KAZAMAR AMARYA Na Rahama Kabir Mrs Msg
[6/25, 11:52 PM] Rahma Kabir: *KAZAMAR AMARYA*
Na
© Rahma Kabir MrsMG.
Wattpad @rahmakabir
Page 1.
*Gargad’i*
_Ban yarda a juya mini labari ba ko ayi afmani da wani ɓangare na labarin ko kuma satar fasaha, ko a mayar mini da shi Audio a ɗaura min shi a wata kafa na media ba tare da izini na ba, dan Allah a kiyaye_
BISMILLAHIR RAHMANIR RAHIM
Alhaji Hamid.
Yana zaune a cikin mota ya fito daga wani super market da ya yi siyayya, yana ƙoƙarin tayar da motar sai ga kira ya shigo wayarsa, da ya ga sunan daya bayyana akan wayar ai da ya saki lallausar murmushi kafin ya ɗaga yana mai cewa.
Amincin Allah ya tabbata a gareki hasken idaniya, yanzu na fito daga super market domin siyayyarki.
Uhum na ɗauka ka matan da ni ne ai, ɗan naga yinin yau baka kira ni ba.
Ta faɗa a shagwaɓe. Hamid ya yi ɗar dariya.
Aiki ne yasha kaina amma kina raina Madeenar Hamid da fatan kina lafiya.
Ni bana jin daɗi dan zazzaɓi ke damuna na rashin ganinka.
To kisha kuruminki ina tafe bayan sallar magrib In Sha Allah, yanzu haka gida na nufa na kimtsa kafin na zo.
To beb sai na ganka dan ina kewarka sosai ka kula min da kanka.
An gama ranki ya daɗe Madeenar Hamid.
Ya faɗa cikin yalwar farin ciki itama ta saki murmushi mai sauti daga haka suka kashe kiran, Hamid ya sauke gauron numfashi tare da jinsa cikin wani yanayi na shauƙin soyayya, bai taɓa tunanin akwai ɗanɗanon so irin wanda yake ji akan Madeena ba, saboda koda yayi auren farko lokacin yana cikin duhun kai akan sanin daɗin soyayya, duk da ya yi boko dan digree gareshi a fannin kasuwanci amma akwai tarin kuriciya a kansa, musamman matar daya aura Sakina ta kasance kidahuma ba wani ilimi gareta ba, hasalima a gidansu daga primary mace bata ƙara wani karatu ake yi mata aure, na islamiya ma na allo ne shima bata sauke ba, kuma ya aureta cikin ƙuriciya dan tana ‘yar shekara sha huɗu shi kuma yana da shekara ashirin da biyar, shiyasa rayuwar aurensu banda tarin wauta da sakarci ba abinda suka sani, sauƙin ta ma cikin rufin asari suka yi shi domin mahaifinsa Nuhu tsohon soja ne da yayi retire, kuma yana da comfanin sabulu wanda Hamid ke gudanar da shi, Abba shi ne yayi masa aure bai san wani wahala da angwaye kesha ba, har kawo yanzu da aurensu shekara sha biyar suna cikin wadata dan babban gida filat gareshi kusa da na iyayensa ya yi gini, wanda ‘yar ƙaramar ƙofa ya fitar a tsakani dan sauƙaƙa hanyar shiga, da kuɗinsa yayi ginin saboda Hamid mutum ne mai himman da niman na kansa, duk da yana kula da companyn mahaifinsu to sai da ya haɗa da kasuwancin motoci da yake shigo dasu daga ƙasar waje, yaransu huɗu ta farko itace Mufeeda sai Nuhu mai sunan Abbansa sai Yaƙub da autarsu Rauda wacce a yanzu haka Sakina ta yayeta ‘yar shekara biyu da rabi.
Tun lokacin da Allah ya haɗa Hamid da Madeena a bikin wani abokinsa wanda Madeena itama ƙawar amarya ce, a ganin farko da yayi mata Allah ya ɗaura masa mugun sonta da hangen ita ce daidai da sa’ar aurensa, musamman yadda yake jinsa da ɗanyan kuɗi to yana buƙatar matar nunawa sa’a da kece raini dan kuwa Sakina ba tada zubin matan da zai iya fita taro da ita, ga rashin wayewa da rashin ilimi duk da tana da kyanta dan black beauty ce, amma sam Hamid baya ganin kyanta, ko dan sun jima a tare ne da kuma son kasancewa da farar mace yasa yake jin haka ƙila, domin Madina fara ce gata da tsayi dan ba za a sanya ta a jerin gajeru ba kuma tsayin na ta bai yi yawa ba ga shape Masha Allah domin akwai hips da dukiyar fulani, ga kuma manyan idanu da kuma dimple, a takaice itace irin matan nan da ake kira full option, domin ta haɗa komai rashin sumar kai ne kaɗai yayi mata cikas amma bata tsaya hakan ba sai da ta ƙara da na atach, sannan tana da ilimin zamini sosai dan tayi digree a fannin masscom sannan ta kuma yi masters, islamiya ba laifi tana da sani sai dai tafi mayar da hankali wajen boko, wajen shiga kuwa ba a magana dan ta iya ɗaukar wanka da iya kwalliya, sannan ta iya bulbula turare a jikinta dan duk inda ta gibta sai ya ɗauki ƙamshinta, wannan dalilin yasa Hamid ya riƙe mata wuta akan lallai sai ya mallaketa, dan Madina ba irin matar da za a kalla a wuce bane tana buƙatar a killaceta a guri ɗaya, kuma yayi sa’a a gun Madina dan ya samu karɓuwa domin shima ba baya ba wajen iya shiga da kashewa kansa kuɗi, dan fa yana cin guminsa, duk da baƙine shi amma Kana ganinsa kasan hutu ya zauna, yana da kyansa daidai misali kuma yana da tsayi bai da tumbi dan bai yarda cin daɗi ya sauya masa halittarsa ba yana kulawa da hakan sosai, gashi ɗan gaye saboda shigar manyan kaya ko ƙananun kaya babu wanda baya karɓansa, yana da matuƙar tsafta da kuma son mai tsafta, shiyasa yadda yake ganin Madina tsaftsaf kullum shi yake ƙara masa sonta da hangen in ya aureta zata share masa hawayensa, domin Sakina ba tada kula da tsaftar gidansa duk da tana iya nata ƙoƙarin kuma tayi tayi ya ɗaukar mata ‘yar aiki yace shi baya so, ƙazantar ta da yake gani shine ma ya ƙara masa ƙaimin ƙara aure, kuma ga dukkan alamun da yake gani yayi gamdakatar dan Madina yake hange itace mai share masa hawaye da maye gurbin duk abubuwan da Sakina bata yi masa, yanzu ne yake jinsa zai yi rayuwar aure mai daɗi a da can wasan yara ne yayi, duk ya ƙosa wata guda daya rage na aurensu yayi dan a hannu yake kamar bai da mata, domin Madina ce sanyin idaniyarsa.
Haka ya cigaba da tuƙi yana tunaninta har ya isa gida, ya buga hon mai gadi ya buɗe masa gate ya shiga kana ya adana motar, ya fito riƙe da ƙaramin farar leda daya siyawa yaransa kayan ciye ciye dan koda ya siyawa Madina nata bai manta da su ba yana matuƙar son yaransa, ya tsaya a jikin mota ya kwalawa Ibro mai bawa fulawa ruwa da gyaran farfajiya kira, ya tawo da saurinsa yana risinawa tare da gaisheshi ya amsa fuska sake.
Yauwa Ibro ga motata ina so a wanketa amma banda ciki, ba zan jima ba zan fito dan akwai in da zani.
To yallaɓai a fito lafiya.
Ibro yace cikin sauri ya nufi inda kayan aikinsa ya ke domin ya gabatar da aikin Alhaji. Hamid yana tura ƙofar falo da sallama ya hango tsakiyar falon da datti nan take annurin fuskarsa ya ƙaurace ya maye da ɓacin rai, haka ya ƙarasa ciki ya tsaya yana ƙarewa falon kallo, ba kowa a ciki sai hayaniyar yaran da ya ke ji a kitchen, ya kalli carpet ɗin dake tsakiyar falon da yake kalar fari da brown amma har ya fara sauyawa zuwa kalar datti, ga ledan biscut da sweet a kai ga kuma icen alayyahu da aka yi amfani da shi aka barshi, pillon kujerun duk a ƙasa ga plate ɗin abinci da aka ci aka barshi duk an zubar, cikin ƙunan zuciya ya shiga kwalawa Sakina kira kamar tarar aradu.
Sakina! Sakina!! Sakinaaa.
Read Also Here Gudun Kaddara Here
Cikin sauri ta fito daga kitchen tana amsa kiran tare da yi masa sannu da zuwa, Hamid bai amsa ba ya bita da wani irin kallon tsana.
Wannan wani iri hauka ne zan zo naga falo kamar filin dambe, yanzu da ace da baƙo na shigo haka zaki saka na ji kunya, a matsayina na Alhaji Hamid ya dace aga falon gidana haka kaca kaca, wlh tallahi na gaji da wannan ƙazantar taki, ayi mace sai ka ce tunkiya uwar tamɓele, taya ma bazan ƙara aure ba kina irin wannan jakancin, madadin na shigo naji falo ya ɗauki ƙamshin turaren wuta, ina can waje ina hura hanci da fankama mutane na ga Alai Hamid ina yaƙe baki dajin ni wani shege ne, amma matata ba abun ke ba ilimin ba kuma tsafta, in je taro dake ana zuba ruwan turanci kina zare ido kamar kyanwar data ci barkono kina baje hanci kamar kinji warin jaɓa, to Wlh da sake Sakina aure ba fashi nan da wata guda Madina zata zo ta wanke min baƙin cikin da kike ƙunsa mini.
Abban Mufeeda ina iya kokarina kuma ka ce baka so ka dawo ka tadda ban gama girkin dare ba, kuma ina ta sauri ne na gama da kitchen kafin na fito falo na gyara kan ka shigo fa.
Ta ƙare maganar hawaye yana cika mata ido dan sosai maganganunsa suka ƙona mata zuciya, duk da yaci ace ta saba da irin cin zarafin da yake yi mata wani sa’ilin ma a gaban yaransu, Hamid ya ja guntun tsaki.
Amma ai na fada miki ki riƙa fara yin komai da wuri kafin lokaci ya ƙure miki, idan kin ɗaura girkin ai sai ki zo ki gyara nan ɗin…
Hamid ya kake so nayi ne, kuma kace Waina kake so nayi maka yau, ga ƙullun bai tashi mini da wuri ba dan ban daɗe da gama suyar ba, yanzu ne na samu damar ɗaura miya ina wanke ganye ne ka shigo, kuma saurin da nake yi na gama na zo na gyara nan. Kasan halin yaran nan in sun dawo makaranta ɓata guri suke yi ga Mufeeda Hajiya ta aiko kiranta tana can gidan bata dawo ba dama…
Dama me? ai kin iya jero magana kamar wacce ta haɗiyi Radio, wlh rashin ilimi ba ƙaramin cutar dake yake yi ba Sakina, dole zan zo na fara shirya yadda zaki koma makaranta koda yaƙi da jahilci ne ki samu wataƙila zaki san yadda kan duniya take ciki, shiyasa ko taron makarantar yaran nan ban yarda kije ba dan karki bani kunya. Ki kuma gyara gidan nan kafin na fito daga ɗakina na ji yana ƙamshi, shashasha sai anyi magana ki riƙa fuskar tausayi kina sunsun da kai uwa mumina.
Ya ƙare maganar yana danƙara mata harara kana yayi gaba ya wuce ɗakinsa, Sakina da ido ta bishi wanda hawaye cike fal da idonta kamar zasu zubo mata, sauke numfashi tayi tana girgiza kai ta juya dan ta koma kitchen sai taga yaran sun tsaya suna kallonta, wato komai ya faru a kan idonsu, baba ƙarami ɗan shekara sha ɗaya shi ne yace.
Mama kiyi haƙuri ba zamu ƙara ɓata falon ba tunda faɗa Abba yake yi miki.
Baba ƙarami bana son surutu maza kaje ka kwashe jakar makarantarku ka kai ɗaki.
To yace kana ya nufi inda jakarsu na makaranta yake ya ɗauka ya nufi ɗaki, ita kuma tsintsiya ta ɗauka ta fara gyaran falon, ba jimawa ta gyara falon ta saka turaren wuta a burner sai ta wuce kitchen dan duba sanwar miyanta, sai dai zuciyarta kunshe yake da tsananin damuwar abin da Hamid yake yi mata tun da ƙuruciyarta har kawo yanzu, babu abinda yafi kona mata rai sama da yadda yake zaginta da jahila, ga komai tayi bata taɓa burgeshi, tunda ya haɗu da Madina ya rushe sauran ɓarɓashin son da yake yi mata, ga tarin wulaƙanci daya ƙara, ita tun tana jin zafin kishin auren da zai yi har ta haƙura tana burin wannan amarya tazo gidan ko zata huta da cin kashin da Hamid ke yi mata.
Rahma ce matar MG
[6/25, 11:52 PM] Rahma Kabir: *KAZAMAR AMARYA*
Na
©®Rahma Kabir MrsMG.
Wattpad @rahmakabir
Page 2.
Sakina tana idar da sallar magrib ta dawo falo ta zauna bayan ta yi wankanta ta saka doguwar rigar shadda da hula baƙa, powder kawai ta shafa da man baki dan ko tayi kwalliyar uban gayya ba yabawa yake yi ba, wani sa’ilin ma in ta shafa janbaki cewa yake bai yi mata kyau sai tayi kamar akuya taci dusa, in tayi ja gira kam wai kamar ta dambara kwalta, dole sai dai ta haƙura da kwalliyar ta bar wa ‘yan zamani suyi ita yayin ta ya wuce ko tayi bata fasali, shiyasa ta tattara duk wata kwalliya ta aje shi gefe ta cigaba da sabgarta, tana zama da mintuna sai ga Mufeeda ta shigo riƙe da kwando da kuloli aciki, da mamaki ta bita da kallo har ta ƙaraso tana cewa.
Mama wai Hajiya tace ki saka musu waina bata samu ɗaura girkin dare ba.
Haba Mufeeda kina sane da wainar nan ba da yawa na yita ba shiyasa ban yi da niyyar aika mata da shi ba, waye ma yace ki sanar da ita waina nayi.
Cewar Sakina da ta katse mata hanzari cike da faɗa, Mufeeda ta mele fuska cike da damuwa.
Mama tambayata tayi me kika girka shine na faɗa mata, kuma wlh nace mata bada yawa kika yi ba.
Ai kema kin san ta da kwazzaba sai taci, dan haka wanda nayi niyyar ku tafi makaranta dashi da safe shi zan bata kwaci indimie ‘yar kullun da kuka saba tafiya da shi, koda yaushe ina nuna miki ki riƙa tunani akan irin haka amma abanza, dalla muje na saka mata.
Cewar Sakina ceke da takaici, haka ta wuce Mufeeda na binta a baya nan ta kashe gas ganin miyarta ta yi ta zubawa Hajiyar waina takwas da miya a ɗayan kular tare da ƙashi biyu da tsoka ɗaya ta bawa Mufeeda tare ta a jaddada mata akan ta dawo yanzu tazo tayi sallah ta san bata yi ba saboda baƙin aikin da Hajiyar ta sakata. Sai ta dawo falo ta zauna ta cigaba da kallon shirin sirrin ma’aurata a tashar sahad tv, dan yana matuƙar burgeta a nan take ƙara sanin halin maza bisaga labaren da mutanen shirin suke bayarwa, shiyasa ta ƙara kwantar da hankalinta ta rage damuwar ƙarin auren da Hamid zai yi tunda ba fashi sai yayi, ido zata zuba masa ta ga iya gudun wuransa tasan dai wulaƙanci sai ta sha shi kwando kwando, haƙuri da juriya shine zai zaunar da ita musamman saboda yaranta. Tana nan a zaune sai ga Mufeeda ta dawo da kulolin, sheƙeƙe ta ke kwallonta wannan karan tasan dama sai Hajiya ta raina dan ita sam ba tada godiyar Allah, tace cikin haɗe rai.
Ehen ta ce ki dawo in ƙara mata ko?
Eh wai bazai ishe ta ita da Alhaji ba sannan Jidda ma ta dawo ko ita kaɗai zata cinye shi tace.
Wannan tsohuwar da shegen ƙulafuci Wlh, ni ban isa nayi girki iya ni da iyalina ba sai ta saka rai, to ai shikenan tunda kin ja mana cin tuwo dan wainar ba zata ishe mu ba. Muje na ƙara musu guda biyu suci da haƙuri…
Iyeee Sakina ni kike yiwa ɗibar albarka haka, to duk abinda kika faɗa a kunnena, ashe ba kida mutunci, abincin da ɗana ya kawo shine kike faɗar son ranki akan nace ki zuba mini, to kome zaki faɗa ki faɗa amma wlh wainar nan ita zamu ci mu ƙoshi mu kwanta, ke Mufeeda muje kitchen ɗin na zuba da kaina sai kiyi duk abinda zaki yi.
Cewar Hajiya data shigo falon buguzum buguzum kamar zata kifa ta wuce kitchen tana cigaba da sababi, Sakina dai sosa kai tayi tana mele baki dan tasan tayi ɓarin zance kuma taji kunyar maganar data yi, dan tasan uwa uwa ce kawai dai Hajiyar ce take cikata har take wasu maganganu cikin ɓacin rai, Hajiya kam kusan rabin wainar ta kwashe ta zube kashin miyar sai guda ɗaya da tsoka biyu ta bari ta fito tana sababi riƙe da kwandon.
Shiyasa na goyi bayan Hamidu ya ƙara aure tunda ke kin zama tijararriya mara ɗa’a, ai da uwarki ce ba zaki hanata abincin ba, Allah yasa ya samu ɗiyar arziki ba mai rowa ba irinki.
Ta ƙare maganar tana dalla mata harara da kwafa ta wuce, Mufeeda ta ƙaraso falon tana cewa.
Mama kiyi haƙuri laifina ne dana faɗa mata da duk haka bai faru ba. Kuma kusan rabi ta kwashe fa sai ki barwa Abba wannan mu ko cous cous ne zan dafa mana muci da miyar bari nayi sallah.
Sakina waje ta samu ta zauna takaici ya cikata dan ta kasa magana ma, Mufeeda ta wuce ɗaki duk jiki a sanyaye tana jin haushin kanta akan meyasa ta sanar da Hajiya waina suka yi, alƙawari ta dinga yiwa kanta akan ba zata sake wannan wautar ba tunda tasan halinta ba tum yau take yiwa Mamansu haka ba. Sakina kam miƙewa tayi ta shiga kitchen ɗin ta duba taga wainar ba zai ishe su ba, ga babansu kuma tasan da safe shi zai ci, dan haka ta ɗaura tuwon semo ba ɓata lokaci ta tuka musu mara talge, ƙarshe yaran waina ɗai-ɗai suka ci suka ƙara da tuwo ita kuwa tuwon kawai taci ta barwa Hamid wainar ta haƙura, hatta naman ma basu ci ba ta bar masa tunda Hajiya ta kwashe kuma ba zai yuwu mai maza a bashi kai da wuya ba.
****
Madina.
Zaune take tare da Kausar data zo mata yini gidansu wanda tun bikinta da suka yi sai yau ne mijin ya kawota da zummar zuwa dare zai zo ya ɗauketa, Kausar ne ta dubeta tana cewa.
Kin ce Hamid zai zo banga kuma kin yi wanka ba.
Wanka kuma? Haba dakatsami zanyi kawai ɗan wlh sanyi nake ji.
Madina kina nan da wannam ɗabi’ar tun na makaranta, meyasa ba zaki sauya ba, karfa kije gidansa kina yi masa haka, kuma kinga Hamid ɗan gaye ne ga kwalisa.
Kausar kema kin san bazan bari ya tsaƙi wari a jikina ba kuma ko yanzu bana tsamin zufa, kawai dai hammata ta zan wanke nayi brush sannan zan bulbula turare kinga na kwauda komai bamai cewa banyi wanka ba.
Sai ni dana san dakatsami kika yi ba, lokaci yayi da zaki sauya tunda ba makaranta muke ba da ake tsumulmular ruwa, nan gida kike in kin so kiyi wanka sau biyar akwai wadataccen ruwa.
Hmmm wai ce miki aka yi bana wanka ne? Malama ki sarara mini.
Ta faɗa tana miƙewa tare da yatsine fuska ta shiga toilet ɗinta, da murmushi Kausar ta bita dan tasan halin Madina ciki da bai sai dai ta bawa wani labari, Madina tana son gayu amma kuma tana da mugun kuiya bata jure walahar gyaran jikinta dan wanka ma in da zata samu ayi mata zata so, hatta girki bata iya ba ko a makaranta sai dai su ‘yan ɗakinsu su girka taci, tafi amanna da shan cornflaks da sauran kayan da basu da wahalar haɗawa dangin su Indomie da curstard, wanka kam sai ta kwana ta yini bata yi ba sai dai a wanke hammata a fashe jiki da turare a fita babu maicewa bata yi ba tsabar yadda take wahalar da turaruka, da yake tanada gata ga mahaifiyarta data ɗaure mata ga kuma samari da suke kashe mata kuɗi, sam bata san wahalar rayuwa ba.
Madina su biyu rak mahaifiyarsu ta haifa duk mata, Aisha itace babba tana auren wani ɗan siyasa wanda suke zaune a Abuja, duk da tanada kishiya amma bata da damuwa da ita domin gidansu daban daban sannan mijin yana mugun sonta, tana da ma’aikata kusan uku bata san wahala ba sai hutu, kamar dai yadda mahaifiyarsu ta gina musu rayuwa a gidansu duk da ana tunatar da ita illar haka amma kullun hangenta yaranta ba zata auren dasu gidan wahala ba sai inda zasu huta, matan babansu uku momynsu ce amarya suna da manyan yayyi maza da mata dan kusan sune ƙanana a gidan, lokacin da suka taso ƙiri ƙiri Momynsu take hana a saka su aiki wai ba za a bautar mata da yara ba dan anga sune ƙanana, ta gwammace ko girki ne tayi da kanta ko wanke wanke bata bari a saka su, acewarta mugunta ne ai sauran yaran bata ga ana bautar dasu ba har suka yi aure sai nata da aka raina, mahaifinsu yayi iya kokarinsa akan ya fahimtar da ita amma tace zugoshi aka yi dan haka ya zuba mata ido, shiyasa Aisha tana samun miji tana tsaka da karatun secondary SS2 ta aurar da ita ganin mai mugun kuɗi ne, a ɗakinta ta ƙarasa harta ɗaura da jami’a yanzu yaranta uku. Madina kuma tana tasowa lokacin data gama jss ta sa aka kaita makarantar kwana, tana gamawa kuma aka samar mata ABU Zaria ta tafi, huku kawai ke kawota gida shima in tazo bata matsarwa sai dai ayi mata, jin daɗi da gata kam tana cikinsa dumu dumu, har zuwa sadda babansu ya rasu aka raba musu gado koya ya kama gabansa, Momynsu ta samu gida a cikin gadonsu dan haka nan suka koma ƙaramin filat mai kyau sai ta cigaba da harkan zannuwa da kayan yara ta zama babban dila a cikin gidanta, shiyasa Madina take duk abinda take so domin Momy tana bata duk wata kulawa fiye ma da mahaifinsu yana raye, kuma kullun hangen momy Madina matar manya ce dan tafi Aisha komai kyau fari da wayewa sosai, shiyasa da Hamid ya fito aurenta sai da ta yi bincike akansa ta tabbatar da yana kama manyan kuɗi Madina zata samu farin ciki a gidansa, shiyasa ta amince da auren, domin har mota Hamid yayi mata alƙawarin bata kuma zata riƙa zuwa aikinta data fara a gidan Sahad TV babban gidan tv dake tashe anan jihar Kaduna, wannan yasa hankalin momy ya kwanta da Hamid musamman yadda yake kashewa Madina kuɗi da siyayya kala kala baya gajiya.
Madina koda ta fito sauri sauri ta shirya cikin doguwar riga ready made ash da fari tayi rolling galen kayan akanta ta fesa turaruka kusan kala uku kana ta kalli Kausar.
Nayi ko banyi ba.
Kinyi ko ba wanka farar mace alkebban mata. Saboda kin ga kina da kyau shiyasa baki damu da yawan make-up ba.
Natural yafi ai, bari naje falo na jira kan kiyi sallah.
Ke ba zaki ba yi?
Yau nake gama period ɗina jinin ya ɗauke amma ina so na tabbatar shiyasa naki yin wanka.
In dai ke ce zaki iya bari ma sai gobe kuma wlh sallar yau tana kanki tunda jinin ya ɗauke.
To malama Kausar naji wannan fatawar.
Ta faɗa tana yatsine fuska ta wuce ta fita, da addu’ar shiriya Kausar ta bita sanin tasan halin Madina akwai sakaci sosai wajen kula da addini. Madina ta samu momy a falon tana duba wasu atamfofi da aka kawo mata su ɗazun daga kwatono, ta zauna tana cewa.
Mom Hamid zai zo yanzu.
Yauwa ina so ki yi masa maganar da nayi miki akan ba zaki zauna gida ɗaya da matarsa ba dan gaskiya kayan dana yi niyyar miki sunfi ƙarfin kiyi haɗaka da wata a falo guda.
Nayi maganar dashi jiya a waya yace yafi so na zauna tare da matarsa domin na koya mata yadda ake rayuwa, saboda ba tada wayewa ko kaɗan, shiyasa naga gwara na zauna anan in yaso naga bazan iya ba sai na saka ya sauya mini gida.
Amma kuma Madina ina guje miki halin namiji da daɗin baki, nafi so dai ki zauna a gidanki ke kaɗai ya samar miki ‘yar aiki da zata kula da gidan dan baqn yarda ki je kina wahala ba.
Mom kinga fa yace zai siya mini mota zai barni nayi aiki ina ganin ko na zauna a gidan matarsa ita zata yi wahalar gidan, ko banza ta zame mini ‘yar aikin tunda dole tayi in tana son zamanta a gidan, dan yadda Hamid ya nuna mini yayi mugun tsanarta zaman dole yake da ita.
In hakane to ya saketa mana ana dole ne a wannan zamanin.
Ba zan iya kula masa da yara ba shima abinda yace baya so ya ɗaura mini ɗawainiyarsu amma da tuni ya saketa, kinga ta zauna ta riƙe yaranta.
Amma ai yanada uwa sai ya kaisu can ta riƙe su in haka ne.
Kiran daya shigo wayar Madina ya katse maganar Momy tana dubawa taga Hamid ne sai ta miƙe da sauri.
Mom shine yazo bari naje.
Ki gaishe shi.
Cewar momy Madina ta wuce tana murmushi, ta fita ta same shi a jikin mota a ƙofar gidan ya rumgume hannayensa sai zuba mata murmushi yake yi har ta ƙaraso, ita ma murmushin take mayar masa ta isa gabansa ta tsaya.
Farin cikin Madina barka da zuwa ya hanya.
Lafiya lau Hasken Hamid.
Naga ka fito daga mota, yau hirar waje za muyi ko gida zamu shiga.
Na fito na fara tarban gimbiyata ce kafin mu shiga, kin ce mini Kausar tazo nayi zaton zata fito mu gaisa ai.
Na barta zata yi sallah maybe kan ka wuce ta leƙo.
Cewar Madina cikin murmushi, sai dai kuma nan take cikinta ya murɗa taji kamar zata yi kashi ga wani wawan tusa dawo turnuƙota sai ta soma matse cinyoyinta tana mayar da tusan dan ta san ba ƙaramar mai wari bace saboda ɗazun kwai taci dafaffe kusan guda biyar, kuma muddun taci sai ya dinga sakata tusa, duk yadda taso ta matse ta kasa nan take ta saketa a hankali buuss mara ƙara, Hamid ko hankalinsa yana kan waya da aka turo masa saƙo yanzu, amma lokacin da wannan wari ya ziyarci masarrafar jin ƙanshinsa sai da ya ɗauke numfashin wucin gadi kafin ya saki a hankali ya kuma tsakar warin daya ji tamkar zai suma, da sauri ya buɗe motarsa ya shiga yana jin kamar zai yi amai, Madina kuwa kunya ce ta rufeta amma sai ta basar ta fuskar tamkar bata ji warin ba.
[6/26, 10:21 PM] Rahma Kabir: *KAZAMAR AMARYA*
Na
©®Rahma Kabir MrsMG.
Wattpad @rahmakabir
Page 3.
Madina dakewa tayi tana ce masa.
Hamid lafiya ka shige mota da sauri haka ko an turo maka da saƙon tashin halkali ne?
Hamid yana jinta ya kasa magana, sai da ya ja numfashi ya sauke a hankali kana ya ƙara jan iskar dake motarsa mai ƙamshi sannan iya sauke glass ɗin mota yana cewa.
Madina wani irin wari naji mai hamami daya hautsina mini lissafi.
Ai tun jiya muke fama da warin nan mun rasa a ina aka yasar mana da mushen dambar data hana mu saƙat.
Hmmmm ai ni kam bazan iya zama ba dan wannan ɗoyin ya farraka duk wani farin cikin dana zo da shi, dan haka ga siyayyarki ki je gida mayi waya.
Ya ƙare maganar yana miƙa mata ledan siyayyarta, Madina ta amsa tana yi masa godiya tare da sallama kana ta juya da nufin tafiya, wanda nan take wani tusan ya kuma kubce mata mara ƙara ta sake shi, warin ya ƙara kaiwa Hamid ziyara zuwa mararrafar jin ƙamshinsa, wani tari ne ya surnuƙeshi wanda yasa shi ɗaga glass ɗin motar da sauri tare da tayar da ita yaja baya da gudu, tamkar zai yi amai yake ji, gabaɗaya tusan ta gigita lissafinsa ya juya da motar ta wuce da sauri, sai da ya isa kan hanka kafin ya yi parking ya sauke glass yana shaƙar iskar gari dan ji yayi tusan nata ya gauraye da ƙamshin motarsa, ya fesar da iska yana cewa.
Kayyasa kaga shegiya tana niman halakani da warin tusa kamar wacce ta haɗiyi mushe, har da zabga mini ƙarya wai munshen dabba ce, dana san wannan baƙar huƙubar zata yi mini da ban zo wannan hirar ba, gabaɗaya ta dama mini lisaafi, wannan dana cigaba da zaman hirar ƙarshe sai dai na nima numfashi na rasa a jikina ta sumar dani haka kurum.
Ya ƙare maganar yana tofar da yawu cike da takaici, haka Hamid ya isa gida da ƙunshin haushin Madina, dan sosai abinda tayi ya fusata shi.
Madina kuwa koda ta shiga gida bata samu momy a falon ba sai kawai ta shige ɗakinta ta samu Kausar ta idar da sallah, sai ta zauna gefen gadonta tana turo baki fuskarta a dagule, Kausar ta dubeta tana ɗan murmushi.
Mrs Hamid ba dai har ya tafi ba? Ko faɗa kuka yi naga fuskarki a dame.
Uhum yau kwai dana ci ya tona mini asiri, bai tashi wulaƙanta ni ba sai da naje gaban Hamid, cikina ya murɗa na sakar masa tusa mai wari wanda ya sa shi gigicewa ya tafi ba shiri.
Kausar kwashewa da muguwar dariya tayi, sai da tayi mai isarta kafin ta tsagaita tana cewa.
Kai amma yau kin tafka abin kunya, gaskiya tusa bata yi miki adalci ba kut.
Hmmm wayancewa nayi na nuna masa mushen dabba ce aka yar a makwarara, da yake tusan ba mai ƙara nayi ba.
To da dama dama, amma duk da haka kema kin yi wauta, taya zaki tsaya har ki saketa, da kinyi sauri kin ce masa kina zuwa ki ruga gida ki saki abinki sai kin huce ki koma. Amarya mai ruɓeɓɓen ciki naso naga idonki a lokacin, ina ruwan mujiya hahaha.
Ta ƙare tana dariyar mugunta, Madina ko haɗe rai tayi tana cin magani dan sosai dariyarta ke ƙular da ita.
Kausar yafa ishe ki haka ki sarara mini na sha iska, ina ce kowa ma yana tusan da kashi, dan haka banga abin dariya anan ba, ko shi Hamid ɗin zai ce baya yi ne.
Dariya dai Kausar tayi tana cewa.
Ni tafiya ma zanyi kafin nima ki kumbura mini ciki, bayan fitarki Babyna ya kira yace na shirya yana hanya, har ina cewa zasu haɗu da Hamid ashe ba rabon su haɗu.
Kyaji da shi dai.
Madina ta faɗa tana gyara kwanciya cike da takaicin Kausar ɗin.
***
Hamid.
Yana isa gida ya fito daga mota fuska ba annuri, dan shi abu kaɗan ke harzuƙashi yayi ta fuffuka kamar fulawar daya ji yeast, kuma abin takaici sai ya huce akan wanda bai ji ba bai gani ba musamman Sakina da ya raina, haka ya wuce falo fuska a ɗaure, yana tura ƙofa ya ga pow ɗin kashin Rauda a gefe tayi kashin an barshi a gurin, nan take zuciyarsa ta tashi ya wuce zuwa ɗakinsa a guje kamar zai kifa, toilet ya wuce direct ya shiga kelaye amai kamar zai amayar da hanjin cikinsa, bayan ya gama ya wanke baki ya fito ya kwanta a gado rigingine yana mayar da numfashi. Lokacin da ya shiga ɗakinsa baba ƙarami ya ruga ya sanarwa Sakina da Babansu ya dawo yaga kashin Rauda a pow, gaban Sakina sai da yayi mummunar faɗuwa saboda tasan sun jawo mata faɗan famau, kuma sallah ta shiga yi lokacin Rauda na pow tace Mufeeda ta wanke mata inta gama shine suka bari har babansu yazo ya gani. Da sauri ta cire hijab ta fito tana kwalawa Mufeeda kira wanda ta fito itama da sauri riƙe da hannun Rauda tana cewa.
Muje in wanke miki kashin, ke ba dama a barki a pow sai kin tashi kiyi ta yawo da tutu a jiki.
Ai kin kyauta Mufeeda tunda kin bari har babanku ya dawo yaga kashin.
Sakina ta faɗa cikin ɓacin rai sai ta juya ta nufi ɗakin Hamid ɗin tun kafin ya fito ya yi mata tijara a gaban yara, tana buɗe ƙofar ta shiga sai suka yi ido biyu da shi, a fusace ya miƙe tsaye yana dubanta.
Allah ya wadaran halinki Sakina, na shigo gida da niyyar samun sassaucin abinda ya sameni a waje da aka kusa sumar dani, amma sai na zo kuma na tarar da ke kuma kasheni kike son yi, so nawa ina faɗa miki Rauda ta daina kashi a falo ta riƙa yi a ɗakin yara, da ta gama a wanke mata.
Kayi haƙuri wlh Sallah na shiga yi ban san tayi kashin ba.
Ɓace mini da gani shashasha ballaza mara tunani kawai.
Yanzu akan wannan shine na cancanci zagi irin wannan Hamid, ɗazun kayi mini…
Bata rufe baki ba ya wanke ta da mari tare da nuna mata ƙofar fita.
Suf-suf ta fice riƙe da kuncinta tana jin zuciyarta kamar ta faso ƙirjinta ta faɗo dan tsananin takaici, bayanta ya biyo yana cewa.
Daga ke har yaran nan bana son sake ganin gilmawar wani a falon nan.
Bata tanka masa ba ta wuce ɗakinta ta rufe ƙofa, Mufeeda suna jin abinda babansu yace ta tasa ƙeyar ƙannenta zuwa ɗakin su Baba Ƙarami, Hamid ya isa wajen kayan kallo ya kashe su kana ya wuce kitchen ya ɗiba waina guda biyar ya zuba miya kama ya ɗauki gorar ruwa da drink da cup ya fito dinning ya zauna ya fara ci, tunda ya soma haɗiye wainar yake wani lumshe ido saboda daɗinsa yakai masa karo, yana matuƙar son waina musamman irin wanda Sakina take yi masa, wani lokacin iya girkinta yakansa ya raga mata akan wasu abubuwan, dan Sakina ba baya ba tasan hannunta sosai ba girkin zamani ba bana gargajiya ba duka gwana ce, wani sa’ilin ko fushi yayi da ita amma fa ba zai iya fushi da abincinta ba sai yaci, haka ya ci ya ƙoshi kafin ya bar mata kayan anan dining ya fice zuwa gidan iyayensa ta ƙaramar ƙofar daya ratsa ta gidansa.
*
Sakina.
Zama tayi a gefen gado tana matsar kwalla duk wani motsinsa tana ji har fitansa, a lokacin ne ta ɗauki wayarta dake wajen madubi ta kira yayarta Ummulkairi wacce ta zame mata tamkar uwa saboda mahaifiyarsu ta jima da rasuwa, Umma tana ɗaukar wayar Sakina tayi shuru tama kasa magana sai nishin kuka, Umma tace cikin tsananin kulawa.
Innalillahi wa inna ilaihir raji’un, Allahumma ajirnee fee musibati wa akliflee khairan minhaa, Allahu Allahu rabbi laaa ushrika bihi shai’a, Allahumma iyyaka na’abudu wa iyya ka nasta’in. Sakina karki yarda Shaiɗan yana shagaltar dake kusantar Allah a duk lokacin da kika samu kanki cikin ruɗani da damuwa, Allah shine kaɗai gatanki a wajensa ne zaki samu sassauci. Ba sai kin faɗa mini meke damunki ba domin nasan a wannan lokacin da Hamid yake shirin ƙara aure to dole zaki fuskanci barazana a aurenki, ba duka maza bane suke iya kamanta adalci, mutunci da kuma girmamawa ga matansu lokacin ƙara aure ba, domin idonsu yakan rufe da hangen wacce zasu aura itace zanyin idaniyarsu itace zasu samu farin ciki a gunta, dan haka Hamid ya kasance ɗaya daga cikin irin waɗannan mazan, shiyasa nake baki haƙuri ki cije ki jure har ayi auren nan a gama lafiya ba tare da kin ja wani rigima a tsakaninku ba.
Amma yaya Umma ya fara kaini bango bazan iya jurewa ba, ji nake kamar na gudu na bar masa gidansa, Hamid baya ƙaunata kwatata nayi mamakin ma da yake zaune dani har yanzu bai iya saki na ba, domin bana taɓa daidai a gunsa komai nayi kuskure ne.
Tunda kin fahimci haka sai ki ci maganin zama da shi da haƙuri, Sakina duk wanda kika ga yayi haƙuri bai ci nasara ba to kaɗan yayi, kiyi ta addu’a kina faɗawa Allah sai kiga auren nasa ya zame miki wani sauƙi acikin zamanku, In Sha Allah gobe ina nan zuwa mu yi magana.
To shikenan yaya Umma Allah ya saka da alkhairi ya kaimu goben lafiya.
Ameen Ƙanwata Allah ya shiga lamarinki.
Sakina ta amsa da amin tana ɗan sakin murmushi, haka suka rabu tana sauke ajiyar zuciya dan taji daɗin maganganun Yaya Umma, itace macen da take iya kai kukanta gunta dan ta zame mata uwa da uba, domin yaya Umma macece mai kirki da sanin yakamata, su biyu ne rak mata a ɗakinsu, Yaya Umma itace babbansu sai Hamza ke bi mata sannan Sakina sai sauran ƙannensu maza su uku. Mahaifinsu malami ne yana da almajirai da yake koyar dasu karatu wanda zuwa yanzu tsufa ya cimmasa, sai babban wansu Aliyu da Hamza sune suka cigaba da jan ragamar makarantar. Matan baba uku mamansu ce ta biyu, gidansu akwai tarbiyya sosai ba ruwansu da wayewar zamani komai nasu cikin tsari na addinin musulunci suke yinsa, dan baba Malam bai yarda da boko ba shiyasa yaran maza ma bai basu damar yi ba bale matan, tun rasuwar mamansu Yaya umma ta zame musu uwa dan Sakina gidanta ta koma da zama lokacin tana budurwa har ta aurar da ita a hannunta, duk da mijinta talaka ne dan kayan koli yake sayarwa ita kuma tana dan sana’ar cikin gida, amma suna rayuwar farin ciki dan mijinta yana da zuciya sosai basu taɓa kwana basu ci ba, yaranta bakwai dan har ta aurar da babbar ‘yarta, shiyasa duk wani abu daya shigewa Sakina duhu ita take tunkara kuma cikin hukuncin Allah duk shawarar data bata in tabi to sai ta samu mafita, ta riƙeta da muhimmanci sosai kuma da yake mijinta yana da rufin asiri tana taimaka mata sosai da abubuwa, dan Hamid yana kulawa da danginta tanan tana matuƙar yaba masa dan sai yayi musu alkhairi bata sani ba sai in ta haɗu da ‘yan uwanta ne suke faɗa mata, shine ma yakai babansu Makka, shiyasa wani lokacin inta tuna da alkhairinsa sai ta riƙa jurewa da haƙuri da halinsa, dan dama dole ne duk mugun halin mutum bazai rasa wani hali na kirki ba.
Haka ta fito falo ta shiga ɗakin yaran sai da ta tabbatar da su baba ƙarami sun kwana, kafin tasa ƙeyar Mufeeda itama ta kwanta a ɗakinta ta kashe mata wuta ta rufe mata ƙofa, sai ta koma nata ɗakin tare da Rauda suka yi shirin barci suka kwanta, da tunani barci ya saceta bata ma san yaushe Hamid ɗin ya dawo ba.
[7/1, 4:17 PM] Rahma Kabir: *ƘAZAMAR AMARYA*
Na
©®Rahma Kabir MrsMG.
Wattpad @rahmakabir
Page 4.
Hamid yana isa falon Hajiya ya sameta zaune a carpet tana kallon tv ga kuma kular abinci da plate a gurin, ya zauna a capet ɗin cike da fara’a yana gaisheta ta amsa tare da tambayarsa aiki.
Lafiya lau Alhamdulillahi, kuma wainar kuka ci? ashe Sakina ta aiko muku da ita.
Hmmm sai da naje na ɗiba da kaina dan ƙurilla taso yi mini, wlh Sakina ta sauya hali rashin mutunci tayi mini akan wainar nan ni kuma na nuna mata ina da iko akan lamarin gidanka, yanzu muka kammala cima.
Ikon Allah Sakinar ce tayi miki haka, aiko wlh sai na ci mutuncinta.
A’a karka yi mata magana ka rabu da ita nasan zafin kishiyar da zaka yi mata ne yasa tayi mini haka kuma aure babu fashi. Yau ka samu leƙawa gidan su Madinar kuwa.
Nan take fuskar Hamid ta sauya domin ya tuna da tukuicin wahalar tusar da ta ba shi ɗazun, sai da ya sauki ɓoyayyen ajiyar zuciya dan ji yayi kamar maƙaƙin warin yake ji a maƙoshinsa sai yace.
Naje sai dai ban jima ba na dawo, tace a gaishe ku.
‘Yar albarka muna amsawa Allah yasa dai kar tayi halin Sakina. Ni da zaka ji tawa ma daka raba musu gida kai kanka hankalinka sai ya fi kwanciya.
Ba ni da ra’ayin raba gidan nan dan ina so yarana su tashi kansu a haɗe, ki dai taya ni da addu’a Allah ya haɗa kansu.
Ameen amma mai matsalar dai itace Sakina dan haka ita zaka jawa kunne.
Kayya Hajiya kina bani mamaki bisa yadda kika ɗaurawa yarinyar nan karan tsana, kuma daidai gwargwado tana yi mana biyayya bata taɓa yin wani abu na rashin kirki ba, banda ke da kullun kike zubar da girmanki a gurinta kin bi kin saka mata ido, shiyasa yaran yanzu suke cewa uwar miji hawan jini kuma kema kina ɗaya daga cikinsu wlh.
Cewar Alhaji da shigowarsa falo kenan ya tsinkayi maganar su, ya zauna yana duban Hamid zai yi magana Hajiya ta riga shi.
Ai dama Sakina bata laifi a gunka na rasa wannan dalili da kullun kake fifita ta akan Hamid.
Saboda ita amana ce a garemu domin mun rabata da iyayenta dan haka dole ne mu fifita ta akan namu kar mu zama masu son kanmu da yawa, ni ba irin ki bace mai ƙaramin kwakwalwa, madadin ki ɗaura Hamid akan ya kula da amanar daya ɗauko amma kullun kece ke zugashi da yawan ƙorafi akanta, yanzu da Asma ce akewa haka zaki ji daɗi ace uwar mijinta ta matsa mata.
Ya ƙare maganar yana ware idonsa akanta, Hajiya ta ce cikin haɗe rai.
Kai kullun in ana magana sai ka riƙa kawo wasu zance daban, ai tarbiyyar dana bawa Asma ba irin na Sakina ba ce, ita Asma tana da biyayya da kunya amma Sakina yanzu ta fitsare kanta bata ganin girmana.
To waye ya ja? ai kece kika yada girmanki ta take shi, in banda kin zama babbar banza ki bita har gidanta ki kwashe mata abincin data girka bayan ta zuba miki daidai wanda zata iya baki kika raina, taya ba zata raina ki ba. Kai kuma Hamid in kasan ba zaka iya adalci ba karka fara auren nan dan ban yarda ka wulaƙanta Sakina ba.
Abba in sha Allah ba abinda ma zai faru zan yi iya ƙoƙari na wajen kamanta adaci a tsakaninsu.
Allah ya baka iko ka kuma daina biyewa mamanku dan zata kaika ta baro.
Cewar Alhaji sai ya ɗauki remote ya sauya tasha zuwa na labarai, Hajiya dai bata kuma magana ba dan tasan halin Alhaji sai ya cigaba da kwafsa mata a gaban Hamid, daga bisani ma tashi tayi ta wuce cikin ɗaki tana kwalawa Jidda kira akan tazo ta kwashe kayan abincin. Hamid kallon labaran ya cigaba da yi tare da yiwa Abba hirar company, sai wajen goma da rabi ya yiwa Abba sallama y dawo gidansa.
AbdulHamid shine ɗa na farko a gidan sai Asma’u ke bi masa wacce take aure a Zaria yaranta shida, Jidda itace babbar ‘yarta data ke zaune tare da su Hajiya tun lokacin data kawota yaye shikenan Hajiya ta riƙeta a hannunta makaranta da komai anan take yinsa, shekarunta sha shida dan tana SS 2 a secondary, islamiyya tana ajin sauka, daga Asma sai Kubura itama tana aure a Abuja yaranta biyu, sannan Salim autansu da yake karatu a can ɗan Fodio yana matakin ƙarshe na kammala digree ɗinsa. Tun sadda Hamid ya auri Sakina su Asma suke ganin rashin dacewarsu a ganinsu gidansu ‘yan boko ne taya zai aure wacce bata da ilimin zamani, shiyasa sam basa wani shiri da Sakina komai nasu basa sakata a ciki dan ko haihuwa suka yi Sakina taje baya baya take dasu dan basa sake mata, shiyasa ma bata damuwa da lamarinsu itama ta kama kanta dan ko Kaduna suka zo sai in sun gadama sun leƙota kafin take zuwa daga baya su kuma gaisawa. Shiyasa tunda Hamid ya ɗauko zancen ƙarin auren nan suke mugun farin ciki musamman ma da suka ji wayayya ‘yar boko zai aura, haka suka ƙara mara masa baya akan gwara ya ƙara ko zai samu matar bita taro, shiyasa tunda aka saka bikin suke cikin shiri dan ankon tsadadden leshi suka fitarwa Family ɗinsu domin so suke ayi bikin kece raini, sun ci burin yin shagalin zamani dangin su Dinner da su kamu da dai sauransu, shiyasa tun biki yana saura sati biyu suka ɗaura niyyar zuwa dan gabaɗaya sun ƙosa ma lokacin yayi.
…
Hajiya tana shiga ɗaki Asma ta kirata nan suka tattauna akan maganar bikin daga bisani Hajiya ta faɗa mata abinda Sakina tayi mata, wani ashar Asma ta wulwulo tana ɗaurawa da cewa.
Wallahi duk randa na shigo Kaduna haɗuwata da Sakina ba zai yi kyau ba, dan saina ga uban daya tsaya mata da take niman ci miki mutunci.
A’a Asma ki rabu da ita nasan duk haushin auren nan ne yasa tayi haka, da ki ɓata ranki abanza gwara ki cigaba da shirin biki mu tusa mata baƙin ciki.
Hmmm ai Hajiya ina nan ina shiri na ƙosa lokacin zuwanmu yayi, zata ga ƙarshen rashin mutunci kuwa.
Nan dai sukai ta mayar da maganar daga bisani suka yi sallama.
Washe gari da wuri Sakina ta shirya yaranta kamar yadda ta saba, hatta Rauda da bata zuwa makaranta tayi mata wanka ta sauya mata kaya masu kyau saboda Hamid ya gargaɗeta akan karya wayi gari yaga gidansa kaca kaca da yara, ko kafin ya fito su Mufeeda sun tafi makaranta a motar Bus dinsu da ya siya musu driver ke kaisu, ta gyara ko ina ta saki ƙamshin turaren wuta kana ta shiga kitchen ta gyara ko ina tare da dumama masa wainarsa da kumun tsamiya data san duk in zaici ɗumamen abinci to shi yake cewa tayi shiyasa bata rabo da garin kunu, bayan ta kammala ta je tayi wanka ta saka baƙar jallabiya wacce tasha aiki da fararen duwatsu sai ta saka ash ɗin hula ta feshe jikinta da turare ta fito falo dan zaman jiran fitowarsa, saita kunna tv ta soma kallon MBC 2 da suke wani action film, Rauda kuma tana wasa da kayan wasanta akan carpet. Bayan kamar minti sha biyar sai ga Hamid ya fito cikin shirin fita, yadda ya shaƙi ƙamshin turare mai daɗi a falon yasa shi jan numfashi mai daɗi ya sauke a hankali ya tako hartsakiyar falon, Sakina ta miƙe fuskarta ba yabo ba fallasa ta gaishe shi tare da yin gaba zuwa dinning dan ta saka masa abinci, ba musu shima yabi bayanta ya ja kujera ya zauna yana danne danne a wayarsa, nan ta haɗa masa komai ta sallameshi kana ta dawo falo ta zauna, bayan ya kammala karyawa ya taso ya dawo falon ya zauna yana cewa.
Jiya naji wulaƙancin da kika yiwa Hajiyata wallahi Sakina ina mai matuƙar ja miki kunne akan haka, ki shiga hankalinki in ba haka ba zan yi miki mummunar hukuncin da zaki dana sani.
Allah ya huci zuciyarka amma ni banyi mata wani abu ba.
Mahaifiyar tawa ce take karya ko sharri zata miki. Sakina! Sakina in kina son ki cigaba da zama dani to dole ne ki martaba iyayena dan wlh akansu zan iya rabuwa dake.
Kayi Haƙuri zan kiyaye In Sha Allah.
Sakina ta faɗa idonta yana ciko da kwalla ga mari ga tsinka jaka, Hamid yayi ƙofa.
Karma ki kiyaye, ni zan fita saura na dawo anjima na tadda gida kaca kaca, kuma sakwara zaki yi mini da miyar agushi zan aiko da kayan cefane.
To adawo lafiya, yauwa Yaya Umma zata zo anjima nace bari na faɗa maka dan ta sanar dani jiya.
In tazo ki gaishe ta ga wannan ki bata.
Ya ƙare maganar yana zura hannu a aljihu ya zaro kuɗi ya ƙirga dubu ashirin ya miƙa mata.
Ki duba store ɗinku in akwai sauran shinkafa ki ɗibar mata rabin buhu, tare da sauran kayan masarufi.
Angode Allah ya ƙara riƙo da hannunka ya sada ka da Alkhairi ya ƙara buɗi.
Ameen ya faɗa fuska a gimtse ya wuce, da ido Sakina ta bishi ga kirki ga rashin mitunci, yanzu banda yaya umma tasan waye shi da ba zata riƙa yarda da ita ba akan ƙorafin da take faɗa mata nashi saboda alkhairin da yake yawan yi mata, taja guntun tsaki dan sam bai burgeta ba duk wannan abin daya ce a bata, tunda ko wace mace farin ciki da kwanciyar hankali take nima a gidan aurenta komin talaucin mijin, yadda take ji a ranta da Hamid zai rasa komai ya talauce amma ya dawo yana mutuntata suna zaman lafiya zaifi mata wannan daular da suke ciki ba farin ciki.
Wajen ƙarfe ɗaya da rabi na rana yaya Umma tazo, lokacin Sakina ta gama haɗa musu girkin rana jelof ɗin shinkafar manja da busasshen kifi da naman sa, sai kuma zoɓo mai daɗi data haɗa musu, a nan falo kan carpet suka yada zango, sai da suka ci suka ƙoshi kafin suka soma hira, wanda anan Sakina ta ke sanar da ita abubuwan daya bayar yace a bata, yaya umma ta saki murmushi.
Hamid Zuma ne ga zaƙi ga harbi, Allah ya saka masa da alkhairi ya daidaita zamanku.
Nifa wlh yaya Hamid ya fita a aaina a yanzu na fara addu’ar rabuwa dashi in hakan shine mafi alkhairi, nasan yara Allah yana tare dasu ko ina raye ko bana raye zasu rayu dan ƙaddarar ko wani bawa yana tare dashi.
Karki ƙara faɗar irin haka Sakina komin lalacewar auren nan yafi miki rufin asiri akan ace babu shi, wata macen da zata ji labarinki sai tace dama itace ke saboda nata munin ƙaddarar yafi naki, Allah baya taɓa jaraba bawa da abinda ba zai iya ɗauka ba sai dai bawa yayi gajen haƙuri, kuma ni bazan ce ki cibaga da zama domin yaranki ba wannan ba hujja bace, ki dai cigaba da zama a matsayin auren ibada ne saboda ko wani ibada yana tafe da ƙalubale, Allah bai halicce mu hakanan domin muji daɗin duniya ba, ya halicce mu ne domin mu bauta masa, dan haka ina mai ƙara jan kunnenki akan ki cigaba da juriya Allah zai duba lamarinki In Sha Allah matsawar kin dogara a gare shi.
Sakina ajiyar zuciya ta sauke dan sosai maganar yaya Umma ya ratsata.
Shikenan In Sha Allah zan cigaba da ƙoƙarin danne zuciyata, amma wlh lamarin da matuƙar ciwo a zuciyata.
Wata rana zai zama labari In Sha Allah, yanzu abinda nake so dake ki cigaba da bashi dukkan kulawa karki gaji, nasan kina da tsafta amma ki ƙara domin mijinki yana son haka, ki kuma kula da shinfiɗarsa sosai kinji kafin zuwan amarya.
Sosai Yaya Umma ta bata shawarwari wanda yasa Sakina ta samu ƙarfin guiwa da jin zata iya jurewa komai domin samun kyakkyawar sakamako a gurin Allah. Sai yamma lis yaya Umma ta tafi da kayan arzikin da Hamid yace a bata.
Da dare.
[7/1, 6:52 PM] Rahma Kabir: *ƘAZAMAR AMARYA*
Na
©®Rahma Kabir MrsMG.
Wattpad @rahmakabir
Page 5.
Da dare.
Sakina bata yarda tayi wani kuskure da zai fusata Hamid ba, dan har hira suka ɗan yi a falo bayan ya kammala cin abinci, daga bisani ya shige ɗaki ya barta da yara, itama ta tasa ƙeyar yaran ko wanne ya kwanta a ɗakinsa, kana ta kwantar da Rauda tayi barci sai ta tashi ta shirya cikin wasu kayan barci masu kyau ta gyara sumar kanta da yake a cefe ta feshe jikinta da turare kana ta saka hijab ta yiwa Rauda addu’a sannan ta fito ta jawo ƙofar a hankali ta nufi ɗakin Hamid, tun kafin ta shiga ta ji muryansa yana waya, sai da ta tsaya jim ta fahimci da Madina yake wayar, kamar zata juya ta koma ɗakinta sai kuma ta danne zuciyarta tunawa da shawarar da yaya Umma ta bata, sai kawai ta kama handle ta murɗa ta shiga ɗakin da sallama,Hamid ya waigo daga rufda cikin da yayi yana kallonta ga wayar a kunnensa yace cikin haɗe rai.
Lafiya?
Sakina sai da ta haɗiye miyau kafin ta danne abinda taji a ranta ta samu gefen gadon ta zauna tana cire jihab ɗinta ta ninke, da kallo ya bita ya tashi ya zauna, a lokacin Madina take cewa.
Baby Hamid waye ya katse mana hirarmu ne naji kayi shuru.
Madinar Hamid ki yi haƙuri zan sake kiranki.
Sai ya gimtse kiran ya mayar da dubansa ga Sakina da take ta sakin murmushin yaƙe.
Meya faru? lafiya kika zo nan.?
Haba Abban Mufeeda ya kake tambayata dan na zo mu kwanta.
Na kira ki ne?
Ya faɗa yana haɗe rai.
Yanzu sai ka kira ni ne zan zo mu kwana tare. Ina ce ba yau muka saba haka ba ko ka kwana ɗakina ko na kwana a nan.
To ban gayyace ki ba ki tashi kije ki kwanta a ɗakinki, haka kurum kin katse mini hira saboda jaraba ta kunno ki, ina ce yau kusan kwana biyar baki kwana anan ba, to duk ƙulaficinki sai dai ki mayar da shi dan na fara gyara dan tarban amarya ba zaki zo ki ɓata mini shiri ba.
Wani irin kallo Sakina take binsa dashi cike da mamakin furucinsa, wanda nan take hawaye suka cika mata ido har jikinta ya soma rawa saboda tsananin dukan da maganarsa tayi mata a zuciya, cikin hasala ya cigaba da cewa.
Shekara nawa muka yi muna a tare, dan haka yanzu kya sarara mini na yiwa Amarya tanadi, in ma wani abin kika sha ya tsayar miki da jaraba to sai ki san yadda zaki yi, ki tashi ki fita mini a ɗaki.
Sakina lumshe ido tayi hawayen daya taru a idonta ya sauka a kuncinta, bata ce masa komai ba ta miƙe riƙe da Hijab ɗinta dan tama kasa mayar da shi a jikinta, jiki a sanyaye ta fice daga ɗakin ko rufo masa ƙofar ma ta kasa yi ta koma ɗakinta tare da rufe ƙofar da key ta zauna a ƙasan tiles ta saki wani wawan kuka mai tsuma zuciya, da yake dare ne kukanta har falo ana ji dan da ƙarfi take yinsa saboda wani abu data ji ya danne mata ƙirji, jikinta har ciccira yake tana fidda gumi, haka fuskarta ta dame hawaye da majina tana yi tana gogesu da hijab ɗinta data ƙanƙame da hannunta, tunda take ba a tana wulaƙantata irin wannan ba, Hamid ya kai ƙololuwar ci mata fuska ya muzantata mafi muni data ji kamar ta haɗiyi rai dan baƙin ciki, sai da tayi mai isarta kafin daga bisani ta sassauta kukan ta ja jikinta zuwa jikin gado ta jingina bayanta tare da lumshe ido hawaye ne kawai ke gangarowa a kuncinta, alwashi da alƙawari ta riƙa ɗaukarwa kanta ba zata kuma kai kanta ɗakin Hamid ba zata nuna masa ita ‘yar halak ce, zata nuna masa zata iya rayuwa ba tare da ya kuma kusantarta ba, nan take ta yiwa kanta alwashin bashi wata guda da amarya ba tare da ta amsa girki ba, yadda zai samu damar sauke duk wani gyara da ya yi akanta, koda ta amsa girki bata jin zata bashi haɗin kai kowa kuwa ya kawo kansa yana magiya sai ta jashi a ƙasa kamar yadda ya wulaƙantata yau, dan ba zata taɓa iya yafe masa wannan ba dole ne ta nuna masa ita macece ‘yar halak, haka ta raba dare a haka sai da taji kanta yayi mata nauyi saboda sara mata da yake yi, kafin ta miƙe da kyar ta shiga bayi ta ɗauro alwala ta dawo ta kwanta tayi addu’ar barci kana ta cigaba da jan istigafari a ranta, tayi alƙawarin binne wannan damuwar a ranta ba zata faɗawa yaya Umma ba dan ya kamata ta koyawa kanta riƙe damuwa ta kuma iya ƙoƙarin magance shi da kanta, a haka barci ya ɗauketa.
Washe gari Sakina ta saka Mufeeda ta shirya musu abin kari dan tace musu ba tada lafiya, suka yi mata sannu da fatan samun lafiya, Mufeeda ce ta taimakawa ƙannenta suka shirya har suka tafi makaranta, da yake falon a gyare yake Sakina bata wani damu ba ta rufe ɗakinta da key ta kwanta ta bar Rauda a tsakiyar gado tana wasanta.
