Kalaman soyayyaaa….
Da qaunar ka nake kwanaa
Amfanin fitila haske
Da qaunar ki nake kwana, nake tashi
Ina so kiji tausaina,
Ko mun saba
Da qaunar ka nake kwana, nake tashi
Ina so kaji tausaina, ko mun saba
Idan zan fadi kalmomi, na soyayya
Siffofinki nake duba
Dake za nayi tarayya, abar sona Baza nayi Miki tamka ba
Babu diyar da Nike qauna, da ta kaiki
Baza nayi Miki qarya ba
Masoyin ka Kayi mai so domin Allah ko ba naira ba komai, ai kun saba
Yau jirgin tafiya ya zo mu mun Cilla, Amfanin fitila haske
Don Lada akayo sallah masoyina, da Kai za naci danwake
Ka koya mini na saba da soyayya, sirrin zuci riqe damqe
Ko a ina Kai zan Nuna ina son ka bazan canja tunani ba, ai mun saba
Haaaa…… Ina son ka
Banga tare ba, turmi na gudun tabarya
Ban qi gaske ba, ba Kai ba dora kaya
Ban qi zanyi ba, ha’inci a so da qarya
Banyi kwance ba, mene zai hana ni zarya
Bana tagumi, da rai zai ishe maraya
Kayya duniya, tunani Nake na baya
So da alqawar, mu damqe mu je mu qurya
Babu lafiya, in ban ganki a kusa na
Naji na gani, da Kai zanyi Rayuwata
Bani ba wani, sirrin zuci manufata
Zanyi gunguni, in Dai Har Ka mini rata
Fitilar gani, ido ka taren makanta
Sani dariya, daure ka yi mini gata
Kaini kaini ni, da Kai zan wuce makwanta
Qara kyan gani, a so Kar Kamin mugunta
Nawa Naka ne, bazan barka ko dare baa
Eeeeaaa… Na so kiji tausaina
A soyayya ko da nayi Miki laifi
Da qaunar ka nake kwana nake tashi, ka saurari kalamaina
Da qaunar ki nake kwana, nake tashi
Ina so kaji tausaina, ko mun saba.