Jawabin da kayi bai shafi korafe-korafen da al’umma suka gabatar alokacin Zanga Zanga ba – Almustafa ya faɗi ga Tinubu
Daga dandali.com.ng
Manjo Hamza Almustafa, tsohon dogarin marigayi Janar Sani Abacha, Shugaban mulkin Soja, ya faɗi cewar jawabin da shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu yayi alokacin da aka gabatar da zanga zangar lumana kan tsadar rayuwa da ƙasa ke ciki, bai shafi ko wane bangare da masu zanga zangar suka bayyana amatsayin damuwar su ba.
Acewar sa wannan ya nuna masu faɗa aji na fadar ta shugaban ƙasa ba sa kai mishi rahoton asalin halin da al’ummar ƙasar shi take ciki.