Hamid koda ya fito daga ɗakinsa baiga kowa a falon ba haka ya wuce dinning yaga wayam, kwafa yayi ya juyo cikin zafin rai ya isa ƙofar Sakina ya murɗa sai dai ya samu a rufe, sai ya shiga bugawa tana jinsa tayi banza dashi, nan ya fara masifa da zage zage wanda yasa Rauda ta rarrafa ta maƙale jikin mamanta ta kwanta, dan sosai yarinyar take tsoron baban in yana masifa, Hamid ya ƙaraci kumfar bakinsa ya wuce ya ɗauki jakarsa ya fita ransa a matuƙar ɓace da tunanin irin matakin da zai ɗauka akan iskancin da Sakinar tayi masa naƙin yi masa abincin kari.
A taƙaice sai da suka ɗauki kusan sati basu saka juna a ido ba, dan sosai Sakina take kaucewa haɗuwarsu kuma ta daina girki sai dai ta sa Mufeeda ta girka abinda zata iya dafawa, ita ko saboda hora kanta da tayi da yunwa da kuma zaman kaɗaici sai da ya sakata ramar dole, da rana takan fito falo ta zauna ta yi kallo yamma nayi sai ta shige ɗaki tare da gargaɗin yaran kar wanda ya takurata kuma kar suyi ɓarna. Hamid ba ƙaramin ɓacin rai ya shiga ba dan shima ya ɗauki fushi da ita ganin ta gama raina masa wayo, ga yadda ya horu da abincinta tunda ta daina yi ya shiga damuwa, kullun sai dai yaci abinci a waje kan ya shigo, cin dole yake yi badan ransa yana so ba, shi kansa bai san yana ƙaunar abincinta ba sai a wannan lokacin, shiyasa ko tafiya baya so tayi dan yana shiga wani yanayi kan ta dawo, amma haka ya danne yaƙi saukowa ya bata haƙuri a ganinsa shi ta yiwa laifi, sannan ma gwara ya koyawa kansa rage sabo da abincinta tunda Madina zata zo ta fara girka masa me daɗi dole kuma yaci ya saba da nata, hakan yasa ya cigaba da jan zaren fushinsa ya fita sabgarta kamar yadda itama ta fita nashi.
Haka suka ƙara kwashe sati guda a haka wanda ya kama saura sati biyu bikinsa, wannan lokacin shirin biki kawai ya sa a gaba wanda suke ta tsare tsare da abokinsa Habib Mijin Kausar, a cikin hirarsu ne ma ya bashi labarin irin zaman da suke yi da Sakina, cikin haɗe rai Habib yace.
Haba Hamid kai kuma saika biye mata, ai bai kamata matsayinka na babba ba kayi haka, laifi fa kayi mata tunda aure zaka ƙara, a wannan gaɓar lallashi da tarairaya take buƙata bai kamata ka nuna bata da ƙima a gunka ba.
Hmmm baka san halin Sakina bace gabaɗaya ta sauya ta koyi taurin kai, ni ta yiwa laifi amma tafi ƙarfin ta bani haƙuri, kusan sati biyu rabon da tayi mini girki, wai kishi hauka ne ko akanta aka fara ƙara aure.
Duk da haka kaine ya kamata ka sauko ku daidaita kafin a ɗaura auren nan.
Hmmm Hamid yace yayi shuru yana nazarin maganar Habib, duk da ma bai sanar dashi asalin wulaƙancin daya yi mata ba wanda a ganinsa bai ɗauke shi laifi ba ra’yinsa ya sanar mata, kuma ya dace tayi masa uzuri tunda shekara kusan sha biyar suna tare dan ya nima ta bashi lokaci saboda amarya zata yi fushi haka, tsaki yaja yana cewa.
Wlh raini ne bana so, in taga ta nima mu shirya zata ɗauki kanta wata mai daraja.
Dama ba mai darajar ka ɗauketa ba ashe, ai mace ‘yar mulki ce duk sarautarka saika sauke shi ka bita matsawar bata kauce addini ba.
Ni yanzu ka dama mini lissafi, kaga mu bar maganar nan kawai.
Cewar Hamid, Habib faɗa ya rushe da shi wanda ya nuna masa ɓacin ransa sosai kafin Hamid ya yarda zai nima su shirya, daga haka ya cigaba da bashi shawarwari na yadda zai kyautata mata har ayi auren lafiya a gama, haka suka rabu Hamid yana tunanin maganganunsa.
Bayan sallar magrib kafin ya dawo gida sai da yayi musu siyayyan kayan ciye ciye dan yasan ba lallai tayi girki ba, ya kashe kuɗi sosai duk kuwa cikin shawarar Habib ne. Daya iso gida ya samu su Mufeeda a falo suna kallo, suka yi masa sannu da zuwa kana ya aje ledojin hannunsa a center table ya wuce direct ɗakin Sakina ya shiga bugawa, daga ciki yaji muryanta tana cewa.
Amma Mufeeda bana ce karku dame ni ba, meye kike buga mini ƙofa.
Sakina ki buɗe ƙofar ina son yin magana dake.
Cewar Hamid yana ɗan haɗe rai dan ba ƙaramin daurewa yayi ba ya kawo kansa, ita kuma dama zaman haka ya isheta tana so su shirya amma bata so ta nuna masa har sai in ya kawo kansa, a da ita ce ke shige masa yana wulaƙantata a haka har su shirya amma yanzu ya dace taja ajinta itama ya gane tanada daraja shiyasa ta yi masa haka, bata ce masa komai ba ta miƙe ta zura hijab tazo ta buɗe masa sai ta juya yabi bayanta zuwa ciki, duka suka zauna bakin gado tare da yin shuru dan taƙi yi masa magana, Hamid ya gama ƙuluwa amma haka ya danne ya nisa yana cewa.
Yanzu dai kin nuna mini wuyanki ya isa yanka Sakina, to kanki kika yiwa bani ba, kuma wannan ɓuyar da kike yi ya isa haka, kina sane da bikin nan ya kusa gwara ki warware ayi komai lafiya ba tare da kin bada ƙofar da ‘yan uwana zasu gane baƙin halin da kika sauyawa ba ki gogawa kanki baƙin fenti, tun jiya su Asma suka zo amma kin kasa zuwa ki duba su, dan haka ki gobe In Allah ya kaimu ki shiga ku gaisa sannan ki zauna ki tattauna maganar shagalin bikin, sannan kayan katakon ɗakinki ki yi kyauta dasu, kujerun falo ma ki bawa wanda ya dace, jibi Ins Sha Allah za a kawo sabbi a saka.
Allah ya kaimu lafiya angode Allah ya ƙara buɗi.
Ameen, ki tashi ki je falo na yi mana siyayyan abinda zamu ci, sai ki gyara komai kafin in fito daga wanka sai muci a dinning.
To tace masa sai ya miƙe ya fice, da ido ta raka shii tana murmushin takaici, ita duk maganganunsa ba wanda ya ɓata mata rai sama da wai taje ta gaishe da ƙannensa wanda in da halacci sune ya dace su fara zuwa su dubata tunda ƙannensa ne, kwafa tayi da alƙawarin ba zata je ɗin ba sai dai yayi duk abinda zaiyi, iskanci ne yasa basu shigo gunta ba tasan dama ba sonta suke ba suna murna da aurensa, dan haka yadda suka ɗauketa itama haka zata bi dasu kowa ya zauna a mazauninsa, ib bata nuna musu ita ma akwai zuciya a ƙirjinta ba haka zasu riƙa takata, daga su har wansu zata yi maganinsu, taja guntun tsaki ta miƙe ta fice.
Wannan shine dalilin shiryawarsu sai dai ko kaɗan Sakina bata sake gigin kai kanta zuwa ɗakin Hamid ba, shima bai nuna yana buƙatar ta ba hakan yasa ta cigaba da lamarinta, musamman da biki yazo itama tana ta nata shirin, duk da ba taro zata yi ba amma ‘yan uwanta zasu zo suyi mata ƙara.
[7/2, 10:58 PM] Rahma Kabir: *ƘAZAMAR AMARYA*
Na
©®Rahma Kabir MrsMG.
Wattpad @rahmakabir
Page 6.
Biki saura kwana biyar Hamid ya kawo mata kayan fadar kishiya akwati biyu da kit, duk da kaya a ciki masu kyau leshi uku atamfa biyar da shadda biyu sai material biyu da sauran takalmi da jaka, kala biyar aka ɗinka mata a ciki, koda ya nuna mata ta yi murna da godiya har tsokanarsa tayi tana cewa.
Kaga yadda kake ta sheƙi ko dai kaima kaje anyi maka gyaran jikin ango ne.
Kai Sakina bana son sharri.
Allah ba sharri nake maka ba naga ka ƙara haske sai dai kayi rama kaɗan kuma wlh hakan ya ƙara maka kyau.
Wahalar zurga zurga ne yasa na rame ga kuma kashe kuɗi da nake tayi, jikina da aljihuna yana gaya mini.
Allah dai ya nuna mana ya sanya alkhairi, ni kasan babbar kyautar da zanyi maka kuwa.
Cewar Sakina tana ɗan murmushi, Hamid aje wayarsa yayi a gefensa yana dubanta dan sosai yaji daɗin yadda take farin ciki da zuwan aurensa, saboda yaga ta sake sosai ta aje duk wani kishi da yake gani a tattare da ita, yace.
Sai kin faɗa Sakina.
Hmmm babu wani kyauta da zanyi maka da zai burgeka saboda nasan kana da kuɗi, shiyasa nayi tunanin na baku kyautar cin amarci na wata guda kai da Amarya hakan zai sa ku fahimci juna sosai kusan ina kuka dosa, ni kuma zan yi mata girkin sati ɗaya daga nan taja ragamar kirki har sai ta cike wata gudan dana baku.
Washe baki Hamid yayi yana dariya kana ya ƙara dubanta.
Anya wannan kyautar taki takai har zucci kuwa?
To meye a ciki? naga dai duk gyaran da kayi na amarya ne to ina so ka zube duk wani gyaran da kayi gunta, kan wata guda na tabbatar da komai ya kankama ƙila ma in rabo na kusa ta kunsa.
Sakina kenan in dai da gaske kike yi to ina godiya Allah ya bar soyayya, duk da nasan da biyu kika bayar da kwanakinki saboda abinda ya faru kwanaki shiyasa zaki ce haka.
Haba ai abinda ya faru ya wuce gani nayi ya dace in yi maka wannan halaccin tunda ni tsohowar zuma ce mun jima muna tare, ya dace na bawa Amarya dama itama.
Hmmm shikenan nagode Allah ya bamu zaman lafiya gabaɗaya.
Sakina ta amsa da Amin fuska cike da murmushi, sai dai zuciyarta cike yake da ƙuna akan zafin kishin da take ji akansa, duk da tana ganin karin auren zai iya zama wani mafita a gareta, kuma Hamid bai cancanci ta wahal da kanta gurin kishinsa ba tunda ko tayi ma baisan tana yi ba, amma jin kishi ya zama wajibi taji shi saboda duk wata mace dole ne taji babu daɗi in mijinta zai ƙara aure duk lalacewarsa kuwa , Abun da ciwo sai dai ko wacce da irin nata dauriyar.
Lokacin data koma ɗaki tayi shirin barci a sannan ne ta shiga tunanin maganar da tayi da Hamid, yadda ya nuna yaji daɗin kwanan data basu yasa ta ƙara tabbatar da baya ƙaunar ta, a yanzu ta gane darajar ‘ya’yanta take ci shiyasa yake cigaba da zama da ita, dan sam bata gabansa balle wani sauran daraja, hakan ba ƙaramin ciwo taji yayi mata ba kuma itama dole ne zata cire shi a ranta ta zauna zaman ibada dan kuwa yanzu ne lokacin da zata yi zaman haƙuri, fargabanta irin yadda zaman zai kaya da amaryar a gidan tasan zata ƙunshi baƙin ciki da halin Hamid, dama zai raba musu gida ita hakan zaifi mata kwanciyar hankali, amma tasan bata kai wannan matsayin ba da zata saka yayi mata abu, dan ta gwada yi masa magana akan raba gida basu kwashe ta daɗi ba, da wannan tunanin barci ya kwasheta.
Da safe bayan ta sallami yara da Hamid sai ta shirya ta shiga sashin Hajiya akan amsa kiranta dan tun jiya ta sanar da Hamid ya faɗa mata taje yau, da sallama ta shiga falon basu ma ji ba saboda mata ne da ɗan dama a ciki ga hayaniya da suke yi na kallon kayan akwatin amarya da za a kai anjima, sai da ta ƙaraso ciki sosai ta kuma yi musu sallama a sannan ne wasu daga ciki suka amsa suna cewa.
Uwargidan Hamid ce da kanta.
Nice ina kwananmu fatan mun tashi lafiya.
Wasu suka amsa mata da lafiya lau, su Asma kuwa kawar da kai suka yi suna cigaba da hira tamkar basu ganta ba, itama bata bi ta kansu ba ta samu cushing ta zauna tana cewa Jidda.
Hajiya tana ina? kije kice mata na zo.
To tace mata kana miƙe da sauri ta wuce ɗakin Hajiya dan ta kirata, Kubura ce ta daga wani crazy English wears riga da wando tana cewa.
Anty Asma kinga wannan kayan ba ƙaramin yiwa Madina kyau zai yi ba gata fara ga tsayi, gaskiya yaya Hamid ya iya zaɓar mata.
Faɗi ki ƙara yanzu ne yasan zai yi aure ai.
Cewar Asma tana miƙa mata hannu suka tafa tare da yin shewa, sauran matan ma wasu daga ciki suka shiga yaba kyawun amarya da suka ga hotonta a wayar Asma dan tuni Hamid ya haɗasu suke zumunci a waya, Sakina tana jinsu amma tayi kamar bata gurin, tasan da biyu suka yi haka tunda sun san tana nan, fitowar Hajiya yasa ta miƙe da sauri ta isa gareta ta tsuguna tana gaisheta Hajiya tace.
A’a miƙe bana son wannan ladabin naki na munafurci, ni da baki ɗauke ni da mutunci ba ina zaki yi mini ladabin kunama.
Jikin Sakina a sanyaye ta miƙe tsaye ganin duk hankalin mutanen falon ya dawo gunsu, ta kuma sake miƙa mata wani gaisuwar Hajiya tace.
Lafiya lau, dama na aika kizo ne akan na ji me kike taƙama da shi ne da ba zaki zo ki ji ya yanayin bikin zai kaya ba, sannan ace su Asma sun fi sati a garin nan kin kasa leƙosu, ai koda ƙannen Hamid ne matafiya ne su, ya kamata ki leƙo ku gaisa.
Ayi hakuri Hajiya nayi zaton da suka zo sun koma ganin basu leƙo ba.
Hmmm ni ma da baki ɗaukeni a bakin komai ba balle su, Allah dai ya kyau da wannan baƙin halin da kika sauya, ga akwati can kije ki gani na amarya kar ki ƙorafin ba a nuna miki ba.
To Sakina tace zuciyarta yana yi mata suya, haka ta matsa kusa da kayan akwatin bata saka hannu ba sai ta shiga kallo saboda wasu mata suna ɗaga su, data gama iya kallon da zata yi ta juya ta isa inda Hajiya take zaune tace cikin dakiya.
Hajiya na gama kallon kaya sunyi kyau Allah ya sanya alkhairi ya bada zaman lafiya, zan iya tafiya ko akwai wani aikin da zanyi muku.
Ohhh Sakina har kin gama kallon kayan da yawa fa.
Ai Umma ko hannu bata saka ba balle ta ɗaga kayan ta gani.
Cewar Kubura.
Hmmm ai baƙin kishi ba zaisa ta taɓa kayan ba, kuma hakan bazai sa a fasa ba aure ba fashi, in kinso ki gyara halinki in kin ƙi kuma kya yiwa kanki dan yanzu Hamid ya samu mai faranta masa tunda ke kin zama mai baƙin hali.
Cewar Hajiya, Hawayen daya ciko idonta ya zubo a kuncinta tama kasa magana, domin taruwa mata suka yi kowa yana faɗar abarkacin bakinsa, ƙanwar Alhaji ce data fito ta ji abin da suke mata yasa tayi magana tana cewa.
Haba da wanne zata ji? da auren da zai yi ko da wannan ƙorafin naku, idan ma tayi kishi ai halal ne tunda da zuciya a ƙirjinta, kuma ko wace mace dole taji zafin haka, Sakina wuce abinki Allah ya kawo amarya lafiya kowa halinsa shi zai zaunar dashi, aniyar kowa zata bishi, kije ki ƙara haƙuri wata rana sai labari.
Mariya me kike nufi da maganganunki? nifa bana son tashin hankali in kinsan ba alkhairi ya kawoki ba ki kama kanki.
Cewar Hajiya cike da haɗe rai, Mariya ta juya tana kallonta.
Ni da gidan ɗan uwana aiko ba inda zani sai naga abinda ya turewa buzu naɗi, kuma wlh duk wanda yace tukunyar wani ba zata tausa ba to nashi ko zafi bazai yi ba, ayi dai mu gani in tusa zata hura wuta.
Nan fa hayaniya ya kaure, aka samu ‘yan uwan Hajiya suka shigar mata, Mariya ganin ita kaɗai ce ta fara zuwa a ‘yan uwan Alhaji hakan yasa ta kama hannun Sakina suka fito suka wuce gidanta, a falo suka yada zango ta dinga bawa Sakina haƙuri tana tausanta, ita ko banda zubda kwalla ba abinda take yi dan shine kaɗai zai sa taji sauƙin zafin da zuciyarta keyi mata, sunyi mata wulaƙancin da ba zata taɓa mantawa ba, Mariya sai da ta tabbatar da ta samu natsuwa kafin tayi mata sallama ta koma sashin su Hajiya.
Wannan ɗan saɓanin daya faru sai da su Asma suka faɗawa Hamid bayan ya dawo, suka faɗa masa ƙarya da gaskiya, haka ya shigo sashinsu ya tasa Sakina a gaba ya dinga yi mata faɗa, ƙala bata ce masa ba har ya kai aya a zantukansa ya wuce ɗakinsa, murmushin takaici tayi hawaye yana zuba a kuncinta ta juya ta shiga ɗaki tana jan salatin Annabi s.a.w wanda hakan shine zaisa taji sauƙin halin da take ciki, yanzu ta ƙara tabbatar da auren nan da zaiyi babu wani sauƙi da zata samu kanta a ciki, dan alamu sun nuna wani sabon baƙin ciki ne zata ƙunsa, kiran daya shigo wayarta yasa ta miƙe ta isa inda ta saka chargy ta ciro sai taga yaya Umma ce, ta ɗauka da sauri dan ya kusa tsinkewa.
Sakina ina wuni ya shirye shirye.
Alhamdulillah yaya Umma.
Ta faɗa cikin rawar murya.
Yana ji muryanki wani iri meke damunki?
Yaya Umma bazan iya jurewa da zaman gidan Hamid ba wlh na karaya.
Ta ƙare maganar cikin matsanancin kuka, Yaya Umma ta miƙe daga zaunen da take a tsakar gida ta shiga ɗaki tana cewa.
Sakina hakanan zaki cije ki jure, wlh jarawaba ce ki ɗaure zaki ci In Sha Allah, kuma dama aski in yazo gaban goshi yafi zafi.
Yaya ɗazun su Hajiya sunci mini mutunci a cikin mutane yanzu kuma Hamid ya gama sauke mini nashi masifar, ina zan saka raina, ni ban hanashi aure ba ban tayar da hankalina nace kar yayi ba, amma duk da haka ban fita ba agun danginsa da kuma shi kansa, basa ƙaunata basa son zaman aurena da shi gwara na bawa Shalelen amarya guri tazo ta basu farin cikin da suka ce na kasa basu.
Kul! kul na kuma jin kin ambaci wannan maganar, ki dage da nafilar dare kina faɗawa Allah damuwarki In Sha Allah zaki samu sassaucin halin da kike ciki. Ina ganin jibi zan zo gabaɗaya har sai an kammala biki saboda babansu ya tafi ƙauyensu zai kwaso amfanin gona na nomar daya yi.
To yaya kizo mata tun gobe ganinki zai sa na samu natsuwa tunda ba kowa a guna, abin yayi mini yawa ina cikin damuwa.
Haba Sakina yayi wuri inna zo gobe, amma zan zo sai na tafi da yamma washe gari sai na tawo gabaɗaya.
Yauwa yaya Umma nagode Allah ya kaimu sai kinzo.
Cewar Sakina tana ɗan jin wani sanyi a ranta.
Matar Hamza ma jibin tace zata zo dan nayi magana da shi.
Aiko naji daɗi wlh Allah ya kaimu.
Yaya Umma ta amsa da amin kana suka yi sallama.
Madina.
[7/3, 6:55 PM] Rahma Kabir: *ƘAZAMAR AMARYA*
Na
©®Rahma Kabir MrsMG.
Wattpad @rahmakabir
Page 7.
Madina tunda biki ya matso ta zama busy, shirye shiyre take ba kama hannun yaro duk wani gyara daya tace tayi to tayi shi, dan har gyaran jiki aka soma yi mata kusan kwana biyat da ya wuce, yanzu ma jikinta an shafe shi da kurkur haɗe da kayan gyaran fata tana zauna daga ita sai ɗaurin ƙirji akan wata kujerar ƙarfe a ɗakinta, da ƙawayenta da mai gyaran jiki duk suna ɗakin sai hira suke yi, yayarta Aisha ce ta shigo riƙe da ƙaramin ɗanta da take goyo, Madina tace.
Anty Aisha har masu kawo lefen sun wuce ne?
Eh sun tafi, Kausar zaku iya zuwa ku ga Akwatin.
Aisha ta faɗa tana duban ƙawayenta, da sauri suka miƙe duk suka fice har da mai gyaran jikin, dama tayi hakan ne domin su bata guri dan tayi magana da Madinar, Aisha ta kalleta da kyau tana cewa.
Gaskiya Madina ban ji daɗin ganin lefenki haka ba, Hamid yayi ƙaranta da yawa a yadda muke zaton zai yi miki ba haka yayi ba, domin kuwa babu kaya sosai kwata kwata zannuwa basu fi talatin ba sai sauran kayan tarkace, kuma akwati set ɗaya ne guda huɗu da kit wanda mukai zaton ki samu set biyu.
Madina zabura tayi ta miƙe tana zaro ido cike da damuwa ta dafe ƙirjinta tana cewa.
Amma Hamid yaci mutuncina ban zaci haka ba wlh, yadda yake ta kuranta ya kashe mini kuɗi a akwati, muje na gani.
Ta faɗa tana bin gefen Aisha ta fita zuwa falo, Aishan ma bayanta tabi, suka tadda mutanen falon sunata ɗaga kaya sai yabawa suke yi, mom dai taɓe baki tayi tana cewa.
Ni kam Wlh bai burgeni ba lefen, yadda dai nasan Hamid yana da kuɗi ai Madina tafi ƙarfin waɗannan kayan.
A’a fa Hajiya wlh yayi ƙoƙari domin duk zannuwa masu tsada ya saka babu na banza a ciki.
Cewar wata kasar momy, Madina ji tayi idonta ya kawo kwalla dan gabaɗaya ganin kayan baisa tayi farin ciki ba sai damuwa data samu kanta a ciki musamman furucin mom data yi, momy ta mele baki.
Hajiya Sa’a yaron fa yana da mugun kuɗi wlh, kawai dai ya nuna shi ƙaramin mutum ne amma yadda yake da arziki ya dace yayi kayan da suka fi haka, yace ma zai bata mota ai ya dace yasa key ɗin a ciki.
Nan dai mutanen falon suka shiga mayar da magana wasu suna yaba kaya wasu kuma suna zancen ƙila ƙaryar arziki yayi musu amma yadda madina take da kyau da ilimi ai ta wuce waɗannan kayan, da sauri Madina ta juya zuwa ɗakinta ta fashe da kuka, jikinta yana rawa ta ɗauki wayarta ta kira Hamid bugu ɗaya ya ɗauka yana cewa.
Amaryata kuma farin cikin Hamid ya aka yi.?
Abdulhamid.
Madina ta ambata cikin kakkausar murya, Hamid dake zaune saida ya gyara zama dan bai taɓa jin ta ambaci sunansa gabaɗaya kaitsaye irin haka ba, yace cikin bata dukkan matsuwarsa.
Meya faru ne Madina? naji muryarki wani iri.
Dole kaji muryata haka domin ka bani mamaki, yanzu fisabilillahi ban fi ƙarfin kayan daka saka a akwati ba, duk kuɗin ka ace akwati set ɗaya zaka yi mini sannan kaya ‘yan kaɗan, gashi kasa family sai ƙorafi suke yi acewarsu yadda na haɗu ga ilimi bai dace aga akwatina haka ba, sannan kace zaka bani mota ai kamata yayi ka saka key ɗinsa a cikin akwatin.
Haba Madina ya kike magana kamar baki san yadda na keta fafutukar faranta miki ba, kin kuwa duba kayan ciki gabaɗaya kuwa, to babu zanin daya gaza dubu sha biyar a ciki daga haka ne zuwa dubu ɗari biyu da wani abu fa, duk kayan ciki masu tsada ne, ai in baki yaba mini ba bai dace ki kushe mini ba, dan haka ni gaskiya abinda zan iya yi miki kenan. Maganar mota kuma ni ban iya ƙarya ba bazan saka key ɗin a ciki ba haka nayi niyya, idan kin zo gidana sai na baki.
Haka ma zaka ce ko.
To ya kike so nace miki, kinga Madina abinda kika gani shine iya ƙarfina, bazan yi abinda zan dawo ina dana sani ba bana ƙarya a rayuwata kuma…
Bai gama maganar ba ta kashe wayar ta jefar a gado tana matsar kwalla, Kausar da mai gyaran jiki da suka shigo suka tsaya suna kallonta dan duk sunji wayar da tayi, sauran ƙawayen suna can basu gama kallon akwatin ba, Kausar tace cikin taɓe baki.
Lallai sannu Madina ai wannan kukan daɗi kike yi, ni banga abun kushewa a kayan nan ba domin Hamid yayi matuƙar ƙoƙari, harda zinari fa a ciki wanda Habib ya faɗa mini kusan na dubu ɗari tatwas ne shi kaɗai, ni akwatin da aka kawo na aurena wlh ko rabin naki bai kai ba kuma haka muka karɓa muna murna, idan zaki aje rayuwar ƙaryar nan da zai fi miki, dan wlh aure da kike gani ba abin wasa bane rayuwar gaskiya da gaskiya ake yi a ciki.
Ai kinsan dani da ke akwai tazara a tsakaninmu, dan haka ni wannan kayan daya zuba bai mini ba wlh, dan yadda yake da arziki yaci ace yayi mini set biyu.
Hmmm gaskiya ki gode Allah Madina dan wlh zamanin aurena ni akwati biyu da kit na samu, a wannan zamanin da muke ciki na hannu baka hannu kwarya to ki godewa Hamid dan yayi ƙoƙari.
Cewar mai gyaran jiki, Madina ta tashi tsaye a fusace tana kama kanta.
Kunata wani yayi ƙoƙari kunsan adadin dukiyarsa ne, na fiku sanin waye Hamid, kuma yadda ya nuna mini wlh babu ƙaranta a lamarinta, dan haka kuja bakinku kuyi shuru.
Tana gama faɗa ta fice daga ɗakin, da ido suka bita mai gyaran jiki ta taɓe baki.
Gaskiya wannan yarinyar ba tada godiyar Allah, ƙawarki ce ita amma sam halinku ba ɗaya ba tana sa ɗaukar kanta da nisa.
Ga ta ga duniyar nan ai ya isheta riga da wando, kuma in dai namiji ne zata haɗu da shi wlh saiya gyara mata zama. Duk wannan gigiwar sai ya sauke mata shi
Cewar Kausar cike da jin haushin Madina dan sosai taji ɓacin rai ya kamata, waje ta samu ta zauna tana jan tsaki.
**
Hamid.
Yana zaune ne a office ɗin Habib na company motocinsa yaje dan su yi maganar bikin, a lokacin ne Madina ta kirashi tana yi masa wannan bayanin mara tushe wanda yasa ransa ya ɓaci sosai, bai taɓa zaton haka daga gareta ba yadda take nuna masa salaha ce ita kuma abin duniya bai dameta ba, bayan ya aje wayar ne ya ja tsaki yana duban Habib tare da bashi labarin abin da ta ce masa a wayar, dariya Habib yayi yana buga table ɗinsa.
Madina duniya, kasan fa yarinyar ɗiyar macece sai yadda aka yi da kai, dama tuni na hango maka wannan matsalar saboda suna da buri da yawa dan yayarta babban ɗan siyasa take aure, Kausar tasha faɗa mini labarinsu, dan haka tunda kasa ƙafarka saika ida wlh, yanzu tashi zaka yi kaje ka ƙara haɗa wani akwatin ka kai mata.
Kutt wlh babu abinda zan ƙara kaiwa, haba akwatin dana kashe sama da miliyan biyar shine ba zasu gode ba, a wannan karan zan nuna mata bata isa ta juya ni ba wlh, ni bana ƙarya a lamarina.
Ai na zata so ya rufe maka ido zaka yi mata duk abinda tace tana so. To bama wannan ba naji kayi maganar zaka bata mota to ita Sakina ina nata motar ko ka bata nata ne.
Wani sheƙeƙe Hamid ya dubeshi yana ‘yar dariya.
In bawa Sakina mota karan hauka ne ya cijeni, matar da bata da ilimi taya zata iya da mota, akwai motar dana aje musu a gida in zata fita anguwa, ko Hajiyarmu in zata fita driver yake jansu a ciki, dan haka ita ta isheta bazan yi asarar kuɗina ba tunda ba iya tuƙawa zata yi ba, Madina ma ganin ta iya driving ga kuma aikinta da zata riƙa zuwa yasa nace zan bata mota, kuma Sakina ba fita take yi ba sai tafi wata biyu bata je anguwa ba, dan haka in na bata mota kamar na ɓata kuɗina ne.
Hamid kana zaton hakan shine dai dai ko, to Wlh bari kaji muddun baka yi adalci a tsakanin Sakina da Madina ba Wlh baza ka ga daidai ba, Sakina ya dace ka fara bawa mota ita da kuke tare kafin Madina, idan baka yi wasa ba wannan son zuciyarka shine zai rusa maka gidanka Allah.
Ba amin ba, kuma na dai gama magana bazan bata mota ba saboda ina da dalili.
To in ba zaka bata mota ba ya zama wajibi ka bata wani abu da zai yi daidai da kuɗin motar da zaka bawa Madina, wannan shine adalci.
Hmmm sai dai fa kayi ni na gama maganata kuma….
Bai ƙarasa maganar ba saƙo ya shigo wayarsa, ya duba sai yaga Madina ce cikin sauri ya buɗe saƙon kamar haka.
_Hamid dana san haka zaka yi mini wlh da bazan taɓa yarda da maganar aurenka ba, domin ina da samari masu mugun kuɗin da suka fika amma haka na zaɓeka saboda ina sonka kuma ina kyautata zaton zaka yi mini duk abinda nake so, dan haka ni na fasa aurenka ka aiko a kwashe kayanka da kuɗin auren bana yi_
Hamid hular kansa ya cire yana duban Habib tare da cewa.
Wannan yarinyar ba tada hankali wai saƙo ta turo mini ta fasa aurena, idan ta isa Allah ya tsinan duk tsawon lokacin dana ɗauka ina tanadin aurenta tace haka.
Wani wawan dariya Habib ya kwashe dashi yana buga table ɗinsa.
Da alama taci kai, amma nasan dai faɗe take yi kawai dan ta rikita ka.
Habib bari naje na ganta mu sasanta dan bazan taɓa yarda da wannan mugun wasan ba, wlh har hantar cikina sai da ta kaɗa, yadda naje jin sonta a raina in tayi mini haka ai kasheni kawai zata yi da raina.
Dariya sosai Habib yake yi masa, Hamid ya miƙe da sauri ya mayar da hular kansa.
Daɗina da kai abinda ba lokacin wasa ba sai ka mayar dashi wasa, ni kaga tafiyata yadda duk nayi da ita zan kiraka a waya na faɗa maka, saboda daga can zan wuce gida.
Hamid yana gama faɗar haka ya fice da sauri, Habib dai dariyarsa yake yi sosai dan yayi mugun bashi dariya duk ya wani irikice lokaci guda daga tace ta fasa, wanda yasan ƙarya take yi kawai tana son hautsina masa lissafi ne kawai, shiko ya ƙosa ma ayi bikin a gama ya huta da wannan rikita rikatan.
Hamid yana isa ƙofar gidansu Madina ya shiga kiranta a waya, sai dai taƙi dagawa daga baya ma yaji wayar a kashe, hakan yasa ya ƙara zaucewa da tunanin Madina da gaske take yi, nan take ya kira Anty Aisha bayan ta ɗaga ya gaisheta kana ya soma magana.
Dama ina ƙofar gida na zo ganin Madina to ina ta kiranta taƙi ɗagawa daga ƙarshe ma ta kashe wayar, dan Allah kiyi mata magana ta fito.
Madina ba zata fito ba domin ana yi mata gyaran jiki ne, dan haka sai dai ka dawo anjima.
Anty dan Allah ki bata wayarki nayi magana da ita wai cewa tayi ta fasa auren saboda ban yi mata lefe yadda take so ba.
Gaskiya dai kam Hamid yadda muke zatonka bamu tunanin ganin kayan lefen haka ba, Allah ya rufa maka asiri ai sai ka nunawa duniya kana ƙaunar Madina kuma ta kayan lefene zaka yi haka, amma bari zan mata magana dan hakan ba zai sa a fasa ba tunda aikin gama ya riga da ya gama.
Kuyi haƙuri wlh abubuwa ne sai a hankali shiyasa, kin san hidimar biki yawa ne da shi.
To shikenan bari na kai mata wayar.
Daga haka ta kashe wayar ta wuce ɗakin Madina ta sameta fuska haɗe yaki yiwa kowa magana.
[7/5, 8:34 PM] Rahma Kabir: *ƘAZAMAR AMARYA*
Na
©®Rahma Kabir MrsMG.
Wattpad @rahmakabir
Page 8.
Aisha ta miƙa mata wayar tana cewa.
Hamid zai kiraki yanzu dan Allah ki ɗaga karki ɗauki lamarin da zafi, kibi komai a sannu tunda an riga da an kawo kayan.
Nifa Anty nama fasa auren.
Wannan kuma ƙarya kike yi, ashe bama sonsa kike yi ba da zaki ce haka. Amsa wayar gashi nan ya kira ma.
Madina ta amsa tana wani ɓata fuska kamar tana gabansa, koda ta ɗauki kiran bata ce komai ba Hamid yasan ita ce dan haka ya shiga yi mata magiya yana bara haƙuri, ita kuma sai wani kumbura take yi tana jan guntun tsaki, sosai hankalin Hamid ya tashi dan yana mugun sonta, cikin yanayin lallashi yace.
Madinar Hamid kiyi haƙuri In Sha Allah nayi miki alƙawari in kin haihu zan sake yi miki wani kayan lefen ke da babynmu, sannan yanzu ki faɗi irin motar da kike so sai in baki ita, in ma babu a cikin motocin sayarwana zan sa a kawo miki.
Nan take Madina ta saki wani shu’umin murmushi, kana ta sanar da shi kalar motar da take so cikin muryar shagwaɓa, sai da gaban Hamid ya faɗi dan motar kusan miliyan ashirin da uku tace tana so, bawai baida kuɗin saye bane kawai dai shi bai son rayuwar ƙarya dan ko shi motocinsa da yake hawa babu wacce ta haura na miyar goma, amma ya zai yi tunda yana so ta sauko dole yayi amfani da wannan damar ya amince mata, amma fa har ga Allah baya jin zai siya mata motar data zaɓa, cikin murmushin yaudara yace.
In dai ita kike so karki samu damuwa zan saka a kawota In Sha Allah da zarar kin zo gidana zaki samu motarki dan kinfi haka a guna, yanzu ma dan za a ɗauki lokaci kan a kawo ne amma dana ce kafin biki za’a kawo miki.
Dagaske kake zaka siya mini ita.?
Dagaske nake yi Madinar Hamid, ni dai ki daina fushi dani.
Uhum ai shikenan komai ya wuce nagode Hamid ɗina Allah ya barmu tare.
Ameen ya amsa yana murmushi da haka suka yi sallama ta kashe wayar tana buga tsalle dan murna, sai dai kawayenta suka bita da ido, Kausar tace.
Hmmm Madina kenan har kin sauko daga dokin fushin saboda zai siya miki mota.
Malama bana son sa ido ki rabu dani ehe.
Cewar Madina tana murguɗa mata baki, Kausar ‘yar dariya tayi tana yi mata addu’ar shiriya, daga haka kuma ta warware suka cigaba da shirye shiryen bikinsu.
Hamid koda ya sanar da Habib yadda suka yi, dariya yayi yana cewa.
To kai yanzu motar zaka siya mata kenan baban soyayya.
Kai dalla rabu da ita hauka nake yi ko karan hauka ne ya cije ni, motar miliyan uku nayi niyya kuma ita zan bata wlh, in tazo gidan taga motar ai bata isa tace ta fasa auren ba tunda an ɗaura.
Ai nayi zaton so ya rufe maka ido zaka biye mata ka siya.
A’a fa bazan zo nayi abinda daga baya yazo yana damuna ba.
Haka suka cigaba da tattaunawa daga bisani suka yi sallama.
….
Saura kwana biyu biki aka kawo kayan amarya, Sakina rufe kanta tayi a ɗaki bata yarda ‘yan uwan amarya sun ganta ba, yaya Umma da yaya Falmata sune suka dinga hidima dasu, ɗaki ciki uku aka bata kamar na Sakina da take amfani da shi nata da yara, ɗakin Hamid shine ya raba tsakanin ɗakunansu, na Madina hannun dama yake na Sakina gefen hagu wanda nanne ɓangaren kitchen yake, ɗakin kusa da Hamid nan suka saka mata kayan gado, ɗaki na gaba suka zuba mata kujerunta dan yana da girma sai ya zama kamar falo, ɗaki na gaba kuma tarkacen kayan kitchen da basu samu jerasu duka a kitchen ɗin ba, duk da Sakina ta kwashe rabin kayanta ta basu guri tunda kitchen guda ɗaya ne, dole ta zuba sauran kayan a ɗakin Mufeeda. Su Asma sun zo suma da ‘yan uwansu sai baza surutu suke yi da yada magana, haka dai ‘yan jere suka gama gyaran ɗakin amarya suka tafi da magana a bakinsu.
Duk da gidan Hamid baida makusa kuma yana da girma ya isa mata biyu su zauna, amma sai da ‘yan uwan Madina suka kushe gidan akan yayi kaɗan mata biyu su zauna, kayan Madina duk a takure suke, mom ranta yayi mugun ɓaci amma ya zata yi tunda aikin gama ya gama kuma Madina tace taji ta gani zata zauna a gidan, shiyasa tace a bar maganar kar Madina taji tunda ita taso haka, shiyasa suka yi shuru da maganar akan in Madinar taje ta gani ita tasan yadda zata yi dashi akan ya sauya mata gida.
****
Ranar ɗaurin Aure.
Sakina ba dan ranta na so ba tayi kunshin jan lalle yankan seletep da kitso wacce matar yaya Hamza ce tayi mata, yaya umma ce ta matsa mata akan dole sai tayi shi, duk wani shirye shirye suna ta yinsa a tare har kawo ranar ɗaurin aure, ganinta a cikin ‘yan uwa yasa ta ɗan samu natsuwa damuwar Hamid ya ragu sosai a ranta. Da wuri ta shirya yaran su duka cikin ankon shadda da babansu ya ɗinka musu, mazan riga da wando da malum malum daya sha aiki, sai matan dogayen riga suma sun sha nasu aikin, itama ta saka leshi ta fito fes duk da taƙi yarda ayi mata kwalliyar zamani wacce ɗiyar Yaya umma taso yi mata, yara mazan sune suka bi babansu ɗaurin aure. Sakina ta fito falo sai kamshi take zubawa ‘yan uwa sunata mata guɗa, murmushi kawai take zubawa amma na ciki na ciki dan wlh sosai take jin ba daɗi a ranta na ƙarin auren, wanda tasan kishi ne da ya zame mata alaƙaƙai, duk da bata yi gayya ba amma mutane sunyi mata kara domin in dai aka ce biki na gidan masu hannu da shuni ne to wanda ma ba a gayyata ba sai an ganshi.
Ɓangaren ango tun zuwan su yaya Umma ya tattara ya koma gidan su Hajiya, rabon da Sakina ta saka shi a ido tun shekaran jiya, ta san dai yayi mata waya jiya ya tambayeta ko akwai abun da suke buƙata, daga nan shikenan dan koda zasu je taron mothers day da momyn Madina ta shirya bai faɗa mata ba sannan ma ba wanda ya gayyaceta, itama bata saka a ka ba dan ko ance taje ba zata je taga kayan haushi ba. Tunda mazan da suke tsaye farfajiyar gidansu suka watse tasan an tafi ɗaurin aure, dan haka a wannan lokacin ambaton Allah kawai take yi a zuciyarta ko zata samu salama. Ƙarfe sha ɗaya da rabi Asma da Kubura tare da wasu ‘yan uwansu mata suka zo gidan suna rangaɗa guɗa an ɗaura auren Hamid da Madina, su yaya Umma suka taya su yin guɗar suna sanya alkhairi, Sakina kuwa dariyar yaƙe take yi tana ambaton barka barka Allah ya sa mutu ka raba, Asma tace.
Yo ku ana ta nuna komai a tv tashar Sahad ba zaku kunna ku gani ba, kun mayar da gidan biki sai kace gidan mutuwa, ko da yake nan sashin dannen ƙirji ne ƙila kuna taya ta jimami. Uwargida ran gida yanzu girma ya kama ki, dole sai kin toshe kunne kin rufe idonki da kawaici saboda amaryar zamani ce zaki ga amarci kala kala.
Asma wlh tayi komai zamaninta ne nima na ci nawa a baya, in dai Hamid ne na bar mata shi har tsawon wata guda suci amarci susha romon soyayya. Wanda nake fatan a cikin lokacin ta ƙunsa tsarabar juna biyu musha suna nan da wata tara In Sha Allah
Maganganunta yayi matuƙar burge ‘yan uwanta, sai suka saka guɗa suna shewa matar yaya Hamza tace.
Amma Sakina kinyi bajintar da ba ko wace mace zata iya ba, ina jinjina miki uwargida a gidan Hamid ko anƙi ko an so girman naki ne.
Faɗi ki ƙara yaya Falmata, to me akai akayi kishi? balle Hamid daya zama ni ni na zama shi, an daɗe da gauraye ruwan jiki.
Sakina ta faɗa tana murmushi, su Asma sai sakin baki suka yi suna kallonsu, sun zo dan su ƙunsa mata haushi amma sai suka ga ta dama su ta shanye tamkar ta shiryawa zuwansu.
Mu dai mun san dole ayi kishi yayanmu, mutum ga kyau ga kuɗi ga ƙuriciya sannan ya auro ‘yar tsaras jiki duk madara.
Hmmm koma zuma ce zata zo ta gama lokacinta mu dawo dai dai Asma, kuma sauran Hamid zata samu, ko kin manta haihuwa huɗu nayi da ɓari biyu, ai na gama kwashe duk wani kayan alatunsa barbaɗe na rage mata.
Kubura ce ta ja wani dogon tsaki tayi gaba, Sakina ta rakata da dariya Asma ma bata kuma magana ba ta fice tare da sauran matan da suka shigo, sai a sannan ne Sakina ta sauke nannauyen ajiyar zuciya ta samu guri ta zauna sai ta fashe da kuka dan dauriya kawai tayi ta basu amsa, da sauri Falmata ta zo tana cewa.
Ya da kuka kuma? bayan kinyi abinda ya dace, Dan Allah kiyi shuru ki cigaba da dauriya watarana sai labari.
Wlh abin da ƙuna a zuciyata dannewa kawai nake yi.
To ai sai kiyi ta yi idan kika bawa makiyanki dama suka san kinyi kuka dariya zasu yi miki, nasan da zafi kishiya amma haƙuri zaki yi ki jure, dan hakan yana cikin ƙaddararki.
Cewar Yaya umma, Sakina ta ɗago ta goge idonta tana cewa.
Na daina bari na shiga na sauya kaya mu je sashin Hajiya muyi mata murna dan kar tace kishi yasa ban je ba.
Babu inda zaki wlh, salon kije su sakar miki maganar da zai ƙara miki baƙin ciki, yi zamanki bayan kwana biyu kya je in komai ya lafa.
Cewar Falmata, nan duk ‘yan uwa suka ce tayi zamanta ai ita ya dace azo ayiwa murna da ban haƙuri, kuma dole ta rage jin tsoron Hajiya da ‘yan uwan Hamid dan ta riƙa kwatar kanta tunda ba su da mutunci, ganin sun taru mata yasa ta fasa zuwa.
…
Hamid
Tunda aka ɗaura auren yake cikin wani tsananin farin cikin da ba zai misaltu ba, yana tsaye tare da abokansa suna karɓan gaisuwa daga mutane, bayan komai ya lafa suka shiga gidansu amarya domin suyi gaisuwa kafin su wuce, a falon Momy aka yi musu masauki nan suka gsisa da mutane kafin daga bisani suka fito farfajiyar gidan suka tsaya dan jiran amarya ta fito suyi hotuna, ba jimawa Madina ta fito tare da ƙawayenta tayi shigar farin leshi da golden brown ba ƙaramin kyau tayi ba, Hamid ko tunda ya ganta sai washe baki yake yi dan yaga yau tafi ko wace rana yi masa kyau, tana matsowa kusa dashi ya rusuna itama ta rankwafo suna jin numfashin juna Hamid yace mata.
Madinata kin zama mallakin Hamid.
Murmushi tayi itama tace masa cikin raɗa.
Nima yau ka zama Hamid ɗin Madina na har abada.
Da sauri Hamid ya dago yana zare ido da murmushin yaƙe saboda wani irin wari daya sallamowa hancinsa, da kyar ya iya haɗiye miyau yana baza murmushin dole dan tuni cikinsa ya soma murɗa masa, saboda ba dama yaji wari sai ya nima kassara masa farin cikinsa ko ya haushina masa ‘yan hanjinsa, haka ya basar bai sake yi mata magana ba dan kar ya shaƙi warin bakinta. Haka aka shiga ɗaukar hotuna suna baza style daga bisani suka yi musu sallama akan sai sun zo ɗaukar amarya daga can kuma a wuce dinner. Hamid dai tunani ya faɗa akan dama Madina tana da warin baki bai sani ba ne ko kuma yau brush ne bata yi ba, sosai lamarin ya dama masa lissafi, tunda yake da ita kuma bai taɓa jin wannan warin ba ko dan basu taɓa yin magana a kusa sosai bane, bayi da amsa kuma babu wanda zai iya gayawa wannan maganar dole sai dai ya danne a zuciyarsa, da lissafin yadda zamansu zai kaya in dai kuwa haka bakinta yake wari.
[7/6, 5:56 PM] Rahma Kabir: *ƘAZAMAR AMARYA*
Na
©®Rahma Kabir MrsMG.
Wattpad @rahmakabir
Page 9.
Madina tunda ta wayi fari ta manta bata yi brush ba, sai ta kama ciye ciyen abubuwa shaf ta manta dan ko data zo wanka sauri sauri tayi saboda ana jiran ta fito ayi mata kwalliya, shiyasa ta manta da yin brush dan dama ba tun yau ba ta saba haka, ita da gari yana wayewa taga abunda take sonci ba wanke baki zata hau cinsa, sai in tazo wanka ne take wanke baki, yau dai kam ta sha’afa ga ango yasha ƙamshin bakinta, har suka rabu bata gano ma yaji ba itama bata ji ba saboda tsabar busy da zumuɗin auren. Amarya ansha hidima dan zuwa yamma ta gayi liƙis kamar anyi mata duka, ganin magrib ya kusa yasa anty Aisha ta haɗa mata ruwan wanka mai zafi sosai danta gasa jiki tace ta shiga tayi ta haɗa da yin brush da alwala, kana ta fito ta shirya dan Habib ya sanar da Kausar ana yin sallar magrib zasu zo ɗaukar amarya, dan dole Madina tayi wanka amma da ta ra’ayinta ne ba zata yi ba dan ita bata ga dattin da jikinta yayi ba, haka ta shiga tayi wanka da ruwa mai ƙamshi dan Aisha ta sanya mata turaren wanka, ta yi wanka da brush sai a lokacin ta tuna ma yau kwata kwata bata yi shi ba, da kuma ta wanke bakin ita kanta taji daɗinsa, sai ta yi alwala ta fito ta shirya cikin wani rigar gown ɗin amare light brown da ratsin cream color a jiki, nan aka yi mata kwalliya sama sama dan cewa tayi bata so, ganin sun matsa tace ayi kaɗan kar a cika mata fuska kamar na ɗazun, bayan ta idar da sallar ne aka yi mata ɗauri, nan amarya ta fito fes daga gani kasan shigar dinner ce, bayan an gama mata shirin sai Anty Aisha ta kama hannunta suka isa ɗakin momy akan za a yi mata faɗa, nan ta zauna akan dadduma ga iyaye nan daga ƙawayen momy sai ‘yan uwanta, ko wanne ya shiga faɗar albarkacin bakinsa, faɗa ne dai na yau da kullun da iyaye suka saba yiwa duk ɗiyarsu da za a kaita gidan miji, Hajiya Sa’a ce ta kalli momy tana cewa.
Ƙawata baki ce komai ba kinyi shuru ko har kin fara kewar babyn naki ne.
Hmmm kewa ai ya zama dole gidan zai rage sai ni kaɗai da ‘yan aiki, kuma yanzu ma ni me zance bayan kun gama yi mata faɗar, sannan tun biki na saura wata nake yi mata nawa faɗar.
Dik da haka kice wani abu matsayi ki da uwa a gareta.
Cewar wata ƙanwar momy, guntun murmushi momy tayi.
To Allah ya sanya alkhairi ya baku zaman lafiya yasa abokin zamanki ne na har abada, sai dai tunin da zan ƙara yi miki ban yarda ki zauna kishiya ta taka ki ba, sannan kina da gata da ƙima a gidanku muddun Hamid yaso cin zarafinki bance ki saurara masa ba, domin gidan aure ba gidan bautar miji bane gida ne na jin daɗi da farin ciki da ko wani magidanci ya kamata ya bawa matarsa, kinga dai yadda na zauna da mahaifinku har ya bar duniya yana daraja ni domin banyi saken daya raina ni ba, kuma a kishiyoyina babu wacce na ragamawa balle taga damar yi mini iskanci gashi kuma mun rabu lafiya da kowa, dan haka ki tuna ke mai daraja ce babu wani wanda ya isa ya takaki ki kyale shi. Uwarsa kuma in ta ɗauke ki a ‘ya to kema ki ɗauke ta a uwa, in kuma ta nuna son kanta ta nima takura miki ki nuna mata ke ‘yar zamani ce bance ki ragawa kowa ba wlh.
Nan fa mutanen cikin ɗakin wannan ya kalli wannan, wasu sunyi mamakin maganganun momy amma wasu basu yi ba sanin halinta, dan haka suma suka ɗaura da nasu faɗar, daga bisani aka sanar dasu ‘yan biko sun zo, nan aka tasa ƙeyar Madina aka fito da ita falo, sun kawo abinci kala biyu waina da miya da jelof ɗin shinkafa ga kuma kular farfesun kaza daban, abu dai na girma da arziki aka yi shi, su Asma dasu aka zo ɗaukar amarya zai wani kauɗi da iyayi suke yi, ba wani ɓata lokaci aka basu amarya suka rankaya zuwa gidan Hamid.
*****
Sakina.
Sunyi shagalinsu cikin kwanciyar hankali kowa ya watse aka bar ta daga ita sai su yaya Umma, sunyi ƙoƙarin gyara gidan kafin a kawo amarya, sun sakarwa falo turaren ƙamshi ko ina yayi tsaf kamar ba a yi shagali a falon ba, Sakina ta sake yin wanka ta saka atamfa ɗinkin riga da siket tayi ɗauri irin na Maryam Babangida, ba kwalliya tayi ba amna tayi kyau daidai misali, bayan ta idar da sallar magrib ne ta ɗauko sabon mayafinta ta yafa suka fito falo suka zauna dan tarban amarya wanda Hamid ya kirata ya sanar da su sun taho, yanata mitar a gyara falon kar akawo amarya gida kaca kaca da to kawai Sakina ta bishi ta kashe wayar. Lokacin da suka ji ƙarar shigowar mota hakan ya tabbatar da amarya ta iso, su yaya umma suka fita tarbota ita ko Sakina ta kame a cushing tana jiran shigowarsu dan komai yaya umma ta tsara musu basa so suyi abinda za a tafi dasu a baki, cikin fara’a suka yi musu iwo har cikin falo, basu tsaya anan ba dan su Asma ne jagoransu, sai da suka sada amarya a ɗakinta aka zaunar da ita a bakin gado kafin suka shiga rangaɗa guɗa ana yiwa amarya kirari, sun ɗauki kusan minti sha biyar a ɗakin kafin suka fito da amarya falo zuwa gurin uwargida, a nan wasu suka zauna a kujeru wasu kuma suka tsaitsaya, suka gaisa cikin mutunci kana ƙanwar momy tace.
To uwargida ga amana mun kawo miki da fatan zaki riƙe, Madina dai yarinya ce duk abinda aka ga tayi sai ayi mata uzuri, Allah ya haɗe kanku ya kauda fitina.
Duk mutanen falon suka amsa da amin, Yaya Umma tace.
In Sha Allah mun karɓi wannan Amana Allah ya kauda shaiɗan a tsakani.
Nan ma duk suka amsa da Amin. Sakina ta ɗaura da cewa.
To Amarya Allah ya sadamu da alkhairinki ya bamu zaman lafiya, yasa nan da wata tara a kuma wani taro haka kin haifo mana ɗan Hamid.
Nan fa Yaya Kaltume ta ɗauki guɗa wasu mata suka taya ta, wasu kuma suna dariya tare da ambaton amin, haka aka yi komai cikin mutunci ba tare da wani damuwa ba daga bisani ne aka ce su fito za a wuce dinner, sai suka fice sunata faɗar maganar Sakina tana da sakin fuska da alama ba tada matsala, bayan tafiyarsu ne yaya umma tace.
Ada in an kawo amarya, uwargida kan yi mata kyautar turmin atamfa ko wani abu mai kyau, amma banda yanzu da lamura suka lalace.
Yaya ko a yanzu ma ba za a rasa waɗanda suke bayarwa ba, ni dai sisina ba zai yi ciwo ba salon na bata ace na yi mata kyautar mugun abu, kunsan mutane da ƙirƙirar matsala, a tsakanin kishiyoyin zamanin nan kullun cikin zargin asiri suke yiwa juna duk da akwai masu yi.
Haka ne, to Allah ya shiga tsakanin nagari da mugu.
Cewar Falmata, duk suka amsa da amin sai yaya umma tace.
Sakina ɗazun naji kin ambaci kin bawa amarya wata guda, faɗa kika yi ko kuwa da gaske hakane.
Wlh yaya umma da gaske nake yi dan tuntuni na faɗawa Hamid kuma yaji daɗi sosai ya amince.
Anya kina da hankali kuwa Sakina? an faɗa miki ana yiwa namiji irin wannan riƙon sakainar kashin ne, yanzu fa lokaci ne da zaku kafa gasar kula dashi ko wa ya iya allonsa ya wanke.
Cewar yaya umma tana tsureta da ido, Sakina tayi murmushin takaici.
Yaya Umma mai ɗaki shi yasan inda yake yi masa yoyo, ki barni da Hamid shi ba irin mazan nan bane da za ayi wa wannan rawar ƙafar, ya dai je ya ji da amarya ni kuma na basu filin wasa su buga yadda ransu yake so.
Hmmmm shikenan ai tunda kin riga da kin ƙaddamar da son ranki sai dai mu koke gaba, amma duk da haka ba zama zaki yi ba zaki samu kayan gyara ki tayar da komaɗa ki zaburar da kuzarinki ta yadda kina amsar girki ya gane cewa kema da sauranki.
Cewar Falmata, nan yaya umma ta gasgata wannan sharawa suka shiga sanar da ita yadda zata yi komai, Sakina ta baza kunne tana saurare, da yake Falmata ‘yar Maiduguri ce ta san harkar kula da miji da gyaran jiki, hakan yasa ta ɗaura Sakina akan seti da shawarwari, tace kuma musamman zata aiko mata da mai gyaran jiki bayan an kwana biyu tayi mata koda na kwana uku ne, sannan zata yi mata oder ɗin tsumin ‘yar gata da kazar amare wacce Ummu sultan take haɗawa, ko su kaɗai tayi amfani dasu ta gama haɗa kanta, sosai Sakina taji daɗin shawarwarinsu dan ba ƙaramin abubuwa suka tunatar da ita ba da kuma ƙara haska mata yadda namiji yake son mace ‘yar kwalisa, wanda tana kyautata zaton yana ɗaya daga cikin abinda yaja ra’ayin Hamid ya auri Madina, sannan itama tasan tana da sakaci wajen gyara, dan maganin mata bai dameta bane koda kuwa ita ta haɗa da kanta bata damu tasha ba, amma yanzu dole ne zata dage damtse dan in tayi sakwa sakwa to tana ji tana gani Madina zata amshe mata miji, ta san ba tada damuwa da girki dan ita gwana ce, kuma in ta nan ne ta ciri tuta a gurin Hamid, amma duk da haka zata ƙara dage damtse dan in kana da kyau aka ce ka ƙara da wanka.
….
A gurin Dinner taro yayi taro wuri ya tumbatsa da al’ummar Annabi, an ƙawata gurin sosai dan da ganin hol ɗin sai wanda yaci ya tada kai zai iya kama shi, saboda an tanade shi domin manyan mutane, Hamid yana zaune a gefen Madina a wani kujera na alfarma, suna zaune gabda juna dan haka yasa in Madina zata yi masa magana irin na raɗa sai ya kauda kansa cikin dabara ya kafa mata kunnensa dan kar ya shaƙi warin bakinta daya ji ɗazun, sosai yake fargaba da hakan saboda kar ya bata farin cikin da yake ciki, a haka aka yi taro aka gama cikin natsuwa da burgewa sun sha hotuna sosai, an kafa tarihi a dinnar Hamid da Madina, saboda mutane da yawa sunce sun jima ba suga shagalin dinner daya yi matuƙar burgesu ba irin wannan, daga nan ango ya taho da amaryarsa a mota zuwa gida, suma ‘yan kawo amarya daga wajen taro kowa ya watse.
Lokacin da Hamid suka dawo babu kowa a falon da alama duk sunyi barci, ɗakin Madina suka wuce ta zauna a gefen gado yana ce mata.
Tashi zaki yi ki watsa ruwa sannan ki ɗauro alwala kiyi shirin barci, bari naje na shirya nima in zo.
Da to ta bishi kana ya fito tana cewa a hankali.
Wlh babu wankan da zanyi wanda nayi ɗazun ya isa, haka kurum mura ya kama ni, ai ba wari nake yi ba banda ƙamshin turare.
Tana faɗar haka tare da shinshina hammatar rigarta, bata ji wani wari ba sai ƙamshi, hakan yasa ta miƙe ta cire kayan duka ta isa waldrob ɗinta ta ɗauki kayan barcin da yaya Aisha ta ce mata ta aje, riga da wando ne masu kyau, sai ta saka kana ta wuce toilet tayi alwala ta fito ta saka dogon hijab data gani waldrob ta zauna zaman jiransa.
Hamid yana fita falo ya zauna ya kira Sakina a waya cikin barci taji kira, sai ta ɗauka yace ta fito falo, ba musu ta ce to sai ta fito saye da kayan barci ta saka hijab a samansu, ta zauna tana dubansa.
Kun dawo lafiya da fatan an watse taro lafiya.?
Alhamdulillahi komai ya tafi a tsare kamar yadda ake so, fatan dai Allah ya bamu zaman lafiya gabaɗaya.
Ameen ta amsa masa kana ya ce.
Ina so ki haɗa mata tea mai kauri a cups biyu sannan ki haɗo da plate ɗaya. Sannan ni karki cika mini sugar, ita kuma kisa mata yaji sosai dan nasan Madina akwai son zaƙi.
To ko na kawo musu ruwa a flacks ne da sauran kayan sai ku haɗa da kanku.
Bance ba! ki dai haɗo mana, ko so kike dole sai munyi aiki bayan gajiyar da muka kwaso.
