbearable,” said Cynthia Morgan.

Nigerian singer Cynthia Morgan, now known as Madrina, has...
spot_img

Related Articles

Popular Categories

spot_imgspot_img