To tace masa sai ta miƙe ta wuce tana shanye hawayen daya taru mata, wato saboda ya raina mata hankali yasan tayi barci amma ya taso ta dan ta yi masa hidima, madadin shi ya yiwa kansa tunda ba abu ne mai wuya ba, salon dai ya ƙirƙiri abinda dole sai ya hana ta barci da damuwarsa.
[7/8, 7:44 PM] Rahma Kabir: *ƘAZAMAR AMARYA*
Na
©®Rahma Kabir MrsMG.
Wattpad @rahmakabir
Page 10.
Haka Sakina ta shiga kitchen ta haɗo masa komai ta kawo falo ta aje tayi tafiyarta ɗaki ta kwanta dan huta gajiyar bikin. Da Hamid ya fito yana shirin kwala mata kira sai ya hango tire da komai kan center table, kwafa yayi yana girgiza kai ya wuce ya ɗauka ya juya zuwa ɗakin Madina, ya samu tana kwance ya saki murmushi.
Ki tashi muci abinci sai mu rama sallar Isha’i da nafilar godiya ga Allah akan kasancewarmu guri guda.
To tace masa ta sauko suka zauna a madaidacin carpet da aka saka a gaban gadonta, nan Hamid ya miƙa mata ruwan tea ta amsa ta fara sha dan sosai take jin yunwa, shi kuma ya ciro kazar da ya siya musu a hanya ya baje shi a plate suka fara ciyar da junansu, Madina tun tana nuna kunyarta harta ta saki jiki ta ɗirki kazar nan dan har sai da ta fishi ci, ita fa in abu yayi mata daɗi zaƙewa take yi sai taci ya kai mata wuya kafin take sararawa, Hamid yaji ta burgeshi sosai dan yasan ba kowace amarya ce take yarda taci kazar amarcinta ba amma yaga Madina ba wani fulako taci kayanta, bayan sun kammala ya miƙe ya ɗauraye baki a bayinta ya fito itama tayi kamar yadda yayi suka matsar da tire ya jasu sallah, bayan sun idar ne yayi duk addu’ar da ya kamata ango ya yiwa amaryarsa daga bisani ya miƙe yana cewa.
Bari nayi brush ina zuwa.
To tace masa ta miƙe tana cire hijab ta aje tare da dadduma sai ta haye gado babu zancen wanke baki kamar yadda shi yace zai yi, a ganinta ɗazun da yamma tayi brush da zata yi wanka, duk da bawai babu brush ɗin bane, akwai sabo a toilet ɗinta har biyu da maclean da aka aje mata su, Hamid ya dawo ya sameta ta kwanta ya kashe musu haske ya kwanta a gadon yana cewa.
Madinata yau zaki bani tukucin kazar da kika cinye mini.
Wani irin tukuici bayan tare muka ci. Nifa barci nake ji dan duk jikina ciwo yake mini.
Bari nayi miki tausa wata ƙila zaki fi jin daɗin barci.
Yauwa kamar kasan ina so dan so tari ina saka mai aikinmu ta matsa mini ƙafa har nayi barci.
Ta faɗa tana gyara kwanciyarta tare da lumshe ido, ita fa bata kawo Hamid zaiyi wani abu ba a ganin daga ita har shi a gajiye suke, a hankali ya fara yi mata tausan tun yana yi a hankali har ya sauya salo ya shiga aika mata da zafafan saƙonni, da yake tasha maganin gyara tuni ya kunna mata nau’urar dake sadar da zumuncin ƙauna, daga nan kuma suka lula duniyar masoya duk da Hamid yana ankare da warin daya ji ɗazun a bakinta, dan haka duk wani sako daya ke aika mata bai yarda sun haɗa bakinsu ba, ita kuma da alama tana son sumbata wanda ko a film taga ana yi yakan dasa mata wani shauƙi, ganin fa bazai yi mata ba yasa ita da kanta ta nima hakan, ba yadda zai yi dole ya amince duk da yaji ba wani wari amma kwakwalwarsa tana hasko masa warin daya ji ɗazun, dauriya kawai yake har dai taci galaba akansa ta lular dashi wata duniyar.
A wannan dare Hamid bai sarara mata ba sai da ya tabbatar da hakkarsa ya cimma ruwa, dan ya sameta a cikakkiyar budurwa kuma Alhamdulillah komai yaji yadda yake so, soyayyarta ya ƙara ninkuwa a zuciyarsa fiye da da, ji yake kamar ya mayar da ita jikinsa su zama abu guda dan tsantsar ƙauna. Itama sosai ta kuma dulmiya cikun kogin ƙaunar Hamid duk da tasha wuya amma kuma babu abinda ya rage daga son da take yi masa sai ma ninkuwa da yayi, tasan Hamid shi ne dai dai irin mijin da take buri a rayuwarta gashi ta same shi a yadda take so, haka suka lula barcin gajiya har sai da aka yi sallar asubahi gari ya fara haske kafin Hamid ya farka, yana ganin gari ya waye ya tashi ya zauna yana kallonta tare da sakin murmushi gani yake Madina itace cikon farin cikin rayuwarta, tunda ya sameta yasan ya samu cikon addininsa, haka ya tashi ya shiga toilet ɗinta ya haɗawa kansa ruwa ya fara gabatar da wankan tsarki kafin wankan sabulu ya biyo baya, ya fito ya tada sallah, yana zaune a dadduma ya idar, Madina ta farka tana ambaton.
Wayyo Allah na.
Tare da miƙa, Hamid yayi saurin shafa addu’a ya miƙe yana dubanta.
Madina Aljannar duniyata kin farka.
Waigowa tayi tana dubansa sai ta saki murmushi bata iya cewa komai ba domin tuni miyau ya cika mata baki.
Ki tashi ki tsarkake jikinki kiyi sallah domin gari ya waye.
Ka taimaka ka haɗa mini ruwan wanka.
Ta faɗa da miyau a bakinta, nan take Hamid ya ji wani kyankyami ya kamashi tare da tuna fa jiya sun haɗa bakinsu guri ɗaya, bai iya cewa komai ba ya juya ya shiga toilet ɗin, miyau ya fara tofarwa kafin ya iya haɗa mata ruwa mai zafi ya fito yana ce mata.
Ki tashi kije kiyi, bari naje ɗakina ina zuwa.
Kai beb na ɗauka kai zaka yi mini wankan har ka taya ni na shirya, ko ba haka naga masoya suna yiwa kansu ba.
Ta yi maganar har miyau na fitowa a bakinta, sai ta juya gefen gadonta ta fetsar da miyau a jikin bango, Hamid ya ji zuciyarsa tana niman tashi da sauri yayi hanyar fita kafin ta jagula masa lissafi yana cewa.
A cikin labarin hikaya kika san wannan, ki tashi ki zama jaruma kamar ko wace mace ki shirya gani nan zuwa.
Ya buɗe ƙofar ya fice yana jin ransa yana so ya ɓaci da ita, dan gani yake ƙazanta ce a fetsar da miyau jikin bango, ko masu ciki in suna tara miyau abu mai zurfi suke samu su zuba ƙasa suna sanya miyau a ciki, amma kuma wani ɓangare na zuciyarsa yana yi mata uzuri ƙila abinda ya faru jiya shine ya sa ta tara miyau, da tunanin ya shiga ɗaki ya kwanta dan faɗa mata kawai yayi zai dawo amma yafi so ya kwanta yayi barci shi kaɗai baya son wani ya raɓe shi saboda yayi barci mai kyau. Madina da mamaki tabi ƙofar daya rufe bata yi tsammanin duk irin son da Hamid ke yi mata ba bazai iya yi mata wanka ba, ta ɗauka ruayuwa zata yi da shi tamkar mijin novel data ke jin labarin hikaya amma sai abin ya zama ba haka bane, kenan duk masu rubuta miji ya yiwa matarsa wanka a daren farko zance suke yi dan su ƙarawa labarinsu armashi, ashe hakan ba mai faruwa bane sai dai a duniyar turawa ko larabawa ake yin haka, tuntuni tana hasasho irin soyayar da zasu zuba ita da Hamid saboda tsantsar son da yake nuna mata, ashe bai kai yadda take tsammani ba, guntun tsaki tayi ta miƙe tana jan ƙafa ta shiga bayi, ta jima tana gasa jikinta daga bisani tayi wanka ta fito ta shirya sauri sauri ta yi sallah ta koma ta kwanta, ga sumarta duk a jiƙe ta tsaya ta tsane shi ta gyara ya ga gareta, saboda barcin data ke ji sosai, haka barci ya ƙara ɗaukarta mai nauyi.
….
Sakina tunda suka tashi suke hidima a kitchen na abinda zasu karya, kunun tsamiya suka dama sai ƙosai da Yaya Falmata ke soyawa, suna aiki suna hira gwanin sha’awa, yaya umma tace.
Sakina me za a dafawa su Hamid ne naga gari ya waye sosai ana niman ƙarfe tara.
Hmmm yaya Umma bai fito yace ga abinda zan dafa ba, kin san halinsa ba ayi masa gwaninta, na zo na dage na haɗa abu yace bashi suke so ba.
To ko zaki buga musu ƙofa ki tambaya ko ki kirashi a waya.
Waro ido Sakina tayi tana dafe ƙirji tare da cewa.
Ki rufa mini asiri kar kisa da sassafen nan ya rufeni da masifa, duk lokacin da suka tashi ya sanar da abinda yake so na dafa musu.
Dariya Falmata ta saki tana cewa.
Ya kamata ki rage wannan tsoron da kike yi masa, haba Sakina kina abu sai kace ‘yar shekara sha takwas, kin kai munzalin da ya dace ace Hamid yana shakkarki fa.
Um um fa Falmata ban yarda da wannan zancen naki ba, gwara su cigaba da tafiya a haka, domin ba a samun aljanna cikin sauƙi, ban yarda ki ɗaurata akan keken ɓera ba.
Cewar Yaya umma, Falmats tace cikin murmushi.
Yaya umma wlh maza irin su Hamid sai mace ta busar da idonta ta nuna musu iyakarsu kafin ake zama daidai, yanzu kina nufin ta cigaba da jin tsoronsa haka yana wulaƙantata a gaban kishiyarta, gaskiya ya kamata Sakina tasan kanta cewar itama macece mai daraja.
Ki bata duk tsawarar daya dace amma ban yarda tayi fito na fito da mijinta ba, domin girma ne Allah ya bashi bai dace ace ta daina jin tsoronsa ba.
Sakina dai tana jinsu tasan yaya umma ba zata taɓa yarda ta ɗauki shawarar Falmata ba, domin ita komai nata cikin lalama da biyayya take son ayi shi, wanda kuma ita Sakina ta fara tunanin bin hanyar da Falmata ta sanar mata dan taga ganin Hamid Zuma ne dole sai da wuta, a yanzu bata jin zata ɗauki wulaƙancin da zaiyi mata gaban kishiya sai dai duk abinda zai faru ya faru ɗin.
Miji goma ai ba uba goma bane.
Ta ambata a cikin ranta wanda tasan iyaka bai wuce ya saketa ba, kuma tuni ta fara shiryawa hakan dan ba zata zauna ya ɗaura mata cutar da zai halakata ba ko ya nakasata tana ji tana gani, Allah ma yasan tayi iya haƙurin da zata iya. Haka suka cigaba da aikinsu har suka kammala suka fito falo suka yada zango suna karyawa lokacin ana niman goma saura.
Hamid a lokacin ya farka ya duba agogon wayarsa yana ganin lokaci ya waro ido waje dan ya yi barci sosai, ƙugin da cikinsa yake yi masa kawai ya tabbatar da yunwa yake ji, dan a irin wannan lokacin ya jima da fita aiki, ya sauko ya riƙe wayarsa ya fito falon, da yake su Sakina sun bawa ƙofofin bedroom baya basu ganshi ba suna ta hira da kallon tv, shima bai bi ta kansu ba ya nufi ɗakin Madina ya shiga, nan ya sameta ta jingina da filo itama bata jima da tashi ba ta shiga danna wayarta, Hamid ya sakar mata murmushi yana cewa.
Barka da safiya farin cikina.
Madina ta gimtse fuska ga miyau daya soma cika mata baki tana cewa.
Nayi fushi.
Sai ta mulmula ta miƙa kanta gefen gadonta ta tirtsar da miyau, sai ta dawo inda take ta jingina da filo, cikin dan mamaki Hamid yace.
Lafiya kike yawan tara miyau a bakinki sai kace mai ciki.
Wlh duk inna tashi barci haka miyau ke taruwa mini har sai na ci wani abu ko nayi brush kafin yake bari.
To tunda kinsan haka kike me zai hana ki tashi kije ki wanke bakin kafin kiyi mini magana, nifa wlh ƙazantar hakan nake gani.
Kana kyamata kenan?
Ta faɗa tana tsare shi da ido, guntun murmushi ya saki yana zama a gefen godon.
Taya zanji kyamarki bayan jiya komai ma ya faru a tsakaninmu, kawai dai ni mutum ne mai saurin kyankyamin abu makamancin haka, ki ɗaure ki daina.
Zanyi ƙoƙari duk da hakan ya zame mini jiki.
In har kina son farin cikina dainawar shi yafi. Me kike so kici yanzu na sa a haɗa miki.
Ok ina son a dafa mini indomie da dafeffen kwai uku, sai farfesun nama ko wani iri da kuma ruwan tea mai zafi.
An gama ranki ya daɗe.
Ya faɗa tare da miƙewa ya fito falon, takunsa da suka ji yasa suka daidaita zamansu ya ƙaraso suka shiga gaisawa, ya amsa fuska sake yana cewa Sakina tazo za suyi magana. Ta miƙe tabi bayansa suka matsa can gefen falon ya ce mata.
Indomie zaki dafawa Madina da dafeffen kwai uku, sai farfesun kaza ko naman kai nasan muna da komai a frigde sannan da tea mai kauri, ni kuma doya da kwai nake so yaji kayan miya irin wanda kika saba yi mini da yaji sai kunun gyaɗa, dan Allah maza ki hanzarta na baki awa guda nasan zaki gama komai.
Kallonsa take tsaf har ya gama maganarsa, ta nisa tana cewa.
Haba Hamid abu kusan kala hudu kace zan gama a awa guda sai kace agogo, zan dai dafa indomie da kwai tare da tea, sannan doya da kwai zanyi sai kuyi haƙuri da sauran dan lokaci ya ƙure, akwai kuma kunun tsamiya in zaka sha.
Ni kike faɗawa haka Sakina? Ace na faɗa miki abinda nake so kina kawo mini uzuri, tun kafin raina ya ɓaci kije kiyi abinda na sanar dake.
Gaskiya abinda na faɗa maka sune zasu samu, sauran bazai yuwu ba sai dai zuwa anjima nayi muku shi a matsayin abincin rana kuma…
Bata rufe baki ba ya kwasheta da kyakkyawar mari.
[7/9, 8:53 PM] Rahma Kabir: *ƘAZAMAR AMARYA*
Na
©®Rahma Kabir MrsMG.
Wattpad @rahmakabir
Page 11.
Sakina ta shiga duban Hamid cike da tsananin ɓacin rai idanunta suna kawo kwalla, ya nunata da tsaya yana cewa.
Karki sake ki dafa komai na fasa bana so, kije da mugun halinki kuma wlh sai na ɗauki mummnar mataki akanki, na kula da take takenki rashin kunya kika koyo zaki fara sauke mini, to bazan ɗauka ba ballagaza shashasha darajar yaran nan kawai kike ci wlh amma dana baki mamaki.
Hamid mamaki na nawa zaka bani ai ka gama bani shi, domin duk abinda zaka yi mini yanzu bana shakka ko tsoronsa.
Ta faɗa maganar cikin hargagi da kukan baƙin ciki, Hamid yayi kwafa ya zo ya wuce buguzum buguzum kamar guguwa, su Yaya Umma tun sadda ya mareta suka miƙe suna kallon ikon Allah, hatta Madina sai da ta buɗe ƙofar ta leƙo tana kallonsu, bayan Hamid ya wuce ne ta saki murmushi tana taɓe baki ta koma cikin ɗakin, su Falmata suka isa inda Sakina ke tsugune tana kuka yaya umma cikin ɓacin rai tace.
Sakina dama haka yake yi miki? lallai Hamid ya cika cikakken mara mutunci, ace a gaban idonmu zai sharara miki mari saboda shi isassahe ne, to gaskiya da sake wannan wulaƙancin yayi yawa.
Hmmm yaya Umma dama ai shiyasa nake cewa ta rage tsoronsa ɗazun kike cewa ba haka ba, kinga ai ya gwada miki shi ɗin ɗan akuya ne kinga zahiri, wlh Sakina ki tashi tsaye ki nuna masa kuransa kiyi fito na fito dashi shege ka fasa.
A’a Falmata ba kiji me yake faɗa ba cewar darajar yaranta take ci, abu kadan zata yi masa dan nuna masa iyakarsa ya kaɗata gida, dan haka haƙurin dai zata ƙara yi, sannan zanyi magana da Hamza muga ta ina zamu shawo kan lamarin dan bazai yuwu ya cigaba da ƙunsa mata baƙin ciki ba wani lalurar ya sameta. Sakina tashi mu shiga ɗaki kar ma ya dawo ya ganki, Falmata tafiya ya kamamu da wuri dan bazan cigaba da zama ina kallon kayan baƙin ciki ba.
Falmata tayi ƙofa tare da kama hannun Sakina suka shiga ɗakinta suna bata baki.
Hamid yana fita sashin su Hajiya ya wuce ya samu mutane a falo suka shiga gaisawa, can ya hango Asma a kitchen da alama suma abin karyawa duke haɗawa, ya isa can ya samu harda Hajiya ke ciki nan suka gaisa hajiya tana watse baki tace.
Ya kwanan yata amarya fatan ta tashi lafiya.
Alhamdulillah yanzu ma nazo naji me zamu samu na karyawa, wlh Sakina ba tada mutunci yanzu ta gama yi mini iskanci akan ba zata dafa mini abinda na umarceta da dafa ba.
Kai ma kaso ranka ya ɓaci ne amma dama kasan baƙin kishi bazai bari tayi ba, dama tun ɗazu nace a soya maka waina da miya.
To akwai farfesu na ko wani nama?
Eh akwai na kayan ciki da Alhaji yasa a dafa masa ɗazun aka gama.
Dama Madina ke so sai a haɗo da ruwan tea.
To yanzu za a kawo, karka samu damuwa anjima ma duk nan za a baku abincin kar Allah yasa ta yi girkin, yanzu dai zaka san kayi aure gida biyu maganin gobara.
Cewar Asma, murmushi Hamid yayi sai ya shafa ƙasumbarsa yayi musu sallama ya wuce. Koda ya dawo falon ba kowa ya wuce ɗakin Madina ya zauna bakin gado.
Ki tashi kiyi wanka ki shirya kafin mutane su fara zuwa bai dace a ganki haka ba.
Kash! nifa wlh zai wajen 12 nake wanka yanzu ina karyawa barci zan koma.
Haba Madina ya kike manta cewar ke baƙuwa ce a gidan nan kowa so yake ya ganki, sannan nan gidan Hamid ne ba gidanku ba da kika saba yin duk abinda kike so, ko dan ki faranta mini ya kamata kiyi duk abinda na saka ki ba tara da nayi mita ba.
Zumɓuro baki Madina tayi bata ce komai ba ta sauko ta wuce bayi, Hamid ya girgiza kai yana murmushi yasan zai sha fama da ita saboda ya kula tana da yawan shagwaɓa da shauni, fatansa Allah yasa ba tada ƙazanta saboda yadda zasu more rayuwarsu da kyau. Haka ya zauna zaman jiranta har ta fito ɗaure da towel a lokacin ne aka buga musu ƙofa, ya miƙe ya fito falon yaga Jidda da kwandon kulolin abinci a hannunta, ya wuce zuwa ɗakin da yake mazaunin falon Madina ya murza key ya buɗe suka shiga ta je kwandon sai ta wuce, shi kuma ya koma ya sami Madina ta sanya doguwar rigar shadda dark pink yasha aiki tun daga sama har ƙasa, kayan ba ƙaramin fito da kyawunta yayi ba, ta zauna tana shafa mai data gama ta sanya kwalli da powder sai man baki sannan ta feshe jikinta da turare ta ɗaura ɗan kwali, ba ƙaramin kyau ta yiwa Hamid ba, ta juyo tana rausayar da kai da fari da ido.
Ya ka ganni.
Kinyi kyau irin sosai ɗin nan, Madina kin morewa jiki Allah yasa kita zama a haka kirki yi ƙiba sosai.
Dariya tayi ta isa ta zauna bisa cinyarsa tana cewa.
Wa jibi zanyi ƙiba sai dai ba mai muni ba tunda kaga yadda jikin anty Aisha yake duk momy muka ɗauko, itama ai kaga tana da jiki amma mai kyau.
Gaskiya ne tawan. Tashi zaki muje mu karya.
Wai Sakina ce da dafa ko kuma ya akayi? naji kun fara rigima ɗazun wai dama haka take ba tada kirki.
Kaɗan ma kika gani in dai Sakina ce, sashin Hajiyarmu naje na yi magama ashe ma sunyi mana waina, gashi can a falonki sun kawo.
Wow aiko zan so cin wainar nan, amma farfesun fa.?
Ta faɗa tana cuno baki.
Shima an samu na kayan ciki.
Ina godiya Babyna, amma har yanzu banga tukuicin jiya ba nasan da yawa angwaye suna yiwa amarya kyauta.
Motarki tana nan a waje an rufeta da rigarta, itace kyautar.
Ni dai gaskiya yamin kaɗan ai nasan da ita, wannan kyauta ta mamaki ya kamata ka bani.
Madina muyi yaruwar gaskiya da gaskiya kinji, ni bansan wannan bayanin naki ba muje mu karya yunwa nake ji.
Ya miƙe yayi gaba, Madina ta bishi da harara ita tana yi masa kallon wayayye yasan irin waɗannan abubuwan ashe ba haka bane kallon kitse ta ke yiwa rogo, guntun tsaki taja tabi bayansa dan tuni ya fice abinsa, koda ya shiga ya samu har an kawo flacks ɗin ruwan tea, ya shiga haɗa musu komai ta sameshi ta zauna a carpet ɗin daya malale tsakiyar falon, haka suka karya ba tare da wani hira ba dan sosai Madina take wani shan ƙamshi, Hamid ya kula da hakan shiyasa ya rabu da ita dan ba zai yarda ta saka shi yin abinda bai yi niyya ba, shi mamaki ma take bashi da irin wannan salo salo da take ɓullo masa da shi wanda bai santa da shi ba, ko da yake dama ance ana ɓoye hali sai anyi aure komai ke fitowa to ya fara ganin zahirinta, dole ne ya nuna mata shi kaifi ɗaya ne mace bata isa ta juyashi ba. Bayan sun kammala cin Abincin ya tattara kayan ya miƙe, da sauri ta miƙe itama.
Beb wai fushi kake yi dani ne?
Ya zanyi fushi da amaryata kawai dai in ina cin abinci ban fiye son magana ba, bari na mayar musu da kayan in dawo in shirya in fita.
Haba Hamid ni kaɗai zaka bari gaskiya ka jira ‘yan uwana su zo sai ka tafi.
To Madinar Hamid bari na shirya ina zuwa sai muyi hira ko, dan ban gaji da kallon wannan kyan naki ba.
Murmushi tayi masa sai ya fice ita kuma ta cigaba da zama a cushing ɗinta tana danna waya, shuru shuru bai dawo ba har kusan sha biyu a nan ta fahimci jirgata yayi dan tuni ya shirya ya fice bai jin zai biye mata.
Ana yin sallar azahar su Yaya umma suka tattara yanasu yanasu suka tafi, wanda Sakina bata so haka ba taso ace sai yamma zasu wuce, koda tayi musu rakiya zuwa gate sosai suka ƙara bata shawara akan In dangin mijin ko wasu ‘yan uwan amarya sun zo suna nimanta da rigima karta kulasu ta cigaba da haƙuri kuma shima Hamid ɗin karta sake shiga lamarinsa ta bashi lokaci, tace musu to kana suka wuce ta juyo tana jin kamar ta bisu, kitchen ta shiga taga babu wani abu da zata yi dan komai sai da suka wanke mata suka gyara mata, sai ta koma ɗaki ta tasa ƙeyar Rauda ta rufe da key tayi kwanciyarta tana tunanin ya makomar zamanta zai kasance, tasan biyayyar data yi masa a da ba zata taɓa kamanta irinsa ba a yanzu, sannan ba zata iya bin shawarar yaya umma ba a yanzu dan ta gaji da halin Hamid, dole ne ta nuna masa itama akwai zuciya a ƙirjinta, girkin sati ɗayan data ce zata yi musu wlh ba zata yi shi ba, sai dai yasan yadda za suyi har tsawon wata gudan data ɗibar musu, da tunani barci ya ɗauketa, sai dai hayaniyar mutane da suke zuwa ya hanata barcin sai kawai ta zauna tana duba wayarta na hotunan da suka ɗauka jiya.
Madina tunda ‘yan uwanta suka zo sai ta mance da zancen Hamid, ga kuma dangun miji da suketa shigowa suna ganinta, haƙiƙa ba ƙaramin farin ciki take ciki ba iri yadda ‘yan uwan Hamid suke nuna mata so, ko ba a faɗa mata ba mamanshi ma tana mugun sonta yadda ƙannensa suke nan nan da ita. Wajen ƙarfe biyar ‘yan uwanta suka kaita sashin Hajiya kamar yadda ake yi a aladar Hausa Fulani sun samu tarba mai kyau daga bisani suka dawo da ita ɗakinta, zuwa magrib kowa ya watse aka bar amarya a ɗakinta.
Hamid bai shigo ba sai bayan sallar ishai, ya riƙo musu tsire ita kuma Sakina ya siya musu kaza tunda jiya bai bata ba duk da yasan akwai ɗanyan kajin a freezer, bawai dan yayi niyar ma siya mata bane sai da Habib yace dole ya siya dan haka ake yi, ya zauna a falon ya kira Sakina a waya, data ɗauka yace tazo falo itama Madina ya kirata, ba jimawa duk suka fito, Madina ta sauya wani shiga na leshi riga da siket tayi kwalliya sai kyallin amarci take yi ko gyale bata yafa ba, Sakina kuwa harta saka kayan barci ta kwanta dan haka hijab kawai ta ɗaura a saman kayan ta fito, duk suka samu guri suka zauna Madina ta zauna gefen Hamid tana cewa.
Sannu da zuwa Babyn Madina nayi kewarka sosai yau.
Ta faɗa tana shafa gefen sajensa, Hamid ya saki murmushi.
Nima haka Madinata kin ƙara kyau sosai fatan kina lafiya.
Gyaɗa masa kai tayi tana kallonsa fuskarta cike da murmushi, Sakina tana zaune tana kallon ikon Allah bata ce uffan ba, koda Hamid ya kalleta ɗaure fuska yayi yana cewa.
Ke kuma saboda mugun hali kin kasa ce min komai ko to kanki kike yiwa. Dama na kiraku ne na haɗaku domin kusan juna da kuma sharruɗɗan da zan kafa muku. Sakina ga Madina nan amana aka bani ke ce zaki tayani dan ganin na yi adalci a tsakaninku, Madina ga Sakina yayarki ce dan haka ki bita abinda baki gane ba na gidan ki tambayeta. Bana son rikici bana son tashin hankali ku haɗa kanku, sannan batun raba kwana na yanke yin kwana bibbiyu ga duk mai girki In amarya ta gama wata ɗayan da kika bata, sannan ban yarda da raba girki ba duk me miji ita zata yi girkin duka gida, sai dai ke Sakina dole zaki yi haƙuri kina yin karin safe kullun saboda Madina tana zuwa aiki ke kina gida , kuma kina yin abincin yara na makaranta kinga sai kiyi duka, sannan girkin rana ma ki yi keda yara ita in ta dawo ta san me zata ci, girkin dare kawai nake nufin duk me miji zata haɗa tayi duka gida, bana son kazanta ku riƙa gyaran min gida, Sakina aikin dai zai fi yawa a gunki tunda Madina bata zama.
Hamid tunda Madina ta iya karɓan kwana to zata iya ɗauke duk hidimar gidan nan, nima na huta ai ba agogo nake ba da zaka cika mini aiki saboda son kai, wlh bazan yi komai a ranar girkinta ba ta gyara gida ta yi duk abinda mace keyi na gida, batun karin safe da abincin rana kowa yaci nashi na daren me girki sai ta haɗa tayi, wannan shine adaci.
Cewar Sakina data katse masa magana tana kawar da kai gefe.
Wato ban isa da ke ba kenan ko? ina bayani har kin samu zummar saka mini baki ba tare da na baki damar yin magama ba ko, Sakina me kike son zama ne? Duk take taken iskancinki wlh bazan ɗauka ba tom.
Hmmm tace masa bata kuma magana ba, Madina sai a sannan tace.
Beb mai zai hana ka samar mini ‘yar aiki mai girki da kuma gyaran gida, kaga zan samu sauƙin abubuwa in yaso kowa yaji da kansa tunda ta nuna ba zata taya ni ba.
Madina a tsarin gidana da ra’ayina babu zancen ‘yar aiki, ke zaki yi girki, batun gyaran gida ki yi ƙoƙarta kiyi dan gaskiya ban yarda da ƙazanta ba, kuma na isa da gidana dole ne Sakina tayi abinda na tsara.
Beb nifa…
Karki yi mini gardama tashi ki wuce ɗaki ina zuwa.
Hamid ya katse Madina da zata yi magana, bata ƙara cewa komai ba ta miƙe rai a jagule ta wuce, tana mamakin Hamid yadda yake faɗin ba zai ɗauki mai aiki ba, ita fa wlh ba zata iya da wahalar gidansa ba dan ba ɗawainiyar gidansa yasa ta aureshi ba.
[7/11, 8:40 PM] Rahma Kabir: *ƘAZAMAR AMARYA*
Na
©®Rahma Kabir MrsMG.
Wattpad @rahmakabir
Page 12.
Hamid ya miƙe yana duban Sakina.
Ke kuma ki cigaba da cika mini ciki duk ranar dana tashi amayar dake ba zaki ji daɗi na ba, kuma wlh ina kan maganata baki isa ki sauya mini tsarin dana gindaya muku ba. Ga kaza nan kici ke sa yara ki tabbatar da safe kin haɗa mana abin kari mai kyau.
Yana kaiwa nan a maganarsa ya wuce zuwa ɗakinsa, Sakina tayi gunyun tsaki wanda ya tsaya a iya leɓenta.
Wlh bazan yi ba kayi duk abinda zaka yi.
Sai ta miƙe ta ɗauki ledar kazar sai da taje kitchen kafin ta tsaya ta duba kana ta saka shi a freezer, ita sam bata son irin gassasun kazan nan, kuma suna da soyayye ga kuma wasu ɗanye a frigde, a ganinta dama bai ɓata kuɗinsa ba ya siya shida amaryarsa kawai, ta gama abinda zata yi ta fito ta koma ɗaki ta kwanta. Hamid sai da yayi wanka ya kimtsa kansa kafin ya tafi falon Madina, suka ci tsire da drinks tare da kallo a tv, sai wajen sha ɗaya tukuna suka dawo ɗakinsa, a ranar nan suka kwana cike da soyayya.
Da safe.
Sakina da wuri ta kimtsa yara ‘yan makaranta suka tafi, sai ta shiga gyaran ɗakunansu, tana tsaka da moping ɗin ɗakinta sai taji maganar Hamid, da sauri tazo ta murza key ta koma bakin gado ta zauna, Hamid fuska a haɗe ya fito saboda rikicin da suke yi da Madina akan tun ɗazun yake godo da ita tayi wanka taƙi yi wai sanyi take ji, ƙiri ƙiri wankan tsarki ya gagareta tun asubahi wai sai gari ya waye zata yi karshe juya masa baya tayi ta koma barci, har yaje Masallacin asubahi ya dawo tana kwance, Hamid da haushinta ya koma barci. Da kuma ya farka yanzu ya samu idonta biyu tana danna waya yayi mata maganar wanka wai zata yi amma sai ta karya ita yunwa take ji, bai kuma yi mata magana ya fito falon ya ganshi caf sai ƙamshi yake tashi, yasan aikin Sakina ce sai ya wuce gurin dinning yaga wayam ba komai a kai, ya girgiza kai tare da wuce wa kitchen nan ma ya samu komai naf kamar ba ayi girki ba, ya fito a fusace yana kwalawa Sakina kira tana jinsa tayi banza dashi harya ƙaraso ƙofar ɗakinta ya murɗa yaji a rufe, sai ya buɗe murya yana cewa.
Sakina ina breakfast ɗinmu dana ce ki haɗa mana, me kike nufi dani ne? wlh zanyi matuƙar saɓa miki dan na gaji da iskancin da kike yi mini.
Sakina ta miƙe ta iso bakin ƙofar ɗakin ta tsaya tana cewa.
Madina ita ce ta dace ta dafa muku abinda zaku ci, dan tun jiya ka mari girkin dana ce zanyi muku na sati ɗaya, wlh Hamid bazan amsa girki ba har sai ta gama wata ɗayan dana baku.
Haka kika ce ko.?
Eb haka nace.
To mu zuba ni da ke.
Sakina bata tanka masa ba ta koma ta cigaba da moping ɗinta, Hamid rai ɓace ya koma ɗakinsa, Madina ta matsa gefen gado tana shirin fetsar da miyon daya cika mata baki, Hamid ya daka mata tsawa.
Kar ki kuskura ki soma zuma mini miyau a bangon ɗaki, wlh bazan ɗauki wannan ƙazantar ba, maza ki tashi ki fita kije can ɗakinki kiya ba dai a nan ba.
Ya ƙare maganar yana nuna mata hanyar ƙofa, Madina da wani irin kallo ta bishi sai ta sauko daga gadon ta shiga toilet ɗinsa ta zubar da miyan ta kuskure baki ta fito ta tsaya tare da kama ƙugunta.
Hamid nice fa Madina ko idonka ya rufe ne da kake niman yi mini tsawa, to gaskiya ba a yi mini haka karka ƙara daka mini tsawa, ohhh saboda Sakina ta kunno maka masifa shine zaka zo ka sauke a kaina to ai bani nakar zomon ba.
Da tsananin mamaki yake kallonta dan tayi maganar ne cike da tsiwa tana zare ido kamar tana yiwa ɗanta faɗa, Hamid yasa hannunsa a kirjinsa alamar nuna kansa.
Ni kike faɗawa haka?
Zan faɗa maka fiye da haka matsawar kana kaifafa harshenka akaina, haka kurum kwana na biyu da zuwa gidanka ka fara ɗaga mini murya, me nayi maka da zaka ɗauko fushin matarka ka huce a kaina.
Ta ƙare maganar cikin yanayin son yin kuka, sai ta wuce ta ɗauki gyalen data yane kanta ta raɓa ta gefensa ta wuce ranta a haɗe, Hamid baice mata komai ba dan ba ƙaramin mamaki ta bashi ba yadda take yin magana kaitsaye mai cike da gargaɗi, girgiza kai yayi ya sauke ajiyayar zuciya ya wuce ya fara shirin fita aiki. Bayan ya kammala ya fito ya shiga ɗakin Madina nan ya samu ta fito daga wanka ta saka wata doguwar riga wanda ya fito da surarta sosai, saida yaji ta burgeshi amma sai ya kawar da abin da yaji ya kalleta cikin sauke kansa.
Haba Madina fushin ne har yanzu? To kiyi haƙuri bana son kina ɓata fuska, yanzu ga wannan number ɗin na wani rastuarant ne dana saba yin oder a gunsu, ki kira ki sanar dasu duk abinda kike so zan tura miki 20k nasan zai ishe ki.
A lokacin ne ta ɗan saki fuska tana cewa.
To ai kaine kake yi mini faɗa shiyasa nayi fushi.
Ta faɗa tana turo baki, murmushi yayi dan duk in tana yi masa shagoɓa burgeshi take yi, sai ya isa gareta ya rungumeta yana cewa.
Bazan sake ba, amma ki daina zuba miyau a bango bana son haka dan Allah, da fatan kinyi sallah.
Ta gyaɗa masa kai alamar tayi, sai yayi mata kiss a goshi ya raba tsakaninsu yana cewa sai ya dawo, hannu ta ɗaga masa tana murmushi.
Bye my Hamid.
Kanne mata ido yayi yana murmushi sai ya juya ya fita, bai bi takan Sakina ba yayi ficewarsa sai dai taji ƙugin fitar motarsa, hakan bai wani dameta ba dan tasan halinsa zai yi fiye da haka ma, ayyukanta ta gama ta samu ta watsa ruwa tabi lafiyar gado dan ta huta.
Madina bata yi wani oder ba fitowa tayi ta shiga kitchen ta isa gefen inda kayanta suke da komai yake sabo, ta ɗauki abin suya ta dawo ta duba inda aka aje kwai ta fasa guda shida ta yanka albasa da koren tattasai ta soya shi, kana ta haɗawa kanta tea mai mugun kauri ta cika sugar yanda take so, sai ta ɗauki biredi da taga saura, ta jerasu a tire ta fito dinning ta cika cikinta tsaf kafin ta mayar da kayan zuwa wajen wanke wanke, ta fito abinta zuwa falo ta zauna tana chart. Wajen goma da mintuna su Asma suka shigo suka sameta a nan main falo, tana ganinsu ta saki murmushi suka ƙaraso ciki suka zauna tare da gaisawa sai Kubura tace.
Gaskiya kina burgeni komai naki cikin sauƙi har kin fara fitowa nan.
Wannan ai shine wayewa Kubura ko kin mance Madina da iliminta.
Cewar Asma data bata amsa, Madina tace cikin murmushi.
Ban daɗe da karyawa ba nace bari na zauna na shaƙi iskar nan falon, ya Hajiya da Abba fatan duk suna lafiya.
Alhamdulillah lafiya lau, dama mun zo yi miki sallama ne anjima duk zamu koma garin mu. Ina Uwargidan take ne ko ta fita?
Waya sanin mata tunda ta gama yiwa yayanku rashin mutunci ta kulle kanta, rabona da ita tun jiya da dare.
Ai ta saba yi masa haka, yanzu dai in ta bata masa rai nasan ke zaki faranta masa, dan Allah ki kula mana da yayanmu.
Karki ji komai ai ina sonsa dan haka dole ne zan kula da shi.
Sun ji matuƙar daɗin maganarta sai suka ɗan taɓa hira daga bisani suka yi sallama akan sai sunyi chart ko waya, da ido ta rakasu har suka fice tana kwafa.
Da yake na auri yayanku ne dan kawai na ƙare da wahalarsa ko, to zanyi maganin wannan shisshige mini da kuke yi, nasan duk na munafurci ne, da ai kafin ya aure ni Sakina kuka sani.
Ta faɗa a zuciyarta tana cigaba da dubar wayanta. A ranar da dare Hamid ne ya shigo musu da abincin dare da ya yi musu oder, bai bi takan Sakina ba dan ko yaran ma bai gansu a falo ba bai kuma nime su ba, ɗakinsa ya wuce ya kimtsa sai ya nufi wajen Madina dan yau a ɗakinta zai kwana ba zai yarda da ƙazanta ba dan yadda ya bar ɗakin haka ya dawo ya same shi ba shara balle a gyara shinfiɗar gadon, ya saba Sakina kullum ita ke yi masa da ya dawo zai samu ɗakin yana ƙamshin turare, sai da ya karkaɓe gadon da kansa ya gyara sai ya saka air freshner, ɗakin ya ɗau ƙamshi kafin ya fito ya sameta a falonta tana kallon tv.
Washe gari.
Kamar yadda Hamid ya bawa Madina dubu Ashirin dan ta siya abinci jiya yau ma haka ya bata, dan baya so ya ɗaurawa hajiyarsa aikin ɗawainiya dasu, saboda duk mutane sun watse ba mai tayata aiki sai Jidda ita kuma tana zuwa makaranta, shiyasa koda ta tambaye shi Sakina tana basu abinci yace eh kawai dan kar yaja maganar tayi tsawo. Yau har jikin mota Madina ta raka shi ya wuce suka rabu cike da kewar juna. Sakina tana jin fitarsa ta fito ta cigaba da aikinta, Madina ta shigo ta samu tana goge Centre table da fara’a Sakina ta ɗago tana cewa.
Amaryar Hamid ya baƙunta?
Madina kallonta tayi sama da ƙasa kana taja tsaki ta wuce abinta tana yatsine fuska, da sakin baki Sakina ta bita tana mamakinta ko da yake ba abin mamaki bane tunda wanda take zama danshi shine ya fara wulaƙantata ya nuna bata da daraja dole itama ta ɗauki hanya, amma tayi da ‘ya zata nuna mata itama ta iya rashin mutunci dan ba zata ɗauki rashin kunya ba domin ta girme mata, tana gama aikinta ta shiga ɗaki ta kwanta sai ta kira yaya Umma, nan suka ɓata lokaci suna magana wanda duk haƙuri yaya Umma ke bata, duk da ma bata faɗa mata komai dake faruwa ba, dan tayi alƙawarin danne damuwarta har sai ya kai wani matakin daya fi ƙarfinta ne kafin zata faɗa mata, kuma in tace mata ga irin hukuncin data ɗauka akan Hamid na ƙin yin girki faɗa zata yi mata, shiyasa ta bar maganar a zuciyarta.
Madina kuwa tea ta haɗa tasha da cincin da diblan ɗinta na gara da aka kawo mata, sai ta bi tafiyar gado ta kwanta ta yi barci.
Wajen sha biyun rana Sakina ta fito ta ɗaura sanwar tuwon samo da miyar kuɓewa busasshe da zata yi musu tun daga rana har dare, bayan ta yi talge sai ta ɗaura sanwar miya ta samu guri ta zauna dan dama ta saba haka in tana girki har sai ta gama take fita daga kitchen, a lokacin ne Madina ta shigo kitchen ɗin koda ta ga Sakina sai ta kawar da kai ta wuce gefen kayanta, ganin kayan jiya data ɓata an aje mata a gurin ba a wanke ba, sai taja gunyun tsaki ta ƙara ɗauko wasu masu kyau ta aje, tazo ta ɗibo kwai guda shida ta kunna wayarta ta soma kallon video ɗin yadda zata haɗa kwai, sai da ta dafa guda uku kafin ta fasa uku ta yanka waɗannan data dafa ƙanana a cikin ruwan kwai ta yanka albasa da tarugu guda ɗaya tasa maggi da curry a ciki ta juya kamar yadda take kallon video, wata baturiya ce ke yi tana bayani da turanci, sai ta aje wayar ta kunna gas ɗinta dan tana da nata itama ba ruwanta dana Sakina, ta soya wannan kwan kamar yadda matar ta nuna a video ɗin, ta zuba a plate sai ta ɗauki coke drink ta fice falo ta zauna tana ci tana sauraren waƙa music tare da kaɗa kai, bayan ta kammala ta ɗaura ƙafa akan center table sai ta cigaba da chart, a haka ne Jidda ta shigo riƙe da kula a hannunta, ta ƙaraso gunta ta gaisheta kana ta miƙa mata tana cewa.
Hajiya ce tace in kawo miki dambun shinkafa ko zaki ci.
Da sauri Madina ta amsa ta buɗe sai ƙamshi ke tashi, ga soyayyen naman sa a gefe zai kai yanka shida, tana cewa.
Aiko in son dambun shinkafa na daɗe ban ci ba, ki ce mata nagode ina gaisheta.
To Jidda tace mata kana ta wuce, Madina ta miƙe ta ɗauki plate ɗinta ta shiga kitchen ta a je kular abincin tare da plate ɗin a gefen kayanta da ba a wanke ba, ta ɗauki wani cup na plastic ta isa inda aka jera kayan tea ta ɗiba madara tsokali kusan huɗu kana ta ɗiba milo tsokali ɗaya, ta zuba sugar sai ta saka ruwa kaɗan ta dama shi yayi kauri, sai ta soma ɗiba da cokalin tana sha ta wuce dashi a hannu, da ido Sakina ta bita tana wani murmushi, wato Allah ya haɗa Hamid da dai dai shi ya samu mai almubazzaranci, kullun in ya siyo kaya sai yayi mata faɗa akan ta riƙa binsu a hankali karta ɓarnatar dashi, lokaci guda tayi amfani da kwai tsida wanda inda ita ne kwai biyar in ta fasa musu ita da yara ya ishe su, girgiza kai tayi ta cigaba da tuka tuwonta.
[7/13, 8:28 AM] Rahma Kabir: *ƘAZAMAR AMARYA*
Na
©®Rahma Kabir MrsMG.
Wattpad @rahmakabir
Page 13.
Sakina sai da ta kwashe tuwo a leda ta saka a kula ta adana kafin ta rage wutar miyar ta fito domin tayi sallar azahar, a lokacin ne su Mufeeda suka dawo daga makaranta kasantuwar jarabawa suke yi basa kaiwa yamma, da gudu baba ƙarami yazo ya rungumeta yana cewa.
Barka da gida mama, an gama abinci.?
Sarkin ci daga shigowarka sai maganar abinci, ya jarabawar Mufee
da.?
Ta ƙare maganar tana duba ‘yarta, murmushi tayi mata tana zama a cushing.
Lafiya lau mama.
Tashi za kiyi kije kuyi sallah kafin nan na kaɗa miya ku ci, naga duk kun shigo a yamutse ne yunwa ba tada hankali ko.
Dariya suka saka sai ta zame baba ƙarami a jikinta ta wuce ɗaki, nan ta samu Rauda a gado sai wasa take yi ta tashi daga barci, ta ƙarasa tana dariya.
‘Yar Albarka kin tashi yau ba rigima.
Mama inci Aninci.
Rauda ta faɗa cikin tsamin baki, tana yi kamar zata yi kuka.
Ai yau kinyi jarumta har ƙarfe ɗaya baki ci komai ba tun safe.
Sakina ta isa gadon ta ɗaukota sai ta duba parmpers ɗinta taga bata yi komai ba, da sauri ta cire mata ta shiga bayi ta ɗauki pow fito ta ɗaura ta kai, sai ta koma ta ɗauro alwala tazo ta tada sallah. Mufeeda itama ɗakinta ta shiga ta ɗauro alwala ta tayar da salla, Baba Ƙarami kitchen ya nufa da Yakub yana biye dashi a baya, suka fara buɗe budte ko zasu samu abinda za su ci, can suka hango kular dambun da aka aikowa Madina, da sauri Yakub ya isa gurin ya ɗauko kular ya aje a ƙasa, Baba ƙarami wajen plate yaje ya ɗauko yazo suka buɗe kular Yakub ya washe baki.
Wannan kular gidan Hajiya ce an aikowa Mama da dambu amma taƙi bamu, wlh ci zanyi dan yunwa nake ji, dama bana son cin tuwo.
Ya faɗa yana ɗaukar tsokar nama ɗaya yana ci, nan suka ɗiba da yawa kaɗan suka rage tare da barin tsoka biyu a ciki suka mayar da kular suka zauna nan suna ci suna santi, da suka gama suka sanya plate ɗin a gurin wanke wanke kana suka sha ruwa suka fice zuwa falo ko wanne yaja ya zauna a kujerar data yi masa suna kallon tv. Madina bayan ta idar da salla har ta kwanta ta tuna da dambunta sai ta sauko ta fito da nufin ko kaɗan ne ta ɗiba taci anjima taci a matsayin abincin dare, kuma tana son dambu sosai momy bata cika yi musu ba, shiyasa duk inda taje aka yi mata tayinsa bata alkunya sai ta ci. Ta shiga kitchen sam bata kula da kasan tiles ba dasu Yakub suka zubar ba, sai da ta isa wajen kular ta ɗauko plate da nufin zubawa tana buɗewa taga an cinye mata kaɗan ya rage, wani ashar ta wulwula shi tana waige waige, can ta hango plate ɗin da suka ci, sai ta fito falon riƙe da sauran dambun tana buɗe murya.
Wani ɗan kutumar abu kaza kaza ne yaci min dambu na, wlh Sakina ki fito sai kin biyani, saboda tsabar mugunta ke baki dafa kin bani ba, kuma an kawo mini saiki cinye mini tsabar zalama.
Sakina da fitowarta kenan a bayi ta wankewa Rauda kashi da sauri ta fito tana dubanta, su Yaƙub kuwa miƙewa suka yi suna zare ido shaf sun manta da wata amaryar babansu balle suyi zaton nata ne, Mufeeda da idar da sallarta kenan itama ta fito tana dubanta, Madina ta kuma ƙundumo ashar.
Na rantse da Allah yadda kika cinye mini dambun nan kuuma ba zaku ci abincinku ta daɗin rai ba.
Sai ta juya zuwa kitchen da sauri, Sakina tabi bayanta da yaran duka ko kafin su ƙarasa ciki Madina ta ture tukunyar miyar Sakina ya faɗi gefe ji kake coiiin ruwan miya ya sauka kan gas, da gudu Mufeeda ta isa gurin ta ɗaga tukunyar miyar da ya zube kaɗan ya rage a ciki, Sakina kujera ta samu ta zauna tana jin wa irin tururin masifa yana kunnota sai fitar da numfashi take yi mai zafi, Madina ta cigaba da cewa.
Duk ɗan iskan daya kuma ci mini abinci bayan na aje wlh sai inda ƙarfina ya ƙare, kuma ba zan fasa ajewa a kitchen ba sannan ki jira abinda zai biyo baya akan wannan iskancin da kika mini.
Tana gama faɗar haka ta fito daga kichen ɗin da ragowar dambun ta nufi part ɗin Hajiya kai ko ɗankwali babu. Mufeeda da sauri ta kashe gas tasa tsumma ta goge inda ruwan miyar ya sauka ta gyara gurin kana ta ƙara kunna gas ta mayar da tukunyar miyar ta ƙara ruwa a ciki, cikin ƙanƙanin lokaci ta ƙara haɗa sanwar miyar sai dai bata tsaya saka manja ba soyayyen man gyaɗa ta zuba wanda Sakina ke yawan ajiyewa saboda amfanin gaggawa, ta koma kusa da mamanta ta tsuguna akan guiwarta tana cewa.
Dan Allah mama kiyi haƙuri karki biye mata rigima kawai take nima dake amma sanin kanta tasan ba zaki taɓa mata abinci ba. Laifin su Yakub ne sune suka ci abincin kuma wlh ki kamasu kiyu musu ɗan banzan duka nan gaba ba zasu ƙara ba.
Ya zaki ce ta duke mu bayan bamu san ba nata bane danbun, mama dan Allah ki yafe mana ba zamu ƙara ba.
Cewar Yaƙub yana maƙale jikin ƙofar kitchen, shi ko baba ƙarami tsabar tsoro ya kasa shigowa sai raba ido yake yi saboda fargaban kar Sakina ta duke shi, ajiyar zuciya Sakina ta sauke bata iya cewa komai sai addu’ar samun natsuwa da kore shaiɗan da taketa maimaitawa a zuciyarta, kuma Alhamdulillahi taji zuciyarsa ta yi sanyi sosai, yaran ganin bata ce komai yasa suka yi shuru cike da damuwa musamman Mufeeda da take da wayo ta fara gane yanayin zaman gidansu daya sauya a tsakanin Abbansu da mamansu sam abin baya mata daɗi, miƙewa tayi ta kora su baba ƙarami akan su je ɗaki su cire uniform su yi sallah, ba musu suka wuce jiki a sanyaye dan sosai lamarin ya damesu.
Madina tana shiga part ɗin su Hajiya taga ba kowa a falon sai ta buɗe murya ta shiga kiran Hajiya da ƙarfi.
Hajiya! Hajiya! Umma umma.
Da sauri Hajiya ta miƙe daga sallaya ta fito falon, Alhaji kuwa da bai jima da dawowa daga Masallaci ba ya kwanta kenan yaji muryar wacce bai sani ba tana kwalawa Hajiya kira, da sauri ya miƙe ya fito dan gabaɗaya yanayin kiran ya ruɗar dasu. Hajiya sam bata ganeta ba saboda bata gama wayar fuskarta ba ga kuma kai ko ɗankwali babu, balle kuma Alhaji da ko a hoto bai ganta ba, cikin nanayi na mamaki Alhaji ya riga Hajiya magana.
Yarinya daga ina lafiya.?
Sakina ce ta cinye mini danbun da kika aika mini kuma wlh tunda aka kawoni bata taɓa yin girki ta zuba mini ba, kullun Hamid ke siyo mana na dare da safe in zai fita ya bani kuɗi na yi oder abin kari da zanci.
Ta ƙare maganar tana nuna musu kular abincin kamar zata fashe da kuka tsabar shagoɓa, nan take su Hajiya suka gane wacece saboda bayaninta ya ɗaurasu a hanya, hajiya tace cikin ɓacin rai.
Ashe dama Sakina bata baku abinci Hamid yace tana dafawa daku, lallai yarinyar nan ta cika mata mutunci, bata baku ba sannan an baki ta cinye, maza muje naji dalilin daya saka ta taɓa miki abinci, haba mace sai kace jaka sam bata san mutunci ba sai kace akanta aka fara yin kishiya.
Ke Hajiya bana son haka ya zaki yanke mata hukunci baki ji ta bakinta ba. Ke yaran sun dawo makaranta?
Abba ya ƙare maganar da tambayar Madina yana kallonta fuska haɗe, da sauri tace.
Sun dawo ba su daɗe da shigowa ba.
To ke yanzu fisabillahi ba zaki iya tunanin yaran zasu iya taɓa miki abinci ba suyi zaton na mamansu ne, na tabbatar Sakina ba zata taɓa ɗibar miki abinci ba domin nasan halinta sosai tana da gudun ɓacin rai.
Shuri Madina tayi taƙi cewa komai sai Hajiya ce tace.
Haba Alhaji kai sam baka ganin laifinta, kuma fa Sakinar daka sani ta sauya hali na tabbatar zata iya aikata komai domin kar a zauna lafiya, dan haka ni zanje naji dalilinta na ɗibar mata abincin.
Zaki je dai ki ƙara zubar da girma dan haka ban yarda ba.
Allah sai naje Alhaji in aka zuba ido zata riƙa tsokanar yarinyar nan tana nimanta da rikici dan taga ta girme mata.
A sauka lafiya.
Abba ya faɗa yana samun cunshig ya zauna, Madina ce ta fara tafiya kafin Hajiya tabi bayanta suka nufi gidansu, Abba murmushin takaici yayi yana girgiza kai, yanzu ne ya tabbatar da Hamid ya saki rashe ya kama ganye, gabaɗaya bai hango tarbiyya a tattare da Madina ba, dududu kwananta nawa a gidan amma ji yadda tazo gidansu ko ɗankwali babu tana kwalawa Hajiya kira kamar wata sa’arta, babu wani kunya ko nuna kamewa matsayinta na baƙuwa, in ko haka ake wayewa to tabbas yana kunshe da tarin jahilci da rashin tarbiyya, ya tabbatar daga Hamid har Hajiyarsu idonsu a rufe yake sai nan gaba ne zasu gane cewar tafiyar da suka ɗauko tabbas akwai GARGADA.
Madina tun a hanya take kukan makirci wanda ita kanta bata san tana da shi ba, wato shi iya makirci halittar Mutum ake da shi matukar ya kasance mai son zuciya da mugunta, Hajiya kuwa sai masifa take tana aibata Sakina har suka ƙarasa cikin falon, ta shiga kwala mata kira Sakina da ke zaune har lokacin bata miƙe ba ta cire taguminta ta miƙe ta fito falon ta tsaya a bakin ƙofar kitchen tana dubansu.
Ban taɓa sanin ke matsiyaciya ɓace sai yau, ashe tunda aka kawo yarinyar nan baki taɓa bata abinci ba, hatta shi Hamid da yake kawo abincin baki bashi ba saboda kin riƙa wuya ki ya isa yanka, to wlh zan nuna miki ƙarfin uwa yau sai kin san kin taɓawa Madina Abinci.
Ai Hajiya ba iya Abinci ta taɓa mini ba duk in taga Hamid ya fita har ɗaki take zuwa tayi mini zagin ƙare dangi tana cewa yadda na shigo gidanta to haka zan bar mata shi tunda Hamid Dan ita kaɗai aka halicce shi, ba ƙaramin barazana take yi mini ba duk da haka ban taɓa faɗawa Hamid ba saboda ina ganin zata gaji ta daina.
Hajiya salati ta shiga yi tana tafa hannu.
Ke Madina maza ɗauko wayarki ki kira mini Hamid.
Da sauri Madina ta aje kular abincin ta wuce ɗaki dan ɗauko wayarta, Sakina tana nan a tsaye kamar an kafata tana kallon ikon Allah.
[7/14, 8:20 PM] Rahma Kabir: *ƘAZAMAR AMARYA*
Na
©®Rahma Kabir MrsMG.
Wattpad @rahmakabir
Page 14.
Madina ta dawo falon riƙe da waya a hannunta ta tsaya tare da kiran Hamid, bugu biyu ya ɗauka kafin yayi magana ta rigashi da cewa.
Ga Hajiya za kuyi magana.
To ya ce mata sai ta miƙa wayar ga Hajiya ta amsa ta kara a kunne.
Hamid duk in da kake ka dawo gidanka yanzu ina son ganinka.
Bata jira me zai ce ba ta miƙawa Madina wayar ta kashe, sai duk suka zauna suka cigaba da maganar Sakina ganin sun kira mai gayya mai aiki yasa ta koma kitchen ta zauna ta rafka tagumi yaran suma duk suka bita suka tsaya cike da damuwa a fuskokinsu, babu wanda ya yiwa ɗan uwansa magana sai Mufeeda data isa gurin miyarsu ta duba taga yanata tausa saita rufe ta koma gefe itama ta tsaya. Kusan tsayin minti talatin da biyar kafin Hamid ya ƙaraso gidan, ya shigo falon da sallama suka amsa masa ya ƙarasa har ciki ya samu cushing ya zauna yana gaishe da Hajiya, ta amsa fuska ɗaure kana ta ɗaura da faɗa masa dalilin kiran nasa, duk abinda Madina ta faɗa mata bata rage komai ba, ita kuma Madina tayi fuskar tausayi kamar zata fasa ihun kuka, Hajiya ta ɗaura da cewa.
Ashe Sakina bata baku abinci kace mini tana baku, taya zaka zuba mata ido tana yin iskancin data ga dama ko tafi karfinka ne? sannan ace ta riƙa yiwa yarinyar nan barazana ya dace haka, itama da tayi shirme taki faɗa maka, to gaskiya Sakina ta fara wuce gona da iri ba zai yuwu azuba mata ido haka ba, wannan yarinya amanarta aka baka ranar Lahadin nan, bai dace ace ta fara fuskantar matsala ba.
Hajiya nima nagaji da halinta, amma ina zuwa.
Ya miƙe a fusace ya fara kwalawa Sakina kira kamar tarar aradu, Sakina ko gezau bata yi ba sai Mufeeda ce tayi sauri ta je ta rufe ƙofar kitchen ɗin da sauri ta saka key, nan ya gane tana kitchen sai ya nufi can yana huci tare da zazzaga masifa akan ta buɗe yau baiga uban da zai hana shi bai duketa ba, sai ta faɗa masa me take taƙama da shi, yau kam har zaginta sai da yayi yana kumfar baki tare da buga ƙofar kitchen din da ƙarfi kamar zai ɓallashi, yaransa duk suka gigice suka fara kuka Sakinar ma hawaye ke bin kuncinta wani yana bin wani, jikinta har rawa yake yi saboda tashin hankali kuma ko gezau bata motsa ba a inda take, dan da ace Hamid ya cimmata to haka zai shiga dukanta bata jin zata motsa ba dan ta gama sarewa da halin da take ciki, mamakinta bai wuce yadda Madina ta iya haɗa mata makirci ba, tasan ba tada wata mafita sai a gurin Allah. Da sauri Hamid ya koma falon ya tsaya yana cigaba da masifa tare da niman number ɗin Yaya umma, nan take ya kirata tana ɗagawa ko gaisawa bai bari sunyi ba ya shiga cewa.
Yaya umma wlh na gaji da halin Sakina ta kai ni bango bazan iya da matsalarta ba, ya kamata kizo kija mata kunne dan wlh ina gabda yanke ɗanyan hukunci akanta.
Ƙit ya kashe wayar yana huci, yaya Umma wayar ta sauke daga kunnenta tana jin wani karaya dangane da auren Sakina, sosai ta tausayawa ‘yar uwarta halin da take ciki dan Hamid ba zai taɓa sauya hali ba. Nan take ta kira mijinta ta sanar dashi zata je gidan Sakina ba lafiya, tsaki yaja yana cewa.
Ku dai tsaya ku karɓarwa yarinyar nan ‘yanci, iskancin Hamid ya yi yawa fa, in ya gaji da ita ne ya sauwaƙe mata mana haba.
Allah ya kyauta bari naje naji meke faruwa.
Nan suka yi sallama ta miƙe da sauri ta shiga ɗaki ta soma shirin zuwa gidan.
Hamid yana gama waya da Umma Yaya Ali ya kira babban yayansu Sakina, shima nan ya faɗa masa magana kamar yadda ya sanar da Umma, ya kashe wayar yana cigaba da huci ya samu guri ya zauna Hajiya tana cewa.
Gwara ayi ta ta ƙare dan gaskiya lamarin Sakina ya wuce ayi mata uzuri yanzu.
Maganar da Hajiya tayi kamar ya ƙara tunzura Hamid ne ya miƙe ya isa ƙofar yana bugawa tare da zaginta da duk kalmar daya fito bakinsa. Shigowar Alhaji da sallama yasa duk suka mayar da hankalinsu gurinsa, ya shigo falon ya tsaya yana ƙare musu kallo bai ce komai ba, tunda yaji Hajiya shiru yasan suna shirya wani abu, dalilin daya saka kenan ya zo yaga meke faruwa dan yasan halin Hajiyar, yana ko shigowa gidan ya hangi motar Hamid, daya ƙaraso kuma zai shiga falon ya soma jin irin zagin da Hamid ɗin ke surfawa Sakina, shiyasa ya shigo da sauri yaga ko dukanta yake yi. Alhaji ya kalli Hamid cikin tsananin ɗaure fuska.
Zo nan Hamid.
Ba musu ya bar ƙofar kitchen ɗin ya ƙaraso gaban Abba yana sunkuyar da kai ƙasa, Alhaji bai yi wata wata ba ya tsinka masa mari, a gigice ya ɗago tare da dafe kuncinsa yana dubansa zai yi magana.
Idan ka furta kalma guda ɗaya sai nayi ƙasa ƙasa da kai a gurin nan shashasha mara tunani kawai.
Haba Alhaji ya zaka mareshi yana son yin hukunci a gidansa sannan..
Idan baki yi mini shuru ba wlh sai nayi miki abinda ba zaki taɓa mantawa dani ba, munafukan banza munafukan hofi, kun zo kun faɗa masa ƙarya da gaskiya da yake mara hankali ne shi ya hau ya zauna yana surfawa ‘yar mutane zagi kamar tsohon bamaguje, idan duk kun ƙita to ni ina son Sakina dan tamkar ‘ya take a gurina.
Ya ƙare maganar yana nuna su da tsaya, Madina nan ta shiga taitayinta tana kama jikinta dan taga Alhaji yana da zafi sosai, Hamid yaja ya tsaya yana jin wani baƙin ciki a cikin ransa ace akan Sakina ce Mahaifinsa zai mareshi bayan akan gaskiyarsa yake, wani irin tsanarta yaji ya ƙara ɗarsuwa a zuciyarsa wanda yake jin lokaci yayi da zai rabu da ita ya yarda kwallon mangoro ya huta da ƙuda kawai. Alhaji ya isa bakin kitchen da kansa ya sassauta fushinsa yana cewa.
Sakina buɗe ƙofar Abbanku ne.
Da sauri Mufeeda ta buɗe ta isa gareshi tana sassheƙar kuka, ya kamo hannunta yana share mata hawaye, sai gasu baba ƙarami suma sun fito cike da tsoro kamar mage a kwali, sosai Alhaji yaji tausayinsu ya kama shi ya shiga kiransu yana jawo su jikinsa tare da share musu hawaye har yana ɗan yi musu wasa, haka ya jasu zuwa falo duk suka zauna, Sakina sai a sannan ne ta iya yin jarumta ta miƙe tare da gyara mazaunin ɗankwalin kanta ta isa gurin miyar ta rage wuta ta share hawayen ta kana ta fito falon, bata zauna a kujera ba ta samu gefen carpet ta zauna kanta a ƙasa.
Abba ina yini da ƙarfin jiki.
Lafiya lau jiki Alhamdulillahi. Sakina ina so ki bani labarin duk abinda ya faru, waye ya taɓawa Amaryar Hamid abinci?
Abba ba ruwan Mamanmu nine da baba ƙarami muka ɗiba muka ci saboda bata gama girki ba, kuma wlh mun ɗauka hajiya ta aiko mata da shi tunda munga kularta, sai da ma ta shiga ɗaki yin sallah kafin muka ci bata sani ba, anty Amarya kiyi haƙuri ba zamu sake ba.
Cewar Yaƙub cike da damuwa a fuskarsa da ya tari numfashin Alhaji, nan baba ƙarami ya gasgata zancen Yaƙub, Alhaji ya duba Madina yana cewa.
To ke kinji ga waɗanda suka taɓa miki abinci nan, da ace tun farko kin tsaya kin bincika lamarin a hankali ba zai kai ga sai kin sanar da Hajiya ba, bai dace daga zuwanki ba ki nima haɗa rikici irin wannan ba, dan haka duk abinda aka yi miki ba daidai ba ki fara bincike kafin ki yanke hukunci, ke kuma Hajiya idan munje gida ina da magana dake, sannan kai Hamid ban san kai rakarai bane sai yau, kawai ana faɗa maka magana ba bincike zaka hauka kana cin zarafin yarinya, kamar yadda ka auro Madina kana mararinta giyar soyayya ya ɗibeka to haka itama Sakina auren soyayya kuka yi bana haɗi ba, ka tsaya ka yiwa kanka adalci ka zama mutum tsayayye a gidanka, in ba haka ba wlh zaka jefa kanka a tudun dana sani, sannan..
Assalamu alaikum!
Sallamar su Yaya Ali da Hamza ne ya katse wa Abba Zancensa, suka ƙaraso cikin falon Alhaji yana cewa.
Kardar Hamid ne ya taso ku?
Basu bashi amsa ba sai miƙa masa gaisuwa da suka yi, Alhaji ya amsa tare da gabatar musu da gurin zama, suka zauna suka gaida da Hajiya da kuma Hamid, Sakina ma ta gaishesu amma Madina tayi biris dasu saboda haushin da Alhaji ya bata akan katse hukuncin da Hamid yayi niyyar ɗauka akan Sakina, shuru ne ya biyo baya daga bisani Alhaji yayi musu bayanin komai ya ɗaura da cewa.
Dana san ya kiraku to kafin ku tawo zan dakatar daku, gabaɗaya lamarin ne sunyi shi babu bincike, na rasa me Hamid yasha yake niman yin abu saikace yaro, kuyi haƙuri In Sha Allah tunda ina nan ni zan tsawatar da komai zaku iya tafiya.
Angode Alhaji Allah ya ƙara sutura, Hamid ayita haƙuri da su lamarin mata biyu sai ana kai zuciya nesa, ke kuma Sakina ki riƙe mutuncinki bana son sakarci ki tabbatar da kin fita haƙƙin kowa.
Gyaɗa kanta tayi yayin da yaya Ali ya kai aya a maganarsa, sai suka miƙe da nufin tafiya a nan ne Umma ta shigo falon suka jira ta ƙaraso duk suka gaisa, yaya Ali yace su tafi kawai dan Alhaji ya kashe maganar, yaya umma taso ta keɓe da Sakina amma Ali yace su tafi zai sauketa a gida dan a motarsa suka zo, haka suka yiwa mutanen falon sallama suka wuce cike da tausayin ‘yar uwarsu. Bayan sun hau kan hanya sosai Ali ya ja dogon tsaki.
Wlh Hamid ban taɓa sanin baida hankali ba sai yanzu, to idan ya gaji da Sakina ne mu muna sonta ya saketa ta dawo gida Allah zai bata mafiyinsa,
Yaya maganar bata kai haka ba, adai ƙara haƙuri kuma itama Sakinar kullun maganar da nake yi mata kenan tayi haƙuri komai zai wuce.
Cewar Umma, Hamza yace.
Lamarin dai duka haɗuwa zamuyi mu yi haƙuri, kuma ayiwa Hamid uzuri yanzu baya cikin hayyacinsa gigin amarci ke ɗibarshi, sai lokacin daya sake shi ne kafin zai dawo hayyacinsa.
Allah ya kyauta.
Yaya Ali yace yana mayar da hankalinsa kan hanya sosai, sai da suka kai umma gida kafin suka wuce inda zasu.
Gidan Hamid kuma, Alhaji ya haɗasu ya yi musu faɗa da Nasiha daga bisani ya sallami kowa ya tasa ƙeyar hajiya zuwa sashinsu. Aiko suna shiga ya rufeta da faɗa ko magana yaƙi bari tayi, yayi mata kaca kaca akan karta ƙara shiga lamarin gidan Hamid ya kula itama tana ƙara haɗa rikici, yace kuma karta sake ta ƙara aikawa amarya abinci in har ba zata aika tare dana Sakina ba, ta barsu suci abinda suke da shi a gidansu baya son tashin hankali, cikin tsananin ɓacin rai Hajiya ta shige ɗakinta tana jin Zuciyarta ba daɗi tare da ƙara tsanar sakina a cikin ranta, wanda take ganin duk itace ta jawo wannan faɗar da Alhaji yayi mata, wannan yasa ta ƙara ƙullatarta a cikin ranta.
Sakina kuwa su Alhaji suna fita ta miƙe ta tasa ƙeyar yaranta suka koma kitchen ta ƙarasa miyar suka kwashe abincinsu da tukunyar miyar suka kai ɗakin Mufeeda, dan tunda Hamid yayi aure nan ta mayar gurin cin abincinsu da yaran, saboda kar ma suyi abinda zai jawo fadar Hamid ɗin, nan ta saka musu tuwon suka soma ci tare da su duk da damuwar da take ciki yasa bata son ganin abincin, amma saboda tana so yaran suci kar su gane halin da take ciki yasa ta dinga tusawa ba dan tana jin yunwar ba, bayan sun gama tasa Mufeeda ta fita da plate ta kai kitchen ta wanke kana ta koma ɗakin suka cigaba da wasa da ƙannenta, Sakina kuma ta kwanta a gadon Mufeeda ta rufe ido badan tana jin barci ba sai dan ta yi tunanin makomar rayuwar aurenta, dan tabbas tana ganin lokacin barinta gidan yazo dan ba zata iya da irin wannan tashi hankalin ba, Hamid baya sonta, Hajiya bata ƙaunarta ga kuma Madina da irin nata salon makircin, da wanne zata ji.
[7/18, 9:03 PM] Rahma Kabir: *ƘAZAMAR AMARYA*
Na
©®Rahma Kabir MrsMG.
Wattpad @rahmakabir
Page 15.
Hamid kuwa miƙewa yayi jiki a sanyaye ya mufi ɗakinsa ya shiga tare da zama a gefen gado ya dafe kansa da duk hannunsa biyu, ranta a matuƙar ɓace yake, ya rasa me zai yiwa tunani, a lokacin ne Madina ta shigo ɗakin ta tsaya ta kama ƙugunta.
Yanzu shikenam ni banda sukuni a gidanka tunda mahaifinka ya goyi bayan Sakina, ya nuna ƙarara ita yake so. Ashe ba kada ƙarfin yanke hukunci a gidanka sai wanda mahaifinka ya yanke, gaskiya Hamid bazan iya ba ka sauya mini gida kawai, dan da tun farko nasan da haka da bazan taɓa yarda na aureka ka haɗani gida ɗaya da matarka ba.
Hamid ɗago kai yayi yana dubanta idonsa yayi jajir saboda ɓacin rai yace cikin damuwa.
Madina dan Allah kije ɗakinki a yanzu bani da natsuwar saurarenki, sannan ki saka a ranki ni Hamid bazan taɓa sauya miki gida ba domin hakan shi ne tsarina.
Gaskiya ba zan zauna ana danne mini haƙƙi na ba kuma ai…
Dalla ki fita mini a ɗaki kafin in huce haushina akanki.
Hamid ya faɗi haka a tsawace tare da zabura ya miƙe yana nuna mata hanyar fita, hakan ya tsorata Madina wanda yasa ta fashe da kuka ta fice daga ɗakinta tana ƙananun magana, tsaki Hamid yayi yana girgiza kansa dan takaici. Da kyar ya iya rarrashin kansa ya samu ɗan natsuwa, sai dai ya gama yanke duk abinda Sakina zata yi masa nan gaba to hukuncinta saki ne ba zai taɓa bari ma gidansu suji abinda tayi masa ba sai dai su samu labarin ya saketa, da wannan tunanin ya miƙe ya fice gabaɗaya daga gidan.
Bai dawo ba sai bayan sallar isha’i ya samu falon yayi shuru ba kowa, wanda ada ya saba samun yaransa suna kallo, da sun ganshi cikin farin ciki zasu fara yi masa oyoyo da sannu da zuwa, ƙofa kawai yayi dan duk laifin ya ɗaurashi ne akan Sakina data sauya zuwa ga mugun hali. Ɗakinsa ya fara shiga ya watsa ruwa kafin daga bisani ya saka jallaniya ya nufi ɗakin Madina, bedroom ya fara shiga ya samu bata nan sai dai kan gadonta a hargitse bata gyara ba, ga kuma datti a ƙasa na ciye ciyen data yi ɗazun na kayan zaƙi duk ta zubar dasu a nan, girgiza kai yayi yana jin abin nata ya fara yawa ba zai taɓa yarda da haka ba, ya juya ya nufi falonta a nan ya sameta kwance a kujera ha kular dambun ɗazu data ci a gefe, koda tas’ji gishowarsa bata motsa ba ta cigaba da danna waya tana murmushi, Hamid ya samawa kansa gurin zama yana dubanta, sanye take da ƙananun kaya rigar kamar vest ce sai ƙaramin siket iya cinya, gashinta a har gitse sai taunar cingom take yi.
Madina baki san na dawo bane kika yi biris dani haka? Meyasa kike son nuna mini halin da ban sanki da shi ba
In na ganka me kuma zanyi maka? Ai ka aureni ne domin ku haɗu kai da matarka kuna muzguna mini, mahaifinka ya yanke hukuncin da ransa yayi masa.
Wai maganar nan ba zata wuce ba ne a gunki, ban sanki da riƙo ba kuma ai na gama yanke hukuncin da zan ɗauka akan Sakina in har ta ƙara shiga lamarinki, yanzu tashi za kiyi kije kitchen ki sama mana abinda zamu ci dan gaskiya na gaji da cin abincin waje.
Da sauri Madina ta aje wayar hannunta ta tashi zaune.
Haba Hamid yaushe nazo gidan da har zan fara yin girki, gaskiya ni a gidanmu sai dai a dafa a kawo mini na ci, dan haka ni dole ne ka nima mini ‘yar aiki da mai girki dan banzo dan na riƙa wahala ba kuma kasan ina zuwa aiki, to da aikin zanji ko da da hidimar gidanka.
Hamid kallonta kawai yake baki sake har sai da ta kai aya kana ya sauke ajiyar zuciya, dan har ya fara jin ransa yana ɓaci da maganarta.
Madina wlh bazan ɗauki ‘yan aiki ba dan haka tsarin gidana yake, batun gidanku daban nan gidana daban bazai yuwu kice zaki shimfiɗa duk mulkin da kika ga dama ba sai abinda nake so shi zaki yi matsawar kina son samun aljanna, dan haka kula da abincina da tsaftar gidana ya zama wajibi akanki ko kuma na gwada miki ɗanyan kai irin wanda kike gwada mini a yanzu.
Madina kasa magana tayi dan yadda taga ya ɗaure fuska yana magana tamkar an sauya mata Hamid ɗin data sani ne, wanda yake nuna mata mugun so da ƙauna kamar zai cinyeta bata taɓa zaton zai riƙa yi mara gaddama akan duk abinda tace tana so ba, sai gashi ba aje ko ina ba ya fara nuna mata iyakarta.
Anya son da yake nuna mini kuwa ba yaudara bace dan ya samu ya aureni ne kawai ya mayar dani baiwarsa.
Motsin fitarsa taji yasa ta sauke ajiyar zuciya, Hamid ya fita zuwa babban falo ya zauna tare da kunna tv ya soma kallo, wanda sam baya fahimtar komai a cikinsa sai duniyar tunani daya faɗa, ya ɗauka in ya dawo gidan Madina zata faranta masa rai daga ɓacin ran ɗazun, amma sai gashi ita ƙara masa ma tayi, wato duk irin hangen kulawar da yake tunanin samu a gurinta ashe shirme ne babu wani tanadi data yi masa dan farin cikinsa, ta aureshi ne kawai ta miƙe ƙafa ta zauna sai dai ya zama bawonta, ana cewa namiji yana ƙara aure domin ya samu cikar farin ciki da natsuwa to amma shi kam yana ganin kamar wata matsala daban ya ƙara kunnowa kansa, yana zaune a haka yaji Madina ta faɗa jikinsa tana shagwaɓa.
Haba beb sai kayi fushi dani kuma daga wannan maganar, dan Allah kayi haƙuri ka daina fushi haka, tun rana kake abu ɗaya kar ka jawowa kanka wani ciwo fa.
Madina ta faɗa tana jan gemunsa, wanda a ranta sam bata so kawo kanta ba, amma saboda ta samu abinda take so dole ne ta sauke kai su shirya ta lallaɓashi ya samar mata ‘yar aiki, dan maganar da suka yi da Kausar kenan a waya tace ta zo ta bashi haƙuri ta tararrashe shi dan agunta ne kawai zai samu sassaucin halin da yake ciki, ƙila hakan yasa yayi mata abinda take so. Hamid sauke ajiyar zuciya yayi mai nauyi yana jin wani sanyi a cikin ransa take ya kawar da tunanin da yafa yi a kanta, ya dan saki murmushi yana cewa.
Na ɗauka ke ma zaki bi layin Sakina ce ku kaɗu ku saka mini hawan jini na mutu tun kwanana bai ƙare ba.
Da sauri Madina ta rufe masa baki da hannunta.
Haba ruhin Madina dan Allah karka sake faɗar haka ni taka ce kuma farin cikinka, bazan sake ɓata maka rai ba, duk abinda kace kana so shi zan yi, yanzu dai kaina ciwo yake yi mini wlh dana ɗaura maka koda indimie ne.
Ta faɗa tana yatsine fuska ta dafe gefen kanta irin dagaske ciwon yake mata, Hamid ya ɗagota yana dubanta.
Shine baki faɗa mini ba, kin sha magani kuwa?
Ban sha ba saboda banci wani abinci ba sai sauran danbun ɗazu, sai zaƙi dana aiki Jidda ta siwo mini sweet dasu cingom.
Bari naje na siya mana wani abu mu ci ko.
Beb nima zan ji.
Ok je ki shirya mu siya mu ci acan daga nan mu ɗana soyayya ko.
Dariya ta saki ta miƙe ta nufi ɗakinta taji daɗi sosai da fitar da zai yi da ita, hakan yasa ta gane shawarar da Kausar ta bata shi kawai zata bi ta samu kan Hamid. Cikin sauri ta shirya ta fito sa sameshi tsaye a falon yana kaɗa makullin mota, tunda ta fito yake kallonta dan riga da siket na atamfa ta saka sai ƙaramin gyale a kafaɗa, tayi ɗauri mai kyau.
Madina ko ba kwalliya tana yin kyau sosai.
Ya faɗa a cikin ransa yana jin ya samu matar nunawa sa’a, haka suka fita basu dawo ba sai wajen sha ɗaya da rabi, a ɗakinta suka sauka Hamid ya shiga bayinta yayi brush dan akwai nashi a nan, daya fito sai da ya kakkaɓe zanin gadon kafin ya kwanta, itama shirin barci tayi dan a gajiye suka shigo gidan, ta kashe wuta ta kwanta a gefensa, yau dai rungume ta yayi suka kwanta domin sun gama cinye soyayya a cikin mota, a haka barci yayi awon gaba dasu duka. Madina a cikin barci ta dinga sakar masa tusa saboda mugun ciye ciyen data yi yau, Hamid tun yana jin wari a cikin barci kamar mafarki yake har sai da ya farka yaga a zahiri ne, tashi yayi ya zauna yana jin wani maƙaƙi maƙaƙi a maƙoshinsa, gabaɗaya iskan ɗakin kamar an buɗe shadda mai wari, bai gama farfaɗowa daga yanayin da yake ba Madina ta ƙara gwara kwancinya rubda ciki ta saki wani mushen tusa mai ƙara da wari wanda yasa Hamid ya kusa faɗuwa a ƙasa garin saurin sauka a gado, da duka hannunsa ya toshe hanci yana jin kamar zai saki amai, dan har cikinsa ya fara juya masa, da sauri ya nufi ƙofa ya buɗe a hankali ya fice, sai a lokacin ne ya saki hancinsa ya shaƙi ƙamshin falon tare da sauke ajiyar zuciya, ɗakinsa ya nufa ya shiga ya kwanta dan in har yace zai cigaba da barci ɗakin Madina ƙarshe wayewar gari za a sameshi ya sanƙare ba numfashi, ji yayi dole ya raba ɗaki da ita da zarar ya biya buƙatarsa zai kama kansa, kuma ba zai taɓa yarda ta kwana masa a ɗakinsa bq ko tazo masa, shi dai zai riƙa binda dan bazai yarda da zubda yawu jikin bango ba, da saƙe saƙe barci ya ƙara ɗaukarsa.
Da safe Madina ke tambayarsa bai dawo ɗakin ba tunda ya tafi masallaci, Hamid yace cikin ‘yar dariya.
Ai tun tsakiyar dare kika koreni da warin tusa wanda ya kusa sumar da ni, anya Madina wani abu bai ruɓe ba a cikinki ba kuwa da kike irin wannan fidda sauti mai hamami.
Madina tsabar kunya sai da ta sunne kai ƙasa tama kasa magana, Hamid ya taɓe baki.
Idan ba kida lafiya gwara tun wuri mu je asibiti a duba lafiyar ki dan gaskiya wannan tusa bana lafiya ba.
Nifa lafiyata ƙalau, kawai inna ci kwai da yawa ne yake yi mini haka.
Har kwai nawa kika ci daya saka ki tusa haka.?
Madina ta yatsine fuska.
Bama fa da yawa na ci ba guda shida ne kawai, ina ganin har da ciye ciyen zaƙin dana yi ne a jiya.
Waro ido Hamid yayi yana dubanta.
Haba Madina kwai shidan ne ba yawa ai ni duk yawan sona da kwai baifi naci uku ba, bama kullum nake ci ba, gaskiya ki rage cinsa haka ki riƙa tausayina ni mai kawowa dan kwai shida kwana nawa kired zai ƙare, ga yanayin rayuwa sai addu’a.
Kai Hamid, yanzu sai ka saka kanka a cikin talaka? kawai dai maƙo ne da kai amma banga aibin cin kwai shida ba, nifa banƙi kullum naci ba.
Madina ni ba talaka bane amma a riƙa sara ana duba bakin gatari hidimomina da yawa. Kuma kwai ɗaya shine zai miki aiki a jiki sauran ƙiba zasu saka ki ki zama ƙatuwa, dan Allah a tausayawa aljihun Hamid karki zama mai almubazzaranci.
Sakin baki Madina tayi tana kallonsa Hamid har ya fice daga falon, kenan itace mai almubazzaranci dan taci kwai shida, anya Hamid ba irin mazan nan bane masu maƙo kuwa?
Ta faɗa a ranta dan sosai ya bata mamaki da maganarsa, saboda bata ga wani aibun cin kwai shida ba, kenan duk rayuwar data sabayi a gidansu bata isa tayi anan ba data ke ganin ta samu ‘yancin yin komai fiye da gidansu ma, kwafa tayi ta wuce ta zauna cushing tana ganin Hamid ya ɓoye mata mugqyen halinsa da yawa wanda sai yanzu ne yake nuna mata, ashe duk kashe kuɗin da yake yi mata dan ya samu zuciyarta ne kawai ba dan zai iya cigaba da shagwaɓa ta ba a gidansa.
Hamid fita yayi dan ya samo musu abin da zasu karya da shi saboda in ya biyewa Madina ba zata girka ba, ya dai barta tayi sati ɗaya ne kamar yadda ya yanke, da zarar ta cika sati ɗayan dole ta fara yi musu girki tunda Sakina ta zama mai taurin kai ya zuba mata ido ne itama yaga iya gudun ruwan iskancinta.
*****
Bayan wana biyu.
Tun bayan faruwar wannan lamari gidan Hamid ya zama shiru yaran tamkar basa gidan, da zarar sun dawo makaranta suke maƙalewa a gurin mamansu dan kar suyi wani laifi da zai jawo cin fuska ga Sakina, da zarar ta kammala aikinta da girki sai su natsu a ɗakinta ko su fita can bayan gidan wajen lambu suyi harkokinsu sai an kira sallar magrib suke dawowa ciki, suyi sallarsu a tare su ci abinci tare barci ne ke rabasu ko wanne ya kwanta a makwancinsa. Hamid bai sake bi ta kan Sakina ba bai nimeta ba itama bata nimeshi ba dan bata yarda su haɗu, sai dai suji maganarsa a falo shida Madina suna hidimarsu, in ya gadama ne yake kiran yaran su fita su gaisheshi, sai ya tambayesu ko akwai abinda suke so, in sun faɗa ya siyo musu in basu faɗa ba kuma shikenan, sam sun kasa sake jikinsu da shi dan kar suyi laifin da zai hasala ya sauke akan mamansu, yanzu ya zama kamar baƙo ne a gunsu.
Ranar Asabar su Mufeeda suka samu hutun makarantar boko da islamiya dan sun ƙare exam ɗinsu, suna dawowa daga makarana misalin ƙarfe goma na safe suka sauya kaya suka nufi gidan Hajiya dan sunce a can zasu yini sai dare zasu dawo, Sakina taso ta fita zuwa gidansu ta gaishe su daga can ta wuce gurin yaya Umma amma ta rasa taya zata tambayi Hamid, tasan ma ba zai bari ba ƙila ma ya samu damar gaya mata magana, haka ta haƙura ba dan ranta ya so ba, nan take tayi tunanin shiga maƙotansu wanda Hamid ya bata damar duk in wani abu ya taso ko bata tambaye shi ba taje tunda yasan bata fita, tunawa da maman Murja maƙociyarta ta aiko ba zata samu zuwa ba ranar auren Hamid saboda rasuwar da aka yi musu ta tafi Jigawa, hakan yasa ta yanke shiga gurinta dan tasan ta dawo saboda sunyi waya tayi mata gaisuwa, wajen sha ɗaya ta fito ta samu motar Hamid yana nan bai fita ba, dama asabar da lahadi bai fiye fita ba sai can rana haka, ta wuce ta fita abinta, aiko tana saka ƙafa a gidan maman Murja kiran Hamid ya shigo wayarta, ashe akan idonsa ta fita shi kuma ya fito daga sashin su Hajiya ya hangeta ta fice, kamar ba zata ɗaga kiran ba ta ɗauka ta ƙara a kunne ba tare da tace komai ba.
Rashin mutuncinki ya kai har ki fita ba tare da izini na ba ko, Sakina kin raina ni kin mayar dani banza a banza ko.
Gidan maman Murja na shiga saboda rasuwa da aka yi mata na shiga yi mata gaisuwa, kuma kai ne da kanka ka bani izinin shiga maƙota in har wani abu ya taso na Allah ya sanya alkhairi ko Allah ya kyauta.
To daga yau na soke haka, duk inda zaki shiga ki tambaye ni, dan haka ki juyo ki dawo tun kafin in nuna miki iyakarki.
Hamid na riga na shiga gidan dan Allah ka yi haƙuri yanzu zan fito.
Na dai gama magana in kuma zaman kanki kike yi sai in sani.
Ƙit ya kashe wayar yana gama faɗar haka, Sakina wani irin miyau ta haɗiye da baƙin ciki tana tunanin ya zata yi? gashi ta riga ta shiga gidan har yaran sun ganta.
[7/20, 6:40 PM] Rahma Kabir: *ƘAZAMAR AMARYA*
Na
©®Rahma Kabir MrsMG.
Wattpad @rahmakabir
Page 16.
Sakina ƙarasa shiga ciki tayi dan ba zata iya juyawa ba, kuma ta san koda ta koma ba zai fasa yi mata faɗa ba dan haka ta tsaya a ƙofar falo ta buga, Murja ce ta buɗe tana ganinta ta saki murmushi ta gaisheta, Sakina cikin sakin fuska ta amsa tana cewa.
Mamanku tana nan kuwa.?
Eh bari na kirata ki shigo ciki.
Cewar Murja sai ta juya da sauri ta nufi ɗakinta maman, Sakina ta shiga ciki ta samawa kanta gurin zama a cushing, ba jimawa maman Murja ta fito daga bedroom ɗinta cikin fara’a ta zauna rana cewa.
Baki fushi dani ba ban samu leƙowa ba ganin amarya.
Haba dai Maman Murja nice ya dace na shigo na fara gaisuwa tunda mutuwa tafi ƙarfin wasa, ina kwana ya yara da kuma ƙarin Haƙuri, Allah ya jikanta da Rahma ya gafarta mata.
Ameen ya rabbi, yara duk ƙalau muke, ya haƙuri da juriya dan nasan kina cikinsa.
Alhamdulillah muna ta fama, kinsan namiji ya ƙara aure dole sai ka bashi lokaci kafin ya dawo hayyacinsa.
Hakane, dama wlh ina so mu haɗu muyi magana, dan haka tashi muje ɗakina dan maganar sirri ce.
Cewar maman Murja tana miƙewa cikn murmushi, Sakina ta miƙe itama tabi bayanta zuwa ɗakin, a gefen gado suka zauna maman Murja tana duban Sakina.
Wai maman Mufeeda kafin auren Hamid kin niwa kanki mafita kuwa? kin san fa mazan nan sai ana yi ana maganinsu gudun wulaƙanci.
Ban fahimceki ba maman Murja kiyi mini dalla dalla.
Hmmm kin san Allah Sakina yadda kika ganni nan ban zauna haka ba shiyasa kika ga har yau babansu baya maganar ƙara aure, dan ba zai yuwu na gama shan wahala akansa ba wata banza tazo ta shiga tsakaninmu ba, shiyasa tun wuri na nimawa kaina mafita wanda ko aure zai ƙara bai isa ya yi mini iskanci ba. Mace yanzu ko ita kaɗai ce a gidan miji yana da kyau ta nima maganin mallaka ta kame mijinta da kyau ta yadda zai riƙa yi mata biyayya akan komai, shiyasa naga wautarki da kika bari Hamid yaje ya ɗauko miki kishiya, amma ko a yanzu ba zaki yi ƙasa a guiwa ba, ki tashi tsaye ki nimawa kanki ‘yanci dan na tabbatar wlh sai kinga sauyi a gurinsa saboda gigin aure yana ɗibarsa.
Anya kuwa? ni bazan iya haka ba gaskiya, gwara ya cuce ni da in kauce hanya akansa, dududu duniyar kwaya nawa take Maman Murja.
Aiko ki zauna ki cigaba da ƙunsar baƙin cikin da Namiji in har ba zaki yiwa tufkar hanci ba, matan zamanin nan sun waye basu zauna haka ba sai da maganin mallaka suka samu kan mazajensu, bawai na cutarwa zaki samu ba wanda zaki mallake zuciyarsa ne yaji yana mugun sonki da shakkar ɓacin ranki, kuma duk abinda kika ce kina so shi zai yi miki, ita kishiyar taki kin san dame da shigo gidanki? wlh ki farka daga mugun barcin da kike yi in ba haka ba kina ji kina gani zaman gidan Hamid zai gagareki.
Maman Murja ta ƙare maganar tana riƙe haɓa tare da ƙanƙance idonta akan Sakina, Sakina ko shiru tayi tana nazarin maganarta sosai, dan tabbas an kawo gaɓar da aurenta ke lilo tun ba a je ko ina ba da zuwan Madina, tana nisa tana cewa.
Gaskiya ne maganarki amma zanyi tunani akai da shawara, duk abinda na yanke zan kiraki ko a wayane muyu maganar.
Ki aje batun shawara da tunani ki samawa kanki ‘yanci in dai kina son zamanki ya ɗaure a cikin gidansa, sannan in kin shirya akwai wani malami da zan kaiki wlh aikinsa kamar yankan wuƙa ne, sannan karki ƙasa a guiwa wajen tuntuɓar yayyinki da suke malamai su baki laƙanin mallaka, ke ga abu ma a gidanku, duk sai ki haɗa ki riƙe Hamid tamau ba yadda zai riƙa bijirewa umarninki wlh ko uwarsa Albarka.
Gaskiya na yarda da zancenki dan haka ki bani lokaci kinsan yanzu gidan nawa sai a hankali Hamid ya juya mini baya sosai a ɗarare nake, bari naje kar yaga na daɗe yayi mini faɗa.
Ai kinji irinta, shida ya dace yaji tsoronki amma ke ce kike jin shoronsa haka, gaskiya ki yiwa kanki karatun ta natsu kisan halin da kike ciki.
Sakina murmushi tayi mata tana yi mata godiya tare da gasgata maganarta, nan ta miƙe suka yi sallama suka fito, har gate Maman Murja ta rakata tana ƙara jaddada mata maganar, Sakina dai gyaɗa kai kawai take yi amma hankalinta yayi gida, haka suka rabu sai ta fito ta mufi gate ɗin gidansu Hajiya, dan wajen Alhaji kawai zata je shine zai shiga tsakaninta da Hamid, tuni ta aje maganar maman Murja a gefe domin kashe matsalar dake gabanta da Hamid shine a yanzu ya tsaya mata a rai.
Alhaji tun bayan ranar da rikicin nan ya faru, ya yiwa Hajiya mugun gargaɗi wanda har barazana yayi da aurenta akan in har bata fita sabgar gidan Hamid ba to wlh zata tafi gidansu, kar taga sun tsufa hakan ba zai hana ya rabu da ita ba, sai da ya kwana biyu yana mitar lamarin dan Alhaji yana da faɗa sosai, musamman in aka yi abu na rashin kyautawa ko rashin gaskiya, Hajiya sai da tayi dana sanin zuwa gidan Hamid ta shigarwa Madina faɗa, wanda da kyar ta samu ta shawo kan Alhaji tana bashi baki da haƙuri akan ba zata ƙara ba, sai dai kuma tayi matuƙar ƙullatar Sakina a ranta wanda a yanzu take ganin gwara Hamid ya saketa su huta dan hakan ne mafita, sai dai tayi alƙawarin ba zata sake shiga gidan ba in ba Alhaji ne yace taje ba, haka ta sanar da su Asma a waya suma sai zagin Sakina suke yi suna kiranta da matar ƙaddara, sosai suka shiryawa duk ranar da suka zo Kaduna su ƙare mata tanadin rashin mutunci.
Yau koda su Mufeeda suka shiga gidan dan suyi musu yini kadaran kadahan Hajiya ta amshe su, dan sosai baƙin jinin uwarsu ya shafesu, yadda take sakin musu fuska da wasa sam basu ga haka ba sai a gurin Alhaji, Mufeeda itace ta fahimci haka saboda hankali ya fara shigar ta, amma sauran yaran ko a jikinsu basu gane komai ba, shiyasa suketa wasansu amma Mufeeda sai duk ta jita a takure sai ma aiki da Hajiyar keta sakata, sai duk ta ƙosa La’asar tayi ta tattara ƙannenta su tafi gida dan ba zata jure zama har bayan magrib ba. Alhaji yana zaune a farafajiyar gidan cikin wata rumfa zaune a farar kujera yana karanta wani littafin musulunci, Sakina bayan ta buga gate mai gadi ya buɗe mata, tana hango Alhaji taji wani sanyi a ranta sai ta wuce gurinsa ta isa da sallama, Alhaji ya ɗago fuska sake yana amsawa, har kasa ta tsuguna ta gaishe shi ya amsa kana yayi mata umarni ta zauna a ɗaya daga kujerun da suke gurin, ta sunne kai tana cewa.
A’a Abba yanzu zan wuce dama na kawo maka maganar Hamid ne.
Alhaji ya ajiye takardan dake hannunsa kan farin table yana dubanta, nan Sakina ta samu damar zayyana masa yadda suka yi dashi kan shiga gidan maman Murja, ta ƙara da cewa.
Abba wlh bazan iya juyawa ba saboda na shiga gidan yaranta sun ganni gudun kar abin ya zama magana na shiga, tunda ba zama zanyi ba iya gaisuwa zanyi mata na fito, shiyasa dana fito daga gidan na tawo nan dan ka bawa Hamid haƙuri dan nasan sai yayi mini faɗa ni kuma wlh bana son rikicinsa ne.
To ai banga wani laifi da kika yi ba amma jeki cikin gidan ina zuwa.
Sakina ta miƙe tana cewa to kana ta nufi gidan dan ta gaishe da Hajiya ta kuma jira Alhaji, tana shiga ta samu su baba ƙarami suna ta wasa a falon da gudu Rauda taje ta rungumeta tana yi mata Oyoyo, cikin fara’a ta tarbeta su Yaƙub suna yi mata sannu da zuwa, hayaniyarsu yasa Hajiya leƙowa tana masifa.
Nifa bana son hayaniyar nan mutum yana mafa da ciwon kai ku ƙara masa wani damuwar.
Ganin Sakina yasa ta haɗe rai bata ma amsa gaisuwar data yi mata ba tace.
Meya kawoki gidana? maza koma in da kika fito bana gayyarki, tunda ba kida mutunci to nima ba zaki taɓa samun fuska a guna ba, dan aurenki da Hamid babu inda zai je ba zamu iya ba, da tun farko munsan haka kike wlh ba zaki taɓa aurensa ba, yadda kike son Yaƙub ɗanki ko baba ƙarami nima haka nake son Hamid, duk cikin ‘ya’yana nafi sonsa saboda yana yi mini biyayya duk abinda nake so to shi yake so, dan haka baki isa kizo kice zaki tarwatsa masa farin cikinsa ba in barki.
Dan Allah Hajiya kiyi haƙuri ni babu komai a zuciyata sai alkhairi, kuma ban hana Hamid yayi aure ba adalci kawai nake buƙata, yanzu ma dana shigo Abba ne yace nazo na zauna na jirashi.
Tsaki Hajiya taja tana wucewa kitchen ranta a matuƙar ɓace, tunda ta ambaci alhaji to ba tada magana dole ta bari ta zauna a falon dan bata mance gargaɗinsa ba a kanta. Alhaji kuwa wayarsa ya ɗaga ya kira Hamid akan yazo yanzu yana son ganinsa, ba ɓata lokaci sai ga Hamid yazo ya tsuguna Abba yace ya zauna, sai yaja kujera ya zauna, sai ya ɗaga wayarsa ya kira Sakina tana ganin Abba ne bata ɗaga ba ta fito kawai dan tasan bai wuce yace taje ba, ilai kuwa tana fita ta hango Hamid cikin sauri ta isa gurin ta tsuguna Abba ya sata ta zauna itama, nan yace Sakina ta faɗa masa abinda ta sanar dashi ɗazun, ta shiga yi masa bayani kamar yadda ta faɗa masa, data kai aya ya cewa Hamid.
Anyi Haka?
Eh! ya bashi amsa a takaice fuskarsa a dagule, Abba yace.
Hamid inaso kayi haƙuri kayi mata uzuri tunda har ta riga ta shiga gidan, ke kuma tunda yace ya soke fitarki ko ina zaki dole sai kin tambaye shi to ki tabbatar da kin nima izininsa kafin ki fita, zaman auren nan dole sai kunyiwa juna uzuri kun yi haƙuri kafin zai ɗaure, ada bansan ku da irin wannan rikicin ba sai a yanzu, dan haka ku sani girma kuke yi bai dace kuna irin wannan ba, Sakina tashi ki tafi Allah yayi miki albarka.
Ameen tace masa tare da godiya ta miƙe tayi masa sallama ta wuce ta ƙaramar ƙofar daya ratsa ta gidansu ta wuce gida. Abba ya mayar da dubansa ga Hamid ya rufesa da faɗa sosai har sai da ya dinga bashi haƙuri akan zai gyara kafin yace.
Bana son na kuma jin ka tayar da maganar saboda bana so akai gaɓar da yarinyar nan zata raina ka, dan in har hakan ya faru ba zaku ji daɗin zama da juma ba, karka kure haƙurinta ina gaya maka, kuma ka zama mai adalci ka tuna tsawon shekarun da kuka yi da ita, wannan amaryar taka gobe ne zata cika sati guda dan haka karka nuna tafi Sakina daraja saboda giyar soyayya, dan wlh koda goma ta lalace tafi biyar albarka. Ka tashi ka tafi.
Hamid ya miƙe yana godiya kana ya wuce zuwa gidansa. Koda ya isa falon ba kowa dan haka kiran Sakina yayi a waya dan ba zai tsaya ɓata lokacin kwara murya yana kiranta ba, tana ganin kiransa ta ɗauka yace ta fito falo sai ya kashe wayar, miƙewa tayi daga kwanciyar da tayi a gado, ta fito falon ta samu guri ta zauna yana wasa da yatsunta, Hamid saida ya ɓata kusan minti biyar baiyi magana ba, daga bisani ya sauke ajiyar zuciya ya soma magana.
Kina ganin kin tsira ne da kika kai karata gurin Abba? to ina gargaɗinki ki daina haɗani da Mahaifina dan bazan ɗauki haka ba, wlh idan baki wasa ba zan datse igiyar alaƙar dake tsakanina dake dan na gaji da halinki, sannan batun girki baki isa kice sai bayan wata ɗaya zaki yi ba, duk da kin bani hutu kin barwa amarya ni saboda baƙin kishi to wajibi ne ki yi girki duk bayan kwana biyu in Madina tayi, dan haka gobe in Allah ya kaimu Madina zata fara girki zata yi na kwana biyu daga bisani sai ki amsa kema kiyi kwana biyu, haka zaku riƙa yi har ta cike wata gudan data ɗauka kafin kwana ya dawo gunki. Sannan kamar yadda na tsara girkin safe ke ce zaki riƙa yi duka gidan saboda Madina zata fara fita aiki jibi monday in Allah ya kaimu, aikin gida ki riƙa tayata tunda ke kina gida ba inda kike zuwa, da fatan kin ji abinda nace.
Sakina sai da tayi jim kaɗan kafin tace.
Shikenan Allah ya bani iko yanzu akwai abinda kake so a dafa ne.
Eh ki yi mana tuwon shinkafa miyar kuka kisa wake a ciki kuma yaji nama, Madina kuma ki dafa mata koda taliya ce nasan ba lallai taci tuwon ba.
To, tun daga safe har dare zan girka abincin?
Eh kiyi haka ɗin, ita ki mata taliya da miya nasan zata ci har dare, zan fita yanzu ki yi mini lis ɗin abubuwan da babu.
Akwai komai dan babu abinda ya ƙare sai kwai ne da madara suka kusa ƙarewa.
Wani irin kwai da madara? da yawa fa na siyesu kafin biki nan, na tabbatar zasu yi mana kusan wata. Amma ina zuwa nasan Madina ce ma.
Ya faɗa yana miƙewa zuwa ɗakinta, Sakina da ido ta bishi dan ta jira fitowarsa tunda yace yana zuwa, maganganun maman Murja ne yake yawo a zuciyarta wanda kusan duk abinda ta faɗa gaskiya ne, in har bata ɗauki mataki ba to haƙiƙa haka rayuwarta zai zama abaibai a gidan Hamid dan ba tada ‘yanci ko galihu tamkar zaman dole yake yi da ita. Hamid yana shida ɗakin Madina ya samu tana shan haɗin madara data haɗa, da kallo ya bita yana cewa.
Me kike sha a kofi.?
Madara da milo ɗanɗana kaji shegen daɗi gare shi, wlh yana mugun kashe mini kwaɗayi in na haɗasu irin haka, kullun sai na haɗa saboda daɗinsa..
Madina kina nufin madara da milon gidan nan kike yiwa wannan haɗin?
Eh mana, to a ina zan samesu in ba a gidan nan ba.
Hamid wani waro ido yayi waje ya kama ƙugunsa da duka hannunsa yana gyaɗa kai, daga bisani ya saki hannunsa ya nunata da tsaya.
To daga yau karki ƙara yi mini wannan shashancin, ko an gaya miki ni mai kuɗin banza ne da zaki riƙa yi mini almubazzaranci, dama tunda aka ce kwai da madara dun ƙare, to kace na fara zargi dan kince kina cin kwai shida a rana. Dan haka ni bamu saba wannan wasa da kayan kuɗin ba, a hankali muke binsu har su ƙara, daga yau in zaki ci kwai guda biyu ya ishe ki, madara da milo kuwa in ba a tea ba ban yarda ki ƙara shansu haka nan ba, kinji na faɗa miki.
Madina miƙewa tsaye tayi tana ƙanƙance idonta tsabar rashin kunya.
[7/20, 7:32 PM] Rahma Kabir: *ƘAZAMAR AMARYA*
Na
©®Rahma Kabir MrsMG.
Wattpad @rahmakabir
Page 17.
Madina tace cikin gatsali.
Yanzu ka tabbatar mini da kai Alhajin Maƙo ne, duk dukiyar da kake dashi meye na mitar kwai da madarar da nake amfani dasu, ohohh matarka ta kai maka gulmata kazo kana ƙare mini gargaɗi akan ɗan abinda bai taka kara ya karya ba, to ni a gidanmu haka na saba yi kuma a gidan mijina zanyi abinda yafi haka dan ina da cikakken ‘yanci.
Madina ni kike faɗawa haka.
Eh na faɗa maka tunda har ka iya rabani da gidanmu to dolenka ne ka ɗauki duk ɗawainiyata wlh, cin kwai da madara yanzu na fara idan ba zaka iya ba sai ka je ka faɗawa Hajiyata ka gaza da riƙeni su zo su ɗaukeni.
Tana gama faɗar haka ta ɗauki kofin haɗin madararta ta wuceshi ta buɗe ƙofar tare da banko masa shi, ta barshi a tsaye baki sake cike da tsantsar mamakinta, tunda yake da Sakina bata taɓa yi masa irin wannan rashin kunyar ba shiyasa in Madina tayi masa yake mamakin yadda bata jin nauyinsa balle kunyar mayar masa da duk abinda yazo bakinta. Madina tana fitowa falon ta ƙarasa gurin da Sakina take zaune ta tsaya tana cewa.
Duk munafurcinki zai ƙare akanki baki isa ki haɗani da Hamid ba ni da shi mutu karaba takalmin kaza, kwai da madara yanzu na fara sha sai ki sauya wani salon dan wannan bai samu muhalli ba.
Tana gama faɗar haka ta wuce ta zauna tare da cigaba da shan madarar, Sakina cikanki bata ce mata ba dan ba tada lokacin ɓatawa wajen musayar magana da ita, Hamid kam maganar Madina yaji yasa shi fitowa falon sai dai koda ya fito ya hangeta zata zauna, bai bi ta kansu ba ya wuce ɗakinsa ya shirya ya fito yana duban Sakina.
Ki dafa tuwon kawai kibar batun taliyar dana ce kiyi, anjima in zan dawo zan tawo da madarar da kwai.
To tace masa sai ta miƙe ta wuce kitchen, Madina kuwa har ya kusa fita ta dakatar dashi.
Hamid ka tawo mini da abincin da zanci dan bana cin tuwo.
Ƙala bai ce mata ba ya fice abinsa, Madina turo baki tayi ta miƙe da sauri tabi bayansa har ya shiga mota ta tsaya a jikin window tare da marairaice fuska.
Farin cikin Madina dan Allah ka daina fushi dani, taya daga ana faɗa maka magana zaka zo ka rufeni da faɗa, dan Allah karka bari maƙiya suji tsakaninmu, kuma tunda kace baka son ina cin kwai da yawa In Sha Allah zan rage amma ka daina yawan mini faɗa ban saba da hakan bane shiyasa.
Shikenan ni zan fita sai in na dawo.
To ai baka ce mini ka haƙura ba, kuma me zaka tawo mini dashi anjima.
Ai Madina mamaki kike bani wlh amma ya wuce, kiyi mini text ɗin abinda zan kawo miki amma ki nima abincin ranar da zaki ci, kuma gobe In Allah ya kaimu zaki fara girki dan haka ki kwana da shirin haka.
Sai ya tada mota Madina bata iya magana ba ta matsa yaja mota yayi ribas ya wuce, jiki a sanyaye ta juya falo sam Hamid ya kasa fahimtarta ita fa girki gabaɗaya bata ma iya ba, sannan yadda yake nuna mata shi ɗan ra’ayi ne bata jin zata jure domin itama tana da nata ra’ayin, sauran madarar ta ɗauka ta wuce falonta ta zauna, sai ga kiran Kausar ya shigo wayarta da sauri ta ɗaga dan dama tana son suyi magana.
Ƙawata dama haka aure yake? Gaba ɗaya Hamid ya sauya fa, sai wani ra’ayi yake nuna mini ban isa inyi yadda nake so ba a gidansa.
Hahaha me aka fara ma ai tukunna ma, Madina na gaya miki aure fa zaman gaskiya da gaskiya ne yanzu ne zai gane asalin halinki kuma kema yanzu zaki gane nashi. Bani labarin me ya faru.?
Nan Madina ta soma bata labarin komai, Kausar taja guntun tsaki.
Madina dole zaki aje rayuwar gidanku fa ki fara dasa sabuwar rayuwa a gidan Hamid, ba zai yuwu kina yi masa almubazzaranci ba kice bai isa yayi magana ba, sangarcin da Hajiya tayi miki daban nan gidan aurenki daban fa.
Hmmm wai ma girki yace zan fara gobe kuma ni babu abinda na iya, wlh zatona zai yarda da ɗaukar mini masu aiki.
Tunda kin fahimci ga ra’ayinsa sai ki bishi a hankali sai kiga kin sauya shi cikin ruwan sanyi, yanzu dai ki nima girki mai sauki kiyi, in ma ya fahimci baki iya ba da kansa zai samawa kansa mafita.
Kausar wlh ban iya komai ba in dai ba farar shinkafa ba ko farar taliya sai indimie.
To kiyi shinkafa da miya ki haɗa da cosilo, zan yi miki voicing yadda zaki haɗa sannan ki shiga youtube ki duba miyar stew da cosilo nasan zaki iya tunda ba abu ne mai wuya ba.
To shikenan ina jiran voicing ɗinki nagode.
Da haka suka yi sallama Madina tana sauke ajiyar zuciya da jin dole zata lallaɓa Hamid dan ba zata jure yin girki ba.
Sakina.
Kamar yadda ya umarce ta haka ta yi musu tuwo ta gama ta saka nata taci kana ta koma ɗaki ta kwanta dan ta huta, a sannan ne maganar data yi da maman Murja ya faɗo mata a rai, sam ta kasa samun natsuwa da yin haka domin in har tace zata kauce hanya dan samun farin ciki a gidanta, to kamar ta butulcewa Allah ne, domin tasan ya jarabceta ne domin ya gwada imaninta muddun ta nima maganin mallaka tofa ta kasa jure wa jarabawarta, kuma sakamakon abinda zai biyo baya nan gaba ba zai yi mata kyau ba, mutuwa zata iya ɗaukarta a ko wani lokaci dan ba zama ya kawo mu duniya ba kuma tabbas bautar Allah da jin tsoronsa shine zai tseratar damu daga azabar wuta, ba zata ɗauki alhakinsa ba akan ɗan farin cikin da ba dauwamammiya bace, data rasa imaninta akan Hamid ta kauce hanyar Allah to gwara auren ya mutu gabaɗaya ta tsira da imaninta, dan haka ta yanke ba zata taɓa bawa shaiɗan ƙofar zai ci gabala akanta ba, kuma itama maman Murja dole zata ja baya da ita dan ba zata cigaba da mu’amala da wacce bata sanya tsoron Allah a zuciyarta ba, da wannan shawarar ta rufe babin maganar ta ɗaga waya ta kira yayarsu Jalila wacce take aure a kano, yarinyar yayan babansu ce kuma suna mugun shiri da ita. Tana ɗaga wayar suka gaisa cike da farin ciki tana cewa.
Sakina naji magana mara daɗi a gurin Umma akan mijinki, kita Haƙuri kinji wata rana sailabari wh naso zuwa bikin nan amma kuka dage akan in barshi ba taro za kuyi ba.
To yaya Jalila haƙurin shine ya zama wajibi na yi, amma wlh auren gabaɗaya ya fice mini a rai.
Ki daina faɗin haka kodan saboda yaranki, kuma dukkan tsanani yana tare da sauƙi. Yanzu abinda nake so dake ki tsaya kiyi gyaran jikinki kafin ki amsa girki tunda umma tace wai kin basu wata guda saboda wauta.
To ya zanyi yaya Jalila? hakan ya nuna mini shiyasa na basu dama. In Sha Allah zanyi gyara dan har Yaya Falmata tace zara haɗani da wata mai gyaran jiki.
To madalla cikin satin nan akwai kaya da za a aiko mini daga Sokoto, in sun zo zan saka miki wasu a mota ki yi amfani dasu suna da kyau sosai.
Nagode yaya Allah ya saka da alkhairi.
Ta amsa da amin kana suka dan taɓa hirar zumunci daga bisani suka yi sallama.
***
Hamid.
Sai bayan sallar Isha’i ya shigo gidan, yau ya samu yaran suna kallo a falo ba ƙaramin daɗin hakan ya ji ba, Rauda da gudu taje ta rungume shi ya ɗagata sama yana yi mata dariya, haka suka ƙaraso falon Iro yana biye da shi a baya riƙe da leda guda biyu, ya ajiye a center table ya juya ya fita Hamid ya zauna yana cewa.
Ina mamanku? jeki kirata tazo.
Ya cewa Mufeeda, da sauri ta je ɗakin ta kirata Sakina ta fito saye da doguwar rigar atamfa ta zauna a cushing tana yi masa sannu da dawowa. Ya amsa fuska a ɗan sake kana yace.
Ga madara na kawo da kwai kirad shida, ki ɗauki kired huɗu ki aje a ɗakinki in zaki amfani dashi ki riƙa ɗiba, amma ki bari waɗanda suke kitchen su ƙare, sannan madara gashinan huɗu ne ki ɗauki uku shima ki aje nasan kina ƙoƙarin adanawa ba, sannan milo gwangwani ɗaya na siya ki aje shi a kitchen kawai.
To tace masa ta miƙe ta wuce ta ɗiba iya abinda yace ta adana taje ɗakinta ta ajiye, kwai da Iro ya shigo dasu shima ta je ta kai kired huɗu ɗakinta kana ta yi masa sai da safe ta shiga ɗaki. Hamid ya miƙe da sauran ledan siyayyar ya nufi ɗakin Madina, ya samu kallo take yi ya zauna suka gaisa kana yace.
Ga madara nan gwangani ɗaya nasan zai kai miki wata guda naki ne ke kaɗai, akwai gwangwanin milo a kitchen wannan duk zaku riƙa amfani dashi, sai kwai kired biyu shima nasan zai kai miki wata ɗaya, ga kuma abincinki nan bari naje dinning naci tuwo ina zuwa.
Yana kaiwa nan a maganarsa ya fice bai jira mai zata ce ba, dan bakinta a buɗe yake tana mamaki tare da kallonsa har ya fice, wato dagaske yake ba zata yi wandaƙa da madara da kwai ba shiyasa ya yanke yi mata haka, aiko zata bashi mamaki dan ba zata taɓa fasa yin yadda ta saba ba in ya ƙare dolensa ya siyo mata bai isa yace wai wata zata yi dasu ba, tayi ƙofa tana girgiza kai akan dole zata gyara masa hankali wlh.
Hamid tunda ya fara cin tuwon nan ya mayar da natsuwarsa gabaɗaya a nan, sosai yaji daɗin tuwon dan rabonsada abinci mai daɗi haka tun kafin bikinsa da Madina, yayi kewar abincin Sakina sosai wanda yasa shi yau sai da yaci tuwon da yawa har ya nima yin mugun ciki, daya gama ne ya miƙe yana cewa yaran suje su kwanta dare yayi kana ya wuce ɗakinsa yayi wanka ya fito ya shirya kwanciya, sai ya zo Kofar ɗakinsa ya murza key ya je ya zauna a kujerar hutu da take a ɗakin ya kunna syatem ɗinsa ya saka wani action film yana kallo hankalinsa kwance. Madina shuru ahuru Hamid zai zo ba har barci ya fara damunta hakan yasa ta shirya yin barci ta fito zuwa ɗakinsa, yana jin ta kama handle ɗin ƙofarsa ta murɗa sai ya rage ƙarar film ɗin da yake kallo, yayi banza da ita dan yana jin tana bugawa tare da kiran sunansa, sai da ta gaji dan kanta ta juya ranta a ɓace ta shiga ɗaki ta kwanta tare da tura masa text.
Ni zaka wulaƙanta Hamid saboda ka samu abinda kake so a jikina ko, wato kaci moriyar ganga ka yada korenta, babu komai ai nasan hanyar gidanmu in baka da buƙatata zan koma can kawai.
Hamid koda ya karanta dariya yayi dan yasan cika baki ne kawai take yi, shi kam so yake yayi maganinta akan rashin kunyar data yi masa ɗazun kana bai mance tusar data yi masa jiya ba, shiyasa yayiwa tukfar hanci gwara ya haƙura da kwana da ita dan tasan shima ba kanwar lasa bane. Ya gyara zama ya tura masa text.
Haba Madinar Hamid kiyi haƙuri, gaskiya bazan iya kwana dake ba kina sakar mini tusa ki nima halakani da sauran kwana na, shiyasa yau na zaɓi ki kwana a ɗakinki nima na kwana nawa ɗakin, kin ga in kin so saiki haƙura da cin kwai shida da wasa da madarar da kike yi kina kumbura cikinki da tusa.
Ya tura mata, tsaki taja dan ta gane da gangan ya yi mata haka, ta kasa haƙuri ta mayar masa da saƙo.
To ai nace na bari kuma duk yau banci kwai ba madara ne kawai na sha kuma shi baya saka ni tusa. Ni bazan kwana ni kaɗai ba in ba so kake yi matarka ta yi mini dariya ba.
Koda Hamid ya karanta dariya yayi kana ya ɗauki syatem ɗinsa ya buɗe ɗakin ya fito ya nufi ɗakinta, a tare suka kwana a ranar cike da soyayya, Hamid yana son Madina sosai wanda baya iya jure dogon fushi da ita, yana yi mata uzuri matsayinta na baƙuwa a gidansa da kuma yarinta dake damunta. itama in tace bata son Hamid tayi ƙarya dan sosai take jinsa a ranta, saboda ya kasance zaɓinta komai nashi yayi mata amma ban da murɗaɗɗen halinsa daya ke nuna mata a yanzu, kuma ta ɗauki ɗamarar sauya shi ko ta halin ƙaƙa dan ba zata jure yana nuna mata isa da mallaka ba.
Da Safe.
[7/21, 12:01 PM] Rahma Kabir: *ƘAZAMAR AMARYA*
Na
©®Rahma Kabir MrsMG.
Wattpad @rahmakabir
Page 18.
Da safe Hamid da wuri ya shirya ya fito ya samu dinning cike da kayan abinci Sakina ta haɗa musu abin kari, kunun gyaɗa da ƙosai sai soyayyen irish da kwai, sai da ya ɗan saki murmushi saboda jin daɗin abinda ya gani dan yayi kewar kunun gyaɗa, haka ya juya zuwa ɗakin Madina ya shiga ciki ya sameta kwance da alama ko wanka bata yi ba tana nan naɗe cikin bargo, ga waya a hannunta da kullun safe shi take fara karyawa dashi kamar ibada.
Madina ba dai har yanzu ba kiyi wanka ba.
Wlh na kasa tashi ina ga sai anjima zanyi.
Ta bashi amsa miyau cike da baki Hamid kawar da kai yayi dan takaici, Madina ta matsa jikin bango ta fetsar da miyau ta dawo tana cewa.
Da me zamu karya? ko zaka fita kayi mana oder ɗin sinasir da miyar ganye shi nake sha’awa.
Kinyi sallah da kike maganar karyawa? Madina gaskiya na fara gajiya da tara miyau nan da kike yi a baki wlh in kina magana tsigar jikina tashi yake, sai naji zuciyata tana tashi kamar zanyi amai.
Kai Hamid nafa gaya maka dalilin miyau nan kuma ni tun ɗazu nayi sallah.
Allah ya kyauta, amma ki sani ni bana son ƙazanta, ji ɗakinki ina ga tunda aka kawo ki baiga tsintsiya ba, ga ƙura har ya fara samun muhalli a wajen madubi, yau dole ki gyara ɗakunanmu tunda kin fara girki, ki gyara mini ɗaki ki saka turare nan ma ki gyara shi da falonki ki tabbatar na dawo naga komai a gyare, sannan batun girki ki dafa da yawa saboda zaki aika gidan Hajiya suma su fara cin girkinki, me ma zaki dafa?
Shinkafa da miya sai kosilo, amma Hamid ga girki ga gyaran ɗakuna aikin gaskiya ya mini yawa bazan iya ba.
Hakanan za kiyi shi, da haka zaki koya ki saba, kuma ina son pepe chicken ki haɗa kiyi shi.
Zan dai yi abinda zan iya.
Ta faɗa tana turo baki, Hamid yayi murmushi yana cewa ta fito su karya. Bata tanka shi ba ya fita kana ta sauko ta saka hula a haka da yalolon kayan barcin ta fito falon, tun daga nesa Hamid ke kallonta har ta ƙaraso dinning ɗin ya haɗe fuska sosai yana cewa.
Madina meye haka? Ya zaki fito a haka bayan kin san ba ke kaɗai bace a gidan, ga yara duk suna gida yanzu zasu fito mu karya, gaskiya kije ki sauya kayan nan ni ba zan lamunci yawo da kaya irin wannan ba a babban falo.
To banyi wanka ba taya zan sauya kaya.
Ta faɗa cikin shagwaɓa tare da jan kujera ta zauna kusa da shi, tsaki yaja yana jin tashin tsamin gumi a jikinta duk da akwai ƙamshin turare amma tuni hancinsa ya gano ƙamshin gauraye yake da tsamin zufa, tashi yayi ya sauya kujera ya bayar da tazarar kujera biyu a tsakaninsu dan ba zai yarda ta hanashi karyawar da yake so ba, ƙunƙuni ta cigaba da yi tana danna waya bata da niyyar tashi ta sauya kayan, a haka Sakina ta fito da yaran duk sunyi wanka sun saka kaya masu kyau, ita kanta Sakina wani material ta saka doguwar riga tasha aiki da adon stone sai hula data saka mai kyau shima fuskar daga Power sai man baki da kwalli ta saka sai ƙamshi take zubawa, suka ƙaraso yaran kowa ya zauna a kujera hatta Rauda sai da ta ɗaurata a kujera kusa da Hamid, ta soma zuba musu ko wanne yana faɗan abinda yake so, data gama sai ta zubawa Hamid kunun a kofi ta zuba masa ƙosai dan tasan yafi sonsa da kunu ko doya da kwai, tana gamawa ta juya zata wuce da sauri Madina ta dakatar da ita.
Malama nifa baki zuba mini ba? ko nayi miki kashi a gado ne da zaki mini haka.
Ba kida hannu ne?
Sakina ta bata amsa tana cigaba da tafiya, Madina zata yi magana Hamid ya dakatar da ita.
Bana son rikici ki zuba abinda zaki iya ci ai bata san me kike so kici ba, na tabbatar tea da irish zaki ci. Sakina ke ba zaki karya bane?
Nayi nawa tun ɗazu dana gama.
Sakina ta bashi amsa tana zama a cushing tare da ɗaukar remote ɗin tv ta kunna ta soma kallo, Madina cike da takaici ta zubawa kanta Irish, kwan kusan duka ta ɗibe ta haɗa tea mai shegen kauri Hamid yana kallonta bai ce komai ba, haka suka karya kowa yana hidimarsa. Bayan sun gama duk suka dawo falo har da yaran sosai Sakina taji ranta ya sosu da ganin Madina da waɗannan kayan barci, komai na jikinta ana gani daga pant har birezia, kawar da kanta tayi dan kar sheɗan ya zamu muhalli a zuciyarta, Madina tsabar son tsokana a cinyar Hamid taje ta zauna, da sauri Sakina tace.
Mufeeda ja ƙenannenki ku shiga ɗaki.
Hamid shi kanshi sai da yaji kunyar abinda tayi, ga hamamin tsamin zufa da take yi masa, da Sauri Mufeeda taja ƙannenta suka shiga ɗakinta, Hamid ya ture Madina yana cewa.
Bana son irin haka a gaban yara, kar ki ƙara.
To meye dan nayi haka ai sun sai ni matarka ce.
Hamid ina so zan je gidanmu da yara anjima.
Sakina tace haka tare da miƙewa dan ta basu guri, Hamid ya dube ta yana miƙewa.
Babu inda zaki je yau Madina zata fara girki, ki saka mata hannu ko da gyaran ɗakina ne da abinda ya dace.
Hamid kenan, gaskiya duk abinda ya shafi Madina ka daina saka ni a ciki, tayi aikinta nima nayi nawa.
Ba za kiyi abinda nace ba kenan.?
Bata bashi amsa ba ta wuce zuwa ɗakinta, da kallo Hamid ya rakata har ta shiga Madina ta juya tana cewa.
Beb nace ka sama mini ‘yar aiki wlh bazan iya ayyukan nan ba ni kaɗai, ban saba yi ba a gida.
Da haka zaki saba, ni zan fita sai na dawo.
Ya bata amsa yana wucewa, da ido ta rakashi tana jin wani haushinsa ya kama ta, shi kuma da haushin Sakina ya fita ya shiga mota ya ɗauki wayarsa ya kira Sakina, tana ɗagawa.
Ni zaki wulaƙanta a gaban Madina saboda kin mayar dani ɗan iska ina magana ki wuce ki bar ni a tsaye, sannan in ce kiyi abu kice ba zaki yi saboda kin raina ni.
Hamid wlh na gaji da cin fuskar da kake yi mini, yadda nake matarka haka itama take matarka ba zai yuwu saboda son kai ka jona mini aikinta ba, ni waye yake tayani nawa aikin? Saboda ni na zama jaka ban san ciwon jikina ba ko, sannan ni baka tausayina balle ka gane nima ina bukatar mataimaki a aikin gidan, girkin dare kaɗai zata yi ni ka ɗaura mini aikin safe koda ranar girkinta ne naji na ɗauka, to na gaya maka in dai aikin daya shafi Madina ce wlh bazan yi.
Kit ta kashe wayar saboda baƙin ciki, da kuka ta fashe ko zata samu sassauci, ga takaicin kayan da Madina ta saka ya mannu a zuciyarta yanzu fa ita da Hamid sun gama sanin juna ita ta zama hoto ba tada sauran amfani sai aikin gida, wani baƙin kishi ne taji yana taso mata data kasa danne shi, ga kuma wulaƙancin Hamif a gefe, duk yadda take ƙoƙarin yin haƙuri da shi amma yana niman kaita bango, kukan kawai zai sa ta samu sassaucin yanayin da take jin kanta a ciki. Hamid da ido ya bi wayar yana jin dole ma ya hukunta Sakina akan abinda tayi masa, lallai an kawo gaɓar da raini ya soma shiga tsakaninsu to kuwa ba zai ɗauka ba, da damuwar haka ya fita daga gidan.
Madina tana shiga ɗakinta taga ya dace ta fara gyaran ɗakunan kafin anjima ta ɗaura girki, gama wanke wanke data tara tun zuwanta gidan ba a wanke ba, da sauri ta fito falon ta soma kwalawa Mufeeda kira, wanda tun da tazo gidan sai yaune ta iya kula yaran dan sam bata shiga lamarinsu ko gaisheta suka yi sai ta gadama take amsawa, da sauri Mufeeda ta fito daga ɗaki a tsorace dan ta bayar ƙila zata ce tayi mata wani laifin ne dan ba zata mance rashin muruncin da suka yi rannan ba ita da Hajiya, Sakina dake kuka da sauri ta share hawayenta ta saita kanta ta fito itama ta tsaya jikin ƙofa suna kallon Madina, Madina ta ƙaraso kusa tana cewa.
Mufeeda ina so ki shiga ɗakin Abbanku ki share ki gyara masa gado ki wanke bayi ki saka turare, in kin gama kizo ki gyara mini bedroom ɗina da falona, in kin gama akwai wanke wanke a side ɗin kayan kitchen ɗina ki kwashe ki wanke su. Zuwa anjima in zanyi girki zan kiraki ki tayani ko.
To ba zata yi ba dan Mufeeda ba baiwa bace, yadda kika amsa sunan matar Hamid to dole kece za kiyi duk waɗannan ayyukan da kika lissafa, Bana saka Mufeeda aikin shara ko wanke bayi domin bata kai yin su ba hatta wanke wanke ni ke yin kayana, girki kaɗai nake bari ta saka mini hannu saboda ina so ta iya da wuri, sauran aiki sai nan gaba duk zara fara yinsu.
Kina nufin ban isa na sakata tayi mini aiki ba.
Eh baki isa ba wlh tunda ba haifarta kika yi ba. Ba zaki bautar mini da yarinya ba saboda son zuciyarki, nima ba yi mini take yi ba nike yin kayana. Mufeeda maza ki koma ɗaki ku cigaba da wasanku.
Mufeeda da sauri ta juya ta koma ɗaki dan dama a tsorace take, Madina tayi tattaki ta ƙaraso gaban Sakina ta kama ƙugu.
Wlh sai kinsan kin hana Mufeeda tayi miki aiki yau, shegiya matar ƙaddara.
Sakina wani wawan mari ta kwasheta da shi wanda ya saka Madina dafe kuncinta da sauri tana zaro ido.
Ni kika mara? Wlh yau sai kinga ƙarshen makirci da alama kin kusa komawa cin tuwon gidan ubanki malam mai allo.
Sakina ta ƙara kai mata mari wannan karan da sauri Madina ta kauce tayi baya cike da tsantsar tsoronta, dan da alama in tayi sake Sakina saita nakaɗa mata duka, bata sake magana ba ta juya zuwa ɗaki. Sakina itama ta koma ɗaki da tunanin yau tasan za ayi ta ta ƙare dan tasan Hamid sai ya yi mata rashin mutunci tunda dama ɗazun suka gama rikici a waya.
Madina Hajiya ta kira tana kukan makirci ta faɗa mata komai, Hajiya haƙuri ta bata tana cewa.
Ki bari anjima in Hamid ya dawo ki faɗa masa duk abinda tayi miki nasan zai ɗauki mataki, kinga ni Alhaji ya saka mini dokar zuwa gidanku, kiyi haƙuri zan aiko miki da Jidda sai ta taya ki duk ayyukan.
To nagode Hajiya.
Madina ta faɗa cikin kuka, nan ta kashe wayar tana sakin shu’umin murmushi.
Wlh tunda hannunki ya taɓa jikina yau sai nasa Hamid ya nakaɗa miki duka, tsinanniyar mata kawai.
Ta faɗa a fili tana miƙewa tare da cire kayan barci ta saka wata doguwar riga taje ta saka kayan barcin a cikin dosbin a bayinta wanda ta tara kayan wanki duk kuma panties ne da birezia sai kayan barcin a ciki, ga bayin tunda tazo ba a wanke ba har ya fara fitar da tsamin wari. Jidda sai gurin sha biyu tazo lokacin ta dawo daga islamiyya uniform kawai ta cire Hajiya ta turo ta, Madina ta jibgawa yarinyar nan aiki kamar ta samu jaka, tun tana yi dan daɗi har sai da ta gaji ga yunwa na damunta dan ko abinci Hajiya bata bari taci ba, ta gama gyaran ɗakunan ta shiga kitchen na haɗa wanke wanken Madina, kafin ta soma yi ta isa ɓangaren Sakina nan taci karo da sauran kunu da kosai aiko zama tayi ta soma ci sai da tavcika cikinta kafin ta miƙe ya fara aikin, tana tsaka na wanke wanke Sakina ta shigo, cikin ladabi Jidda ta gaisheta ta amsa kana ta fara haramar yi musu girki, shinkafa da wake take so da mai da yaji dan haka nan ta ɗaura sanwa, ta kuma ɗaura tafashen kaza dan so take ta soya su riƙa ci da yara, Jidda ta gama aikinta tsaf kana ta fito a lokacin ne Sakina ta samu damar wanke nata kayan da suka ɓata da safe, ta kimtsa kichen ɗin kana ta cigaba da aikinta, Jidda dai kwanciya tayi a falo dan Hajiya tace karta dawo har sai Madina ta sallameta. Sai wajen karfe biyu da rabi Sakina ta kammala aikinta ta zubawa Jidda abinci kana ta saka Mufeeda ta kai mata da sauri ta amsa dan kunun ba wani kama mata ciki yayi ba, ta soma ci kenan Madina ta fito zuwa falon ta tsaya tana kallonta.
A ina kika samu abinci?
Maman Mufeeda ce ta bani kuma tun ɗazu banci komai ba yunwa nake ji.
To uban waye yace ki amsa, ai gurina aka ce ki zo bana son kwaɗayi, maza tashi ki mayar mata da abincinta ki je ki dafa indomie kici.
Ni gaskiya wannan zanci dan ko da safe da indomie na karya.
Ta bata amsa tana miƙewa tare da zumɓuro baki.
Ni kike faɗawa haka ko.
To taya zaki hanani cin abinci ina jin yunwa.
Ta faɗa tana wucewa kitchen ta samu guri ta zauna ta cigaba da cin abincinta, Madina ƙofa tayi tana cewa zata gyara mata zama dan ba zata ɗauki raini ba. Sakina tana jinsu bata bi ta kansu ba ta tasa yaranta zuwa ɗakin Mufeeda, suka ci abinci suka ƙoshi, ta aje sauran anan dan anjima shi zasu ci, ba zata yarda yaranta suci abincin Madina ba dan bata gamsu da ta iya girki ba.
[7/22, 5:34 PM] Rahma Kabir: *ƘAZAMAR AMARYA*
Na
©®Rahma Kabir MrsMG.
Wattpad @rahmakabir
Page 19.
Madina sai wajen ƙarfe uku ta fito ta shiga kitchen bayan ta ɓata lokaci a daki wajen kallon video ɗin miyar da zata yi, duk da Kausar ta tura mata voicing ɗin yadda zata haɗa amma bai gamsar da ita ba sai da ta kalli videon wata baturiya wanda wannan ne yafi kwanta mata a rai, nan take tayi saving ɗin wasu videon abincin matar kala kala, kafin ta samu damar fitowa dan fara aikin girkin. Ta saka Jidda ta fara yanka mata kayan cosilo daga bisani ta ɗibo kayan miya ta wanke sai ta markaɗa su, ta fito da naman kaza daga freezer ta wanke dan a cikin miyar tayi niyyar sakawa ba zata yi masa wani pepe chicken ba, ta ɗaura miya tana yi tana kallon video ɗin nan, a takaice miya ce tayi na kasar da ba namu ba dan har sugar aka saka a ciki, sannan kazar nan ba tafashe ba soyawa haka ta tsalmasu cikin miyar sukaita dahuwa har suka rafke a ciki tsokar ya bar jikin ƙashi. Miya dai a ido yasha mangyada shar sai dai a baki ne sai in anci anji, daga nan ta ɗaura tafashen shinkafa ta lafta mata ruwa har sai da ta dafe kafin ta wanke, Allah yasa shinkafar ‘yar gomnati ce mai shan ruwa koda ta mayar ta turara ta yi mugun laushi. Wannan girki ya ɗauketa kusan awa uku ana abu guda, ta ɓata kaya da yawa sai Jidda ce ta wanke su ta gyara kitchen ɗin, nan ta haɗa cosilo ta saka a tire guda biyu mai kyau ta rufesu da foil paper, kana ta saka nasu a frigde ta haɗa abincin su Hajiya a kula mai kyau na miya daban dana shinkafar ta saka a babban kwando ta bawa Jidda ta kai yare da tiren cosilo, ta amsa tana yi maya sai anjima ta wuce sai dai ta saka a ranta ba zata ƙara zuwa ta wahalar da ita aiki irin haka ba, dan ba ƙaramin gajiya tayi ba. Koda ta shiga falon wajen shida saura ta samu Abba da Hajiya duka a falon, tayi musu sannu da gida kana ta dire kayan abincin a gaban Hajiya tana cewa.
Anty Madina tace in kawo.
Ikon Allah yanzu fa nake shirin kira in ce kizo ki ɗaura mana abincin dare Allah yasa ma bamu yi ba da sai dai ayi asararsa, ɗauka ki kai kitchen ki aje.
Hajiya wlh bazan sake zuwa tayata aiki ba dan ta wahalar dani sosai, wai fa har kular rannan da kika saka mata dumbu bata wanke ba, ta haɗa uban wanke wanke sai da naje nayi mata, ga gyaran ɗaki da wanke bayi, dustbin ɗin bayinta ta cika da wanki wai cewa tayi gobe inje inyi mata kuma ni Allah ba zani ba.
Kai Jidda tun ba aje ko ina ba zaki fara numa ganda da rashin kunya ko, to aiko sai kinje kin yi mata su, sannan banda rashin kirkin Sakina ko Mufeeda ba zata saka tayi mata wanke wanke ba.
Hajiya wlh Anty Madina ba tada kirki itama, ɗazun fa wai dan maman mufeeda ta bani abinci inci wai ba zan ci ba sai dai in mayar mata, kuma ita bata girka ta bani ba.
Idan baki mini shuru ba sai ɓaci mutuncinki, dalla je ki aje kayan abincin ki ɗauko mini wayata a ɗaki.
Cewar Hajiya a tsawace, Jidda cikin turo baki ta wuce tana ƙunƙunin ba zata je tayi mata wankin ba. Hajiya ta dubi Alhaji tana cewa.
Kaga ɗiyar albarka wai abinci ta aiko mana da shi.
Ta aiko miki dashi dai dan babu ni a wannan cimar, idan akwai sauran farfesun kan ragon nan ki ɗumama mini shi anjima zan ci da biredi.
Haba Alhaji ai kasa albarka a abincin amarya kaji ya girkin ta yake ko.
Wannan sai ke uwar kwaɗayi amma ba Nuhu a wannan zancen.
Yayi maganar yana ‘yar dariya, Hajiya ta gimtse bakinta ganin yana niman danƙara mata magana, kiran sallah yasa suka miƙe dan yin alwala.
***
Madina.
Tunda ta koma ɗaki ta zauna tana mayar da numfashi dan ba ƙaramin gajiya tayi ba, da kyar ta miƙe ta samu tayi wanka ta saka kaya marasa nauyi ta gabatar da sallar magrib, kafin ta fito falonta ta kwanta a doguwar kujera tana chart da Kausar dan har hoton abincin ta ɗauka tana tura mata tare da bata labarin yadda ta sha walahar aiki, Kausar ta turo mata da voicing tana cewa.
A ido kam abinci yayi kyau Masha Allah, sai dai saura a baki aji yadda yake.
Haba ai wlh abincin nan ko gamna zaici shi ya yaba dan yayi daɗi sosai.
Cewar Madina data rubuta mata amsar tana murmushi a fuskarta, sai daɗi take ji yau tayi abin arziki a girki, fatanta Allah yasa Hamid ya yaba duk da ita ta ɗanɗana taji komai yayi daidai, haka ta ɓata lokaci har aka kira sallar Isha’i kafin ta miƙe ta dawo bedroom ɗinta ta gabatar da sallar, tana idarwa ta miƙe ta tsaya jikin madubi ta shiga saka hannunta a idonta yana ruwa tsabar son tayi kuka idon yayi ja, yadda zata samu damar kunnawa Sakina makirci dan bata manta abinda tayi mata ba ɗazun, sosai ta riƙa azabtar da idonta har sai da hawaye ya riƙa fita sosai, sai ta samu gefen gado ta zauna tana murmushin mugunta tasan duk inda Hamid yake to ya kusa shigowa gida, da yake hawayen ta tsokano shi ne ga yajin da idon ke yi na tsokaleshi da tayi ya dinga fidda ruwa, a wannan yanayin taji dirar motar Hamid sai ta kwanta a gefen hagunta ta bawa ƙofa baya yadda zata ji daɗin haɗa makircin, ba jimawa Hamid ya shigo falon yau ya samu ba kowa hatta yaran baiji motsinsu ba, ɗakinsa ya fara shiga ya rage kayan jikinta ya saka jallabiya da nufin in yaci abinci sai yayi wanka dan da yunwa ya shigo gidan, ɗakin Madina ya nufa yana murɗa Handle Madina ta shiga sasahekar kuka, koda ya shiga ya ganta a haka a rikice ya ƙarasa bakin gadon ya tsaya yana cewa.
Madina lafiya kike kuka meya faru.?
Ai kamar tana jiran ya tambaye ta sai ta rushe da kuka mai sauti, Hamid ya kamo hannunta ya ɗagota yana ƙara tambayar me takewa kuka, ganin taƙi magana yasa shi zama a gefen gadon ya rungumota ya shiga rarrashi, sai da ya samu tayi shuru kafin ya kuma jefa mata tambaya.
Madina me ya faru ne? Wlh duk kin tayar mini da hankali.
Sakina ce ta mare ni har tana mini barazanar wai ko naƙi kona so sai na bar mata gidanta, sannan ɗazun da rana dan na saka Mufeeda ta taya ni aiki tace ba zata yi ba wai ban isa na sakata tayi min aiki ba tunda ba haifarta nayi ba.
Ta ƙare maganar cikin sassheƙar kuka, shuru Hamid yayi na ‘yan daƙiƙa daga bisani ya sauke numfashi.
Sakinar ce tace haka, sannan me kika yi mata ta mareki.?
Tun lokacin dana saka Mufeeda aiki ta hana dan nace ai ina da ikon saka ta ta mini aikin, shine ta zageni dan na rama ta mare ni, wlh tun lokacin kaina kamar zai fashe saboda ciwo da kyar ma na samu nayi girki dan kiran Hajiya nayi ta aiko mini Jidda ta taya ni.
Ina zuwa.
Abinda ya faɗa kenan ya miƙe da sauri ya fito ya isa falo ya zauna yana girgiza ƙafa, sai ya shiga kwalawa sakina kira, tunda Sakina taji kiransa haka ta san da magana Madina ta gama haɗa mata bomb, dan haka ta miƙe ta saka hijab ta fito falon ta samu kujera ta zauna tana cewa.
Sannu da dawowa, gani.
Ina so gobe In Allah ya kaimu ki haɗa kayanki ki tafi gida sai in na nimeki idan da yuwuwar cigaba da zama dake, idan kuma bazan iya ba za kiga saƙo.
Allah ya kaimu.
Ta ce murya na rawa tare da miƙewa ta wuce ɗaki, duk yadda taji ta danne hawayenta ta kasa sai da ta riƙa fitar dasu kamar ruwan famfo, dama tasan ƙarshen a lewa ƙasa duk wata barazanar rabuwa da ita ya gama muna mata, ta zauna a gefen gado tayi kuka mai isarta, daga bisani ta lallashi kanta da tunanin wa zata kira ta sanar dashi a waya, tasan in ta kira yayyinta ƙarshe kiran Hamid za suyi su bashi haƙuri ita kuma ba zata so haka ba, dan in har suka yi mata haka sun ƙara bashi damar ya wulaƙantata ne, wannan tunanin data yi yasa ta bar zancen kiran kowa, dan kota koma gida ba zata taɓa yarda wani daga cikin ‘yan uwanta ya nimeshi ba har sai ya yanke hukuncin daya ga ya dace akan aurensu.
Hamid sosai yaji ya tsani Sakina saboda a ganinsa sakin take so tunda ta kasa kwantar da hankalinta su zauna lafiya, ba zai yuwu dan ya auri Madina ta riƙa yiwa ‘yar mutane barazana ba, gwara tun wuri ya yiwa abin tufkar hanci koda bai saketa ba to ta zauna gidansu na wani lokaci dan ta gane aurenta yana da muhimmanci, zaman gidanta yafi zaman gidan iyayenta. A haka Madina ta fito ta sameshi ta zauna a gefensa tana ɗaura kanta a kafaɗarsa.
Beb ka zo ka zauna anan kai kaɗai, abincin fa muje muci.
Murmushi ya ƙaƙalo ya yi mata yana cewa suje ta zuba musu dan da yunwa ya shigo gidan. A dinning suka yada zango yadda yaga kyawawan kulolin data zuba abincin zai yaji ya ƙosa yaci, koda ta buɗe nan ta ke ya hango anyi barnan man gyada dan miyar shanana da mai a sama, ga kuma kosilon da aka cika masa uban kwai dan da yawa ta saka a ciki, shuru yayi kawai yana kallonta amma har ga Allah bai ji daɗin yadda take ɓarnata kayan abinci haka ba, Sakina bata saba yi mata ɓarna da kayan abincin ba, Madina ta shiga zuba masa abincin, data gama ta tura masa plate tana cewa bisimillah.
Sannu da ƙoƙari amma ina pepe chicken ɗin dana ce kiyi? sannan kin aje abinci ba ruwa ba drink.
Au sorry beb na manta ne bari na kawo ruwan, amma fa ban samu yin pepe chicken ba na dai saka kazar a cikin miya, saboda aiki ya mini yawa.
Ok ba damuwa ɗauko ruwan da drink ɗin.
To tace masa ta wuce kitchen shi kuma ya saka cokali ya fara cin abincin, a ido kam masha Allah duk da shinkafar ta dahu sosai, lomar farko ya fara tunanin miye a cikin abincin da yaji zaƙi haka, amma sai ya bayar ko a cosilo ne dan wasu na saka sugar, ba zai ce abincin yayi daɗi ba ko bai yi ba, dan ya kasa gane wani irin ɗanɗano yake yi ga kuma miyar ta ɗanyi yaji, sannan kuma an zabga masa curry yana kama baki sannan kuma kazar duk ta ragwargwaje tsokar ya dafe sosai, sauƙinsa bai ji ƙarni ba dan da yaji ba zai iya cigaba da ci ba, haka ya cigaba da tusawa daban ya fahimci ina daɗin abincin yake ba, kuma baya so ya nuna mata gazawarta dan yaga tayi ƙoƙarin yin girkin, ta dawo ta aje ruwan ta zuba nata ta soma ci, haka dai Hamid ya ci rabi da kyar ya kora da ruwa yana tura plate.
Ni na ƙoshi kuma abincin ba laifi yayi daɗi amma a ƙara gyara hannu dan kin san ni maciyin abinci ne, amma naji zaƙi ya fito a abincin dan banji maggi sosai ba ko kosilo ɗin ne kika saka sugar.
Au ai haka ake yi yanzu, miyar ce na sakawa sugar new method ɗin stew kenan, amma ai yayi daɗi ko?
Sugar a cikin miya? ban taɓa ji ba sai a gunki, to yayi daɗi ba laifi amma ni dai karki ƙara saka sugar a miya kamar zaifi kiyi old method.
To shikenan zan daina amma ni ko a gidanmu haka na saba yi.
Tayi maganar tana murmushi cikin zabga masa ƙarya, shima murmushin yayi ya miƙe yana cewa ta sameshi a falo in ta gama sai ya tafi da gorar Pepsi yana kurɓa. Madina kam ita a haka abincin yayi mata daɗi, ta buɗe ciki ta kwashi girki dan har nashi daya rage ta cinye saboda dama bata zuba nata da yawa ba, data gama ta miƙe ta bar kayan abincin a haka bata kwashe ta mayar dasu kitchen ba, sai ta koma falo ta zauna nan yace suje bedroom ɗinta suyi kallo a system ɗinsa ya samo wasu Film masu kyau, haka suka shiga ciki suka fara kallo cike da soyayya.
***
Gidan Hajiya.
Bayan sallar magrib suka ci abincin Madina, amma fa tayi ta ƙorafin zaƙi ya fito a miyar, dan sai da ta saka jidda ta ɗauko mata maggi star ta barbaɗa a abincin kafin taji yayi mata daidai a baki, Jidda ko kaɗan taci dan sam abincin bai mata daɗi ba, kosilo ɗin ta dinga ci dan tana sonshi sosai gashi yaji kwai, Hajiya data gama ci take cewa Alhaji.
Naso ka ɗanɗana abincin yarinyar, kaji zaƙi zakwai sai kace ba a saka maggi ba, ga nama duk ya raɓe a cikin miya sai kace makauniya bata gani tayi wannan ɗanyen aikin.
Ai abinci amarya sai ku Hajiya, ni kam ba zanci ya tada mini hankalina ba, nama ƙoshi da wannan farfesun Jidda zoki kwashe kayan.
Alhaji da zaka amince mini da gobe in Allah ya kaimu naje gidan inyi mata gyara, dan karta riƙa yiwa Hamid girkin turawa ya riƙa lalata masa ciki.
Ba zaki je ko ina ba ba ruwanki shi da ya aurota in girkin baiyi masa ba da kansa zai yi magana ta gyara, kinga ina raba ki da shiga harkar yaran nan, dan gwara Sakina tana miki kawaici amma wannan amaryar tasa ban hango kunya a tare da ita ba kar ki jawo raini ya shiga tsakaninku.
Allah ko Alhaji? ai ni naga gyara kayan ka ne.
To maza tashi kije ki cigaba da yada girmanki tunda ke baki san ciwon kanki ba.
Alhaji ya danƙara mata magana yana jan tsaki tare da miƙewa jin an kira sallar isha’i, haka ya fice daga gidan yabar Hajiya baki sake tana jin zafin yadda yake gwasaleta irin haka, kuma tasan ko gaban waye haka zai yi mata, ƙofa tayi ta miƙe da kyar tana kiran Jidda akan tazo ta kwashe kayan abinci ta gyara falon, sai ta wuce cikin bedroom ɗinta ta ɗauro alwala ta tayar da sallah, tayi raka’a biyu kenan taji cikinta yayi wani mugun ƙullewa gefe ɗaya wanda yasa ta kasa duƙawa Ruku’u, nan take kuma taji tashin zuciya, tusan data ji yazo mata da ƙarfi yasa ta sake shi sai kuma ya tawo da zawo, cikin tashin hankali Hajiya ta saki salati.
Na shiga uku kashi fa na saki.
Da sauri ta cire hijab ta kwance zani ta bar siket da ɗankamfai ta nufi bayi a guje, ko kafin ta ƙarasa ciki zawo ya kubce mata da amai, haka ta duƙa tana amai da zawo a lokaci guda, da zarar ya yunkuro mata to tare take fitar dasu, Hajiya ta saki kuka mai sauti tana ambaton sunan Allah a cikin ranta dan ta fara ganin mutuwa a zahiri yana tunkaro ta.
_Wlh yau naci dariya over, wani abu ma sai page na gaba_
[7/23, 8:23 PM] Rahma Kabir: *ƘAZAMAR AMARYA*
Na
©®Rahma Kabir MrsMG.
Wattpad @rahmakabir
Page 20.
Hajiya haka ta dinga amai kamar zata amayar da hanjin cikinta, daga bisani daya lafa mata da kyar ta miƙe ta isa wajen famfo ta wanke bakinta kana ta haɗawa kanta ruwan zafi ta wanke jikinta, haka ta fito tabar gurin data ɓata da kayan data cire a ƙasa, ta samu ta yi ɗaurin ƙirji ta kwanta rubda ciki a kan gado tana mayar da numfashi, ta ɗauki kusan minti talatin a haka kafin Jidda ta shigo ɗakin a galabaice tana cewa.
Hajiya amai nake ta yi tun ɗazu duk abinda naci na fitar dashi, cikina sai murɗa min yake yi ga shi Abba bai shigo ba balle na faɗa masa a siyo mini maganin amai, shine nace ko zaki kirashi a waya ki sanar dashi in zai shigo ya siyo mini maganin.
Hajiya a wahalce ta juyo kanta tana kallonta tace a galabaice.
Ɗauki wayar ki kira shi dan nima zawo da amai nake yi duk ruwan jikina yana niman ƙarewa.
Jidda ta isa inda wayar take ta shiga duba numbern Alhaji tana ƙoƙarin kiransa taji yana kwala mata kira, da sauri ta fita falon ta sameshi ya zauna da lodin rake a leda daya siyo musu a center table.
Ke ina Hajiya kira ta tazo ga rake na siyo mana musha na marmari.
Abba Hajiya ba tada lafiya amai da gudawa take yi tana kwance a ɗaki, nima amai nayi sau uku, dama yanzu zan kiraka ka siyo mini magani sai na tadda Hajiya itama ba lafiya.
Subhanallahi me kuka ci cikinku ya lalace lokaci guda haka.?
Abba ya faɗa yana miƙewa ya wuce zuwa ɗakin Hajiya, Jidda zama tayi dan ta jira ya fito saboda ƙarshe ƙila su dangana da asibiti, duk da ita tunda tayi aman ta samu sassaucin murɗawar cikin, Alhaji yana shiga ya samu Hajiya a duƙe akan guiwarta ta kafa kai a ƙasa tana ambaton Allah da wayyo cikinta.
Subhanallahi Hajiya abin har yayi tsamari haka me ya faru ne?
Alhaji kawa Allah kawa Annabi ka kai ni asibiti tun kafin na rasa ruwan jikina, wlh zawo nake kamar ruwa, ga amai kamar zan amayar da kayan cikina.
Ta faɗa cikin ɗago kai tana runtse ido, Alhaji ya rungume hannu.
Wai to me kuka ci ne ya lalata muku ciki? itama Jidda tace wai tayi amai sau uku.
Alhaji har sai ka tsaya tambaya, ai bai yuce abincin Madina ne ya lalata mana ciki, ni gani nake ko aikota akai ta saka mana guba muci duk mu mutu, cikina karta yake yi kamar ana kwaziran bango, dan Allah ɗauko mini doguwar riga na saka wannan zanin na ɓata shi da zawo mu tafi asibiti.
Haba Hajiya ya zaki ce guba ta saka muku? amaryar da kika fi kowa so, sai dai in wani abun kuka ci ba dai girkin yarinyar nan bane zai lalata muku ciki, ina ce wanda kika zuba a plate tas kika cinyeshi duk da kinyi mitar miya tayi miki zaƙi, amma kuma kinci kin ƙoshi.
Alhaji! Alhaji ka wa Allah ka ceci rayuwata Wlh duhu duhu nake gani, wannan Yarinyar duk yadda aka yi aiko aka yi dan ta halakani.
Alhaji yaso ya shanye dariyarsa amma ya kasa sai da ya kwashe da ita yana dafa goshinsa.
Haba baban Hamid magana ake ta rayuwa ko mutuwa amma ka mayar dashi abin dariya, ko sai kaga na faɗi ruwan jikina ya ƙare na daina numfashi shine zaka yarda da abinda nake faɗaaaa, wai wai wai cikina ya tamke wlh kamar ana gobara, innalillahi wa inna ilaihir rajiun.
Hajiya ta ƙare maganar cikin kuka tare da kwantawa a ƙasa jikinta na kakkarwa, a sannan ne Alhaji yayi sauri ya isa waldrobe ɗinta ya duba doguwar rigar ya bata amma ta ƙasa amsa, haka ya cire jallabiyarsa ya kamata ya kaita bayi ya taimaka mata ta watsa ruwa suka fita ta saka rigar, ko hijab bata nima ba ta shiga dafa bango tana cije leɓe kamar mai naƙuda ta fita, Alhaji ya tsaya ya mayar da rigarsa ya fito cikin sauri ya samu ta tsuguna akan guiwarta tana mirgina kai, sosai hankalinsa ta yashi ya nufi inda ya aje wayarsa kan kujera ya ɗauka ya shiga kiran Hamid sai dai duk kiran da yayi masa kusan sau uku bai ɗaga ba, haka ya fita da sauri ya buɗe mota ya koma ya kama Hajiya shida Jidda suka fito da ita suka sanya a back seat ya rufe, kana ya shiga mazaunin driver Jidda ta zauna a gefensa suka wuce asibiti inda family card ɗinsu yake.
Lokacin da Abba ya kira Hamid ya aje wayar a gefen midubin Madina, kuma a silent ya saka shi tun lokacin da zai yi sallar magrib a masallaci ya mance bai cire ba, suna tsaka da kallo Hamid yaji cikinsa yana murɗa masa alamar kashi yake ji, da sauri ya miƙe dan kar ya saki tusa yayi abin kunya irin na Madina, yace.
Bari na ɗana toilet ɗinki yau ina zuwa.
To tace masa ya wuce ciki sai dai yana zuwa gurin abin kashin na zama ya tadda a rufe, sai ya buɗe nan yaga jibgin kashi anyi ba ayi flushing ba, da sauri yayi baya cike da ɓacin rai dan har zuciyarsa ya ji ya tashi masa, haka ya juya ya fito bai tsaya yi mata magana ba ya nufi ɗakinsa dan yaji yayi mugun matsuwa, da ido ta bishi har ya fita sai ta mayar da hankalinta gurin kallo. Hamid koda ya shiga ɗaki bayinsa ya faɗa ya shiga yin zawo kamar zai kasaye hanjinsa, ga kuma murɗa masa da cikinsa keyi kamar ana gobarar wuta, warin kashin nasa shine ya ƙara hassasa tashin zuciyarsa, kafin yayi aune ya shiga kelaye amai sosai yana kashi yana amai duk lokaci guda, sai da ya ɗauki kusan minti goma a haka kafin ya tsaigata masa ya wanke jikinsa da baki kana ya tsallake aman dan ko gani baya son yi, ya fito ya zauna a gefen gado yana sakin gyatsar magwas, hannu biyu yasa ya dafe kansa tare da lumshe idonta yana mamakin me yaci haka daya ɓata masa ciki haka, rabonsa da irin wannan ɓacin cikin zai ce s’tun yana saurayi lokacin a makarantarsu daya ci wani abincin siyarwa ya ci food poison, bai gama haɗa tunaninsa ba cikinsa ya ƙulle tamau wanda ya saka shi rike shi yana ambaton Allah, a haka ya duƙa ƙasa yana jin wani azababben ciwon ciki ga kuma zufa daya rufe shi jikinsa har rawa yake yi dan zaba, ko kafin ya kuma yunƙurawa ya saki zawon yana yi yana yunƙuri kamar mai naƙuda, Hamid zuwa wani lokaci ya gama galabaita ya kuma kasa tashi ya taimakawa kansa, ƙarshe rarrafawa yayi zuwa bayi ya cire kayan jikinta ya tara kansa a famfo ya jingina da bango, a haka ya wanke jikinsa ya fito da dafa bango ya isa wajen kayansa ya ciro jallabiya ya saka ko gajeren wando bai iya sakawa ba, ya fito da dafe bango dan duhu kawai ya soma gani, ko kafin ya isa ɗakin Sakina ya rafke a ƙasa ji kake tum, cikin ƙaraji ya shiga kwalawa Sakina kira yana kuma kiran Madina. Sakina dake zaune a bakin gado tana ta danne danne a waya taji muryarsa yana kiranta kamar an shaƙeshi, kamar ba zata fita ba sai kuma ta miƙe ta buɗe ƙofa ta fito, ganinsa a kwance a ƙasa magashiyyan yasa ta isa gurin da sauri.
Hamid lafiya.?
Ki taimaka ki kira driver ku ɗaukeni ku kai ni asibiti amai da gudawa nake yi.
Haba Hamid ni kuma? Ai sai dai kuje da Madina tunda ni ka riga ka sallameni in tafi gida sai ka nime ni, kaga kuwa bani da abinda zan iya yi maka. Bari na kirata.
Don girman Allah ki aje wannan maganar ki ceci rayuwata, magana ce ta rai ko mutuwa fa domin Allah zaki taimaka mini.
Sakina guntun murmushi tayi tana cewa.
To wai me kaci ne haka ya lalata maka ciki?
Abincin Madina kaɗai naci dana dawoooo, Ya Allahu Ya Rahmanu cikina Sakina, Wlh cikina ciwo yake mini kamar zan mutu, gashi nan zai zubo, wlh ya tawo, shikenan na saki kashin Sakinaaa.
Hamid ya ƙare maganar yana jan maganar tare da zazzaro ido waje gabaɗaya magana yake cikin fitar hayyaci, hankalin Sakina yayi mugun tashi ta shiga kwalawa Madina kira da ƙarfi, ko kafin ta fito tayi saurin komawa ɗaki ta ɗauki hijab, nan ta fito ta samu Madina ta fito tana kama Hamid tare da fashewa da kuka.
Sakina kasheshi kika yi? me kika yi masa? Dama ba kida imani har zaki iya kashe mutum, Hamid! Hamid! wlh ya daina motsi.
Madina ta faɗa tana duba jikin Hamid ko zata ga wani jini a jikinsa ko Sakina wuƙa ta caka masa, sai da warin kashin ya noshi Hancinta kafin ta miƙe da sauri tana toshe hanci.
Idan ni ban kashe shi ba to ke ce zaki kashe shi da ɗan iskan abincin da kika dafa masa yau, na tabbatar ko tantama babu shine ya lalata masa ciki shashasha.
Cewar Sakina a fusace kana ta fice da sauri ta kira driver, ba jimawa suka shigo a tare suka kama Hamid suka fitar dashi zuwa mota jiki yana yararin kashi, suka saka shi a bayan mota kana ya shiga mazaunin driver, Sakina ta koma gida da sauri ta shiga ɗakin Mufeeda ta tashe ta tace ta ɗauki Rauda su koma ɗakin su baba ƙarami su kwanta, Abbansu ba lafiya zasu je asibiti ta kulle ɗaki in ta dawo zata buga ta buɗe, to tace mata kana ta juya ta fito tare da waya tana duba number ɗin Abba dan ta kirashi. Tana shiga mota ta cewa driver ya jira ta kira Abba ta faɗa masa kafin su wuce, nan tayi dialing number ɗinsa ya ɗauka yana cewa.
Yanzu nake shirin kiranki nace ki faɗawa Hamid na kai Hajiya asibiti da Jidda basu da lafiya, saboda tun ɗazu na kira wayarsa bai ɗauka ba.
Abba shima Hamid ɗin gashi nan rai kwakwai mutu kwakwai, zawo yake yi da amai yanzu haka ya suma zamu je asibiti, shine nace bari na faɗa maka.
Subhanallahi to ku tawo nan asibitinmu, bari na fato na jiraku Allah ya basu lafiya.
Sakina ta ce Amin kana ta kashe wayar ta sanar da driver su je asibitinsu.
****
Asibiti.
Ko da su Abba suka isa, emergency aka wuce da Hajiya dan kafin sukai itama ta suma, kuma zawo bai bar fita daga jikinta ba, nan likita da nurses suka shiga bata taimakon gaggawa, da kyar suka samu zawon ya ɗan tsaya sai nurses mata biyu suka gyara mata jiki suka saka mata parmpers ɗin manya tare da rigar masu jinya tunda basu zo da wasu kaya ba, aka sauya mata ɗaki zuwa inda aka kwantar da Jidda ana kara mata ruwa, dan itama suna zuwa asibiti ta ƙara wani aman, a lokacin ne likita ya kira Abba zuwa office ɗinsa, bayan sun zauna ne likita ya fara koro wa Abba bayani.
Gaskiya Alhaji an auna arziki sosai zawon ya ragu, amna me suka ci haka ne?
Gaskiya abinci ne suka ci shinkafa da miya da kosilo.
To a cikin abincin akwai food poison ma’ana akwai abinda yake da illa ga lafiyar su a cikin abincin, amma yanzu mun ɗaurasu akan magungunar da zai yi flushing wannan gubar na abincin, na tura komai zuwa gurin biyan kuɗi.
To likita mun gode amma akwai wani mara lafiyar da za a kawo shi yanzu, shima duk abincin yaci.
Subhanallahi Allah ya kyauta na gaba ya basu lafiya.
Abba ya amsa da amin kana ya fito daga office ɗin likita, ya fita zuwa farfajiyar asibiti dan jiran zuwansu Sakina.
Koda suka iso shima taimakon gaggawa aka yi masa kuma cikin ikon Allah zawonsa ya tsaya har ya farfaɗo daga suman ya shiga yin barci. Likita yasa ma’aikata maza suka gyara masa jikinsa kana suka mayar da shi zuwa ɗakin su Hajiya a nashi gadon, dukkansu barci suke yi hakan yasa Abba ya ce Sakina taje ta haɗo musu kayan jinya, ta ɗibowa Hajiya kayanta kala biyu da duk abin buƙata su Jidda ma haka, in yaso sai ta bawa driver ya kawo shine zai yi jinyarsu zuwa safiya aga abinda hali ya yi, sannan da safe ta shirya musu abin kari mai kyau da zasu iya ci inma da buƙatar wani abu zai kirata ya faɗa mata, to tace masa tare da yi musu fatan samun lafiya sai ta wuce ta samu driver ya dawo da ita gida.
Kamar yadda Abba yace, ta haɗawa Hajiya kaya tare da jidda a jaka guda, ta ɗauko babban carpet da bargo da dadduma, sai flaks ɗin Hajiya wanda ta samu akwai ruwan zafi a ciki, ta fito da kayan driver ya zuba a mota sai ta wuce part ɗinsu, nan ta samu Madina kwance a doguwar kujera ta maƙure tana barci, bata tashe ta ba ta wuce ɗakin Hamid shima ta ɗibar masa kaya ta haɗo kayan tea da kofuna da cokali da komai na buƙata a basket, sai ta fito ta kaiwa driver daya biyota ya amsa suka yi sallama ya tafi, ta dawo tana ƙarewa Madina kallo tare da mamakin yadda ta samu sukunin yin barci bayan Hamid yana cikin wani hali, duk kuwa da soyayyar da take yi masa, ta ɗauka ma zata ce zata bisu amma har suka tafi bata fito ba, ko ina so ɗin da take nuna masa ya tafi oho, yanzu ne ta ƙara tabbatar da Madina bata san ciwon kanta ba, haka ta wuce ta buga ƙofar su Yaƙub, Mufeeda ta buɗe ƙofar, nan Sakina ta ɗauki Rauda tace itama ta koma ɗakinta ta kwanta.
[7/25, 7:13 PM] Rahma Kabir: *ƘAZAMAR AMARYA*
Na
©®Rahma Kabir MrsMG.
Wattpad @rahmakabir
Page 21.
Sakina.
Tunda ta isar da sallar asubahi ta shiga kitchen ta shiga haɗa musu abin kari. Faten doya tayi musu na manja bai yi kauri ba kuma baiyi ruwa ba, sannan yayi matuƙar daɗi yadda dai zasu so cinsa domin doyar ma ƙanana ta yankashi, sai kuma tayi kunun gyaɗa mara shinkafa a ciki, ya zama zallar gyaɗar ne sai ta ɗaureshi da fulawa, bata saka tsamiya ba sai ta sanya madara a ciki ya haɗe yayi shar dashi Masha Allah, sannan ta soya irish da kwai mai yawa da plantain. Bayan ta kammala ta shirya yaranta duk suka yi wanka suka karya kana ta haɗe komai da zata kai asibiti a babban kwando sannan tace yaran su zauna a falo suyi kallo ba zata jima ba zata dawo sannan ta fita dan tuni ta kira driver yazo ɗaukarta, har ta aika yaran sun kai kayan abincin mota ɗazun, ta shiga mota suka wuce asibiti.
Acan asibiti kuwa tun asubahi Hajiya ta farka, da ta buɗe ido ta ganta a asibiti da ranta yasa ta dinga hamdala ga Allah, ta juya gefenta hagu da dama taga Jidda da Hamid kwance, bata yi mamaki ba domin tasan suma abinda ya sameta shine ya same su, daga can gefe ta hango Abba zaune a carpet riƙe da carbi yana ja, bata yi magana ba sai ta lumshe ido duk da ba barci take ji ba jikinta ne keyi mata ciwo saboda kwanciyar guri ɗaya, har garin Allah ya waye tangaras ga hada hadan motoci akan titi sun fara yawo, a sannan ne Hamid ya farka da salati a bakinsa Hajiya ta juya tana kallonsa wanda tuni Alhaji ya miƙe yana hamdala.
Hamid ka farka sannu ko ya jikin.?
Alhaji.
Hajiya ta ambaci sunansa cikin rauni da muryar ciwo, da sauri ya isa gadonta ya shiga jera mata sannu yauwa take ce masa ido na ciko da kwalla.
Shima Hamid abincin daya ci ne ya kawo shi asibiti ko?
Tace tana duban Abba, gyaɗa mata kai yayi yana cewa.
Wlh shima abinda ya sameki shine ya same shi, jidda ce dai nata ya zo da sauƙi tunda amai kawai take yi.
Alhaji wlh a binciki yarinyar nan da wata manufa ta auri Hamid ba hakanan bane…
Meyasa ba zaki bar al’amarinki ga Allah bane, ki daina zargin komai ki fauwala wa Allah, bana son ki riƙa furta wannan maganar har wani yaji. Kawai dai cikinku yaci abincin da bai saba bane yasa muku haka.
Hmmm Hajiya ta faɗa tana taɓe baki bata kuma magana dan tasan Alhaji bazai taɓa yarda da maganarta ba, Hamid dai saurarensu yake yi har suka gama magana ya san Madina ba zata taɓa kashe shi ba kawai dai aboncinta ne ya zo da matsala dan alamu sun nuna bata iya ba. A haka likita ya shigo da nurses biyu ya duba su kana yace zasu iya cin abinci amma a tabbbatar da tsaftarsa kafin su ci, kafin ya bayar da magani in sun karya susha sai suka fita. Abba da kanshi ya taimakawa Hajiya ta shiga bayin asibitin bayan ya haɗa mata ruwan wanka mai zafi a bokiti, da yake ɗakinsu na musamman ne sai wanda yaci ya ƙoshi yake zama a ciki, wato har da heatern ruwan zafi da komai a ciki, ya fito ya bata guri tayi wanka da brush dan duk Sakina ta haɗo musu shi jiya, ta yarda parmpers ɗin data cire a dustbin ɗin bayin, kafin ta ɗauro alwala ta saka wasu kaya masu kyau ta naɗe waɗanda ta cire ta fito riƙe dasu, Abba ya bata leda ta saka kana ya koma bayin ya haɗawa Hamid nashi ruwan, kamar dai yadda Hajiya tayi wanka shima haka ya gyara jikinsa ya saka wasu kayan, Jidda ce dai tayi brush da Alwala kawai da nufin anjima sai tayi nata wanka, Abba da kanshi ya fita ya kira masu aiki suka kuma wanke bayin suka saka turaren ƙamshi da kwashe duk wani datti suka fita, duk suka yi sallar asubahi kafin suka koma makwancinsu bayan an sauya musu zanin gado. suna zauna a haka ne sai ga Sakina ta shigo ɗakin da sallama, duk suka amsa ta ƙaraso ciki Driver ya aje kayan abinci dama yana biye da ita a baya, ya miƙa gaisuwa ga su Hamid tare da fatan samun lafiya kafin ya tafi. Sakina har ƙasa ta tsuguna ta gaida Abba ya amsa fuska a sake tare da yi mata sannu da hidimar aiki data sha, daga bisani ta gaishe da Hajiya ta amsa kadaran kadaham, Hamid ne ya amsa yana tambayarta yara tace lafiya suke kafin yace mata.
Ina Madina?
Banganta ba da safen nen ko tana barci a ɗaki.
Wayata kin ɗauko mini.
A’a ba san inda ka aje ba.
Ok bani wayarki na yi kira.
Sakina tace to ta ciro wayar a jaka ta miƙa masa ta koma mazauninta a farar kujera, a sannan ne ta yiwa Jidda ya jiki ta amsa da sauƙi. Hamid number ɗin Madina ya saka ya kira da layin Sakina, ya kusa katsewa kafin ta ɗaga tana cewa cikin muryar barci.
Helo waye?
Madina har yanzu barci kike yi baki tashi ba? kin manta ina kwance a asibiti ko.
Alhamdulillah beb ka farka, ya jikinka? Wlh jiya ban samu yin barci ba kwata kwata saboda halin da ka shiga sai wurin asubahi barci ya sace ni, shiyasa na makara gashi zani aiki, kuma matarka bata sanar dani komai da kake ciki ba.
Zan aiko driver sai ki shirya kafin yazo ya ɗauke ki, ki tawo mini da wayata.
Beb motata fa? ina ka aje mini key ɗin in ɗauketa kawai tunda na iya tuƙi daga nan zan wuce aiki kasan yau Monday.
Amma Madina ba zaki iya kira ki basu uzurinki ba tunda ga halin da nake ciki, ki bari gobe sai kije kuma maganar mota ki yi hakuri har a sallame mu.
Amma beb…
Kin ga Madina bana son jayayya ki shirya gashi nan zuwa.
Hamid ya faɗa yana kashe wayar ba tare da yaji me zata ce ba. Ya aje wayar akan gadon, duk maganar da suka yi su Hajiya sunji saboda wayar Sakina ana iya jin maganar wanda ya kira in dai ba ta rage volume ba, taji sharrin da Madinar tayi mata shuru tayu kawai tana tunanin mugun makircinta, Abba ne ya katse shurun yana cewa.
Sakina me kika dafo ne? ki zuba musu su karya.
To tace masa kana ta miƙe ta aje jaka ta faɗa musu abinda ta girka tare da tambayar me zasu ci. Hamid yace ta bashi kunun da plantain, Jidda kuma tace kunu da irish da kwai, Hajiya kuma tace faten zata sha da lipton, cikin ƙanƙanin lokaci ta zubawa ko wannen ta miƙa musu duk abinda suka buƙata, daga bisani ta zubawa Abba kunu da Irish haɗe da plantain dan tasan yana sonsu, kusan duk abubuwan da Hamid ke so haka Abban ke sonsu dan Hamid yana yawan bata labarin Abbansu yana son abu kaza da kaza shima haka yake so a gunsa ya koya, ta aje masa a gabansa ya saka mata albarka ta amsa da amin kana ta koma mazauninta ta rungume hannu kanta a ƙasa, ita kaɗai tasan yadda take ji a zuciyarta musamman yadda taji Madina tana zancen mota, wato Hamid mota ma zai bata ita kuma ko oho, tunawa da jiya Hamid yace ta tafi gidansu ta taji Zuciyarta ta karaya kamar ta fashe da kukan baƙin ciki, wato ita a yanzu ba tada sauran amfani a gunsa komai dai yanzu Madina ce a gabansa, zuwa wannan lokaci tunaninta ya kasa bata matsayar abinda ya kamata tayi, musamman ganin halin da iyalen gidan suke ciki kuma ba zata taɓa gayawa Abba ba dan tasan bazai ɗauki lamarin da sauƙi ba ga Hamid, gwara dai ta daure a sallame su kafin nan ta gama tsaida tunaninta guri ɗaya da hukuncin daya dace ta yanke wa kanta.
***
Madina.
Da kyar ta raba kanta da pillow ta miƙe tayi wanka kafin ta gabatar da sallah ta shirya cikin atamfa riga da siket ɗinkin fited, ta fito falo a zatonta zata ga breakfast akan dining tunda Hamid yace lallai dole Sakina zata yi musu, amma sai taga wayam ta kalli yaran da hankalinsu ke kan tv ta daka musu tsawa.
Kai dan uwarku ina mamanku? Kun kafewa tv ido kamar kun warke cutar makanta banda Hamid ne ya haifeku da nace daga ƙauye kuka fito saboda kauyenci, ko da yake ba ku yar a ƙasa ba tunda uwarku ba abinda ta sani.
Tsuru tsuru yaran suka yi suna kallonta dan ba ƙaramin tsoronta suke yi ba saboda suna tsoron tace sunyi mata laifi Abbansu ya ƙare fushinsa akan mamansu, babu wanda ya iya bata amsa sai binta da ido suke yi, Mufeeda ce taji haushin maganganunta amma ba zata iya tanka mata ba tunda tana tsoronta, kuma sarai ta fahimci zagin da ta yiwa mamansu kusan shine Abbansu ke yi mata, da bata ji a gunsaba ba zata faɗi haka ba.
Ba daku nake magana ba kun zuba mini ido sai kashe mayu.
Ta taa tafi asibiti.
Cewar baba ƙarami cikin in’ina, tsaki taja ta shiga kitchen nan ma bata ga komai ba da alama har wanke wanke anyi ba komai mai datti, nan ta fasa kwai huɗu ta soya shi ta dafa guda huɗu ta saka a leda akan zata je aiki dashi, dan bata jin zata zauna a asibiti ita aikinta zata je, taci kwai da tea kana ta fito ta koma ɗaki ta ƙarasa shiryawa, cikinta ne ya murɗa mata sai taji kamar kashi zata yi sai kuma ta saki tusa busss mai wari, itama da alama abincin jiya ya so ɓata mata ciki dan da gyatsar magwal ta kwana data wayi gari ne ta daina yi ga kuma yanzu ta fara tusa, haka dai ta dinga ɗaɗɗage hanci saboda wari, har sai da ya ɗan sire saboda turaren data fesa a jikinta, ta ɗauki jakarta data zuba duk abin buƙatar ta a ciki ta yafa figigin ƙaramin gyalenta a wuya ga ɗaurin ɗankwali data yi shi a goshi irin na ‘yan matan zamani, ta fito tana jin kanta a sama irin manyan mata an fito, ta fita a falon bata kula yaran ba, tana shirin kiran Hamid a layin daya kirata sai ga hon ɗin driver ya tsaya a gate, mai gadi ya buɗe masa ya shigo ciki sai ta wuce ta shiga mazaunin baya ya kuma tada mota suka wuce. Suna a kan hanya Madina ta buɗe jaka ta ciro kwai guda ɗaya ta ɓare ta zubar da dattin a cinkin motar taci kwan, tana gama ci ba jimawa cikinta ya murɗa sai ta saki tusa mara ƙara, nan take motar ta ɗauki wari wanda driver yaji kamar ya siƙe dan sosai warin ya isa hancinsa, duk da ya kunna ac sai kawai ya sauke glass ɗin motar ta gefensa dan ya samu iska mai kyau, Madina kam basarwa tayi ta matse kamar bata ji warin ba sai danne danne take yi a waya, Driver yana kallonta da madubi amma yadda ta bone yaji wani mugun takaici kamar yaje ya koɗa mata mari, gabaɗaya ta nuna tamkar ba ita ta sakar musu tusa ba, kafin su kai tayi masa yakai sau uku alla alla ya ke su kai ya sauketa ya huta dan tusan nata yana nimar ƙullar masa da ciki.
Da suka isa har ɗakin ya kaita bai shiga ba ya juya ita kuma ta shiga da sallama, ganinsu reras akan akan gado ba ƙaramin dariya ya bata ba, amma sai da matse ta zauna a carpet nesa da Abba ta gaishe shi tare dayi masa ya masu jiki, ya amsa fuska sake kana ta gaishe da hajiya, ciki ciki ta amsa, ko a jikinta ta miƙe ta isa wajen gadon Hamid ta miƙa masa wayarsa kana ta yi masa ya jiki ya amsa yana murmushi, ta yi magana kasa kasa.
Beb zanje aiki fa kasan oganmu bayi da kirki.
Ba zaki je yau ba na gama magana.
Ya faɗa yana haɗe rai, bata kuma magana ba ta koma mazauninta tana haɗe rai, ɗakin dai shuru ko wanne yayi busy da abinda ya zaɓarwa kansa, Madina cikinta ya murɗa kafin ta ankara ta saki mugun tusa mara ƙara, nan take ɗakin ya ɗauki mummunar warin tusarta, Hajiya cikin damuwa ta rafka salati.
Warin meye nake ji haka?
Kallon kallo a ka shiga yi dan babu wanda ya amsa mata, Hamid da yake yasan halin kayansa ya tura mata saƙo kamar haka.
Madina cikinki ya lalace kije ki amsa magani wajen likita kisha, ki daina yi mana tusa dan nasan wlh kece kika yi shi, in kuma kinji ya taso miki ki miƙe ki fita waje kiyi.
Tana gama karantawa ta ɗago suka haɗa ido tana marairaice wa, ido ya lumshe ya buɗe yana sakin murmushi, sai ta sunne kai tana yi masa reply.
Beb shine har da sharri, nifa bani nayi ba.
Madina daga aurenmu zuwa yanzu nasan ya kalar tusarki yake, dan haka karki yi mini gardama, da kinji ya taso ki fita kiyi a waje tun kafin kiyi abun kunya su gane ke ce.
Hamid ya mayar mata da amsa, ɗagowa tayi ta murguɗa masa baki shi kuma ya saki murmushi wanda duk abinda suke yi akan idon Sakina, hakan kuwa ba ƙaramin ɓata mata rai yayi ba, gani take kamar da gangan suke yin magana da juya a text da kuma ido domin su mugzuna mata, ji tayi zaman ɗakin ya gundureta dama ba zama zata yi ba zata koma gida, tana shirin miƙewa Madina ta miƙe da sauri ta nufi ƙofa dan tuni tusar ta turnuƙota zata saki, ko kafin ta buɗe ƙofar ta sake shi mai sauti ga kuma wari, bata iya juyawa ba ta fice daga ɗakin gabaɗaya saboda tsabar abin kunyar data aikata, Hajiya ta rafka salati tana ambaton.
Shikenan zata ƙara kumbura mana ciki ta ƙarasa kashemu, kunga mini ‘yar banzan yarinya, wlh wannan ba tada hankali balle kunya, kawai ta sakar mana tusa sai kace an yada mushe.
Sakina me zata yi in ba dariya ba bata san sadda ta sake shi ba, Jidda ma haka, Abba ma murmushi ya dinga yi har haƙoransa suna fitowa, Hamid ma dariyar yayi dan yasan za’a rina, Hajiya dai ta haɗe rai.
Maganata ce ta baku dariya, bama ta warin tusan kuke yi ba ko.
To Hajiya kece da abin dariya, meye na magana ai duk munga abinda ya faru, sai ki ja bakinki kiyi shuru.
Cewar Abba, Hajiya kwafa tayi ta gyara kwanciya dan gabaɗaya takaicine ya cikata na haushin Madina, itace sanadin kawo su asibiti gashi kuma ta zo zata ƙara musu wani cutar a ciki.
[7/26, 3:44 PM] Rahma Kabir: *ƘAZAMAR AMARYA*
Na
©®Rahma Kabir MrsMG.
Wattpad @rahmakabir
Page 22.
Madina tana fita bata tsaya ba ta fice daga asibitin gabaɗaya ta samu napep ta wuce gidansu, koda ta isa ta samu ba kowa a falon ta zauna tana cire gyalenta sai ta ciro waya a jaka ta turawa oganta saƙon sai gobe In Allah ya kaimu zata samu zuwa aiki saboda bata jin daɗi, bata tsaya jiran reply ba ta saka wayar a Airplane mode, sai ta kwanta a doguwar kujera a lokacin ne Momy ta fito daga ɗaki cikin shirin fita tana kiran ‘yar aikinta, ko da tazo umarnin kula da gidan tayi mata sannan in ta kusa dawowa zata sanar da ita abincin da zata ɗaura, mai aikin tace a dawo lafiya, sai ta wuto nan falo ta ga Madina tana zuba mata murmushi ta tsaya turus tana yi mata kallon mamaki.
Ke Madina nake gani ko kuwa idona nane.?
Kai mom sai kace na zama aljana, nice mana.
Lafiya na ganki yau? keda bansa ran ganinki ba sai nan da sati biyu ko uku, Allah yasa dai lafiya lau.
Mom wlh gidan Hamid baya min daɗi kwata kwata, yadda na so ya kasance ba haka na samu ba.
Uban me suka yi miki yanzun nan in tashi hankalinsu, dan bazan taɓa yarda a wulaƙanta min ke ba.
Momy ta faɗa tana samawa kanta gurin zama tare da yaye gelenta, Madina ta turo baki cike da shagoɓa tana bawa maman labarin abubuwa da suka faru tun kaita gidan, bata ɓoye mata yadda Hamid ke sonta ba amma ta kula da taurin kansa bata iya juya shi dan yaƙi ɗaukar mata ‘yar aiki, gashi jiya tayi girki sunci sun kwanta asibiti saboda ya ɓata musu ciki, sai ta ɗaura da cewa.
Mom ashe haka kishi yake da zafi? wlh tunda nasan yadda aure yake naji gabaɗaya na tsani ganin matar Hamid, fatana ya saketa tabar mini gidan ni kaɗai, sai yanzu nake jin da ban auri mai mata ba dan wlh bazan jure sharing Hamid da wata ba, duk da ma ta bar mata muci amarci na wata ɗaya.
Dariya momy ta kwashe da shi.
Eehh yaro yaro ne, wato sai yanzu kika fara hangowa kanki abinda tuntuni na hango miki, Madina kina da masoya masu sonki sosai kuma samari masu mugun kuɗi amma kika kafe son Hamid ya rufe miki ido shi kike so, gashi tun ba aje ko ina ba kin zo kina yi mini ƙorafi, to wlh baki isa ki bani kunya kisa na shiga bakin duniya ba, Aisha itama mai matar ta aura kuma gashi tana rayuwa cikin kwanciyar hankali kamar ba tada kishiya, hakazalika nima na auri babanku da matansa har ya rasu yana sona, dan haka kema tsayawa za kiyi ki kama mijinki da kyau ki yiwa kishiyarki zarra.
Taya mom? Bayan ta fini iya girki kuma Hamid yana mugun son abincinta.
Madina yanzu ne lokacinki da zaki murza kambunki da kyau, yanzu ne yake mararinki da zaki kafa masa duk wani abu da kike so dole ya miki, abu na farko da zan faɗa miki shine ki dage masa akan ya sauya miki gida sannan dolensa ya nima miki masu aiki da zasu gyara miki gida da yin abinci, ko baki ga yadda Aisha take murza mijinta bane sai yadda tayi dashi, kuma ba boka ba malam da son da yake yi mata take aikata komai.
Mom Hamid Bbaya yi mini irin wannan son Wlh da har zan juya shi, yana da mugun kafiya, ni kawai in da yadda zaki taimaka miki kiyi na kori kishiyata na zama ni kaɗai sannan ya sama mini ‘yan aiki.
Madina kin ɗauko da zafi, uban waye zai riƙe masa yara? Dole kece zaki yi wahalarsu, dan haka ki bar uwarsu ta zauna ta kula dasu kema kiji da kanki.
Mom na tsaneta bana son ganinta a gidansa, wlh bazan jure ganin Hamid na mu’amala da ita ba.
Madina ta faɗa idonta yana ciko da kwalla, salati momy tayi tana mamakin wannan zafin kishi da Madina ta ɗauko, kuma a da sam ba haka take ba, kawai tana tunanin ta fara sanin daɗin namiji yasa take ambaton haka, dole ne kuwa tayi abinda zata samawa ‘yarta farin ciki.
Shikenan Babyn momy zan ɗauki mataki akai, zo naji ɗuminki dan nayi missing wannan shagoɓar taki.
Momy ta faɗa tana ware mata hannu, Madina sai ga hawayen shagoɓa nabin kuncinta ta miƙe da sauri ta faɗa cinyar momy.
Dan Allah ki sama mini mafita, a yadda nake jin Sakina kamar a wayi gari ace mini ta mutu tabar duniyar duka, na zama sai ni da mijina.
To shikenan, ai nace miki zan ɗauki mataki, wlh ba zaki taɓa niman abu a guna ki rasa ba, farin cikinku nake so keda Aisha dan ku kaɗai gareni banda kamarku.
Yauwa mom nasan kina sona ai, nima ina sonki irin sosai ɗin nan.
Momy dariya tayi kana ta jaye Madina ta zauna a gefenta, ta ɗauko wayarta a jaka ta shiga niman wata ƙawarta Hajiya Saratu, koda ta ɗaga suka gaisa kana tace.
Ina so ki amso mini maganin mallaka gurin wannan matar da kika bani labarinta, lokaci yayi da zan amsarwa Madina dan samun kwanciyar hankalinta a gidan mijinta.
Ai Hajiya tuntuni nace ki karɓa musu domin wlh mazan zamanin nan sai da mallaka ba a barin su sakaka koda mace ba ta da kishiya, dan lamarin Rijalu sai an riƙe su tamau ake samun kansu.
To ai ya zama mini dole yanzu na amsa, Aisha dai ba tada matsala Madinar ce dai nake so a amsarwa dan mijin nata yana da taurin kai.
To shikenan anjima zan je gurinta zan yi mata bayani duk abinda tace zan faɗa miki dan da zafi zafi ake dukan ƙarfe.
Ta faɗa tana dariya, momy ma dariya tayi tana yi mata godiya kana suka aje wayar, Madina cikin yanayin jin daɗi tace.
Thank you mom ina ƙaunarki.
Nima ina ƙaunar wannan babyn mai rikici.
Ta faɗa tana shafa kuncin Madina, sai ta miƙe tana mayar da gyale.
Kije ɗaki ki kwanta ki huta ba zan jima ba zan dawo, in kina buƙatar wani abu ga Ladi nan zata yi miki komai.
Da zan koma asibiti ne dan kar Hamid yaji haushi ban zauna ba.
Rabu dasu su karata can, uban waye yace ya matsa miki lallai sai kinyi musu girki, ai jiki magayi gobe ba zai ce ki dafa ba.
Ta ƙare maganar tana ‘yar dariya, Madina murmushi ta saki kama tayi mata adawo lafiya sai ta miƙe ta shiga ɗakin momy ta kwanta a lafiyayyen gadonta tana sauke numfashi ba jimawa barci mai nauyi ya ɗauketa.
Momy koda ta fita wani barka taje na ɗiyar ɗaya daga cikin ‘yan meeting ɗinsu na kawaye taje, bata jima ba ta wuce gidan Hajiya Saratu dan ba zata ɗauki lamarin Madina da wasa ba, ba zata yarda ‘yarta tasha wuya a gidan miji ba da ranta da lafiya. Ta samu Saratu tana aikin haɗa turaren wuta dan sana’arta kenan, amma haka Momy ta matsa mata suka tafi gidan mai maganin mallaka. Koda suka isa basu samu mutane ba sai mutum ɗaya da suka jira ta sallama kafin suka shiga ɗakin, nan suka gaisa momy sai raba ido take yi tana ganin irin yanayin ɗakin an baza layu da tarkace sai kace na ‘yan bori, ko kafin suyi mata bayani ta koro musu bayanin abinda ya kawo su, momy tace kwarai kuwa maganar da suka zo da ita kenan. Tayi murmushi tana cewa.
A yanzu haka uwargidansa zata bar gidan a cikin kwanakin nan kuma in ta tafi ba zata dawo ba rabuwarsu kenan, sannan Madina ba itace zata riƙe yaran ba dan zamu saka masa tsanarsu saboda kar su zame mata matsala, zata mallaki Hamid da duk abinda take buri a rayuwarta, dan za muyi amfani da son da yake yi mata mu ƙara ruruta wutar soyayyarta ya zama baya ji baya gani akanta, hatta iyayensa zai iya saɓa musu akanta, ‘yarki zata yi farin ciki na har abada mutuwa ce zata rabasu.
Idan haka ya faru nafi kowa farin ciki, nawa ne zamu bada kuɗin aiki dan yau nake so ayi komai.
Dubu ɗari da hamsin zai isa ayi komai.
Nan take momy ta zaro bandir ɗin dubu ɗari, tace ta bata account number ta tura mata sauran haɗe da dubu ashirin tukuici. Mai magani ta karanto account ɗinta nan take momy ta tura mata dubu saba’in tace ayi komai a gama, mai magani ta tabbatar mata da yau zata tsaya akan aikinsu har sai ta kammala, ba a buƙatar komai dan da aljanu zata yi aikin, nan suka yi mata godiya kana suka wuce sai da momy ta sauke Saratu a gida kafin ta wuce gidanta.
****
Asibiti.
Madina tana fita ba jimawa Sakina tace zata koma gida yara su kaɗai ne me za a dafa musu da rana, Abba yace.
Wannan abincin ma zai ishe mu, sai dai ki dafa na dare anjima, kuma ina saka ran yau zamu koma gida dan da alama jikinsu da sauki Alhamdulillahi.
To Allah ya ƙara musu lafiya. Me za a dafa da daren?
Sakina tuwon masara nake sha’awa da miyar kuka lami wacce ba a saka nama ba.
Cewar Hamid yana dubanta.
Amma kuwa ba mu da garin masara.
Ni akwai a ɓangarena kije ki duba a kitchen yana nan a cikin store kusa da buhun semo. Sannan muma girkin kiyi damu gabaɗaya.
Cewar Hajiya, Sakina to tace musu sai ta yi musu sallama ta fice Alhaji ya bita da addu’ar sauka lafiya, ya mayar da dubansa ga Hamid yana cewa.
Daga jiya zuwa yau ya kamata ku gane gaskiya ɗaya ce, wlh Sakina matar rufin asiri ce amma gabaɗaya idonku ya rufe da wannan aure sam bakwa ganin kirkinta da haƙurinta, duk da abubuwan da kuke yi mata amma ita dai ta jure da komai naku, gashi ita wacce ta jawo muku kwanciyar a asibiti bata damu da ku ba kamar yadda Sakina ta damu, wannan ina ganin ya isheku ishara musamman kai da kake niman wulaƙantata.
Alhaji ni ai tuni na fara dawowa hayyaci na, duk da Sakinar ma ta koyi rashin mitunci, na dai kama kaina.
Cewar Hajiya, Alhaji ya saki murmushi.
Karma ki kama kanki wlh ki cigaba da yada girma. Kai kuma ka cigaba da muzguna mata kaji.
Abba wlh ina iya ƙoƙari wajen yin adalci amma Sakina ta sauya hali, jiyan nan ƙiri ƙiri na sata tayi mini abu tace ba zata yi ba.
To waye ya sauyata ta zama haka in ba kai ba, ai ka guji ɓacin ran mai haƙuri bai iya ba in ya tashi nunawa, kadai ji tsoron Allah wlh ka zama adali.
In sha Allah zan kula Allah ya bani iko.
Duk suka amsa da amin kana suka yi shuru ko wanne da tunanin da yake yi a ransa, Hamid dai tunanin jiya yace taje gidansu ya tsaya masa a rai dolensa ya janye maganarsa ko dan Abincin da zata riƙa dafa masa dan wlh baya jin zai sake cin abincin Madina, kuma dole ta tsaya Sakina ta koya mata girki in taƙi taje makarantar koyan abinci dan ba zai taɓa ɗaukar mata ‘yan aiki ba, dolenta zata kula da gidansa kamar yadda Sakina take yi masa, wannan tunanin yasa yaji kamar ya kira Sakina ya ce karta tafi gida ya janye maganarsa, amma ganin ma ta zauna har zata yi musu girki yasan ba zata tafi ba tunda tasan halin da yake ciki yana bukatar ta a yanzu, kuma koda taje gidan yasan su Yaya umma sai sun dawo da ita, hakan yasa yaji natsuwa a cikin ransa.
*****
Sakina.
Tana isa gida su Mufeeda suka shiga bata labarin abinda Madina tayi musu, hankalinta ya tashi sosai amma sai ta danne tace musu.
Amma babu wanda ya ce mata wani abu ko? kunsan yiwa babba rashin kunya Haramun ne.
Bamu ce komai ba Mama amma wlh zuciyata bata yi mini faɗi akan yadda ita da Abba suke yi miki.
Cewar Mufeeda, da sauri Sakina ta kalleta tana mamakin fitar maganarta dan bata zaci tayi wayon gane abubuwa ba, ta kamo hannunta tana cewa.
Mufeeda munzo duniya domin muyi bautar Allah ne mu samu Aljanna, kinga duk abinda za a yi mini bazai dame ni ba domin Aljanna nake nima, kuma ina so ku zama masu haƙuri ku samu aljanna muci kayan daɗi muna yiwa wasu gwalo ko.
Ta ƙare maganar cikin barkwanci, dariya duk yaran suka yi da alama duk sun yarda da maganarta, ta miƙe tana cewa su cigaba da kallonsu tana zuwa, tana shiga ɗaki ta saka key ta saki kuka mara sauti, tausayin yaranta ya shiga bin dukkan bargon jikinta har take jin shakkar barinsu a gidan, bata san ya makomar rayuwarsu zata kasance ba.
Allah kana gani bana nufin kowa da sharri, ga yarana nan ka zame musu gatansu, na tabbatar kaine mai kashewa da yarawa, bani da tsumi ba ni da dubara ka shiga cikin lamarina.
Kiran daya shigo wayarsa yasa ta share wayenta ta isa gefen gado ta zauna, yaya Umma ce nan ta seta kanta tayi sallama.
Sakina ya yara fatan kuna lafiya.
Lafiya lau Alhamdulillahi, Hamid ne dai da Hajiyarsa suke asibiti jiya ma a can suka kwana.
Nan ta kwashe labarin komai a takaice ta faɗa mata amma banda zancen yace ta tafi gida, yaya umma tayi musu fatan samun sauki ta ɗaura da cewa.
Sakina shiyasa nace ki ƙara haƙuri, gashi ba aje ko ina ba Allah ya fara nuna musu, ko a abinci kin mata zarra, kuma ki daure ki jure ki basu wata guda komai zai dawo daidai.
To yaya umma koda yace na bar masa gidansa sai na zauna?
To ina zaki je? ina kike dashi daya fi nan? yaranki zaki duba ki bashi haƙuri ki zauna ko dansu.
Yaya bakya duba wulaƙancin da zai biyo baya.
Wulaƙanci na nawa ne baki gani ba, ko kin koma gidan dawo dake za ayi tunda baba ba zai bari ki zauna ba, Auren nan kowa haƙuri yake yi Sakina.
Yaya wannan tunanin yasa mata da dama suke kamuwa da ciwo saboda yadda iyayenmu suke tsoron saki, kullum mace tana cikin halin damuwa ba a duba wannan sai dai ace tayi haƙuri ta zauna kodan yaranta, namiji yayi ta wulaƙantata saboda a gidansu yasan ba tada power.
Sakina ta faɗa tana fidda kwalla, Yaya umma tace.
Kima daina wannan maganar, koya ce miki ki je gida ne kike wannan zancen.?
A’a kawai misali nake kawo miki.
To Sakina ibada fa kike yi, ki duba Aljanna kike nima ki rabauta, shiyasa iyayenmu suke bamu haƙurin mu zauna.
Gaskiya ne amma mazan zamanin nan sai addu’a yaya, wai yaushe ma zaki zo ne dan ya hanani fita.
In Sha Allah cikin satin nan in zan zo zan sanar dake.
Cewar Umma, nan suka ɗan taba hira kana daga bisani suka aje kan wayar.
[7/26, 5:11 PM] Rahma Kabir: *ƘAZAMAR AMARYA*
Na
©®Rahma Kabir MrsMG.
Wattpad @rahmakabir
Page 23.
Sakina ta miƙe ta taka kujerar miro ta sauko da akwatinta babban, dama ba komai a ciki ta buɗe shi kana ta buɗe waldrobe ɗin kayanta ta shiga zuba kayan a akwati, da yake duk gogaggu ne haka ta dinga jerasu tana binsu daki daki, sai da ta zuba kala sha biyu kana ta zuba sauran undies ɗinta da hijab kala uku, ta je gefen takalma ta ɗauki kala uku sai jaka guda ɗaya data zuba tarkacenta duk ta saka a cikin akwati ta rufe, ta jashi kefe ta yafa masa zani dan kar yaran su gani su tambayeta, sannan ta zauna gefen gado tana sauke ajiyar zuciya, ji tayi gwara tayi nesa da kowa in da zata samu natsuwa, inta huta sai ta dawo, dama tasan ko taje gida sai sun dawo da ita kuma Hamid ɗin zai ƙara jin daɗin yi mata wulaƙanci, shiyasa tun a hanyar dawowa daga asibiti ta gama yanke shawarar dole ta bar masa gidansa na ɗan wani lokaci, yaranta sune kaɗai inta tuna take jin karayar zuciya, amma tasan Allah yana tare dasu shine ƙarfin guiwarta.
Sallar azahar ya sa ta miƙe ta gabatar da shi kana ta fito falo tasa yaran suyi sallah sannan ta shiga kitchen ta ɗaura musu abinci taliya ta dafa suka ci. Wajen ƙarfe hudu ta je gidan Hajiya ta ɗibo garin tuwo ta dawo ta ɗaura girki cikin sauri ta samu ta kammala komai, zuwa ƙarfe shida ta gama tuwon da miya ta koma ɗaki tayi wanka ta sauya kaya zuwa shadda riga da zani, bata yi kwalliya ba ta fito falon taga yaran sun fita can lambu, wannan ya bata damar komawa ɗaki ta ja akwatinta ta fito dashi zuwa gurin mai gadi tace ya fitar mata dasu ya tsaya a waje gurin kayan gata nan zuwa, yace to cike da bin umarninta, sai ta koma ɗaki ta saka hijab ta ɗauki jaka ta rataya ta shirya tsaf kana ta fito zuwa can lambu ta taso ƙeyar yaran suka dawo falo tana dubansu.
Mufeeda ki kula da ƙannenki zan je na dawo, ko da su Abba sun dawo kice na fita kawai in ya tambaya.
Mama ba asibiti zaki je ba.
Mufeeda tace tana tsareta da ido.
Gidan yaya umma zani bazan jima ba zan dawo.
To mama ki siyo mana alewar tofi musha.
Cewar Yaƙub, shafa kansu sakina tayi tana saka musu albaka cike da tsantsar kewarsu da zata shiga, ta ce su zauna a ɗaki kar su fito kana ta fita da sauri dan ana niman shida da rabi. Tana fita ta bawa mai gadi dubu ɗaya tana ce masa sai ta dawo, a dawo lafiya yace mata kana ya koma cikin gida, sam bai kawo tafiya zata yi ba dan yasan bata cika tafiya ba, balle yaga yaranta suna gida sannan ma mai gidan ba lafiya bai ga dalilin da zai sa tayi tafiya ba, ya bayar da ƙila saƙo zata kai ta dawo. Sakina tafiya tayi sosai akan titin layinsu kasantuwar unguwa ce na masu hannu da shuni ba a fiye samun taxi ko napep ba sai mutun yaje baban titi, amma cikin ikon Allah sai ga wani mai napep ta tare shi ta sanar da shi tashar motar kawo zai kai ta, yace dubu biyu ba musu ta shiga tare da kayanta ta zauna tana koro addu’a a ranta suka tafi.
*****
Asibiti.
Ƙarfe shida likita yazo ya ƙara duba jikinsu ya sallame su akan zai riƙa zuwa gida yana duba su, Alhaji yayi masa godiya kana yaje ya biya komai ya dawo suka fara haɗa kaya zasu tafi, a lokacin ne Madina ta shigo tare da momy ɗinta, shine ya dakatar da tafiyarsu suka zauna suka koro gaishe gaishe da ya jiki, sai momy ke cewa.
Itama Madina ashe bata jin daɗi waya nayi da ita tace zawo take ta yi tun da ta koma gida, shine na biya na ɗaukota muzo na duba ku daga nan itama a haɗa mata magani.
Ashsha ashe shiyasa bata dawo tun ɗazu ba, amma ya jikin ‘yata da fatan zawon ya tsaya.
Ya tsaya, sai kasalar jiki nake ji.
To Allah ya ƙara sauki, Alhamdulillahi naki ma yazo da sauƙi. Yanzu tashi kije ɗakin likita ya dubaki sai mu jira ki fito mu wuce gida.
Cewar Alhaji, Madina ta ce to kana momy tayi musu sallama suka fito tare tana jin daɗin yadda momy ta shirya mata dan kar suga lafinta bata dawo ba, tun a hanya tace ga yadda zasu yi, dan haka har mota Madina ta rakata kafin ta wuce ita kuma ta koma ɗakin likita tayi masa bayani ya rubuta mata magani ta fito taje pharmacy ta amsa sai ta koma ɗakin ta sanar da Abba ta gama, nan suka haɗa kaya suka tarkato zuwa gida lokacin ana ta kiraye kirayen sallar magrib, a gidan su Abba suka sauka daga nan ne driver ya taya su Hamid ɗibar kaya suka dawo gidansu, Hamid ɗakinsa ya wuce ya kwanta yana mayar da numfashi dan gabaɗaya ba ƙarfi a jikinsa, abinda ya faranta masa rai bai wuce yadda yaji ɗakinsa yana fidda ƙamshi mai daɗi ba, dan hatta zanin gadonsa Sakina ta sauya masa mai kyau, ya miƙe ya leƙa bayi ya tadda an gyara komai, ɗakinsa fes gwanin sha’awa, nan ya ƙara tabbatar da zaman Sakina a gidansa shine mafitarsa, dan bai hango tsafta a gurin Madina ba, duk ƙazantar da yake gani a gurin Sakina to Madina ta damata ta shanye, shi yayi auren wayayyiyar mace dan ta rage masa damuwar da Sakina ashe wani damuwar zai ƙara kwasarwa kansa, tsafta dai ashe ba a wayayyiyar mace yake ba kawai daga hali ne da kuma tarbiyyar data samu, duk da yana mugun son Madina amma baya jin zai jurewa ƙazantarta, haka ya haɗawa kansa ruwan wanka ya yi tare da alwala ya shirya ta wuce masallaci, a nan ya zauna yana jiran ayi Isha’i sai ya shiga gida gabaɗaya.
Bayan anyi sallar magrib sai ga Jidda tazo riƙe da kwando da kuloli a ciki, Mufeeda ta tareta da cewa.
Mamanmu bata nan taje gidan Mama Umma.
Ina tuwon data girka na ɗibar mana.
Yana kitchen.
Cewar Mufeeda tare da wucewa kitchen ɗin dan ta zuba musu suma su ci, Suna shiga ta nuna mata nasu a wani kula.
Mamanmu tace wannan ne naku miyar ne bata zuba ba tace in kun dawo saina zuba na kai muku.
To jidda tace ta ɗiba miyar a ɗaya daga cikin kularsu ta haɗa da kular da aka saka tuwon ta fita daga kitchen ɗin ta wuce. Mufeeda ta zubawa su Yaƙub da baba ƙarami nasu daban sannan ta saka nata da Rauda duk suka zauna a carpet ɗin falo suka soma ci. Bayan sun kammala suka kwashe kayan suka mayar kitchen suka wanke hannu tare da shan ruwa suka dawo falo suka zauna, ana kiran sallar Isha’i suka wuce ɗakin Mufeeda suka gabatar, bayan sun kammala suka dawo falo suka cigaba da kallo, a lokacin ne Hamid ya dawo suka yi masa sannu da zuwa Rauda ta rungumeshi tana oyoyo Abba, ya ɗauketa suka zauna a cushing yana cewa Mufeeda.
Je ki kira mini mamanku tazo ta bani abinci yunwa nake ji.
Laaa Abba ai Mamanmu taje gidan mama Umma tun ɗazu kafin ayi magriba, tace ba zata daɗe ba zata dawo amma kaga har yanzu bata shigo ba.
Ta ƙare maganar cikin ƙasa da murya tana langwaɓe kai, shuru Hamid yayi naɗan lokaci yana tunanin kar dai Sakina ta tafi gidan da ya ce mata ne, bayan kuma ya dawo yana so suyi sulhu komai ya wuce, da sauri ya ciro wayarsa a aljihu ya shiga kiran Sakina sai dai baturiyar nan me yin magana tace layin a kashe yake, ya sauke wayar ya lalubo layin yaya umma ya kira, tana ɗauka suka gaisa har take yi masa ya jiki ya amsa yana cewa.
Dama na kira Sakina ce a wayar a kashe, ɗazun tace zata zo gidanki kuma shiru bata dawo ba kice mata tayi haƙuri zan turo driver ya ɗaukota.
Sakinar ce tace ta zo gidana? To gaskiya bata zo ba dan nasan waya kaɗai nayi na ita ɗazun da safe.
To shikenan ƙila gida ta tafi bari na kira yaya Hamza naji sai anjima.
Hamid wani abun ya faru ne?
Wlh ɗan saɓani muka samu jiya nace ta dawo gida kuma wlh barazana kawai nayi mata amma har zuciyata bana nufin haka, yau da safe dama nayi niyya nace na janye maganata sai kuma na kwana Asibiti, ɗazun muka dawo da magriba shine na samu bata nan.
Yaya umma shuru tayi tana tuna maganar da suka yi da Sakina ɗazun, hankalinta yayi mugun tashi dan alamu sun nuna a cikin maganar Sakina lallai ba gida zata je ba.
Allah yasa tana gidan nima bari na kira na tambaya.
Abinda tace masa kenan ta kashe wayar, ta kira Falmata ko taje can gidanta, nan ta tabbatar mata da bata je ba, Hamid shima ya kira yaya Hamza yace yana a gidan yanzu haka kuma Sakina bata nan, cikin tashin hankali ya shiga kiran duk inda yayi tsammanin zata tafi amma Sakina bata je can ba, Yaya umma hankalinta yafi na kowa tashi dan kasa haƙuri tayi ta tafi gidansu suka haɗu da yayyinsu maza tana basu labarin hirar da suka yi ɗazun, hakan ya tabbatar Sakina ta tafi ne kuma ƙila tayi nisa. Cikin daren nan haka suka dinga kiran waya amma ba labarin Sakina hankalin Hamid in yayi dubu to ya tashi, bai taɓa zato Sakina zata yi zuciya irin haka ba har ta iya barin yaranta ta bar gidan, yasan duk barazanar da zai yi mata dole zata ɗauka saboda yasan tana mugun son yaranta, sai gashi a daidai lokacin da yake buƙatarta ta tafi ta barsu, sai da ma ya shiga ɗakinta ya tabbatar da lallai tafiya tayi dan bai ga babban akwatinta ba kuma ta ɗiba kaya a waldrobe ɗinta, jiki a sanyaye ya fito ya nufi ɗakin Madina da ke kwance tana cin biscuit da hajiyarta ta siya mata ɗazun, ya zauna gefen gadonta ya dafe kai damuwa ƙarara ya bayyana a fuskarsa, Madina ta ɗago ta zauna tana cewa.
Masoyi ba dai jikin naka bane naga fuskarka da damuwa.
Sakina ce ta kwashe kaya ta bar gidan yanzu haka maganar da ake yi ba a san in da ta tafi ba.
Wani irin ta bar gida sai kace wata yarinya, ina zata tafi har ta iya barin yaranta? ku dai bincika dai.
Dagaske nake miki ta tafi dan nine naja ta tafi saboda abinda ya haɗaku jiya da kika faɗa mini nace da safe ta safi gida to sai ga rashin lafiya ya kama ni, na ɗauka ta haƙura saboda rashin tafiyata har mu sasanta ashe da niyyar zata tafi ɗin a ranta.
Shikenan ni zata jawo mini zagi ace nayi sanadin barinta gidanka, gaskiya ayi ƙoƙarin sanin inda take ta dawo dan wlh bazan iya rainon yaranta ba.
Da sauri Hamid ya juya yana dubanta jin wai ba zata riƙe yaransa ba ƙiri ƙiri.
Madina nayi zaton yarana yaranki ne ashe ba haka kike ɗauka ba, yau ko uwarsu tana nan na ɗauka zaki riƙe su tamkar naki, ashe da gaskiyar Sakina tace ba zata bari ki bautar mata da yarinya ba tunda gashi tun ba aje ko ina ba kin nuna ba yaranki bane.
Nifa ba haka nake nufi ba kawai dai kasan ba ni da wadataccen lokacin kula dasu saboda aikina, sannan ga shi ban saba da raino ba gidanmu ni kaɗai ce kuma nima komai yi mini ake yi.
Madina ta faɗa cikin shagoɓa. Hamid ya girgiza kai yana cewa.
Aikin ai bai zama dole sai kin je ba tunda baki rasa komai a gidana ba, ina ganin in hakan zai zama takura zaki ɗauki hutu saboda yaran ko ki aje shi gaba ɗaya na riƙa biyanki albashinki duk wata.
Narantse da girman Allah babu wanda ya isa ya hanani aikina, baka san wahalar karatuna ba dan haka banga dalili saboda raya kace na aje ba, gobe In Sha Allah sai na fita aiki.
Ta faɗa a hasale, Hamid binta da kallo kawai yake yi cike da mamaki, bai ce mata komai ba ya miƙe ya fice daga ɗakin, a fusace ta sauko a gadon tabi bayansa tana cewa.
Wlh Hamid bazan iya da wannan damuwar ba, dan matarka tabar gida kace wai saina riƙe maka yara, kaje ka nimota duk inda ta shiga ta dawo dan yaranta ehe.
Hamid tsabar ransa ya ɓaci ya juyo a fusace ya kifa mata mari, ihu ta saka tana tsalle tare da faɗin Allah ya isa bata yafe ba, bai kula ta ba ya wuce a zuciye ta ruga da gudu ta bar part ɗin zuwa sashinsu su Hajiya kamar mahaukaciya. Hamid kam zama yayi a cushing yana tambayar yaransa sunci Abinci, suka ce masa eh, sai ya miƙe ya je kitchen ya ɗiba tuwon ya saka miya ya ɗauko ruwa yazo kujera ya zauna yana ci dan sosai yake jin yunwa ba zai iya jurewa ba, saboda damuwar da yake ciki bama jin daɗin abincin yake yi ba, haka ya tusashi yana jin cekar Sakina yana damun zuciyarsa, yasan duk inda taje zata dawo amma babbar damuwarsa ina taje? kuma yaushe zata dawo gareshi? duk babu wanda zai amsa masa wannan tambayar.
[7/29, 5:39 PM] Rahma Kabir: *ƘAZAMAR AMARYA*
Na
©®Rahma Kabir MrsMG.
Wattpad @rahmakabir
Page 24.
Madina tana isa sashin su Hajiya ta faɗa ciki ko sallama babu, wanda kukanta shine abun da ya fara yin iso garesu, daga Alhaji har Hajiya a cikin tashin hankali suke miƙe tsaye suna kallonta dan duk suna zaune cikin falon kuma zatonsu ya basu ko Hamid ne rai yayi halinsa, tunda ga bigiren da suke ciki na rashin lafiya, Alhaji yayi ƙarfin hali yace mata.
‘Yata kukan me kike yi haka? wani abun ne ya ƙara samun Abdulhamid?
Madina ta seta kukan tana share hawaye tare da koro musu bayanin wai ya hanata zuwa aiki akan sai ta riƙe masa yara saboda Sakina ta bar gidansa ba a san inda ta nufa ba, ba Alhaji ba hatta Hajiya sai ta taji mugun takaicin Madina yadda ta tayar musu da hankali sosai, Alhaji bai iya ƙara magana ba ya yi hanyar fita Madina ta rufa masa baya tare da Hajiya, duk da bata jin ƙarfin jikinta amma dole ta bisu taji kanun labari. Koda suka isa falon sun tadda Hamid yana cin abinci tare da yara suna kallo, baiyi mamakin ganin iyayensa tare da Madina ba dan yasan tunda ta fita to can tayi, yanzu ne ya ƙara tabbatar da Madina sargartacciya ce ga rashin wayo da rashin hankali gabaɗaya ba tada lisaafi, balle ta riƙa yiwa kanta tunanin abunda yake daidai, bai iya yiwa su Abba magana ba suma basu yi masa ba duk suka samu guri suka zauna suna kallonsa, har sai da ya kammala cin abincinsa ya miƙe ya kai plate kitchen ya wanke hannu ya dawo yasha ruwa kafin ya cewa su Mufeeda su shiga ɗaki su jirashi, tace to tare da jan ƙannenta suka shiga ɗakinta a sannan ne Abba ya soma magana.
Madina taje mana da maganar kace ba zata je aiki ba zata riƙe maka yara saboda Sakina ta bar gidanka, to ni bazan tambayeka meya faru da ya saka Sakina ta bar gidanka ba, sai dai ina so ka sani wajibi ne ka cikawa yarinyar nan alƙawarin da kasa muka ɗauka a lokacin da muka je niman aurenta, na lallai dole zata yi aiki kuma muka amince, Madina ba zata zauna dan riƙe maka yara ba kasan yadda zaka yi dasu.
Abba ai har motar da ya ce zai bani yace ya fasa ba zai bayar ba.
Cewar Madina tana turo baki, Alhaji ya dube ta yana cewa.
Ban san lokacin da ya yi miki wannan alƙawarin ba, dan haka bazan iya cewa komai akai ba idan ya ga dama ya baki in bai gadama ba ya riƙe wannan tsakaninku ne. Hajiya tashi mu koma gida.
Ya ƙare maganar yana dubanta, Hajiya cike da damuwa tace.
Ka bari yayi mana bayanin abinda ya haɗasu da Sakina ta tafi tabar yaranta, kasan dai a wannan gaɓar Madina ce ta dace ta riƙe masa su tunda ko ni ba ni da ƙarfin riƙe su, meye amfanin yin mata biyun? yanzu koda ace Sakina tafiya tayi ko taje wani sha’ani Madina ba zata kula masa da yara ba, ai wannan ba magana bace tunda tasan mai mata da yara ta aura, dolenta ne ta saka a ranta zata yi hidimarsu.
Ni bazan saurari maganar matsalarsa da Sakina ba domin na daɗe ina ja masa kunne akan karya ƙure fushinta, na tabbatar tunda ta iya tafiya tabar yaranta to ya kaita bango ne, sannan kina maganar Madina ta kula masa da yara kinga tana da natsuwa da hankalin da zata iya riƙe su? Ita kanta bata gama riƙe kanta ba balle ta kula da wani, ko so kike ta riƙa dafa musu abincin da kullun sai sun ziyarci asibiti, dan haka duk tsuntsun daya ja ruwa shi ruwa kan duka kuma duk wanda ya siya rariya yasan zata zubda ruwa, tun lokacin da akace mini ‘yar mace ce nace ya haƙura domin ba lallai a sameta da tarbiyyar da muke tunani ba fiye ga wacce namiji ya zama jagorarta ba, amma me yace? cewa yayi yarinyar tana da ilimin zamani dana addini mahaifiyarta ta kula da tarbiyyarta sosai, ba yi da tantama akan ta zai samu farin cikin da yake buƙata. Gashi yau kwananta tara a gidan abubuwa da dama sun faru wanda tuni na gano wannan tafiyar cike yake da Gargada, Allah ya sauwaƙe, ki tashi mu tafi gida shi da ya kwanto kura yasan yadda zai yi da ita ai.
Abba ya faɗa cike da ɓacin rai ya juya ya soma fafiya, Hajiya ma kasa magana tayi dan duk bayanin Alhaji gaskiya ce zuwa yanzu bata hango Hamid zai cigaba da samun farin ciki in dai a gurin Madina ce, sam bata yiwa yarinyar kallon mai hankali balle tarbiyya, sun riga da sun tafka kuskure, Sakinar da suke ganin ita mara mutunci ce ashe gwara ita sau dubu da Madina, haka suka fice a falon ba um ba um-um, Hamid ya dafe kansa duka biyu yana jin wani abu yana hajijiya da shi, tabbas yayi zaɓen tumun dare dan ya tabbatar da maganganun Abba a bisa gaskiya suke, gashi ba aje ko ina ba ya fara gane kurensa, Madina miƙewa tayi tana ya mutse fuska.
Duk yadda zaka ɗaukeni da kai da iyayenka to ku ɗauka ɗin, ni ban taso na saba da wahala ba, a kullun rayuwar farin ciki nake ciki wanda Mahaifiyata ke bani, dan haka irinsa nayi mafarkin samu a gidanka, sai dai ashe ni nayi kuskure bansan haka halinka yake ba da tun farko wlh bazan taɓa aurenka ba, yaudarata kayi da tarin soyayya da nuna mini gidanka ne aljannar farin cikina, ina da masoya waɗanda samari ne ba su da mata amma saboda kaifin harshenka da yaja linzamin soyayyarka a zuciyata, nace dole sai kai, dan haka wajibi ne ka shayar dani wannan Aljannar duniyar da ka riƙa hasko mini, dan zama ni da kai mutu ka raba, ba zaka lasa mini zuma a baki ba kace ka daina ba wlh, dan baka isa ka mayar dani ƙaramar bazawara ba ka gama tatse albarkatun jikina ba ehe Alhaji Hamid.
Madina ta faɗa tana tafa hannunta cike da tsiwa kana ta wuce zuwa ɗakinta ko a jikinta, Hamid sauke Hannunsa yayi ya juya bita da kallo harta shige ɗaki, wani irin yanayi yaji a zuciyarsa na ƙunci wanda bai san ya zai misalta shi ba, yana so ya gano meya aikata ne haka da Allah ya jarabce shi da auren Madina wacce ta zame masa ƙadangaren bakin tulu, haka yaji yana niman inda zai fitar da magana ko yayi kuka, wata ƙila ya samu sassaucin ƙuncin da yake ji a zuciyarsa da bai taɓa jin irinsa ba, innalillahi wa inna ilaihir raji’un! ya soma ambata a ransa, ya buɗe baki yana cewa.
Allah na tuba ka yafe mini ban san ko akwai abinda na aikata na kuskure ba da ƙaddara mini auren yarinyar nan ba, ni dai nasan nayi shi ne domin samuwar farin ciki, sai dai ba aje ko ina ba ka fara jarabtata da zazzaafar sakamako wanda ban san me na aikata ba.
Ya ƙare maganar cikin fitar hawaye guda ɗaya mai zafi daga idonsa na dama, sauke ajiyar zuciya yayi ya miƙe ya wuce ɗakinsa ya kwanta, haka ya dinga saƙa da warwara akan meya aikata ne daya cancanci wannan hukuncin, har barci ya kamashi bai hango komai daya yi mara kyau ba, dan ko daya nima auren Madina bai taɓa kama hannunta da sunan suyi wata masha’a ba, duk so da Sha’awarta da yake fuzgarta basu taɓa yin wani kuskure da shaiɗan ya jasu suyi ba, hasalima Madina kunyarsa take ji shi kuma bai taɓa tunanin yayi mata wani abu ba har sai da suka yi aure ya samu damar sauke duk wani kwaɗayinsa akanta.
*****
Sakina.
Koda suka isa tasha, motar Kano ta nima wato drop dan bata so ta takura kuma bata so dare yayi mata a hanya, nan aka samo mata wata mota sharon ta shiga ta biya kuɗi mai yawa kamar yadda driver ya yanka mata, haka ta zauna mazaunin tsakiya da kayanta a gefe ba ɓata lokaci suka kama hanya, sai dai suna wuce unguwar Rigachikun ta kashe wayarta gabaɗaya ta mayar a jaka ta lumshe ido tana jin kamar ta koma saboda yaranta, amma in ta tuno da wulaƙancin Hamid sai taji gwara tayi nesa da shi ko hakan zai zama silar samun ‘yancinta, shiyasa bata yi tunanin zuwa ko ina ba sai Kano gidan anty Jalila wacce tasan zata tsaya mata sosai fiye da ‘yan uwanta na jini. Yaya Jalila tana da zafi da faɗa sosai bata ɗaukar raini shiyasa a dangi kowa yake shakkar abu ya haɗasu, dan zata wanke mutum daga biri har wutsiya, kuma ba a gulma ko munafurci da ita, irin macen nan ne da ake tsage gaskiya da gaskiya, tasan in har taje mata da matsalarta zata yarda ta zauna a gurinta domin ta huta tare da wasu shawarwari da zata samu. Haka ta riƙa shakar iskar hanya tana jin wani sanyi yana ratsa jikinta wanda take nan taji kamar zazzaɓi take ji, hakan yasa ta ɗaga glass ɗin gefenta ta cigaba da kallon hanya, tun gari na da haske har duhu ya rufe sai hasken fitulun motoci da suke karakaina a hanya. Awa biyu da rabi ya kaisu cikin garin Kano saboda ba tsaye tsaye a hanya danma ana ta gyaran hanya da ƙila tun akwa biyu sun isa, direct gidan driver ya wuce da ita tana yi masa kwatance har suka isa, ta sauka da kayanta ta yi masa godiya dan tun kafin su tawo ta sallameshi shima godiya yayi mata ya juta mota ya wuce, ita kuma ta ƙarasa gate ɗin gidan ta buga, mai gadi ya buɗe, ganin baƙuwa ce ga kaya ya buɗe mata da sauri tare da amsar akwatin ta shiga ya bita da kaya a baya, ta kama hannun ƙofa ta tura da sallama, da sauri anty Jalila ta juyo dan ta bawa ƙofa baya tana zaune a kujera, ganin Sakina ce yasa ta miƙe tana salati.
Sakina dama nan kika tawo? duk kin tashi hankalinmu, yanzu na gama waya da yaya Ali yana tambayar ko nan kika zo? nace masa a’a ashe kina hanya, aiko bari na kirasu yanzu na shaida musu dan hankalinsu ya kwanta.
Dan Allah yaya karki kira kowa bana son susan ina nan tukuna.
Sakina tayi maganar tana ƙarasawa gaban Jalila da sauri ta amshe wayar data fara dannawa, ido Jalila ta bita dashi kamar mai karantar wani abu a fuskarta, daga bisani ta sauke numfashi ta huya gurin kayan da mai gadi ya aje ta jasu zuwa ɗakinta tana cewa.
Muje kiyi wanka kiyi sallama kici abinci sai muyi magana.
Ba musu Sakina tabi bayanta zuwa ɗakinta, ita Jalila da kanta ta haɗa mata ruwan wanka Sakina ta shiga tayi tare da alwala ta fito, Jalila ta miƙa mata wata doguwar riga mara nauyi kamar ta barci.
Ki saka wannan dan tsayawa buɗe akwati ki ciro kaya zai ɓata lokaci.
Sakina ta amsa kana ta shirya ta gabatar da sallar magrib da Isha’i tare da shafa’i da wuturi, data idar sai ga Jalila ta shigo da tire cike da abinci, tuwon shinkafa miyar zogale tare da kunun aya sai soyayyar naman rago da aka baɗeshi da yaji kamar suyar salla kona mai jogo, ta dire mata tire a gabanta.
Ki ci ki koshi ki aje duk wata damuwa karki hukunta kanki da yunwa.
Sakina bata ce komai ba tabi unarninta, saboda itama yunwar take ji dan rabonta da abinci tunna rana, kuma shima ba cin kirki ta yi ba saboda zullumin abinda zata aika ya cika mata zuciya, ba laifi taci tuwon dan ta cinye malmale ɗaya, ta kora da ruwan kunun aya, daga bisani ta miƙe da zummar kai kayan kitchen, Jalila ta kallera tana cewa.
Ke zauna ba zan saka ki aiki ba kin shawo gajiyar hanya, kuma naga baki ci naman ba, to wlh ki sani sai kin cinye wannan dana zuba miki kafin kiyi barci, dan yajin gyaran mutuncinki na saka a ciki, saboda ki fara tayar da komaɗa tun yau kafin ki koma.
Kai yaya ni wani gyara zanyi bayan auren ma ya isheni gabaɗaya.
Kin ma isa, ai wlh aurenki da Hamid na zobe ne babu rabuwa, sai da ya gama kwashe albakatunki kika zuba masa yara huɗu sannan yace ya gaji dake, aiko bai isa ba zama daram idan ma dan aure ya ƙara yake niman wulaƙanta ki to sai ya ji a jikinta, dan ba zaki koma ba sai na tabbatar da duk wani martabarki ya dawo, saboda Umma ta sanar sani abinda mijinki ya faɗa mata cewar yace kije gida ke kuma kika yi ɓatan dabo.
Wannan karan dariya Sakina ta saki dajin maganganunta, itama Jalilar dariya tayi tana cewa.
Ai kin kyauta da kika zo nan baki ƙara gaba ba, yanzu zauna ki fayyace mini labarin zaman aurenki tun daga farko, bance ki ɓoye komai ba wanda ya dace ace kin sanar dani, in ba haka ba yanzu zan kira su Hamza nace gaki a gidana su zo su ɗauke ki.
Murmushi Sakina tayi tana zama a dadduma ta jingina da bango, sai ta soma bata labarin duk wata matsala da ta tsaya mata a zuciyarta da Hamid, har sai da ta kawo zuwa abubuwan da suka faru na auren daya ƙara dama matsalar daya faru jiya, murmushi Jalila tayi tana duban Sakina.
Duk abinda Hamid yayi miki wlh kema kina da laifi dumu dumu a ciki.
Laifina kuma anty? Ni da kullun nake burin kyautata masa, ko dai baki gane maganar da nayi miki ba ne.
Na gane maganarki, idan Hamid yana da matsala kema kina da matsala Sakina, mijinki ga dukiya ka kyau ka ƙuriciya, me kike zaton zai buƙata ya samu a gurin matarsa? Zai buƙaci matarsa ta zama ‘yar kwalisa tamkar yadda yake, wannan yasa shi har ya hangi Madina ‘yar boko ya aurenta dan zatonsa a gurinta ne kaɗai zai samu abinda yake so.
Yaya ina iya ƙoƙari na fa, kuma komai nayi baya yaba mini sai ya kushe, abinci na ne kaɗai Hamid zai ci ya yaba mini.
Jalila ta shiga duban Sakina tana jin kamar ta rufeta da duka dan takaici tace.
To saboda kin zauna kanki da murfi Sakina, kin ƙunshe kanki a gida ba kya fita, ko ɗan islamiyar nan na zamani ba kya zuwa balle ki ƙaro ilimin addini dana zamantakewa, na san ba zai taɓa haka ki niman ilimi ba, amma kin mayar da kanki kamar tsohuwa, taya duk iskancin daya ɗauko ba zai yaɓa miki ba, rashin boka hauka ne ko shine rashin wayewa? Ki kalle ni da kyau ni nayi makarantar boko ne? Kin hango rashin wayewa ko duhun kai a tare dani, ina ce kune kuka samu yin primary. Kina zauna a cikin garin Kaduna amma sai kace wacce take aure a daji haba Sakina haba, mijinki yana da arzikin da baki rasa komai ba, amma kin kasa jawo shi jikinki ki nuna masa kulawa, ki goge ki zama ‘yar zamani ya gagara, dududu shekarunki nawa.
Ta ƙare maganar tana kallonta fuska a haɗe.
[7/30, 5:03 PM] Rahma Kabir: *ƘAZAMAR AMARYA*
Na
©®Rahma Kabir MrsMG.
Wattpad @rahmakabir
Page 25.
Anty Jalila ta gyara zama ta ɗaura da cewa.
Sakina kin taɓa zama kin fahimci me Hamid yake so a tare dake menene in kika yi yake kushewa ki gyara, yafi son kina saka ƙananun kaya ko kayanmu na Hausawa? Yafi son kiyi kitso ko yaga kin gyara sumarki kin tufke? kina zuwa salun gyaran kai duk bayan wasu lokaci? yafi son Jan ƙunshi ko kiyi zanen baƙi? wasu kalar kayan barci yafi so ko in kika saka yake yabawa? Me kika fahimci yake so a jikinki da zaki jawo ra’ayinsa gareki dasu? menene in kika taɓa masa a jikinsa kike kunna masa sha’awarsa?.
Jalila taja fasali tana duban Sakina da tayi shuru kamar ruwa ya cinyeta, da taga ba tada alamar yin magana ta ɗaura da cewa.
Lokacin da kika je ɗakinsa kika tadda yana waya da budurwarsa, me ya kamata kiyi masa domin aika masa da saƙo ba tare da kin yi magana ba? har ki jawo ra’ayinsa gareki ya watsar da wayar da yake yi, Sakina taya bazai koreki ba kin je kin ce masa kin so ku kwanta abu gwanin takaici, dama ai in ya ganki a ɗakinsa barcin kika zo, wataƙila baki yi shigar da zaki ɗauki hankalinsa ba. To wai ma ya batun gyaran breast ɗinki ko kin barsu haka kamar silifas balle ya riƙa ganin tudunsu yayi sha’awarsu. Bari kiji wlh zuciyar namiji tana da saurin karaya muddin aka ce Mace tasan kanta musamman a sha’anin gurin saduwa, komai fushinsa da faɗarsa matsawar kin san hanyar da zaki aika masa da saƙo dolensa zai ya sauko ya zama raƙumi da akala, amma sam sam ba kida sigar kalami, ba shagwaɓa ba karairaya, ƙila ba kya gyaran da zai riƙa manne miki saboda ba kida ɗanɗano, ta yaya bazai ce ya yiwa Amarya gyara ba, to ke ko yayi gyaran akanki ba lallai ya samu yadda yake so ba, shi da yake mafaɗaci ne ba yida rufa rufa ƙiri ƙiri yake fito miki da matsalolinki, amma da yake ke kidahuma ce sam baki hango haka ba sai kike alaƙanta haka da ya daina sonki baya ƙaunarki. Wataƙila tsaftar da yake fadar ba kida ita yana nufin tsaftar HQ, hammata, sumarki da bakinki yake nufi bai fito fili ya faɗa miki bane, ya jima yana miki ƙorafi in da ace kin gyara wataƙila ko auren ba zai ƙara ba, amma sam tunaninki kawai ya baki ya daina sonki ne ko.
Sakina hawaye taji yana zuba a kuncinta jikinta yayi mugun sanyi da zantukan Anty Jalila, dan tabbas maganganunta sun zaburar da ita da hasko mata abinda bata taɓa kawo tunaninsu cikin kanta ba, tasan tana wanka ta shafa mai ko kwalliya ta daina yi saboda yana kushewa, ta san tana askin private part ɗinta da hammata amma bata damu da gyaran HQ ba, brush kuma in tayi na safe bata ƙara yin wani, kitso kuwa duk bayan wata ɗaya take yin sabo, ita bata zuwa saloon wanke kai sai dai a gida take wankewa tunda yana siyo musu shampo, sannan ko wankan saduwa tayi haka kan zaita tsami har ya bushe, kuma sai yayi wannan watan kafin zata kwance ta wanke, da yake bata saka relaxa haka yake cukus a cure. Jalila kallonta take yi tana murmushi dan ta tabbatar da lamarin Sakina akwai gyara.
Ban ce miki komai ba tukuna, har sai na fito miki da sauran matsalarki a faifai har zuwa na wulaƙancin da Hamid yake yi miki, ki tashi ki kwanta nima zanje sashin Alhaji na kwanta duk da baya nan amma bana so na takura ki, mu kwana lafiya.
Nagode Anty Jalila, ko a iya bayaninki ɗin nan kin hasko mini abubuwan da ban hangowa kaina ba, Allah yasa kaimu gobe lafiya.
Cewar Sakina tana miƙewa ta naɗe daddumar ta mayar inda yake ta cire hijab ta ninke, sai ta ɗauki kwanon naman ta zauna gefen gado ta soma ci tare da jin wani kwanciyar hankali a ranta, tabbas in har tana da matsala dole ne ta tsaya ta gyara kafin ta komawa Hamid a sabuwar Sakina, Jalila ta ɗauki tiren abincin ta aje mata sauran kunun ayar da ruwa a gefe ta fice.
****
Kaduna.
Washe gari Hamid ya wayi gari cikin wani irin yanayi na damuwa, tunda ya dawo sallar asubahi bai iya komawa barci ba, har wajen misalin ƙarfe takwas na safe da kyar ya miƙe ya samu yayi wanka ya shirya cikin manyan kaya shadda, ya fito falo ya samu yaran sunyi jugum jugum kamar basu da lafiya ko tv basu kunna ba, tausayinsu ne ya shiga bin garkuwar jikinsa ya ƙarasa ya zauna yana miƙawa Rauda hannu cike da murmushin yaƙe a fuskar, taje ya ɗauke ta, a lokacin ne duk yaran suka gaishe shi ya amsa yana cewa.
Mufeeda kije ki haɗawa su Baba ƙarami ruwan wanka suyi, sannan kema kiyi tare da Rauda ku shirya zamu je wani guri yanzu.
To tace masa sai taje ta amsa Rauda suka wuce ɗakin su Yakub sai da ta haɗa musu ruwan wanka tace Yaƙub ya cuɗa baba ƙarami in sun gama su saka kaya masu kyau, daga haka ta fito ta shiga ɗakinta ta haɗa musu ruwan wanka, sai da ta fara yiwa Rauda kafin ta fito da ita sannan ta koma tayi nata, Mufeeda yarinyar akwai kaifin hankali dan duk yadda Mamansu take yi musu ta sani dan haka shirya Rauda bai bata wuya ba dan har parmpers ta saka mata, suka shirya cikin shadda doguwar riga su Yaƙub kuma wani yadi suka saka suka fito Hamid yana cewa.
Yauwa yaran Abba, kun saka turare ko?
Gyaɗa masa kai suka yi suna cewa eh sai yace su wuce suje su karya su dawo, a lokacin ne Madina ta fito cikin shirin fita aiki dan tun ɗazu ogansu ke kiranta akan ta fito da wuri saboda akwai program ɗin da zata yi ƙarfe tara kuma live ne shirin, ta dakatar da Hamid da cewa.
Barka da safiya Beb.
Tace fuskarta cike da murmushi tamkar wani abu bai faru ba jiya, Hamid juyowa yayi bai ce mata komai ba saboda yanayin shigar ta ya tabbatar da aiki zata, ta ƙaraso har gabansa ta rungume shi kana ta yi masa kiss a goshi, su Mufeeda suna ganin haka suka fice gabaɗaya a falon, Madina tace tana murmushi.
Farin masoyi wai har yanzu fushi kake yi dani ne? Shiyasa fa jiya na baka damar ka huce ban zo ɗakinka ba, ni dai dan Allah kayi haƙuri komai ya wuce, yanzu zanje aiki ana jirana ka bani key motata na tafi da ita tare da kuɗin breakfast ɗina dana lunch. Da dare kuma me zan dafa mana mu ci.
Ta ƙare maganar tana tsureshi da ido, Hamid ya saki guntun murmushi yana cewa.
Ai na riga na gama magana akan zancen motarki na fasa baki ita, maganar girki kuma zaki iya dafawa kanki duk abinda kike so akwai komai a kitchen, ki sani ko a mafarki bana fatan sake cin girkinki daya nima hallakani, sannan batun breakfast da lunch shima zaki iya dafa duk abinda kike so ki tafi dashi, bazan jure kashe miki kuɗin abinci ba bayan na wadataki da kayan abinci a gidana, ga 1k kuɗin mota nasan zai isheki kije ki dawo.
Ya ƙare maganar yana zaro dubu ɗaya ya aje mata akan center table ya juya zai wuce, Madina da bata iya riƙe hawaye nan da nan ta soma zubar dasu tana cewa cikin raunin murya.
Beb karka hukuntani da laifin da bani na aikata maka ba, barin Sakina gidan nan ban da masaniya bai kamata fushinta ya shafeni ba, ni duk abinda ya faru jiya iya gaskiyata na faɗa, bazan amsa maka zanyi abinda nasan bazan iya ba. Dan Allah ka kula dani da soyayyarka kamar yadda ka ɗaukar mini alkawari kafin muyi aure.
Hmmm yace yana girgiza kai ya fice abinsa ko waigota bai yi ba, Madina zama tayi a cushing ta rufe fuskarta da tafin hannunta tana kuka, bata taɓa zaton Hamid zai iya juya mata baya ba har haka, tasan yana sonta amma kuma yana bata wuyar sarrafashi, kiran da ya shigo wayarta yasa ta saita kanta ta ɗauko wayar a cikin jaka taga daga gurin aiki ne, yatsine fuska tayi taji duk bata da wani kuzarin fita amma dole ta miƙe ta gyara gyalenta ta fice, ita da tayi aure tana ganin ta taka wani matsayi zata hau motar kanta ba ruwanta da napep amma ashe Hamid romon baka kawai yayi mata, ji tayi auren ya fara sire mata tun ba a je ko ina ba ya fara nuna mata halinsu na maza, ita kam data san haka zai yi mata da bata aure shi ba. Koda ta isa ta sallami mai napep kafin ta shiga ciki ta aro farin ciki ta yaɓa a fuskarta ta shiga tana fara’ar dole ga yunwa tana ji, amma ta bari in gun gama program ɗinsu zata je wajen cin abincin office ɗin nasu na karya.
Hamid rastuarant suka je da yaran suka karya da lafiyayyen abinci, daga bisani ya kaisu super market suka ɗiba abubuwan da suke so kana suka dawo gida, yace su jirashi yana zuwa, sashin su Hajiya ya leƙa ya samu duk suna falo ya gaida su suka amsa, daga bisani ya cigaba da matsa yatsunsa yana sonyin magana yana shakkar Abba, Hajiya ce ta kauda shurun da cewa.
Ya ƙarfin jikin naka?
Da sauƙi Alhamdulillahi.
Masha Allah ya kwanan yaran da fatan babu wata matsala.?
Lafiya lau suke, amm dama nace bai dace a bar su a gida su kaɗai ba shine nace zan haɗosu da kayansu sai su cigaba da zama anan har zuwa sadda Sakina zata dawo, saboda gidan ba kowa Madina ta tafi aiki nima zan fita nawa aikin.
Hamid kace zaka kawo su nan? Haka kurum su nima ƙarasani da hayaniya, har yanzu bana jin daɗin jikina ga yawan ciwon kai, ni bazan iya da hayaniyarsu ba wlh, ranar Asabar da suka zo kamar zan yi hauka saboda surutun da suka dinga sakani, dan haka ka barsu acan ai Madina ba daɗewa zata yi ba, ko dama tana kaiwa yamma a gurin aikin ne.?
Haba Hajiya ai saiki shiga ɗaki ki basu guri nan falo suyi wasansu.
Cewar Alhaji, Hamid ma ya ƙara da cewa.
Kiyu haƙuri In Sha Allah zan ja musu kunne, ita Mufeeda da Rauda su zauna ɗakin Jidda, Yaƙub da baba ƙarami su zauna a ɗakin kusa dana Jidda.
Hamid wlh bazan iya ba Jidda ma ba lafiya ce da ita ba balle ta jure ɗawainiyarsu, riƙon yaran nan dole sai mahaifiyarsu, kaje ka nimota duk inda take ta dawo ta riƙe yaranta. Itama da yake ta sakawa zuciyarta baƙin kishi ta kama hanya ta tafi, ai kome ake yi mata ta zauna kodan ‘ya’yanta, ta tafka rashin hankali wlh..
Abba kasa baki Hajiya ta yarda ta zauna da yaran nan, na tabbatar Sakina ba zata ɗauki lokaci ba zata dawo kuma kaga inna barsu a gida Madina bata zama sannan bazan taɓa yarda ta yi musu abinci suci ba.
Hamid wannan matsalar nake ta maka hange amma baka ji ba, Sakina yarinya ce mai haƙuri amma sai da kayi yadda ka tunzurata tabar maka gidanka, ya kamata ace kana raga mata kodan yaranku amma idonka ya rufe, dan haka gashi ba aje ko ina ba kasan matsayarka, Madinar da kafi so kake wulaƙanta Sakina akanta ta nuna maka ƙiri ƙiri ba zata riƙe maka yara ba, ga mahaifiyarka da tafi kowa nuna tafi sonka itama tace ba zata riƙe ba, dan haka wannan ya zama babban darasi a gareka, ni bazan tsaya ɓata bakin tambayar meya haɗaku ba domin nasan laifin naka ne, shawara ɗaya ka ɗiba yaran nan ka kaisu gidan yayarta Umma ina ganin nan ne kaɗai mafitarka, kuma za a riƙe maka su da amana, iya abinda zan iya ce maka kenan.
Abba yana gama faɗar haka ya miƙe ya fice daga falon gabaɗaya, Hamid sadda kansa yayi ƙasa yana jin kamar ya fasa kuka, idan Madina tayi masa haka ita nata kishi ne, amma ita Hajiya me yayi mata ace yaransa ba zata amshe su ba, sai dai in tsanar Sakinar ne ya shafesu, yana matuƙar kyautata mata ko dan wannan yaci ace ta taya shi kula dasu, maganar Hajiyar ne ya katse masa tunani.
Nifa bana ce bazan riƙe yaranka bane kana sane da jiyan nan aka sallamomu har yanzu ban dawo cikin hayyacina ba, bazai yuwu ina lallaɓa lafiyata ba ka kawo su su ƙara mini wani damuwar, kamar yadda Alhaji ya faɗa ka kaisu gidan Umma tunda sunyi hutu, alabarshi ko sati ɗaya suka yi sai ka dawo dasu nan, nasan lokacin na samu lafiya sosai, ko kuma ƙila Sakinar ta dawo magana ta ƙare.
Shikenan bari na kaisu can ɗin.
Yauwa ka kuma daina damuwa kana ɗagawa kanka hankali, Sakina ba yarinya bace duk inda taje ma zata dawo, idan kuma auren ne ta gaji dashi ita ta sani Allah ya gani kana yi mata uzuri, dan da wani ne take yiwa wannan rashin kirki da tuni ya sauwaƙe mata, kishi ne dai ta azawa zuciyarta na babu gaira babu dalili. Batun abinci ka riƙa zuwa nan kana ci dan wlh ban yarda ko ruwan tea Madina ta dafa maka kasha ba, saboda yarinyar nan ina ganin kanta ba dai dai yake ba, ace a gabanmu ta banka mana tusa ta fice kuma ko kunyar hakan ban gani ba a tare da ita da ta dawo da mahaifiyarta ba, karin takaicina ji yadda ta diro mana falo jiya tana tsala kuka kamar anyi mata mutuwa, kai amma wannan yarinya sam gidansu ba bu mafaɗi irin sangartattun yaran nan ne da uwa ba kwaɓa kaka ba tsanani, kai dai Hamid Allah ya jarabce da mata sai a hankali duk baka yi dace ba.
Haka Allah ya ƙaddara mini Allah yasa naci jarabawan.
Ya faɗa yana cire hularsa tare da shafa kansa zuwa fuska, ya mayar da hular ya miƙe Hajiya tana cewa.
Ka samu ka kai yaran ka dawo ka ƙara hutawa dan kaima naga jikin naka ba ƙarfi sosai, ka haƙura da aikin zuwa gobe ko jibi In Allah ya kaimu sai ka fita.
Dama company kawai zan leƙa naga abinda ke faruwa na dawo.
To a dawo lafiya.
Ta faɗa, ya amsa da Amin ya wuce jiki ba kwari.
[8/2, 5:02 PM] Rahma Kabir: *ƘAZAMAR AMARYA*
Na
©®Rahma Kabir MrsMG.
Wattpad @rahmakabir
Page 26.
Hamid koda ya shiga falo cewa Mufeeda yayi suje su shirya kayansu zasu je hutu gidan yaya umma, cikin tsananin farin ciki suka shiga murna da tsalle, haka suka fara shiga ɗakin Mufeeda ya taya ta haɗa kaya a jaka nata dana Rauda, bayan sun gama suka koma ɗakin su Yaƙub suma ya haɗa musu nasu, ya sa suka kai mota, ya kwashe kwai ɗaya gani ɗakin Sakina kired huɗu, ya ɗiba musu kayan tea ya haɗa dai kayan abinci da yawa dan bai dace ya kai musu ɗawainiya ba tunda yasan halin rayuwar da suka ciki, duk suka zuba komai a motarsu na fita anguwa, daga bisani suka fito suka shiga Hamid ya bawa driver dubu Hamsin akan in ya je ya bawa Umma, ya amsa yace to kana ya jasu zuwa gidan Umma. Koda suka isa gidan da gudu yaran suka shiga domin tunaninsu zasu samu mamansu a ciki, cikin fara’a yaya Umma ta tarbesu.
Sannunku da zuwa mutanen gomna road, kuna ta waige waige to ummanku bata nan ku shiga ɗaki ku aje kayan.
Mufeeda da murmushi a fuskarta ta gaisheta, ta amsa fuska sake tare da danne damuwar da take ciki, su Yaƙub ma suka gaisheta nan driver yayi sallama ya gaisheta ya aje kaya yana komawa ya ɗauko, har dai ya gama shigo dasu, sai ya bata kuɗin da Hamid yace a bata ta amsa tana yi masa godiya kana ya wuce, ɗaki ta shiga dasu tasa yaranta suka kwashe kayan zuwa ɗaki, ta zauna tana jansu da hira tare da kwantar musu da hankali da cewa mamansu taje ƙauyensu biki ne zata dawo, dan abinda tayi tunanin faɗa musu kenan dan su samu kwanciyar hankali.
…
Can bayan sallar La’asar Umma ta kira Hamid a waya bayan sun gaisa sai take ce masa.
Ɗazu sai naga yara driver yazo dasu.
Eh wlh nan ɗin ne naga yafi dacewa su zo na tabbatar zasu fi samun kulawa, sannan Hajiyata har yanzu jikin nata sai a hankali shiyasa nace bari su zo nan gurinki bayan kwana biyu sai su dawo in Hajiya ta warware.
To Allah ya taya ni riƙo, ya labarin Sakina har yanzu dai ba amo ba labari.
Wlh duk inda ya kamata na bincika nayi amma ba labarinta, Ins Sha Allah zata dawo nasan fushi tayi dani.
To Allah yasa, muma nan mun bincika ‘yan uwa duk bata je gunsu ba hatta yaya Jalila ta Kano mun yi waya da ita ɗazun tace bata je can ba, haka ma maiduguri sunce bata je ba.
To Allah ya bayyanata.
Ya faɗa cikin sanyin murya, Amin tace masa kana suka yi sallama.
*****
Sakina.
Suna zaune farfajiyar gidan cikin baranda, Anty Jalila tana lissafin kuɗin kaya da aka aiko mata da shi daga shagonta, ‘yarta Ra’isa ce ta leƙo daga falo tana cewa.
Umma na sauke shinkafar miyar ganyen za ayi ko stew.?
Kiyi mana stew tunda jiya miyar zogale muka yi, amma kisa albasa sosai.
To tace mata kana Ra’isa ta koma ciki ita kuma ta aje kuɗin a cikin jaka ta mayar da hankalinta gurin Sakina tana cewa.
Sakina anya bazan sanar dasu umma kin zo gidana ba, dan naga hankula sun tashi sosai, bana son faɗar baba malam dan nasan sai yayi faɗar ɓoyeki dana yi.
Dan girman Allah ki rufa mini asiri karki sanar dasu, dan na tabbatar in suka san ina nan to ba zan sake kwana ba zasu biyo hanya su tafi dani, kuma nasan gidan Hamid zasu wuce dani babu mai saurarata yaji damuwata, haƙurin da suke bani kullun shi zasu ce nayi.
Hmmm ai abinda ke cutar da mu kenan, iyaye ko yayyi suyita nuna suna tsoron saki bayan sakin nan halal ne in har ya zama da cutarwa gwara a rabu, abun takaici ba za a saurari wace matsala yarinya ke fuskanta ba, sai dai aita bata haƙuri ace ta zauna ko dan ‘ya’ya bayan ita kaɗai tasan me take fuskanta na cutarwa a gidanta, Allah dai ya sauwaƙe.
Ameen, shiyasa na tawo nan dan in huta wlh, dan na tabbatar in gida na tafi korani zasu yi suce na koma, kuma mazan yanzu ba irin mazan da bane da suke da dattako, na tabbatar in na koma wani wulaƙanci zan fuskanta daya fi na baya.
Wai ke Sakina taya kika yi sake har Hamid ke zabga miki mari baki ɗauki mataki ba, na farko kin nuna kina mugun tsoronsa kuma bai dace haka ba, mace an fi so ta kasance tana shakkar ɓacin ran mijinta ba wai tsoronsa ba, kina kafa kafa da duk abinda zai kawo muku saɓani musamman in kin san halinsa, tsoronsa ya sanya bakya jituwa da shi, baki zama ki tattauna matsalarki ko damuwarki akan sa, ba kya hira dashi dan ku ƙara fahimtar junanku da sanin ina makomar zamanku ya dosa. Auren soyayya kika yi da shi tun ƙuriciya ya kamata ace kinfi kowa sanin waye shi da kuma kyakkyawar mu’amala, Sakina ba kida wani abokin hira ko shawara daya wuce mijinki, kuyi wasa da dariya ku yi barkwanci ku zaulayi juna saboda ba kida wani namiji da zaki yi haka da shi, to amma kina tsoronsa taya zamanku zai yi miki daɗi?kuma ba zaki taɓa fahimtar ina ya dosa ba haka shima ba zai fahimceki ba, wannan tsoron da yake gani a tare dake ya sanya yake yi miki duk wulaƙancin daya ga dama. Sannan yana da iyaye akwai abinda ke kaɗai ba zaki iya magance sa ba dole sai manya sun shiga, ko kin faɗawa umma haƙuri zata baki, amma in kika sanar da mahaifinsa na tabbatar zai tsawatar masa kuma dole zai rage yi miki wani abu saboda kince yana shakkarsa, musamman marin nan yafi tsaya mini a rai da kin kai ƙararsa ga mahaifinsa na tabbatar bazai sake kamanta marinki ba, in kuma kika fahimci haka yake fusatacce to da zarar ya fara masifa bashi waje ki wuce ki barshi a tsaye ki shiga ɗaki kisa key yayi ta bambaminshi, na tabbatar wlh sai yaji mugun haushi, kinga kin nuna masa yaje yayi ta haushi shi kaɗai kuma baki ce wani abu ba sannan bai samu damar marinki ba, sai ki ɗan jaye masa da rashin magana yaga kin fita lamarinsa, da kanshi zai nima sulhu ba wai ki riƙa tusa kanki ba wai ku shirya, ke naki kawai ki yi masa duk wani buƙatarsa da ya hau kanki, misali abincinsa ruwan wankansa da komai da yake buƙata, batun ɗakinsa zaki iya kwana a ciki amma ba um ba um um ba walwala, wlh da kanshi sai ya nima ku shirya ko ya fara tambayarki meke damunki, a wannan lokacin kike da damar da zaki fito da damuwarki akan abinda yayi miki faɗa akai, ko kuma ki nuna masa rashin jin daɗin yadda yake yi miki faɗa a gaban yara da dai wani ƙorafi da kike dashi akansa, daga nan zai baki haƙuri, imma bai faɗa ba zai yi miki magana masu daɗi, sannan in yaga yana miki faɗa ba kya tsayawa zai fara dainawa ko ya sameki da maganar meyasa kike niman raina shi yana magana kin barshi a tsaye, anan sai ki ce bawai raini bane kin gujewa kar fushinsa yasa ya mareki ne, ko ba kya jin daɗin faɗarsa a gaban yara harya kai ga marinki, ba kya so yaranku su riƙa yi masa wani kallo na rashin ƙima.
Sakina zaman aure da miji irin Hamid sai da dabara da iya sarrafa harshe, ni na tabbatar a cikin maganganun dana faɗa sai kin kafa masa hujjar da zaisa ya daina marinki a cikin zuciyarsa, kuma in yaga baki ce masa uffan in yana faɗa wlh zai shiga shakkarki kuma ba ko wani wulaƙanci zai yi miki ba, ki daina cutar da kanki da zancen haƙuri kina dannewa, dole kema ki riƙa nuna masa ba zaki ɗauka ba ta hanyar fita harkarsa, duk lokacin daya kawo kansa ki amayar da duk damuwarki, in kuka ne ma kiyi masa, cikin kissa ake karya zuciyar namiji irin Hamid.
Amma yaga komai yayi miki kinyi haƙuri kin sanye ya mareki ya hantareki duk kin shanye, kinyi kuka a gabansa kin kasa nuna masa kema da zuciya a ƙirjinki, taya ba zai wulaƙantaki ba, to komai zai ɗauko ya ɗora miki tunda kin zama damo sarkin haƙuri. Kuma namiji baka yin fito na fito da shi, misali yana miki faɗa kina mayar masa da magana cikin zafi, ko ya zageki ki rama kina ɗaga masa murya, to wlh a wannan lokacin har dukanki sai yayi saboda duk namiji baya ƙaunar haka, amma in ya miki kika bashi guri ko kiyi banza dashi baki ce komai ba ya ƙaraci fadarsa, daga nan ki fita lamarinsa na kwana biyu duk hawa dokin daya yi sai ya nima sulhu.
A lokacin ne Jalila taja fasali tana kallon Sakina wacce ta natsu tana saurarenta, ɗago kai tayi tana murmushi.
Anty zuwana gidanki tamkar nazo amsar maganin warakar matsalata ce, dan duk bayaninki na fahimci nima ina da matsala, musamman yadda kika zaburar dani tsoron Hamid dan tabbas ina tsoronsa, kuma wlh zafinsa yasa ni haka, amma yanzu na gano komai dan a da da ƙuriciya in yana masifa nakan biye masa muyi shiyasa ya ke marina, da hankali ya fara shiga sai kuma na soma jin tsoronsa wanda hakan yasa bana iya rama duk abinda zai yi mini, sai dai nayi shiru kona bashi haƙuri kuma bazai fasa marina ba.
Hmmm yanzu saiki gyara ki nuna masa kina da ‘yanci a cikin gidansa, naso ace ranar daya mareki a gaban su Umma suma su tanka masa, su nuna basu ji ɗadi ba, amma sai suka yi shuru kuma suka dawo suna baki haƙuri, ita umma tayi dacen miji shiyasa duk in kika faɗa mata matsalarki take baki haƙuri saboda ita bata san irin wannan matsalar ba a gidanta, sannan itama tana da ƙarancin wayewar duk da ta fiki shiga mutane.
Ai ita yaya umma yadda na fahimceta bata so ya sakeni ne, wanda kuma ko sauran yayyinmu na gida tunaninsu kenan da iyayenmu, saboda yanayin rayuwar gidanmu mun taso cikin gidan malamai, sannan tana ƙoƙarin kwantar mini da hankali tare da bani addu’o’i ina yi.
Hakan shine dai-dai ba wanda yake ƙaunar saki Sakina, amma in zama da cutarwa sai kiga daga a samu lada sai a koma samun zunubi, yana ɗaya daga cikin dalilan da mata suke kashe mazansu saboda iyaye basa shiga lamarin sai dai in yarinya takai ƙara a bata haƙuri, yanzu musamman akan rashin saduwa da namiji zai jingine mace yaki sauke haƙƙinta sai yarinya ta kai ƙara ace tayi haƙuri, wai shin ita dutse ce ba tada buƙata sai dai namiji? hakan shiya kawo yawan zina ce zina ce da matan aure suke yi, laifin mazan ne da kuma iyaye da basa tsayawa su kwatarwa mace haƙƙinta. Allah dai yasa mu dace ina ganin zuwa dare sai mu ɗaura akan maganarki dan yamma tayi ina buƙatar yin wanka na kimtsa kaina.
Yau Alhaji zai dawo ne?
Sai in zai dawo ne zanyi wanka? To bari kiji ni ina yin wanka ko wani lokaci na caɓa ado dan in burge kaina, bana wasa da kwalliya domin duk wanda ya shigo gidana ya ganni zai tabbatar da na cika uwargidan Alhaji Rashid, wannan yana ɗaya daga cikin abinda danginsu suke girmamani wlh, ni bana yin kwalliya dan miji sai ya yaba, to daya ce nayi kyau da kar yace ni dai nayi dan tsaftar kaina kuma danna burge kaina. Misali yanzu ya dawo kwatsam ya ganni dagaje dagaje zai ce dama sai in yana nan nake zama cikin tsafta, amma ya dawo ya taddani tsaf ya kike tunanin zai ji a ransa. Ina mamakin matan da zasu ce lallai miji sai yi yabe su, in yaki kuma sai su daina dama danshi kike yin kwalliyar? musamman ke da kika ce yana kushewa kin daina yi, to bari kiji maza da dama basu damu da yaban kwalliyar matansu ba amma in sunyi zasu ji daɗin ganinsu tsaf, kuma Allah kaɗai yasan ladan da mace zata samu da wannan farin ciki data saka masa a zuciya, namiji ko ya shigo da ɓacin rai yaga matarsa tsaf sai yaji wani natsuwa na musamman koda bai fito ya faɗa ba, dan haka ki jaye aƙidar ke kin daina kwalliya dan yana kushewa, ki dage damtse kiyi domin kanki in ya yaba to in bai yaba dan kanki kika yi, kuma bai ganki wata iri ba da zai riƙa raina miki.
(A comments dana gani na saurara, wata cewa tayi in tayi kwalliya miji bai yaba ba to next day inta tashi daga kauri abincin safe na rana dana dare zata haɗa taƙi yin wanka dashi zata tarbe shi, to abin tambayar anan wa kika yiwa? ina ce kanki kika yiwa dan na tabbatar a wannan daren baki isa ya kalleki da mutunci ba, balle yayi tunanin kusantarki. Sannan abin misali mata nawa ya gani a waje ya tsallake ya shigo gida, idan kin ɗauki wannan ɗabi’ar dan ki ƙunsa masa baƙin ciki to abanza kika yi, dan na tabbatar akwai wata Uwani ko Jamila a waje da zata fara jan ra’ayinsa da wannan kwalliyar da ke kika kasa yi wata tayi ta burgeshi. Zuciyar namiji an ginata ne domin son abu fiye da ɗaya, shiyasa Allah ya basu damar yin mace fiye da ɗaya, ba ki isa kice dan kina matarsa yana mugun sonki ba ba zai ga wata a waje yaji ta burgeshi ba, haka Allah ya halicce su to da zarar kin iya allonki wajen kama shi a jiki kina yi masa iya kyautatawa da kulawar data dace, shine zaisa hankalinsa ba zai yawan riƙa kaiwa ga matan waje ba, amma ki sani duk lokacin da kika yi sakaci to wa kanki kika yiwa, dan kin bashi ƙofar mayar da ha kalinsa ga ‘yan matan waje ne, da zarar kuma ya samu wacce taja ra’ayinsa, to ko ya aureta ko ya fara raba dare na ba gaira ba dalili yana hirar banza ko waya, wata ma a kan gadonki zai fara chart da ita, to kin saki ƙofar da zaki ja shi a jikinki. Matsalar rashin kwalliya kaɗai kan iya tattara hankalin namiji ya koma waje gurin ‘yan matan da suke baza kwaliya da turare a titi. Idan kinso ki gyara dan kanki)
Sakina sauke ajiyar zuciya tayi tana murmushi.
Kenan in riƙa kwalliya ko da ya kushe domin kaina? gaskiya na fahimci karatunki kuma sai yanzu na tuna in yana kushewar ba wai a cikin ɗaure fuska bane wani sa’ilin da murmushi a fuskarsa.
To Sakina wataƙila shi nashi hanyar yabawan kenan, ko kuma ya kushe amma yaji daɗin ganinki a haka bai zo ya ganki kamar fuskar namiji ba, kuma wannan daɗin daya ji Allah kaɗai yasan ladan da zaki samu, ance fa in kana da kyau to ka ƙara da wanka, mu riƙa tuna bawai dan mazan kaɗai za muyi abu ba muyi domin Allah shida ya halasta auren, mu sani komai muka yi a cikin gidan aurenmu akwai tarin lada da muke yiwa kanmu tanadi na aljanna, dan duniyar makaranta ce muka zo kowa da irin sakamakon da zai ɗauka a jarabawar da ubangiji yayi masa.
Wannan gaskiya ne Anty Jalila kuma na ƙara ɗaukar karatu sosai a wannan fanni. Ina matuƙar godiya Allah ya saka miki da alkhairi.
Ameen, ko wani aure yana da ƙalubale kuma mutum tara yake bai cika goma ba, amma kiyi iya ƙoƙarin ki wajen samar da farin ciki a gidanki, domin ba kida kamar nan kuma shine ƙololuwar jin daɗin duk wani mutum a duniya, idan baki ƙawata shi da farin ciki da jin daɗi ba to kenan baki samu duniya ba, kuma in kika yi wasa lahirar ma saiki rasa ta akan dalilai da suke kamanni da juna, tashi mu shiga ciki garin ya fara saukar da sanyin yamma.
Cewar Anty Jalila, nan suka miƙe suka tattara komai suka wuce cikin falo.
Hamid.
[8/3, 12:19 PM] Rahma Kabir: *ƘAZAMAR AMARYA*
Na
©®Rahma Kabir MrsMG.
Wattpad @rahmakabir
Page 27.
Hamid tunda ya tafi company ya kasa dawowa gida dan ba zai iya zama shi kaɗai babu motsin kowa ba, sai yaji sam gidan bazai yi masa daɗi ba ba yara ba kuma Sakina, wanda yasan ko abincinta zai sa ya zauna a gida tunda zai samu mai daɗi, sai yamma ya koma gida a zatonsa sai samu Madina ta dawo sai dai bata dawo ba har ya ƙaraci zamansa aka kira sallar magrib yayi alwala ya tafi. Madina sai a lokacin ta dawo bayan ta biya ta gidansu ta faɗawa momy duk abinda ke faruwa, momy nan ta kira mai maganin da suka je jiya tace su ƙara haƙuri aikin a hankali ne zai kama jikin Hamid, sannan ai sunga nasara akan tafiyar Sakina kuma daga haka rabuwarsu kenan, tunda Madina taji haka sai hankakinta ya kwanta sannan momy ta bata shawarar ta lallaɓa Hamid har buƙatarsu ya biya, da haka ta dawo gidan da tunanin sauke kai su koma kamar farko da suka fara. Hamid bai shigo ba sai misalin ƙarfe takwas da rabi bayan sallar Isha’i ɗakinsa ya wuce ya aje snack da yayi oder daga Rahma Snacks and more, sai yayi wanka ya shirya ya fito falo ya zauna ya kunna tv ya soma kallo, a lokcin ne Madina ta fito cikin shigar ƙananun kaya ta zauna a gefensa tana ɗaura kai a gefen kafaɗarsa.
Beb ka shigo shine ba zaka nimeni ba, dan Allah kayi haƙuri komai ya wuce bana jin daɗin zamanmu a haka.
Me kuma ya faru ina ce komai ya wuce.
To in ya wuce mai zai sa kaki shigowa ɗakina?
Hmmm meyasa kika yi dare baki dawo daga aiki ba, tun safe fa kika fita.
Aikin ne yayi yawa a office ɗina saboda hutun dana yi amma gobe In Sha Allah bazan kai yamma ba.
Yayi.
Yace a takaice, Madina ta sauke ajiyar zuciya.
Beb dan Allah ka nimo mana abinda zamu ci yunwa nake ji kuma na gaji bazan iya girki ba.
Madina bazan cigaba da kashe kuɗi ba alhalin na wadata gidana da kayan abinci, ki miƙe kije ki dafa duk abinda kike son ci, ni zan kwanta sai da safe.
Ya ƙare maganar yana janye jikinsa a nata ya miƙe, da sauri ta kamo hannunsa.
Hamid Wlh ban iya girki ba shiyasa tun farko nace ka nima miki mai aiki, a gidanmu sai dai a dafa a bani.
Ashe shiyasa kika haɗa girkin daya kusa kasheni ni da Hajiyata, dan haka kisan yadda za kiyi amma tsarin gidana ba bu ‘yar aiki ko ba kiga Sakina kewa kanta komai bane, to kema ki koya ki yiwa kanki komai, gobe In Allah ya kaimu kafin ki fita ki tabbatar da kin gyara shi dan ya fara aje ƙura, kuma na duba kitchen akwai wanke wanke duk kiyi su kafin kije aiki kinji na faɗa miki.
Ya ƙare magana yana nunata da tsaya daga bisani ya juya ya mufi ɗakinsa ya shiga, Madina kasa magana tayi jikinta har rawa yake yi akan sauyawar da yayi mata, kamar ta fasa kuka haka ta koma ta zauna tana tunanin abin yi, sai da ta ɗauki kusan minti talatin a zaune ta rasa me takewa tunani, ga dai gida daga ita sai Hamid ba Sakina ba yaranta babu wanda zai kawo musu cikas wajen cin amarci ko a falo suka so suyi komai ba mai damunsu, amma kuma ya juya mata baya ya sauya mata yadda ko dariyarsa bata gani, ga lissafin aikin gidan da yake yi mata wanda ko kusa ba zata iya yinsu ba, sauke ajiyar zuciya tayi ta miƙe ta mufi kitchen ta haɗa comflex ta zabga madara ta fito da kofin zuwa ɗakinta ta zauna tana sha cike da damuwa, bawai dan yana mata daɗi bane kawai ta kawar da yunwar da take ji ne. Misalin ƙarfe sha ɗaya taji motsin Hamid ya fito ya ɗauki ruwa da drink ya koma ɗakinsa, koda ta fito da nufin shiga sai ta jishi a rufe ta soma kiran sunansa yana jinta amma yayi banza da ita, haka ta koma ɗaki ta soma kukan baƙin ciki wanda a haka barci ya ɗauketa.
Da safe da wuri Hamid ya shirya ya fito falo ya aje mata dubu ɗaya ya fita, ƙugin motarsa data ji ya sata fitowa da sauri ta fito, sai dai ta hango bayan motar ya fice ga kuma sabon mota da take da yaƙinin nata ne driver ya bi bayansa da ita, da sauri ta koma ciki dama shirin fita aiki take yi, ta ɗauki wayarta ta kira Hamid har kiran farko ya tsinke a nabiyu data kuma kira ya ɗaga ba tare daya ce komai ba.
Beb ya zaka fita ba tare da ka bari mun gaisa ba, sannan naga an fita da wata mota ko itace zaka bani duk da naga ba irin wacce nace ina so bane.
Eh sauri nake yi shiyasa na fita, sannan kuma wannan motar itace nayi niyyar baki a da amma yanzu na fasa dan sayar da ita zanyi wani yana so.
Ya salam! anya Hamid ɗina ne kuwa dana sani? me yasa zaka yi mini haka? dan Allah ka daina hukuntani irin haka ko so kaka zuciyata ta buga.
Babu bugawar da zuciyarki zata yi kawai dai ina yin abinda ya dace ne, na bar miki kuɗin mota a center table.
Daga haka ya kashe wayar, Madina da ido ta bi wayar tana mamakin Hamid sosai, wannan karan ji tayi ta tsane shi zata iya yin komai dan ya dawo ƙasanta ta ci ubansa son ranta, dan haka ta shirya da sauri ta fita a hanya ta tsaya wani rastuarant ta karya kana daga bisani ta wuce gurin aiki.
Yau da wuri ta dawo dan ƙarfe biyu a gida tayi mata, ta so ta shiga duba Hajiya amma kuma ta fasa dan bata san tarban da zata yi mata ba dan ta kula Hajiya kamar haushinta take ji, sai kawai ta yanke shawarar kiranta a waya, data kira ba jimawa ta ɗauka sai suka gaisa tana yi mata ya jiki Hajiya ta amsa a daƙile Madina tayi muryar tausayi tana cewa.
Dama na kira in baki haƙuri ne akan abinda ya faru wlh ba da nufin in cutar daku na yi girkin nan ba, ni ban iya sosai bane kuma har gobe ina tunanin me na saka wanda ya kawo lalacewar cikinku, dan Alkah ki yafe mini, ina ta san nazo na baki haƙuri amna ina tsoron tarban da zan samu shiyasa na zaɓi in kiraki a waya.
Shikenan Madina ya wuce Allah ya kyauta na gaba.
Cewar Hajiya tana jin daɗi a cikin ranta da girman da Madina ta bata, nan take ta huce daga haushinta da take ji Madina ta ɗaura da cewa.
Nagode Hajiyarmu Allah ya ƙara girma, dama nace ko za a turo mini Jidda ta tayani aiki gidan namu kwana biyu ban samu gyara ba saboda aiki, yau ma na samu na shigo da wuri ne nace tazo muyi.
To ba damuwa zan turo ta yanzu.
Hajiya ta faɗa Madina ta ƙara yi mata godiya kana suka yi sallama, Madina ta sauke ajiyar zuciya tana cewa.
Wannan uwar tasu dole sai da yaudara za a samu kanta.
Sai ta miƙe ta soma haɗa kayan wankinta dan Jidda na zuwa su zata fara yi. Hajiya ta soma kwalawa Jidda kira ta fito daga ɗakinta ta zo falon tana cewa.
Hajiya gani.
Yauwa Madina zaki je ki tayata aiki ta gyara gidan tunda ba mai yi sai ita.
Allah Hajiya ba zani ba dan na tabbatar yau sai jikina ya gaya mini, tayi kayanta amma babu abinda zanyi wlh.
Jidda ni kike faɗawa ba zaki je ba, to ko uwarki bata isa na sata tayi mini abu ba ta kiyi yi.
Ummata daban ni daban kuma Allah ba zani ba.
Ta faɗi haka tana turo baki ta juya zuwa ɗakinta, Hajiya tana kiranta tayi banza da ita, ƙaramar wayarta ta ɗauka ta kira mamanta Asma, tana ɗagawa bata bari sun gaisa ba ta shiga cewa ita fa zata dawo gida dan hajiya tana niman takura mata akan amaryar Kawunta Hamid, Asma ta tambayi dalilinta da faɗin haka nan Jidda ta kwashe labarin zawon data saka su da mugun abincinta, ta ɗaura da duk matsalar dake faruwa, salati Asma ta yi.
Shine babu wanda ya kira ya faɗa mana abinda ya faru?
Alhaji ne yace kar a faɗa, hajiya ma ta goyi baya, kuma wlh Umma amaryar Kawu bata da mutunci har gwara mamansu Mufeeda gashi dalilinta ta bar gidan.
To Allah ya kyauta in dai haka ne to nima ban yarda kije ki tayata aiki ba, ashe itama ba tada mutunci muna murnan Yaya Hamid ya samu mata ashe dai itama sai a hankali.
Nan dai suka yi sallama Jidda ta haye gado ta cigaba da sabgarta. Hajiya dai ta kasa miƙewa dan sosai Jidda ta kashe mara jiki wai ba zata je ba kai tsaye.
Madina shuru shuru Jidda bata zo ba, sai ta kuma kiran Hajiya bata ɗaga ba dan bata san me zata ce mata ba, haka ta haƙura ta zauna ta rafka tagumi tana duban kayan data fito dasu na wanki, duniyar kawai tayi mata zafi ta rasa tunanin da zata yi sai taji dama Sakina bata tafi ba wataƙila da tana cikin rayuwar farin ciki da mijinta, sallamar data ji a falo yasa ta miƙe da sauri ta fito, wata baƙuwar fuska ta gani, cikin ɗan sakin fuska ta ƙarasa ta zauna itama baƙuwar ta zauna suka gaisa nan take ce mata.
Sunana maman Murja maƙociyarku ce nan da gidanku ke jikin namu, tun lokacin biki banzo naga amarya ba sai yau nace bari nazo mu gaisa, ina Maman Mufeeda ko ta fita ne?
Bata nan sai ni kaɗai ce a gidan.
Allah sarki hala ke ce Amaryar?
Eh nice.
Masha Allah gaki ko tubarakallah lallai Hamid ya iya zaɓe, niko kamar ma naso wayen fuskarki.
Wataƙila kin taɓa ganina a tv dan a sahad tv nake aiki.
Yauwa koda naji, amma naji daɗin ganinki saboda ina son shirye shiryenki, Allah yasa za muyi zumunci dan maman Mufeeda bata shiga mutane.
In Sha Allah za muyi dan nima ina so na saba da maƙotana.
Masha Allah, Maman Mufeeda zata jima ne a anguwar?
Hmmm walh yanzu haka bamu san ina taje ba tayi yaji ko an kira wayarta ba a samu.
Ohhh Sakina dai ta kasa hakuri kuma naga kamar ba kida damuwa da tayi haƙuri kunyi zamanku.
To ta nuna kishinta sosai akaina ko gaisawa bama yi ta tsaneni shiyasa Allah ya gwada mata halinta har Hamid yace ta bar masa gidansa sai ya nimeta.
Amma abu baiyi daɗi ba, kin ga kuwa ke dama ta ƙara baki ki kama mijinki a hannu, ki tarairayeshi sosai yadda koda ta dawo kin gama amshe shi a hannunta.
Madina kamar an sosa mata in da ke yi mata ƙaiƙayi tayi ƙasa da murya tana cewa.
Ai kuma tunda ta tafi na rasa gane kansa wlh, duk ya sauya mini ko dariyarsa bana gani.
To kina nufin haka zata barshi ai tunda ta tafi Allah kaɗai yasan me take shiryawa akanku, ko baki san gidansu na malamai bane? dole sai kin tashi tsaye zaki kwaci kanki.
Allah ko?
Madina ta faɗa tana kama haɓa, maman Murja ta gyara zama dan ta samu damar tusa kanta a jikin Madina dan tana mugun son harka da wayyayyun mata ‘yan boko ba irin Sakina da taƙi karɓan shawararta ba.
To dama an gaya miki me kishiya tana zama ne, kowa ya iya allonsa ya wanke ne.
Amma naji daɗin haɗuwata dake kuma In Sha Allah zan dage da addu’a.
Addu’a kaɗai ba zata miki magani ba idan har kin yarda dani ni zan miki hanyar da wlh Hamid bai isa ya juyaki ba sai dai ke ki juya shi.
Ni tsoro nake yi dan ban san irin wannan abin ba, amma zanyi shawara.
To ga number ta in kin shirya nima a shirye nake da in taimaka miki.
Nan suka amsa number ɗin juna daga bisani suka cigaba da hira har misalin ƙarfe uku da rabi kamar sun daɗe da sanin juna, kafin Maman murja tayi mata sallama, Madina har gate ta rakata dan taji daɗin haɗuwarsu, haka ta juyo ta dawo falo ta zauna tana jin dole ne tayi amfani da wannan damar ta karɓi shawarar Maman Murja domin yanzu zata iya aikata komai domin farin cikin ta ya dawo kamar yadda ta soma rayuwa a gidan.
******
Sakina.
Bayan sun gama cin abincin dare suka soma kallo Ra’isa ta fita hira dan budurwa ce ta kusa gama karatunta na digree, Anty Jalila ta dubi Sakina tana cewa.
Ina so ki fara shan ganin sanyi da gyara sosai kafin ki koma ki tsumu da kyau, akwai wata ƙawata BOJUWA HERBAL’S tana kawo kaya daga ƙasar chadi masu kyau da inganci dangin du Saiwowin sanyi, da maganin sanyi. Saiwowin dahuwar kaza, dafaffiyar gimbiyar kaza, Silky kola na musamman. Tsumin sababi. Hakkin daka gangariya. Gumba special. Gaban ayu. Dukkan Saiwowi da kayanta daga Chad suke zuwa. Gobe In Sha Allah zan kirata domin ta haɗo miki komai na fara tsumaki ki dawo sabuwa gangariya yadda ko Hamid ya jiki sai ya rikita lissafinsa yana niman sanin Sakinarsa ce ko wata aka sauya masa.
Ga masu bukatar kayan BOJUWA HERBAL’S BY SURAYYA. Ku tuntubi wannan number 08032773332.
Sakina Dariya ta yi wanda ta jima bata yi irinsa ba tana cewa.
Kai anty wani gyara zanyi bayan uban gayya bata ni yake ba ta sabon inji yake fa.
To zauna Sakina kiga zama kema in kinso haka zaki tayar da komaɗa ki dawo sabon Inji, ko kin manta da tsohuwar zuma ake magani.
Hakane kuma, to yanzu ni ina biye da duk shawarar da kike ɗaurani akai ina godiya sosai.
Allah ya sa mu dace. Sakina kina yiwa kanki addu’a da yaranki dama shi kanshi uban gayya Hamid kuwa? kina yin sallar Nafila domin samuwar kwanciyar hankalinki da duk buƙata in ta taso miki?
Ina ƙoƙarin yin addu’a musamman na safe da maraice, sai kuma salloli na biyar bana wasa da yin addu’a a cikinsu.
Anty ta jalila ta girgiza kai kana ta ce.
To gaskiya baki mayar da hankali kan addu’a ba ƙila shiyasa Hamid ya zama miki haka, musamman ma da yace zai ƙara aure ya kamata ki tsananta addu’a sosai dan samuwar nutsuwa da zaman lafiya a gidanki.
Aiko nayi saka ci da wannan dan so tari ma inya bata mini rai sai nai na zauna ina kuka.
To kukan yayi miki maganin matsalarki? ai kin wuce ki zauna kina yi masa kuka face ki kai ƙararsa gurin Allah.
Sakina ta jinjina kai alamar gamauwa da bayaninta.
[8/4, 7:08 PM] Rahma Kabir: *ƘAZAMAR AMARYA*
Na
©®Rahma Kabir MrsMG.
Wattpad @rahmakabir
Page 28.
Jalila ta yi murmushi tana cigaba da cewa.
To ina so ki ƙara a saman wanda kike yi, a yanzu ko mu da muke kasuwanci muna dagewa da niman dacewa a gurin Allah tare da kasuwa mai albarka, babu zancen ki bayar a miki a addu’a kema kina da damar da ki roka da kanki, saboda Allah ya baki lafiya da damar da zaki kusance shi dan haka sai ki dage wajen nima a gareshi, musamman yadda Allah ya miki sutura mijinki yana da rufin asiri to yana da kyau ki dage sosai. Musamman Nafila a ɗaya bisan uku dare, ko sallar Walha, ki yawaita istigfari yana maganin masifa yana ƙara buɗi da falala kuma yana wanzar da kwanciyar hankali, ki luzumci jan salatin Annabi s.a.w waraka ce kariya ce kuma nasara ce a duniya da lahira, ya zama kina ware lokuta da zaki yi su ki samu counter ko charbi kina jan Hailala da sauran tasbihi, kina Hasbunallahu wa ni’imal wakil ƙafa ɗari huɗu da hamsin kullum. Sakina kina yawan Sadaka domin ita maganin masifa ce, ki bawa marayu ko naƙasassu ko gakuyayyu, ki bada biyar sai Allah ya mayar miki ita hamsin domin ka bayar da ƙalilan ne ki samu kasiran, karki wasa da sadaka dan wlh ba ƙaramin magani bace daga sihiri kambun baka da samuwar biyan buƙata da kuma falalar lada a gurin Allah, tabbas za kiji daɗin ta daga duniya har lahira. Idan kinga masifa tayi miki yawa to tabbas kin bar Allah kin kasa ɓata lokacin wajen kai kukanki gareshi, kuma koda kina cikin farin ciki kada kiyi ƙasa a guiwa wajen bautar Allah domin ba mun zo duniyar dan mu zauna bane, dan haka kar ki wasa kar ki shagala kar kiyi shauni wajen kusantar Allah In sha Alkah zaki riƙa ganin falala a rayuwarki, domin wannan shine sirrin kasuwanci na kuma sirrin zaman lafiya a gidan mijina, bawai bama saɓani bane muna faɗa sai dai Allah yana saka mini dangana da haƙuri da juriya akan duk girman tashin hankali daya tunkaroni, saboda bana wasa wajen kai masa kukana walau ina cikin baƙin ciki ko farin ciki bana gazawa gurin godiya a gare shi da miƙa lamarina gaba ɗaya a hannunsa. Na tabbata idan kin dage wlh zaki samu nasara sassauci daga matsalar ki kuma In sha Allah Allah sai ya gyara miki Hamid kuma sai ya saka miki wani kwarjini da shakkarki da gudun ya ɓata miki rai, ki dogara ga Allah kaɗai ya isarki miki.
Anty nagode nagode bansan da bakin da zan gode miki ba, hakika zuwana gareki alkhairi ne. Allah ya saka miki da gidan Aljanna.
Sakina ta faɗa tana jin hawayen farin cikin yana bin kuncinta.
Ki godewa Allah Sakina domin yana sonki da Rahma ne, dan da kin biye shawarar maƙociyarki da yanzu ba wannan maganar ake yi ba, Allah kaɗai yasan wani jarabawar zai ƙara jefaki a ciki ba. Ki sani Allah baya taɓa jarabtar mutumin banza matsawar kika ga bawa bai yi nasara a ƙaddararsa ba to yayi gajen hakuri ne, amma tabbas in yayi mai yawa Zai ga kyakkyawar sakamako.
Gaskiya ne Allah ya ƙara mana imani da jin tsoransa a duk halin da muka tsinci kanmu.
Ameen, kinga dare ya yi dan ana niman ƙarfe goma muje mu kwanta.
Anty bana son hirarmu tana yankewa dan ba ƙaramin daɗinsa nake ji ba.
Sakina daga yanzu nake so ki fara addu’a dan haka ƙarfe ukun dare zuwa da rabi zan tashe ki, tashi muje mu kwanta. Ke yarinyar nan ko ta shigo na jita shiru ne?
Laaa tun ɗazu ta shigo fa baki kula bane.
Ban kula ba kuwa kinsan kula da kaya yafi ban cigiya.
Wannan gaskiya ne.
Shiyasa za kiga muna rayuwa tamkar ƙawata, to na jawota a jikina sosai dan na riƙa sani matsalolinta dama duk abinda ya shafe ta, kuma wlh bata ɓoye mini komai hatta zancen samarinta. A wannan zamanin tarbiyya tayi wuya Sakina wlh in baki jawo ‘ya’yanki a jikiba sai kiga duniya ta rainesu sun zamewa mutane damuwa, hatta mazan da suke makaranta kullun sai munyi waya kuma lokaci zuwa lokaci ina kai musu ziyara, masu auren ma bana wasa da tuntuɓarsu akan yanayin zamansu, to Allah ya bamu kiyo kuma zai tambayemu ranar ƙiyama abinda muka kiwata.
Hakane Wlh Anty, nima bana wasa da jan yarana a jiki, musamman Mufeeda da take babba duk wasu abubuwana tana koya.
To kinga a wannan gaɓar ne ya dace ace kina nusar da ita yadda ake zamantakewar aure, duk abinda kike gudanarwa a gidanki tana recording kuma shi zata je gidan mijinta tayi, yadda baki damu da kwalliya ba ko gyaran jiki ko gyaran kai wlh itama haka zata koya ta ɗauka, shiyasa sai kiga wasu yaran ko sun je gidan miji za suyi ta kwaɓa da shirme to abinda suka gani a gidansu suka ɗauka. A yanzu ne kike da damar gyara kurakurenki Sakina domin yaranki su samu future mai kyau.
Anty na yarda da zancenki dan gaskiya kinga gidanmu basu damu da duk wannan kyale kyalen ba shiyasa muma yara muka taso a haka, nifa ko relaxa bana sakawa a kai kuma haka muka taso a gidanmu wai ba kyau sauya launin gashi ne.
Anyi wa abin fahimtar baibai ne Sakina, amma kuwa saka relaxa baya sauya launin sumar kai yana dai gyara shi ne, dan haka ki aje rayuwar gidanku ki dasa taki sabuwa ki gyara goben yaranki. Nima ai duk gidan namu iri ɗaya ne amma zama da wayayyu yasa na goge na fita zakka kuma gashi a ‘yan uwan ana ganina ana koyi dani, kema ki ciri wannan tutar a gidanku.
Murmushi Sakina tayi tana jin daɗi a zuciyarta ta miƙe tana ƙara yi mata godiya, nan suka yi sallama suka wuce ko wanne ya kwanta.
Tun daga wannan ranar sakina ta fara dagewa da yin addu’a, musamman Anty Jalila ta sayo mata caunter ta fara lazumi ta miƙa lamarinta ga Allah ba dare ba rana. Kuma tana ta koyon abubuwa a gurinta.
****. *****
Bayan sati Huɗu.
Abubuwa da yawa sun faru ciki kuwa har da damuwar rashin inda Sakina take, lamari ne da kowa ya ɗauke shi kamar wasa sai kuma ya ke niman zama babba, zuwa yanzu ‘yan uwa sun fara karaya da tunanin ko Sakina ta faɗa mugun hannu ne ko kidnappers, sai aka koma yiwa juna jaje da tsananta addu’a akan Allah ya bayyanata domin babu inda basu tambaya ko taje ba amma ba amo ba labari. Hamid gabaɗaya ya rasa meke damunsa lafiya ce baida ita ko damuwa ce take niman nakasa garkuwar jikinsa, duk wani tunani yayi akan matsalarsa kuma yaƙi faɗawa abokansa dan ganin abin kunya ne daga yin aurensa gidansa ya tarwatse, duk da Habib yana da labarin komai daga bakin Kausar dan Madina ta faɗa mata ita kuma ta bashi labari, zuba masa ido yayi har yaga gudun ruwansa in ta kure masa ya furta damuwarsa sai ya bashi shawara, shiyasa sam Hamid bama ya bari su haɗu.
Madina kuma zuwa wannan lokacin ta kasa gane kan Hamid sai su kwana su yini basu haɗu ba har sai in ta zauna a falo ta jira fitowarsa ko shigowarsa, ba kuma wata magana me daɗi ke shiga tsakaninsu ba, kuma da gangan yake yi mata haka tunda har ba zata bi umarninsa ba to shi kuma ya rantse ba zata samu farin ciki a gare shi ba, tunda gashi falon yayi kura sosai rabonsa da tsintaiya tun lokacin Sakina na nan, kitchen kuwa saboda wanke wanke data tara har ya fara bi tsami ƙamshinsa ya sauya. Ɗakinsa ne kaɗai yake tsayawa ya gyara shima dan yana kwanciya a ciki, a takaice gidansa ya sauya kamanni, shiyasa ya ƙi sakar mata fuska, su cigaba da zama a haka har yaga ƙarshen rashin kirkinta, shi babban damuwarsa a yanzu yasan inda Sakina take yaje ya bata haƙuri ta dawo dan zuwa yanzu ya gama karaya ya tabbatar da itace Hasken gidansa, kuma karin damuwarsa Abba yaƙi cewa komai akan lamarin koda shawara ya bashi amma shuru yayi banza da shi, hajiya kuma ba wani magana mai daɗi take yi masa ba shiyasa ma sai ya kwana biyu bai je ba. Ita kuma Madina taƙi gyaran gidan tunda yaƙi nima mata ‘yar aiki sannan taurin kai bazai sa tayi ba dan ta nuna masa bai isa ba, hatta wankinta ya taru ɗakinta bata matsar da komai dan kullun sai yamma take dawowa aiki sai ta biya gidansu taci abinci harda guzirin na dare kan take dawowa, duk yadda take tsammanin asiri zai kama Hamid to fa ko gezau ba abinda ya sauya shi, hakan yasa ta fara tunanin zuwa gidan maman Murja dan nimawa kanta mafita.
Yau lahadi tana hutu bata fita ba hakan yasa ta shirya cikin doguwar riga, misalin ƙarfe sha ɗaya na safe ta shiga gidan maman Murja, tayi sa a tana nan bata fita ba tayi mata masauki a falonta, bayan sun gaisa Madina ta koro mata damuwarta akan har yanzu Hamid bai sauya ba, maman Murja ta saki murmushi.
Taya zai sauya Sakina tana can tana haɗa miki ƙullin barin gidan, ni na tabbatar kafin ta dawo sai tayi babban shiri.
To yanzu ya kike ganin zanyi?
Akwai wani malami aikinsa kamar yankar suka, in dai kina da kuɗi to kamar kin samu biyan buƙata.
Kamar nawa kike ganin zan riƙe kuma dole sai naje.?
Kamar dubu ɗari haka, kuma in so samu ne muje tare kiji bayani da kunnenki.
To kamar wace rana zamu?
Ko yanzu in kin shirya sai muje ni gidana banda kulle mijina a tafin hannu na yake, bai isa ya hanani yin abinda nake so ba.
To muje kawai in yaso sai mu tsaya a hanya na cire kuɗin tunda ina tare da ATM ɗina a fos.
Yauwa haka nake so ‘yar gari da zafi zafi ake dukan ƙarfe.
Cewar maman Murja cike da jin daɗi jawo Madina jikinta ko ba komai ta samu kawar sirri ba irin Sakina ba. Da sauri ta shirya ta fito tana cewa ‘yarta Murja ko babanta ya dawo ta sanar dashi ta fita, kana suka fito suka samu abin hawa suka wuce gidan malam. A hanya Madina ta cire dubu ɗari da hamsin kana suka ƙarasa gidan Malam mai yasin, ba ɓata lokaci aka yi musu iso kasantuwar ba yi da baƙi ranar, yana ganin maman Murja ce ya saki murmushi.
Yau matar Alai Mamman ce da kanta.
Aiko Malam nice nazo da baƙuwa, itama tana so a ɗaurata akan layi, Allah ya haɗata da juyayyen miji sai wahala yake bata.
To madalla ta kawo kukanta inda za a share mata, kiyi mini bayanin mijinki da kuma abinda kike so ayi masa.
Madina ta muskuta ta gyara zama ta soma zayyano masa duk matsalarta ta ɗaura da cewa.
Malam ina son in juya Hamid tamkar uwarsa, sannan ayi aikin da matarsa da yaransa ba zasu dawo gidan ba ya zama nice kaɗai a duniyarsa sai abinda na haifa.
Data kai nan a maganarta sai ta ja fasali, malam ya yi zane akan ƙasa sai ya ɗago yana cewa.
Mijinki yana da taurin kai kuma yanzu haka kishiyarki ba a zaune take ba tana nan tana aikin da zata farraƙa tsakaninku, dan haka zaki bayar da dubu tamanin na aikin da zamu yi tare da dumu arba’in na rago da zamu yanka na sadaka, sauran biya dubu Hamsin sai bayan kwana biyu ki bawa maman Murja ta kawo mini.
Nagode sosai ni dai fatana aiki yayi yadda ya kamata.
Amarya karki ji komai ki kwantar da hankali ki aikin malam babu wasa a cikinsa.
Cewar maman Murja, nan take Madina ta ƙirga dubu ɗari da ashirin ta bashi daga misani suka yi masa sallama suka fito, maman Murja tace tayi mantuwa Madina ta jirata sai ta koma cikin gidan malam, ta sameshi yana ƙirga kuɗin ta miƙa masa hannu tana cewa.
Bani kasona kafin na dawo kace kayi amfani dasu.
Wlh ba kida sauƙi akan kuɗi, ai kinsan dole zan baki kasonki.
Malam ya faɗa yana ware dubu ɗari gefe ya miƙa mata dubu asirin ɗin sama ya bata.
Hmmm yanzu ɗari zaka ci? gaskiya saika ƙara mini wani abu.
Ki bari in ta kawo cikon Hamsin sai na ƙara miki amma kobo bazan bayar ba anan, a ciki zan siya kayan da zanyi mata aiki.
To shikenan amma dan Allah ayi aiki mai kyau kar ayi mata na ‘yan kasuwa wannan ta musamman ce kuma mun dinga zuwa kenan.
Dole ma nayi mai kyau domin mu cigaba da samun na abinci.
Murmushi tayi masa ta saka kuɗin a cikin jaka saita fito suka wuce. Bayan sun dawo Madina bata shiga gidan maman Murja ba suka rabu akan za suyi magana a waya sai ta shiga gida, ganin motar Hamid yasa gabanta faɗuwa dan bata yi zaton zai dawo da rana ba, kuma ta sanar da shi yau ba tada aiki, hakan yasa ta ɗaure fuska ta shiga ciki sai gashi a falo ya harɗe ƙafa ɗaya kan ɗaya kamar bata ganshi ba, ta nima wuce shi ya dakatar da ita.
Daga ina kike?
Gidan Hajiyarka naje tace mini anyi haihuwa a maƙota in je inyi barka ban daɗe da fita ba.
Madina ta samu kanta da ɗaura ƙarya akan Hajiya, Hamid dai ya jita ne amma bai gamsu ba hakan yasa ya miƙe ya fice zuwa gidansu, ya samu su Hajiya a barandar gidan akan kujera suna sauraren radio kan batun zanga zanga da aketa maganar za ayi a duka jahohin Nigeria, Hamid ya gaishe su kana ya ja kujera ya zauna yana cewa.
Hajiya Madina ta shigo nan ne?
Rabona da ita namanta.
Amma yanzu ta shigo gida take cewa ke ce kika ce taje barka maƙota anyi haihuwa.
Innalillahi wa inna ilaihir raji’un, kaji mini maƙaryaciya yaushe nayi haka da ita. Alhaji kaga yarinya tana niman yi mini sharri, ba nan muke tare da kai ba.?
Gaskiya ne muna tare sai dai ko ƙila kunyi waya kin faɗa mata, ki dai tuna ko kin mance kunyi haka.
Alhaji ya faɗa yana murmushi, hajiya ta dafe ƙirji.
Ni Saratu me zai sa nayi haka, Hamid ki rata tazo muji da wani lokaci nayi haka da ita, bazan ɗauki wannan iskancin ba taje yawonta na garari ta ɗaura mini ina zamana.
Hamid bai ce komai ba ya ɗaga waya ya kira Madina, koda ta ɗauka yace mata ta shigo gidan Hajiya sai ya kashe wayar.
[8/5, 5:46 PM] Rahma Kabir: *ƘAZAMAR AMARYA*
Na
©®Rahma Kabir MrsMG.
Wattpad @rahmakabir
Page 29.
Madina ta saki wani shu’umin murmushi kana ta miƙe ta yafa gyale ta fito ta nufi gidan, koda ta isa ta samesu a zaune, sai ta risina ta gaida Abba ya amsa kana ta gaishe da hajiya, Hajiya ta ɗaga mata hannu.
Riƙe gaisuwarki bana son munafurci. Yaushe nace miki anyi haihuwa a maƙota da zaki haɗa mini sharri?
Kai Hajiya kefa da kanki kika kira ni a waya akan nazo, kuma dana zo kike cewa naje maƙota anyi haihuwa na wakilce ki barka.
Innalillahi wa inna ilaihir raji’un! ni zaki yiwa sharri.?
Hajiya ta faɗa tana nuna kanta, Madina ta turo baki tana cewa.
Yada hankalina zaki ce zan yi miki sharri, bayan ke ce kika bani umarnin naje har kina cewa in Hamid yazo zaki faɗa masa.
Ƙarya kike yi shegiyar yarinya mai fuska biyu, wlh ban taɓa sanin ke munafuka bace sai yau.
Hajiya ta miƙe tsaye tana nunata da yatsa, Madina ta miƙe tana dubanta.
Ikon Allah! shikenan kina so ki haɗani da Hamid, dama ina da labarin kece kika fara tsanar Sakina kafin Hamid ya tsaneta, dan haka ni nafi ƙarfin makircinki kuma sai Allah ya bi mini haƙƙina.
Ke bana son rashin ɗa’a wuce ki bawa mutane guri.
Alhaji ya faɗa cikin haɗe rai, Hajiya ai sai ta fashe da kuka tana cewa.
Allah ya isa tsakanina da ke so kawai kike ki haɗani da Hamid, to ta Allah ba taki ba tsinanniyar yarinya.
Tsinannu dai, ɗaya tan Zaria ɗaya kuma tana Abuja.
Madina ta faɗa tana murguɗa baki, Hamid ne ya miƙe cike da ɓacin rai yayi kanta zai mareta, da gudu ta wuce tana cewa.
Wlh baka isa ka dukeni akan gaskiyata ba, ka tuhumi Hajiya ita tasan inda ta aike ni.
Ta faɗa tana yin gaba, Alhaji ya ce.
Ka rabu da ita a bar maganar haka. Ke kuma banga a bin yin kuka ba tunda kin ce baki aiketa ba ai shikenan.
Wlh abin yayi matuƙar ƙona mini rai saboda tsabar raini ta kulla mini sharri, yaushe rabon dana ganta in ba yanzu ba.
Hajiya ta faɗa tana matsalar kwalla, Hamid ya bata haƙuri yace zai ɗauki mataki akanta, ya miƙe ya wuce zuwa gidansa, a lokacin ne Alhaji ya soma murmushi yana ‘yar dariyarsu ta manya.
Kaɗan ma kika gani ba dai ita kika zaɓa ba akan Sakina, hmmm to banda abinki Hajiya ai wasa farin girki kenan, ko banza ta saka ki kuka.
Au dariya ma zaka yi mini Alhaji? kaima kasan bata zo gidan nan ba sharri dai ta yi mini.
Kun dai fi kusa, wataƙila lokacin data shigo ina nawa sashin.
Hajiya shuru tayi dan takaici, tana jin in dai bata hukunta Madina zuciyarta ba zata yi sanyi ba.
Hamid ko koda ya koma kaca kaca yayi mata, akan in tana iskancinta karta ƙara saka Mahaifiyarsa, Madina ta dube shi tana cewa.
To ai mahaifiyar bata kowa bace, dan haka in dai ta taɓota saita taɓa ta itama.
Ganin zata ƙara bata masa rai yasa ya bar gidan gabaɗaya. Madina ko zama tayi ta haɗe ƙafa tana jin wani farin ciki akan abinda ta yiwa Hajiya, dama tun sadda taƙi turo mata Jidda ta tayata aiki kuma ta kirata taƙi ɗauka sai ta ƙullaceta akan zata rama, gashi kuwa harda kuka ta sakata, dariya ta saki sosai tana cewa.
Wani mulki sai in Hamid ya dawo ƙasan ƙafatq zaki ci ubanki tsohuwa.
Sai ta lumshe ido ta shiga hasasho yadda zata zuba mulkinta son ranta a gidan. Kiran wayarta yasa ta miƙe da sauri ta faɗa ɗakinta, kafin ta isa ma ta tsinke, Kausar ce ta kira dan haka ta bari anjima zata kirata in ta gama girkin data yi niyyar ɗaurawa, sai ta fito ta shiga kichen ta saka tafashen nama yau so take tayi pepe meat da dafadukan taliya taci, saboda ta kalli video zata kwatanta taga ko zai yi daɗi, data ɗaura tafashe sai ta koma ɗaki dan tayi sallar azahar.
Ɓangaren Hajiya kuwa tana ganin Abba ya fita masallacin ƙarfe biyu tayi azama ta fito zuwa sashin hamid, tayi sa a baya nan dan bata ga motar daya saba fita da shi ba, ta shiga da sallama sai dai ba wanda ya amsa, a hankali ta shiga bin falon da kallo duk yayi ƙura sai ta wuce kitchen dan ta soma jin ƙauri, taga gabaɗaya ya fita hayyacinsa sai tashin tsamin abinci yake yi ga ƙauri da ya bure kitchen ɗin, ta isa gurin tukunyar ta kashe gas ta buɗe taga tafashen nama ne har ruwan ya ƙone ya kama tukunya sai ta fito falo cike da masifa tana kwalawa Madina kira, da sauri ta fito sanye da Hijab tana duban hajiya fuska haɗe.
Lafiya kike kirana kamar naci miki bashi.
Ke ƙaramar marakunya ballagaza to nazo naja miki kunne daga yau karki ƙara sakani cikin sakarcinki danni ba sa’ar yinki bace. Ban san cewa ke macijin ɓoye bace sari ki noƙe ba to ahir ɗinki dani. Ƙazamar banda da wofi gabaɗaya kin sauyawa gida kamanni dan ƙazanta, dama ance Allah ya kyauta ranar yabo yau ga ranar Sakina nan, na tabbatar da tana nan ba za’a ga gidan nan haka ba.
To kije ki dawo masa da ita mana tazo ta gyara gidan, dama ni ba baiwa ya auro ba ban saba da walaha ba, cikin jindadi da gata ya ɗauko ni, kuma karki ƙara zuwa gidana kina ɗaga mini murya dan ba haifata kika yi ba.
Au Allah, ni kike faɗawa haka Madina?
Fiye da haka zan faɗa miki tsohuwar ala kwankwan, ni dai nafi ƙarfin ki haɗani da Hamid, dama ance inyi taka tsantsan dake.
Hajiya tsabar baƙin ciki kasa magana tayi dan lamarin Madina yafi ƙarfinta, haka ta juya bata ce komai ba Madina ta bita da shewa tana cewa.
Zama daram gidan Hamid na zama ciwon ido sai haƙuri.
Hawaye masu zafi ne suka soma bin kuncin Hajiya ‘yar data kusa jika da ita ce ke zaginta da cin mutunci, haka ta shiga falo ta wuce ɗakinta tana sauke ajiyar zuciya, ji tayi lallai saita nunawa Madina ta isa da Hamid dole sai ya saketa dan ba matar aure bace, nan ta ɗaga waya ta kira Asma ta faɗa mata komai har da sasshekar kukanta, Asma kamar tayi tusuntauwa tazo dan tsabar baƙin ciki tace kuwa a satin zasu zo su ci uban Madina. Haka hajiya ta ƙara kiran Kubura itama dai masifa tayi sosai akan zasu zo su nuna mata Hajiya tana da masu shigar mata.
*****
Kano.
Sakina tana kitchen tana haɗa musu abincin rana Anty Jalila ta shigo tana cewa.
Matar Hamid wannan irin ƙamshi haka ai dole kisa Hamid ya kusa zaucewa da kewar girkinki, na kula duk iya girkina saina sara miki.
Kai anty banda zolaya.
Ba batun zolaya bane gaskiya ce, dan haka gobe zan amsa girki ni zanyiwa mijina dan kar ya gane an sauya hannu.
Dariya Sakina tayi itama Jalila tana dariya ta soma cewa.
Sakina yanzu fa kinyi wata guda a gidan nan, dan haka ki fara haramar tafiya dan kin gama gigita ‘yan uwa nasan in suka san kina gidana na shiga uku wlh.
Ni tunda kika ce yara suna Hannu yaya Umma hankalina ya kwanta naji komawata da saura dan ban gama ɗaukar karatu a gurinki ba, ɗan har yanzu ina cikin duhu.
Aiko kina cikin duhu Sakina. Domin namiji yana son a shagoɓa shi da tarairayarsa, to ke ba kya masa kissa da tattausan lafazin jan hankali, kin aje soyayya kin ɗauko rayuwar mutanen daji, yadda kika bani labarin kishiyarki a ɗan zaman da kuka yi da ita duk sharrin da take miki kissa ce, kuma ba a son mace tana yin irin wannan kissar dan ya zama da cutatrwa a ciki, kuma da yake shu’uma ce kinga yadda a gabanki take nuna masa soyayya ko kunyar idonki bata gani. Lokacin data ce kin mareta kin hana Mufeeda ta yi mata aiki da kema saiki saki kukan kissa ki shiga koro bayanin ke sam baku haɗu ba yau tun safe, ki fututtuke kice bakisan anyi ba na tabbatar zaku raba masa hankali gida biyu sannan zai kasa ɗaukar mataki akanki balle ma yace kije gida, kinga kinyi maganinta da naki salon kissar amma sai kika yi shuru kika kasa kare kanki, daga yanzu ki ɗauki wannan a cikin ranki da zarar ta zo miki da wani shu’umanci na kissa dan ta haɗaki da Hamid kema ki nuna mata kin fita iyawa ki fututtuke kice bakisan anyi ba koda kuwa dukantsiya kika yi mata, zata shiga shakkar haɗa miki makirci. Ƙanwata dole fa sai kin buɗe idonki kin zama fitsararriya ki nuna mata kema zaki iya yin komai akan mijinki to zata shafa miki lafiya.
Gaskiya ne Anty nima nasan nayi mata sakwa sakwa amma ba tashin hankali ta inda tabi nima tanan zanbi da ita.
Yauwa ‘yar garinmu. Sannan abu na gaba ko damuwa ba kiyi da rashin kwananku guri ɗaya ba kin barshi shi kaɗai a ɗaki yana abinda ya ga dama, wlh mata iri irenku da dama suke saka mazansu faɗawa zina mai tsoron Allah ne yake ƙara aure, wasu kuma damar charting kika bashi da mata a waya suyita masha’a, dan haka ko faɗa kuka yi ki yi ƙoƙarin kwana a ɗakinsa sannan ki yi shawarar dana baki a baya. Na tabbatar daga ranar da Alhajina ya dawo zuwa yau kin fahimci abubuwa da dama a gareni yadda nake gudanar da gidana, dan haka ki cigaba da saka ido har zuwa ranar da zaki bar gidan nan dan na tabbatar in baki yi wani ba zaki aikata wani kuma zaki ji daɗinsa. Kuma ki saka a ranki yin karatun boko ba shine kaɗai wayewa ba ko rayuwar jin daɗi ba, ki sani wayewar da aka yi shi ta addinin Musulunci shine asalin wayewa domin mutum zai yi shi bisa tsari da bin dokar Allah da kiyaye afkawa halaka. Dan haka waɗanda ba suyi bakon ba sai in sun mayar da kansu baya shine zasu riƙa fuskantar barazana a cikin lamuransu. Ko tayaya ki ari rigar ‘yan zamani domin a dama dake, ɗan kalmomin turanci ko a gurin ‘yarki Mufeeda zaki sansu ki riƙa sakata tana koya miki, sannan kiyi ƙoƙarin komawa islamiya dan shiga mutane yana sawa ki san halayyarsu mabambanta sannan kuma ki ƙara buɗe ido kisan kan yadda duniya take ciki.
Gaskiya ne Anty ina jinjina miki wlh domin kin wayar mini da duhun kai dake damu na.
Allah ya baki ikon yi. Wai ya batun magunguna kinata amfani dasu ko dan ina so in ƙara siyan waɗanda zaki tafi dasu.
Ina ta amfani dasu amma anty naji kina maganar tafiya tun yanzu, ni da naso nayi kamar wata biyu zuwa uku.
Tafɗijam to ba a gidan nan zaki yi kwanakin nan ba, zaki koma gidanki dan Umma tace Hamid fa yana cikin damuwa ga kuma yara sun kusa komawa makaranta gwara kije ki kula da su.
Hmmmn ni wlh ban gama hutawa ba ina so na gama ɗaukar karatu a gurinki.
Ba zaki gama ba ko a waya ma ƙarasa, ni dai fatana Allah yasa zaki yi amfani da abinda nake faɗa miki.
In Sha Allah zanyi amfani dasu.
Allah ya baki iko.
Ameen antynmu.
Sakina ta faɗa tana dariya, Sai Jalila ta fita zuwa falo ta barta a kitchen, ta zauna a cushing ta nima number ɗin Umma sai dai harta gama ringing bata ɗaga ba, ta aje wayar tana tunanin maganar da tayi shekaran jiya da mijinta akan lallai ta kira gida ta faɗa Sakina tana gidanta dan a kwantarwa mutane hankali, idan ita Sakinar yarinya ce ita ta nuna ta fita hankali bai dace ta biye mata ba, koda ba zata koma gidan mijinta ba yanzu to ya kamata ace gida ansan inda take dan hankali ya kwanta, hakan yasa Jalila ta gamsu da maganarsa ta yanke kiran Umma ta sanar mata, tana cikin tunanin maganar sai ga kiran umma ya shigo bata ɗauka ba har saida kiran ya tsinke kafin ta kirata, koda ta ɗauka suka gaisa, kana Jalila tace mata.
Ya labarin Sakina har yanzu shiru ko.?
Ke dai bari wlh munata tunanin kidnappers ne suka saceta amma shuru har yau basu kira waya ba.
To ya batun mijinta.?
Wannan ai yayi laushi kamar fulawa duk ya rame da kin ganshi yana cikin damuwa, shekaran jiya yaje gidan baba mun haɗu akan batan Sakinar.
Hmmm ai na fi so ya fi fulawa laushi kafin zan bashi Sakina.
Na’am me kika ce? Ban gane me kike nufi ba.
Hmmm to Sakina tana gidana ganin yadda hankalinku ya tashi yasa nace bari dai na faɗa miki tana cikin ƙoshin lafiya gata nan har ɗan ƙiba ta fara, ba wai na faɗa miki dan Sakina zata dawo bane dan wlh sai mijinta ya san muhimmamci kafin ta koma gidansa.
Innalillahi wa inna ilaihir raji’un! haba Anty Jalila ya zaki yi haka? kinsan kuwa yadda hankalinmu ya tashi.
Na sani, gani nayi kuma kun bada gudun mawa wajen wulaƙancin da Hamid yake yi mata, kun kasa ku tare shi ku nuna masa kuskurensa sai dai kullun ku ba ta hakuri, ko so kuke sai cuwo ya kasheta ne kafin zaku ɗauki mataki, Sakina tana da ‘yanci dan haka tazo gurina domin sabunta ‘yancinta, walau abinda nayi yayi muku daɗi ko kar yayi ni dai na yi haka dan kwatarwa yarinya ‘yanci, ki faɗawa duk wanda zaki faɗawa ina jiran masifar kowa, kin sanni sarai dai dai nake da kowa.
Ƙit ta kashe wayarta dan dama tace zai ta buɗa mata wuta yadda zata kashe mata ƙarsashin yi mata ƙorafi, yaya umma da ido tabi wayar cike da tsantsar mamakin Jalila, kuma wani abin da ta faɗa gaskiya ne amma ace Sakina tana gidanta har kusan wata guda bata faɗa ba sai yau, nan take ta shiga kiran ‘yan uwa tana faɗa musu Sakina tana gidan Jalila dan ba zata yi shuru ba, aka shiga farin ciki daga bisani kuma masifa ya biyo baya sai kiran Jalila suke yi taƙi ɗagawa daga bisani ta saka wayar a airplanemode, ta tabbatar sai ta nuna musu itama jan wuya ce kafin za suyi dai dai kuma ba zata bayar da Sakina ba har sai tace ita da kanta zata tafi.
[8/7, 5:03 PM] Rahma Kabir: *ƘAZAMAR AMARYA*
Na
©®Rahma Kabir MrsMG.
Wattpad @rahmakabir
Page 30.
Sakina jiki a sanyaye ta fito daga kitchen tana cewa.
Anty wai faɗa musu kikayi ina nan? Wlh da baki faɗa musu ba nasan gobe zasu zo su tafi dani.
Sakina hankali ya tashi sosai akan rashin sanin inda kika je, dan haka yasa na faɗa kika nan dan hankalin kowa ya kwanta, amma fa ki sani babu wanda ya isa ya rabaki da gidan nan face da amincewarki, ina nan ina jiran duk wanda zasu zo kema kinsan daidai nake da kowa.
Murmushi Sakina tayi tana cewa.
Har naji sanyi wlh.
Gobe in Allah ya kaimu ki shirya zaki fita tare da Ra’isa ta kaiki saloon a saka miku relaxa ki gyara kanki, daga can kuma zaku je gidan mai gyaran jiki ta fara gyara ki ba zaki dawo ba sai nan da kwana biyar domin gyara na musamman zata yi miki, Ra’isa zata dawo gida in an gama zata zo ta ɗaukeki ku dawo gida, kinga babu wanda zai zo ya same ki balle su matsa ki koma sannan zan riƙa kiran mai gyaran jikin muna waya dake ina sanar dake duk halin da ake ciki.
Sosai Sakina taji daɗin maganarta ta shiga zuba mata godiya.
Sakina dole na yi miki komai dan kankaro miki mutuncinki a gurin Hamid.
Jalila ta faɗa tana ‘yar dariya, murmushi Sakina tayi dan ba ƙaramin farin ciki take da kasancewarta a gidan anty Jalila ba.
***
Kaduna.
Hamid yana zaune a cikin office ɗinsa na motoci sai ga Habib ya shigo ya miƙa masa hannu suka gaisa yace cikin zolaya.
Abokina nasan inna ji kira a gurinka to samu ne, da fatan labari me daɗi zaka bani, ya uwargida da amarya.?
Habib ya faɗa cike da murmushi a fuskarsa ya samu guri ya zauna, Hamid ya sauke ajiyar zuciya yana cewa.
Habib ba zaka gane ba Wlh ina cikin damuwa, musamman ma akan rashin sanin inda Sakina take a yanzu.
Ban gane me kake nufi ba, kamar yaya baka san inda Sakina take ba.?
Ban faɗa maka abinda ya faru bane, amma tun ranar da aka sallameni a asibiti da muka koma gida na tadda Sakina ta haɗa kayanta ta bar gidana, kuma abin damuwar har yau babu wanda yasan inda taje.
Allah sarki Sakina baiwar Allah, wlh Hamid nasan ka kure haƙurinta ne, dama ina jiye maka azo wannan gaɓar, kaga ta barka da amarya kuci soyayya yadda kuke so.
Wani soyayya banda rashin hankali da yarinyar nan take zuba mini, gidana ya fita hayyacinsa saboda ƙazantarta taƙi gyarawa wai dole sai dai na ɗaukar mata masu aiki ita ba zata iya ba.
Nan Hamid ya shiga koro masa matsalolin Madina har kawo yau data ƙullawa Hajiya sharri, ya ƙara da cewa.
Wlh ban taba zaton haka daga yarinyar nan ba, kwata kwata aure wata ɗaya da kwanaki amma na susuce duk ta fice mini a rai, ganin yadda kake yabon Kausar da iya mu’amalarta shi ne ya ƙara kwaɗaita mini aurenta ashe ba halinsu ɗaya ba.
Gaskiya kam Kausar ɗita tana da tarbiyya da sanin ya kamata, kuma tun farko Hamid baka gida auren nan za kayi shi domin Allah ba shiyasa Allah ya jarabceka. Ka kasa yiwa Sakina adalci son Madina ya rufe maka ido baka ji baka gani.
Wlh Abokina nima nasan nayi kuskure, amma koma miye da laifin Sakina.
Laifinta name? matar da bata hanaka ƙarin aure ba bata ɗaga maka ha kali ba, tayi haƙuri da duk wulaƙancinka, ka kasa daidaita adalci a tsakaninta da Madina, nunawa fa kayi Madina ta fita sau dubu, matar da kuka shafe shakaru goma sha amma lokaci guda ka ke ganin baƙinta. To karma kace laifinta ne ba ruwanta dan bata yi maka wani mugun abu ba, hasalima kaine kazalunceta shiyasa Allah ya saka mata tun ba ayi nisa ba. Duk abinda ya faru lafin son zuciyarka ne idan kuma zaka gyara wannan kai kaso.
Ya zaka ce haka? kai da na kira ka bani haƙuri da shawara.
To me kake so na faɗa maka bayan lokacin baya ina ta nuna maka kayi adalci idonka ya rufe, Sakinar dai da kake kushewa ita ce matar rufin asirinka ko kaƙi ko kaso.
To yanzu Habib ya zanyi? Har yanzu ba asan ina taje ba.
Ni nasan In Sha Allah tana cikin natsuwa taje ta huta ne da matsalarka daka ƙunsa mata.
Hamid zai yi magana wayarsa tayi ƙara, sai ya ga yaya Hamza ne da sauri ya ɗaga suka gaisa, kana Hamza ya tabbatar masa da an samu labarin Sakina tana Kano dan haka gobe zasu je su ɗaukota, a zabure ya miƙe yana cewa.
Alhamdulillahi, ai ina ganin nima zan shiryo mu tafi tare in bata haƙuri ta dawo.
To Allah ya kaimu goben da wuri zamu fita dan muje mu dawo a ranar.
Daga haka suka yi sallama, Hamid ya koma ya zauna yana dariyar farin ciki.
Habib anga Sakina ashe tana Kano gidan yayarsu Jalila.
Dama nace maka tana nan cikin kwanciyar hankali, dan haka sai ka sauke duk wani girman kai ka bata haƙuri ka dawo ku gyara gidanku. Ka kuma tabbatar da adalci a tsakanin su.
In Sha Allah zan gyara domin a ɗan kwanakinan na tabbatar Sakina tanada matuƙar muhimmanci a rayuwata, ba kaga har rama nayi ba saboda bana samun cin abinci mai kyau irin nata, kullun a rastuarant nake ci.
Haba angon Madina ina kabar girkin amarya.?
Kai dalla ana maganar girkin arziki kana kawo nata, ai wlh ko a mafarki bana tafan na kuma cin girkin Madina, In Sha Allah in dai Sakina ta dawo to dolen Madina ta je makarantar koyan girki, dan bazan taɓa yarda da girkin masu aiki ba.
Hamid kenan a dai kiyaye adalci kar kuma yanzu ka juyawa Madina baya ka koma gurin uwargida dan na san halinka.
In Sha Allah ba zan kuma aikata kuskuren baya ba.
To Allah yasa.
Hamid yace Amin kana suka cigaba da tattaunawa a tsakaninsu.
Hamid daya koma gida bayan sallar Ishai, ɗakin Madina ya wuce domin yayi alƙawarin gyara alaƙarsu kafin dawowar Sakina, dan ya ɗauki niyyar kamanta adanci a tsakaninsu. Madina tana kwance lamama akan gado abin duniya ya isheta ga ɗaki kaca kaca ga jibgin kayan wanki data aje a gefe bata kwashe ba, Hamid yana tura ƙofa tsamin ɗaki ya fara yi masa sallama, haka ya daure ya Shiga da sallama, cikin sauri Madina ta tashi ta zauna tana dubansa, ya sakar mata murmushi yana cewa.
Da girman kujerarki gimbiya Madina to na kawo kaina mu shirya.
Madina sai hawaye dan farin ciki gabaɗaya ta bayar da aikin malam ne ya fara kama Hamid tunda gashi ba aje ko ina ba ya kawo kansa, sai ta shagoɓe fuska ta soma cewa.
Bayan ka daina sona.
Taya zan daina son ki Madinar Hamid, kawai dai ke ɗin ce bakya jin maganata yanzu, ji ɗakinki yadda ya koma kamar ba amaryar wata guda da kwanaki ba.
Madina ta juya tana kallon ɗakin ita kanta tasan ta hargitsa shi dan akwai akwati biyu data saukesu tana ɗibar kayan ciki ta aje a gefen gado bata ma rufe ba balle ta mayar dasu mazauninsu, Cikin shagoɓa take cewa.
To ai nace maka ni ban iya aikin gida ba amma baka yarda ba, ni dai dan Allah ka samar mini ‘yar aiki.
Ya zanyi dake dole na samar miki domin bazan jure ganin gidana a hargitse ba, sai ki nimo mai kirki amma fa banda girki dan wlh dole kije ki koyi girki ki riƙa yi mana.
Wayyo daɗina, Dagaske ka yarda zaka ɗaukar mini ‘yar aiki.?
Dawasa zanyi miki zancen? sai dai ban yarda wata ƙazama ta gyara mini ɗaki ba ta dai tsaya a iya sashinki da kuma falo da kitchen.
Nagode farin masoyi Allah ya saka da akhairi.
Madina ta faɗa tana isa gareshi ta rungumeshi, sai dai tsamin daya ji a jikinta ya sashi saurin tureta yana cewa.
Ina ganin ƙila sai an nima maiyi miki wanka ko? Madina kinji yadda jikinki ke hamami anya kina wanka mai kyau kuwa, ga sumarki nan duk ya hargitse ke baki yi kitso ba ba ki kuma gyara ba.
Kai Habib Allah nayi wanka tun safe, ina ga kaina ne ke tsami dan tun biki yake a haka.
Allah ya kyauta da amala kinci sunanki ƘAZAMAR AMARYA, award ya rage na baki kawai.
Ya faɗa yana ‘yar dariya, murguɗa masa baki tayi tana cewa.
Allah ni ba ƙazama bace kawai dai ni nace maka ban iya kula da gida ba kuma a hankali zan koya.
Ai har kanki baki iya kula da shi ba balle gidan, ni bari naje nayi wanka ina zuwa.
To in ka fito zamu je muci abinci a waje.
Ya zanyi dake dole mu fita tunda gidan a hargitse yake ni duk kyankyani ma ya cikani.
Ya faɗa yana ficewa, da harara tabi bayansa tana jan guntun tsaki.
Da sannu zanyi maganika domin yanzu ne na kama hanyar data dace dani.
Sai ta shiga kawar da kayan ɗakin tana mayar da abubuwan da suke ba a muhallinsu ba.
….
Washe gari da wuri Hamid ya bar gida yace aiki zai fita bai faɗa masa in da zashi ba, har mota ta rakashi dan jiya dai sun raya daren amma fa sai da Hamid ya litasta tayi wanka ta wanke baki dan wlh ji yayi ba zai iya kusantarta ba sai ta gyara jikinta. Bayan ya wuce ta koma cikin gida ta shiga kiran momynta, koda ta ɗaga sai tace ta turo mata Ladi mai aikinta tazo gidanta ta gyara mata shi zata barshi a buɗe kafin ta dawo aiki har girki tayi mata me daɗi, momy tace zata turota nan Madina ta bata labarin sauyawar Hamid, ba ƙaramin daɗi itama taji ba tace In Sha Allah magani ya fara aiki, Madina dai dariya tayi dan tasan maganin matar nan da momy tasa ayi bai yi aiki ba sai na malamin da suka je da Maman Murja, tace ta samar mata yar aiki ɗan yace ya amince momy tace tunda masu aikinta mutum biyu ne to Ladi zata so ta cigaba da aikin anan sai suyi mata biya mai kyau.
Amma yace baya son mai kwana.
To ai ba damuwa Madina In ta gama miki aiki sai ta dawo nan ta kwana tunda dama anan take da zama.
Cewar momy, Madina tayi mata godiya kana suka yi sallama. Madina bayan ta yi shirin aiki gidan Maman murja ta tafi suka yi magana, sosai mama Murja ta ƙara koɗa aikin malam tace ai haka aikinsa yake ci nan da nan, tace mata in ta dawo zata shigo haka duka rabu ta tafi aiki.
*****
Kano.
Da wuri Sakina suka bar gida da kayanta kala biyar a cikin ƙaramin jaka, saloon Ra’isa ta fara kaita nan fa aka shiga gyaran kan Sakina tana jin abun sabo a gareta, anan ne taji wasu mata suna maganar kyan maganin BOJUWA HERBAL’S BY SURAYYA. Ɗayar tana cewa.
Wlh tunda nayi amfani da kayanta nayi bye bye da cutar sanyi, ga kuma sauran kayan gyara dana sha ya saukar mini da ni’ima da ɗanɗano mai daɗi, ke wlh tun kafin na fara sanin aikinsu a jikina na tabbatar da na samu sauyi, ranar Alhaji har da sambatu yayi mini ya dinga saka mini albarka, shiyasa ba wasa na ƙara kama kayan BAJUWA HERBAL’S dan ance siyan na gari maida kuɗi gida kuma tabbas ni na mayar da kudina har naci riba.
To Maman Nusaiba dame dame suke sayarwa ne nima naje a dama dani.
Suna kawo Saiwowin sanyi, da maganin sanyi. Saiwowin dahuwar kaza, dafaffiyar gimbiyar kaza. Silky kola na musamman. Tsumin sababi. Hakkin daka gangariya. Gumba special. Gaban ayu. Dukkan Saiwowi da kayan daga Chad suke zuwa da su. Ga number ɗinta ki tuntuɓeta in kin shirya kuma ganinsu akwai sauƙin rahusa. 08032773332 Surayya HALIN YAU.
Nan Sakina ta saka musu baki a cikin hirar tana cewa.
Aiko nima na gwada kayanta kuma naji sauyi sosai a jikina tun kafin me gida ya shaida, ya kamata kema ki gwada.
Nan fa suka cigaba da tattaunawa har aka gama mata gyaran, Ra’isa ta sallami mai saloon suka yiwa matan nan sallama suka tafi gidan mai gyaran jiki. Suna isa Ra’isa ta barta anan ta wuce makaranta.
Wajen ƙarfe goma sha ɗaya motar su Hamid ta sauka a ƙofar gidan Anty Jalila, dan da motarsa suka yi tafiyar shi da Yaya Ali a gaba sai Umma da Hamza a baya, suka sauka suka shiga buga gate, mai gadi ya buɗe musu dama tuni Jalila ta sanar dashi da za suyu baƙi, ya shiga gaishe su Umma ce tayi gaba domin ta fara sanar da Jalila sun zo, sai ta sameta a falo cikin shiga ta alfarma, tana ganin Umma ta miƙe.
Lale mutanen Kaduna, sannunku da zuwa. Ina sauran tawagar naku dan nasan ba zaki zo ke kaɗai ba.?
Umma dariya tayi tana cewa.
Na shigo in fara sanar dake tukuna kafin su shigo da har da mijinta muka zo.
Ehhh lallai abin babba ne to kice musu su shigo.
Jalila ta faɗa tana komawa ɗaki ta saka babban gyale ta fito, suma a lokacin suka shigo duk suka zauna aka fara gaishe gaishe, daga bisani Ali yace.
Kin kyauta Jalila da abinda kika yi mana, baba yace zaki zo ki same shi.
Murmushi tayi tana cewa.
Ai abinda kuka kasa yi ne ni nayi muku dan haka bani da laifin komai mutuncin yarinya na kankaro mata.
To ina Sakinar?
Cewar Hamza, Hamid kam ya baza ido yaga ta ina zata fito shi duk ya ƙosa ma ya ganta, bai taɓa zato wai dama yana son Sakina har haka ba sai yanzu, maganar Jalila ce ta dawo da shi hayyacinsa tana cewa.
Sakina bata nan tunda taji kunce zaku zo tace wlh bazata biku ba dan bata shirya komawa gidan Hamid ba, shine ta tafi gidan wata aminiyata ta ɓoye.
Wannan ai zancen banza ne, aiko dole ki fito da ita dan ba zamu bar garin nan ba sai tare da ita.
Cewar Ali, Umma tace cikin ɓacin rai.
Haba yaya Jalila ya zaki biye mata ai da baki barta ta fita ba.
Sakina fa ba yarinya bace ku kyaleta ta yankewa kanta hukuncin data ga ya dace, ita kaɗai tasan gashin ƙumar da take kunsa a gidanta, dan haka ku barta ta yi abinda ya dace akanta na tabbatar har yanzu bata gama hucewa bane shiyasa, kuma nima ina ta bata baki har ta sauko ta amince ta koma gidanta.
Dan Allah da son maikin Allah ki kirata ta dawo na bata haƙuri, wlh Hamid ɗin data sani a baya ba shine a yanzu ba nayi mata alƙawarin sauyawa.
Cewar Hamid cikin damuwa.
[8/8, 5:25 PM] Rahma Kabir: *ƘAZAMAR AMARYA*
Na
©®Rahma Kabir MrsMG.
Wattpad @rahmakabir
Page 31.
Jalila tayi murmushi tace.
Bari na kira kuji.
Nan ta kira ƙawarta dama kuma sun gama haɗa komai ɗazun, data ɗaga tace ta haɗata da Sakina, sai matar ta miƙa mata Jalila tace.
Sakina ga su fa sun zo tafiya dake dan Allah kiyi haƙuri ki yarda ki koma ɗakinki.
Yaya Jalila ki faɗa musu wlh bazan koma gidan Hamid yau ba dan zuciyata bata gama warkewa daga baƙin cikin daya ƙunsa mini ba, shiyasa na zaɓi zuwa gidanki dan hankalina ya kwanta tunda ko naje gida mayar dani zasu yi ya cigaba da ƙunsa mini baƙin ciki, kuma ai da bakinsa yace na tafi gida sai ya nimeni in da yuwuwar ya cigaba da zama dani.
Yuf Hamid ya amshe wayar daga hannun Jalila data saka handsfree suna jin maganganun Sakina, Ya shiga magana cikin damuwa.
Wlh Sakina na sauya kuma a ranar damuka dawo daga asibiti dama nayi niyyar nace karki tafi gida muyi sulhu, amma sai na tadda kin tafi, dan Allah ki dawo mu tafi yaranmu dani muna buƙatarki.
Hamid kenan.
Abinda Sakina ta iya faɗa kenan ta kashe wayar. Hawaye taji yana bin kuncinta wanda bata tantance na farin ciki bane ko akasinsa.
Hamid jiki ba kwari ya koma ya zauna yama kasa magana, suma shuru suka yi suna tunanin zucci, Jalila ta miƙe ta shiga fito musu da abinci dan Sakina ta girka sai Ra’isa ta taya ta, data gama ta zubawa Umma ta kama hannunta suka koma ɗakinta, Hamid ƙamshin abincin daya ji ma ya tabbatar Sakina ce ta girka, Hamza da yaya Ali suka buɗe ciki suka kwashi girki Hamid kam bai iya ci sosai ba saboda damuwa.
Jalila bayan umma ta kammala cin abinci ta korowa Umna bayanin komai, tace kuma nan da sati daya In sha Allah Sakina zata dawo, duk ta faɗa mata plan ɗinsu akan su ɗan bawa Hamid wahala yadda gaba ba zai sake sha’awar yace taje gida ba ko ya cigaba da yi mata wulaƙanci, umma ta gamsu sosai dan itama ba zata mance marin da Hamid yayiwa Sakina a gabansu ba, ya dace ya karɓi hukunci yasan muhimmancinta, dan haka bayan sun fito tace wasu yaya Ali ya kamata su juya dan bada shirin kwana suka zo ba, Hamid yace shi ba zai koma ba sai da Sakina, dan haka har tasha ya kai su ya ɗaukar musu drop ya biya kuɗin mota ya juya cikin gari. A hanya Ali yake cewa.
Ai gwara Sakina ta wahal da shi ko yasan muhimmancinta.
Umma tayi murmushi sai ta basu labarin yadda suka yi da Jalila, duk suka amince suka ce gwara a gwara kansa bazai sake yi mata riƙon sakainar kashi ba. Hamid wani super market yaje ya siya ƙananun kaya riga da wando kala uku da kuma sauran kayan buƙatarsa ciki harda turare da da mai, tafiya ce da ba shiri dan bai yi tsammanin kwana ba amma tunda abu yazo a haka dole ne ya yi shiri dan yana so ƙafarsa ƙafar Sakina. Daga nan ya wuce wani hotel mai kyau ya kama ɗaki, sai da ya samu natsuwa kana ya kira Hajiya yayi mata bayanin komai yace ta sanar da alhaji, Hajiya ta ja guntun tsaki.
Da alama Hamid so kake ka zama shanyayye, gabaɗaya ka sama sususu sai kace wani mara mafaɗi, tunda an san ga inda take kuma kaje tace ba zata dawo ba, to ba sai ka rabu da ita ba in ta gaji zata dawo dan kanta, wannan ai ka bata ƙofar rainaka ne.
Hajiya nine nayi mata laifi dan haka yana da kyau na gyara kuskurena, ni dai ina so kiyi mana fatan Alkhairi, duk yadda ake ciki zan sanar dake ki gaida Abba.
To shikenan tunda haka ka zaɓarwa kanka Allah ya kyauta sai anjima.
Cewar hajiya cike da takaici kana ta kashe wayar tana jan guntun tsaki, shi kam Hamid ya saba da haka bai wani da mu ba, shi ya sara me Sakina take yiwa Hajiya ta tsaneta har haka, sai yanzu ya ƙara hango Hajiya ma ta bada gudun mawa a matsalar dake tsanninsa da Sakina, kuma lokaci yayi da zai gyara kuskurenta ya riƙa riƙe sirrin gidansa a zuciyarsa ko hakan zai kawo daidaito da maslaha a zamantakewarsu. Nan ya kira Madina yake sanar da ita yayi tafiya zuwa Kano kuma zai kwana biyu, sai tace ita ba zata iya zama ita kaɗai a gidan ba dan haka gidansu zata koma, bai yi mata musu ba dan yasan ko yace karta je ba saurarensa zata yi ba, to kawai yace mata sai ya kashe wayar ya tura mata da kuɗi dubu ashirin, Madina tana ganin alart ta saki murmushi tana jin farin cikin yadda in ta yiwa Hamid magana baya yi mata musu, sai ta kira Momy akan Ladi ‘yar aikinsu ta zauna ba sai tazo ba itama gida zata zo anjima saboda Hamid yayi tafiya, momy tace mata to kana suka aje wayar momy tasa a gyara mata ɗakinta.
Bayan ta bar wajen aiki gida ta dawo ta haɗa kaya kala biyu da tarkacenta cikin wata jaka sai ta fito dashi falo ta aje, ta fita gidan Maman Murja ta bata cikon dubu hamsin da malam yace ta bata ta ɗaura da cewa.
Wlh naga sauyi sosai game da Hamid gaskiya aikinsa Masha Allah, yanzu zanje gidanmu nayi kwana biyu saboda yayi tafiya, inna dawo zan zo muje domin ina so ayi mini aiki tsakaninsa da iyayensa, dan so nake sai naci Uwar Hajiyarsa son raina na nuna mata ni ba kanwar lasa bace.
Da kyau ta wajena lallai kin hau kan layi sosai, ai wlh Hajiyarsa ba tada kirki dan ba ƙaramin takurawa Sakina tayi ba, kuma kinga yanzu ba Sakina dole kanki zata dawo ta saki a gaba.
Ai ni nafi ƙarfinta dan wlh ba ƙaramin shiri zanyi akanta ba, sai na nuna mata ni ba irin Sakina bace kidahuma.
Wannan gaskiya ne ki nuna mata da bambanci yadda take hawan jini ke kuma ciwon ido zaki zame mata.
Faɗi ki ƙara, ina godiya sosai maman Murja naji daɗin haɗuwa dake.
Cewar Madina cike da farin ciki, nan ta ɓata lokaci suka sha hira daga bisani tayi mata sallama akan sai sunyi waya ta fito ta tafi, tana shiga gida ta ɗauki jakan kayanta ta fito ta tayi gaba, tun tana hanya Kausar ke kiranta amma bata ɗaga ba sai da ta isa gida ta samu momy bata nan, dan haka gado ta haye ta kwanta kana ta bi kiran Kausar, bayan ta ɗaga sun gaisa Madina tace.
Ni nayi fushi kinata waƙar zaki zo amma shuru tun biki baki leƙo ni ba.
Shiyasa ashe kwana biyu kike basar dani ko chart nayi miki sai kin gadama kike amsani, wato miji daɗi har kin fara sauya hali, to daɗin abin nima da mijina balle naji haushi haka.
Ke banza meye na koro wannan zancen sai kace kin haɗiyi radio, yaushe kike gida dan daga gurin aiki zan zo gidanki saboda Hamid yayi tafiya ina gida.
Dan yayi tafiya saiki koma gida? lallai kina juya Hamid son ranki, me kika taka haka ne.
Babu abinda na taka sai zallar soyayya da nake bashi, kuma kinsan gidan ba kowa shiyasa nace gwara na dawo gida.
To in hakane gobe zanje gidan yayar Habib ɗiyarta ta haihu daga can zan biyo nan gida, kinga na gaishe da momy tunda rabona da gidan ku tun biki.
Shiyasa nake sonki ƙawata sai kinzo amma ki tawo mini da abu mai daɗi.
Uwar kwaɗayi.
Kausar ta faɗa tana dariya tare da kashe wayar, Madina dariya tayi itama tana jin daɗin ƙawancensu, duk cikin kawayenta babu wacce ta shaƙu da ita irin Kausar sai dai kuma halinsu ba daya ba, Madina tunawa da tayi da gargaɗin maman Murja akan ta ɓoye sirrin abinda take yiwa mijinta yasa ta fasa faɗawa Kausar komai da da tayi niyya, karma ta faɗa mata tayi hirar da Habib asirinta ya tonu dan haka tayi alƙawarin riƙe maganar ko momy ba zata faɗawa ba tunda dai buƙatarta ta biya, ba ita ta miƙe ba sai da aka fito sallar magrib, wanda duk kasala ke damunta wanda ta bayar ko gajiyar aiki ne, kuma kusan kwana biyu kenan data fara jin haka ga yawan kwaɗayi da tara yawu a baki, yanzu ma miyau ne ya cika mata baki ta fetsar da shi a bango tana jan guntun tsaki, ita kanta ta fara gajiya da tara yawun tana so ta koyi dainawa tunda Hamid baya so. Ta shiga bayi tayi alwala ta tayar da sallah, a lokacin ne momy ta dawo Madina data idar ko addu’ar kirki bata yi ba ta fice da saurinta cike da farin ciki dawowar momy.
*****
Bayan kwana huɗu.
Hamid duk yayi yadda zai yi dan ganin ya haɗu da Sakina amma abun ya ci tura gashi company da business ɗinsa na motoci suna buƙatarsa, kiran da Abba yayi masa ne ya katse masa tunani ya ɗaga cikin sanyin jiki suka gaisa.
Hamid duk abunda kake ka dawo kazo ka kula da harkokinka tunda har ansan in da Sakina take na tabbatar zata dawo da zarar ta huce.
To Abba In Sha Allah, yau dama nake saka ran dawowa, yasu Hajiya?
Sunanan lafiya, sai ka kamo hanya da wuri tunda yanzu ƙarfe tara da wani abu na safe.
In Sha Allah dama na gama shiri can gidan yayarta zani muyi magana sai na tawo.
To madalla Allah ya tsare hanya.
Hamid yace amin kana ya kashe wayar ya miƙe tare da ɗaukar jakar baya daya siya ya saka kayansa, ya fito ya sallami hotel ya shiga motarsa ya mufi gidan Jalila. Da yake ya zama ɗan gida yana isa falon ya nufa ya kwankwasa, Ra’isa ta buɗe tana ganinsa ta gaishe shi cikin girmamawa ya tambayeta mamanta tace tana ciki, kana tayi masa iso cikin falon ya samu guri ya zauna, ba jimawa Jalila ta fito ta zauna suka gaisa sannan Hamid yace.
Dama na zo na sanar dake zan koma yau tunda nayi duk yadda zanyi kinƙi bayyana mini in da Sakina take, dan haka ina mai ƙara bada haƙuri a yafe mini In Sha Allah abinda ya faru a baya bazan bari ya kuma faruwa ba.
In Sha Allah nayi maka alƙawarin a cikin kwanakin nan zan dawo maka da Sakina da kaina, tun shekaran jiya nake faɗa maka haka kuma bazan karya alƙawarin dana ɗauka ba.
Nagode sosai Allah ya saka da alkhairi ni zan wuce a gaida Alhaji in ya shigo.
Zai ji Insha Allah Allah kuma ya tsare hanya ya saukeka lafiya.
Ya amsa da amin kana ya ajiye bandir ɗin kudi dubu ɗari a center table.
A bawa Sakina nasan tana buƙatar kuɗi a hannunta.
Sai ya ƙara ƙirga dubu talatin ya ajiye kusa dana Sakina.
Wannan kuma a bawa yara ‘yan makaranta. Nagode.
Muma mun gode Allah ya ƙara arziki.
Anty Jalila tace shi kuma ya wuce ya bar falon, sosai ya bata tausayi dan taso ace yadda yayi kwanakin nan ace tare ya tafi da matarsa, to amma bata gama shirya Sakina ba dan tana buƙatar su shiga kasuwa tayi mata siyayya, gashi ma ya bada kuɗi akan gaɓa, dan haka zata yi ƙoƙari cikin kwana biyu su gama koma ta taso ƙeyar Sakina ta koma gidanta hankalin kowa duk sai ya kwanta.
****
Hamid.
Wajen ƙarfe Sha biyu ya isa Kaduna, dan haka Masallacin Juma’a ya fara tsayawa aka yi sallar Juma’a dashi kana ya nufi gida danya yi wanka ya sauya kaya ya fita company. Koda ya iso gida ransa in yayi dubu toya ɓaci dan yadda ya barshi haka ya dawo ya sameshi ya ƙara yin ƙura.
Wato yarinyar nan bata tsaya ta gyara gidan ba ta tafi gidansu.
Ya ƙare maganar yana jan tsaki, yana a tsaye ya lalubo number ɗinta ya kira, data ɗauka sai ta rigashi da cewa.
Masoyi ina shirin kiranka sai gashi ka kirani yau ko aiki ban samu zuwa ba ina fama da zazzaɓi.
Madina yanzu ya dace ace na dawo gidana na taddashi a haka? ashe baki saka an gyara ba kika tafi gida, ina ce na ce ki ɗauki ‘yar aiki, wannan ai wulaƙanci ne nazo na ga haka.
Haba Hamid ina ce maka bani da lafiya kana yi mini ƙorafin gidanka, ai dama na bari in ka dawo sai muzo da mai aikin ta gyara gidan, kuma ya dace tun kafin ka taso ka sanar dani, da ka faɗa ai ba zaka samu gidan a haka ba.
Hakama zaki ce mini.?
To ya kake so nace maka ka rufeni da faɗa sai kace wata ‘yarka, to sannu sarkin tsafta komai aka yi maka ba kada haƙuri ka riƙa yiwa mutane mita.
Hmmm ya iya cewa sai ya kashe wayar gabaɗaya saboda takaici, Madina ta kuma kira yaƙi ɗauka, ta kira ya kai sau uku duk bai ɗaga ba sai ta tura masa da saƙo.
Beb kayi haƙuri anjima zan tawo tare da mai aikin sai ta gyara gidan, kuma nace maka banda lafiya ko kace mini ya jiki kaji meke damuna.
Koda ya karanta tsaki yaja ya fito zuwa motarsa ya zauna ya kira Habib yana tambayarsa ko yasan company da zai kira suzo su gyara masa gida, yace bai sani ba amma ya shiga Instagram yayi searching ba zai rasa samu ba, yayi masa godiya suka yi sallama sai ya shiga Instagram da ya jima bai hau ba, shi sam chart bai dame shi ba sai ma daya haɗu da Madina ne ta sabar masa da yi, cikin ikon Allah yana bincikawa ya samu nan ya ɗauki number ɗinsu ya kira sai dai an samu akasi su a Jigawa suke amma da yake suna da contact ɗin masu irin aikinsu saboda irin haka koda ya taso suka bashi na nan Kaduna, cikin kankanin lokaci Hamid ya yi magana dasu suka ce zasu zo washe gari asabar su yi aikin, nan suka bashi bayanin komai yadda zai tura musu da kuɗinsu, bayan ya gama dasu sai ya wuce sashin su Hajiya ya samu Alhaji bai dawo daga masallaci ba, ya zauna a falo yana kwalawa Jidda kira, da saura ta fito daga ɗakinta tana amsawa.
Read Als Here Labarain kanny word
Kawu sannu da zuwa ya hanya.
Lafiya lau Alhamdulillahi
Me muka dafa a gidan?
Tuwon shinkafa miyar taushe.
Zuba mini ki haɗo da ruwa mai sanyi.
To, mun yi zoɓo a haɗo maka da shi.
Yauwa haɗo dashi.
Sai ta wuce shi kuma ya gyara zamansa ya jingina bayansa a jikin kujera.
[8/9, 9:47 PM] Rahma Kabir: *ƘAZAMAR AMARYA*
Na
©®Rahma Kabir MrsMG.
Wattpad @rahmakabir
Page 32.
Hajiya ce ta fito falon fuskarta ɗauke da murmushi.
Hamid kasha hanya, da fatan ka dawo lafiya, Allah yasa Sakinar ta biyo ka.
lafiya lau kuma na barta zata zo tare da yayarta, na sameku lafiya?
Lafiya lau Alhamdulillahi, amma kuwa ya dace ace ta biyo ka yadda ka ɓata kwana huɗu a can kana biko.
Hajiya bata gama shirye shirye bane shiyasa.
Wane shiri? ita ba Amarya ba, ba sabon aure zata yi ba, kawai dai su wulaƙanta ka ne suja maka rai saboda ka kai kanka, shiyasa naso ka rabu da ita ta dawo da kanta, gashi satin nan yara zasu koma makaranta.
Shiyasa nake tunanin gobe In Sha Allah zanje na ɗauko su ni zan kula dasu in ya so in zan fita sai su zo nan sashin.
To ba damuwa gwara su dawo ɗin Allah ya kaimu. To ya ita wannan sakaryar fa ta dawo ko tana can gidansu?
Tana can anjima tace zata dawo.
Allah ya kyauta ya kuma baka haƙurin jure halayyar matanka dan duk baka yi dace ba.
Amin Hamid yace yana jin ba daɗi a zuciyarsa, ya rasa me yasa Hajiya ta kasa gane Sakina ba tada matsala tafi Madina mutunci, koda yake shima yana da laifi dan yawan ƙorafin daya ke kawo mata yana ɗaya daga cikin dalilan daya saka ta tsaneta, kuma zai yi ƙoƙarin gyara hakan.
Sai wajen kiran sallar magrib Madina ta kira Hamid akan yazo ya ɗauketa ba zata iya dawowa da kanta ba, saboda haushi ma cewa yayi ta kwana a gida da safe ta dawo ya kashe wayarsa, can sai ga text ta turo masa.
Wai masoyi fushi kake yi dani dan Allah kayi haƙuri bana son haka, kuma nace maka bana jin daɗin jikina amma baka nuna damuwarka ba ko dai ka daina sona ne.?
Koda Hamid ya karanta saƙon guntun murmushi yayi.
Madina kenan ga ban haƙuri ga ban haushi.
Ya faɗa a zuciyarsa tare da sauke gauron numfashi sai ya tura mata da reply.
Saboda jikin naki nace ki kwana dan nima a gajiye nake bazan iya fita da mota ba, Allah ya ƙara sauƙi, amma kin sha magani, ko sai kinga likita tukuna? gobe In Allah ya kaimu in kin dawo sai muje a dubaki.
Ya aje wayar Madina murmushi tayi da ganin saƙonsa, tasan duk in tace ko ya daina sonta ne to yakan yi abinda zai nuna yana sonta ɗin, kamar zata sanar dashi ciki gareta dan momy da kanta take faɗa mata da wuya ba shi bane yadda ta ƙara haske da kuma ɗan ƙiba, sannan ga yawan zubda yuwu da kwaɗayi, shiyasa ɗazun ta siyo pt strip taga ya nuna mata positive, amma sai ta fasa faɗa masa dan tafi so su kasance a yanayi mai kyau saita faɗa, wataƙila ma har kyauta zai yi mata kamar yadda take jin labarin wasu mazan suna yi, babban tunaninta ma ya bata motar da yayi mata alƙawari.
***
Da safe masu gyaran gidan Hamid suka zo, maza da mata kusan su bakwai, cikin kwarewa da iya aikinsu suka gyara masa gidansa har da farfarjiya suka share, sai dai ɗakin Madina yace kar su taɓa iyaka nashi dana Sakina sai na yara sannan falo da kitchen suka gyara, nan da nan gida ya dawo hayyacinsa, ya sallame su suka wuce sai ya yi wanka tare da kiran yaya Umma ya faɗa mata zai zo ya kwashe yara saboda monday zasu koma makaranta, ta tambaye shi Sakina yace yaya Jalila tace zata kawota cikin kwanakin nan, a haka suka yi sallama sai ya shiga gidan Hajiya suka gaisa daga nan ya fito ya wuce wajen sayar da motocinsa. Sai bayan La’asar ya samu damar zuwa ɗibo su Mufeeda suka dawo gida, da ihu suka shiga falo wanda yasa Madina saurin fitowa daga ɗaki tana dubansu, dama tun ƙarfe biyu suka shigo gidan tana mamakin ganin yadda aka gyara ko ina amma banda nata, ta shiga fargaba sosai da tunanin ko Sakina ce ta dawo, haka dai ta danne yanayin da take ji ta nunawa Ladi aikin da zata fara yi mata na gyaran ɗaki, in yaso washe gari in Allah ya kaimu tayi mata wankin. Turus tayi ganin yaran ga Hamid ya shigo tana binsu, Hamid da fara’ansa ya ƙaraso gabanta yana cewa.
Mara lafiya ya jikin ashe kin dawo?
Eh ɗazun na dawo naga gida a gyare ko mamansu ta dawo ne?
Ta faɗa tana dubansa, Hamid ya yi murmushi.
Wato kinsan ita ce mai gyara min gida ko, to bata dawo ba company na kira suka zo suka gyara na biyasu, yara kuma na ɗauko sune saboda ranar monday zasu koma makaranta.
To waye zai kula dasu?
Allah daya haliccesu shi ne mai kulawa dasu, kuma ina da Hajiya ga kuma ni yarana ba zasu tagayyara ba. Karki wani damu ko kashin Rauda bazan ce ki wanke mata ba. Ke Mufeeda ku shiga ɗaki ku aje kayanku kuzo muje gidan Hajiya.
Hamid ya ƙare maganar cikin haɗe rai dan ba ƙaramin haushi Madina take bashi ba yadda take nuna kin yaransa ƙiri ƙiri, sai ya juya ya wuce ɗakinsa dan ya rage kayan jikinsa, Madina ta bishi ganin sauyawarsa ta tsaya a jikin ƙofa tana ce masa.
Nifa bawai bana son yaranka bane Hamid, kawai ban iya ɗawainiyar yara bane shiyasa.
To kema da baki iya riƙe ɗawainiyar kanki ba taya zan damu dan baki yi na yarana ba. Dan haka karki wani damu sai dai ina tunanin naki yaran in kin haihu waye zai kula miki dasu? tunda baki iya kula da ɗan kowa ba.
Kafin lokacin ƙila zan koya, kuma kasan ina da mai aiki zata taya ni.
Hakane.
Ya bata amsa a takaice, sai ta isa gefen gadonsa ta zauna.
Beb shine baka saka an gyara mini ɗakina ba banyan biya kayi aka gyara gidan.?
Saboda kin samu mai aikin da zata yi miki, niko babu mai yi mini ko yarana. Anjima ki shirya zamu je asibiti likita ya duba ki.
Ni naji sauƙi.
Ta faɗa tana turo baki dajin haushin maganarsa, bata kuma magana ba shima bai yi ba har sai da ya gama shiryawa cikin jallabiya ya kalle ta sai kuma yaga ta bashi tausayi ya koma ya zauna yana dubanta.
Menene kuma kike ɓata fuska?
To ba kai bane?
Ta faɗa cikin shagoɓa, Hamid yayi murmushi yana son wannan shagoɓar tata yace.
To shikenan komai ya wuce yanzu me zaki ci? sai na haɗa nayi mana oder da yara, mai aikinki kuma zata tafi ba kwana zata yi ba ko.?
Eh mai aikin gidanmu ce momy ta bani ita anjima zata wuce in ta gama aikin.
To yayi, in kuma ta iya girki sai ta yi miki kici mu kuma mu ci a gidan Hajiya.
To shikenan tuwo nake son ci bari zansa ta girka mini, amma ina son ice cream da cake.
Angama gimbiyar Hamid yanzu kije ki shirya kanki kiyi kyau sosai, anjima zamu je mu siya ice cream ɗin tare, yanzu bari na kai yara gurin Hajiya.
Da murmushi sosai a fuskarta tace masa to har tana kama hannunsa ta manna masa kiss.
Nagode Hamid ɗin Madina ina sonka sosai.
Nima ina sonki Ƙazamar Amaryata.
Allah ni ba Ƙazama bace.
Ta faɗa tana turo baki dariya yayi ya fice yana cewa.
Wani zaki faɗawa wannan ya yarda amma banda Hamid ɗin Madina daya sanki ya wayeki kamar hanjin cikinsa.
Dariya sosai itama tayi ta biyo bayansa, akan idonta ya tasa ƙeyar yaran suka wuce ita kuma ta koma ɗaki gurin mama Ladi.
Hamid yana shiga sashin Hajiya da yara ta fito daga kitchen saboda hayaniyarsu da ta ji, da fara’a ta ƙaraso.
Hamid wai harka kwaso su?
Eh bamu daɗe da shigowa ba nace su zo su gaisheki.
Hajiya ta zauna a cushing yaran duk suka zauna a carpet suna gaisheta ta amsa fuska sake har tana zolayarsu, daga bisani tace suje suyi wasa su basu guri, yaran suka fice farfajiyar gidan Hajiya ta mayar da dubanta ga Hamid.
Kai Hamid ka kwaso yara mamansu bata dawo ba kasan dai wannan mahaukaciyar amaryar taka ba iyawa zata yi da su ba ko.
Eh dama ganin Monday zasu koma makaranta yasa da ɗaukosu sannan ai yaya umma tayi ƙoƙari dasu kusan wata guda fa suna gidanta, shiyasa na ce gwara su dawo ni zan kula dasu tunda Mufeeda ta iya wasu ayyukan in yaso abinci sai a riƙa girkawa damu na makaranta kuma koni zan yi musu ko na siya musu su tafi dashi in yaso Rauda sai ta zauna a nan harsu Mufeeda su dawo su zo su ɗauketa kafin dai dawowar mamansu.
A’a ba za ayi haka ba, ina ganin su dawo nan tunda ga Jidda zata yi musu komai nima zan tayata tunda na samu lafiya, in mamansu ta dawo sa koma gidanku.
To nagode Hajiya Allah ya saka da alkhari bari naje na haɗo kayan nasu.
Yauwa ka dubo har uniform ɗinsu in ba a wanke suke ba gobe Jidda sai ta gyarasu kafin monday.
Ai suna nan a goge dan Sakina bata barin wanki, zan haɗo su duka.
Ai Sakina akwai ƙoƙarin tsafta ba kamar ƙazamar amayarka ba, kai wannan yarinya ba zata rasa kwankwame ba.
Cewar Hajiya tana taɓe baki, Hamid yayi dariya.
Wlh kuma ƙalau take ita kuma kalarta kenan.
Aiko an samu saɓanin tarbiyya, Allah ya kyauta.
Amin Hamid yace yana dariya ya wuce ɗauko kayan su Rauda, sosai Hajiya take bashi dariya in suna zancen Madina saboda ta firgitata da halinta.
Madina kuma bayan fitarsu Hamid da mintinan sai ta fito falonta, ta kira maman Murja tana faɗa Hamid ya dawo da yara, itama tayi mamaki tace.
Kuma malam yace ya gama aiki akansu, amma ki bari anjima zanyi waya da shi duk yadda ya faɗa zan sanar dake.
Yauwa ki gaya masa dan wlh banji daɗin ganin dawowar su ba, hakan yana nufin itama mahaifiyarsu zata iya dawowa.
Ke kashe waya bari na kira malam yanzu dan ba muga ta zama ba.
Madina ta kashe wayar, maman Murja ta kira malam, yana ɗagawa ta soma maganar ya zaiƙi yi musu aiki mai kyau bayan tace masa wannan ta musamman ce bana wasa bane, malam yayi gyaran murya ya cire tsinken sakacen dake bakinsa, ya soma magana.
Matar Alai Mamman wlh na tsaya da gaskiya nayi aikin nan, sai dai inda gizo ke saƙa matarsa wancen data bar gida ba a zaune take ba, dan tana addu’a sosai wa kanta da yaranta da shi kan shi mijin, to gaskiya itace ta ɓata aikin kuma bana tunanin asiri zai yi wani tasiri akanta da yaranta sai dai ƙila mijin abin ya riƙa taɓashi jefi jefi tunda bai damu da yiwa kansa addu’a ba, kuma a binciken da nayi zata dawoz dan haka idan zaki yiwa bakinki linzami mu cigaba da cin rabonmu a jikin yarinyar nan to, in kuma kina ganin zaki faɗa mata gaskiya to ba damuwa amma kin yi mana sagegeduwar samun kuɗin shiga.
Sauke ajiyar zuciya maman Murja tayi tana cewa.
To malam yanzu me zance mata? dan bazan ma iya ce mata anyi aiki ya lalace ba ta ɗauka cutarta nayi.
Ki ce mata aiki yana nan ina cigaba da yi, kuma ta ƙaro kuɗi dubu ɗari domin a ƙara tsananta aikin yadda komai zai tafi dai dai, saboda kishiyarta tana ta ɓata aikin da muke yi, dan bata zauna ba tana bin malamai sosai.
Wannan bayanin shine kawai mafitarmu dan haka yanzu zan sanar da ita, amma fa wlh sai dai ka ɗauki Hamsin nima da ɗau Hamsin dan ni ce na kawo hanyar samun kuɗin.
Wlh matar nan kin fiye wayo, ina son aiki dake amma bana ƙaunar shegen son kuɗinki.
In kace baka yarda ba sai na jata wani gurin na kwashi rabona ai gida da yawa maye bai cin kansa.
Maman Murja ta faɗa cikin raha, malam ya saki dauriya.
Ya zanyi dake dole na amince, kice mata tayi ƙoƙari gobe ko jibi ta turo da kuɗin.
Angama malam mai yasin.
Ta faɗa tare da kashe wayar, bata kira Madina ba sai da aka ɗauki kusan minti talatin kafin ta kirata tayi mata bayanin malam, hankalin Madina ba ƙaramin tashi yayi ba ta ce zata zo da safe ta bata kuɗin, a haka suka rabu sai dai tana cikin damuwa sosai jin wai Sakina tana lalata aikin da aka yi mata, shiyasa taga Hamid wani lokacin ya yi mata mutunci wani lokacin kuma ya sauya fuska, aiko dole ta nunawa Sakina itama a tsaye take kuma duk abinda zata yi zata yi shi dan ganin bata dawo gidan ba.
Kano…
[8/12, 5:37 PM] Rahma Kabir: *ƘAZAMAR AMARYA*
Na
©®Rahma Kabir MrsMG.
Wattpad @rahmakabir
Page 33.
Kano.
Anty Jalila nan take ta kira ƙawarta ta haɗata da Sakina tana cewa.
Mijinki yanzu ya tafi Kaduna kuma gaskiya yana buƙatarki, ina ganin anjima zan zo in ɗaukeki mu dawo, gobe In Sha Allah da wuri zamu shiga kasuwa mu kammala siyayyarmu dan ina so ranar Monday da yardan Allah ki kwana a gidanki.
Kai Anty bai yi wuri ba, ina laifin ranar Juma’a mai zuwa.
Sakina anya kina ƙaunar Hamid kuwa? duk wannan kayan gyaran da kika banka baki buƙatarsa, ko dai ba kida lafiya ne in sani tun wuri mu fara niman magani.
Dariya Sakina ta kwashe da shi sosai tana cewa.
Kai Anty meya kawo wannan maganar kuma? ni ƙalau nake.
To ke in baki buƙatarsa shi yana buƙatarki dan ga dukkan alamu hankalinsa ya dawo gareki kuma dole kiyi amfani da wannan damar kija ragamar zuciyarsa, dan haka tafiya ranar monday ba fashi babu wanda zamu gayawa sai dai a ganki, dan ina so ki bashi mamakin ganinki.
To shikenan ke malamata ce duk yadda kika ce shi za ayi, ina bisa umarninki.
Ja’ira kina so kina kaiwa kasuwa sai na zo anjiman.
Jalila ta faɗa cike da zolaya, Sakina murmushi tayi tana sunne kai kamar tana gabanta haka suka yi sallama ta kashe wayar.
Washe gari kamar yadda Anty Jalila ta tsara kasuwa suka shiga da Sakina ta zaɓar mata kananun kaya riga da siket ‘yan kanti waɗanda suke na zamani masu kyau, riga mai cibiya waje da siket iya guiwa da waɗanda suke da tsayi, danma Sakina ta hana ta siya mata wando wai ba zata iya sakawa ba, sai crazy kayan barci kala biyar da suka siya, sannan ta siya mata dogayen riguna ready made guda uku sai mayafi biyu masu tsada, takalmi da jaka kala biyu sannan dan kunne da sarka da inner wears, siyayya sosai suka yi har da sabbin turare irin wanda Jalila take amfani dasu masu kyau da tsada dama kuma kayan kwalliya da man shafawa masu saka laushin fata, a takaice ‘yar kwarya kwaryan ƙaramin akwati suka haɗa wanda in da kuɗi komai mutum zai yi, dama Sakina da kuɗi tazo masu kauri dan ba tada account sai dai ajiya a ɗaki, ga kuma wanda Hamid ya bata sannan Jalila ma ta ƙara mata. Haka suka dawo gida suka yada zango a falo bayan sun rama sallar azahar daya cimmusu a hanya, suka ci abincin da Ra’isa ta dafa musu kana suka shiga duba kaya, Sakina ta ɗaga wasu kayan barci tana cewa.
Anty wlh kamar bazan iya saka su ba kunya nake ji, nifa ɗazun da kike zaɓar mini kayan nan kallonki kawai nake yi amma ina jin kunyar sakasu.
Baki Jalila ta buɗe tana kallonta harta kai aya a maganarta, kana tace.
Kice duk aikin banza nake da banayin dana yi miki a baya, to kar Allah yasa ki iya sakawa, in baki so ni zan mayar miki da kuɗinki nayi amfani dasu dan banyi tsufar saka su ba.
Kai Anty dan Allah kiyi haƙuri wlh ni kunya ce kawai ke damuna har nake ganin kamar bazan iya sakawa ba.
Sakina in baki zama mara kunya a gidan mijinki yanzu ba sai yaushe? Eh nasan akwai inda kunya take aiki musamman wajen sarrafa kissarki, amma kuma a fagen daga na samun zuciyar mijinki dole sai kin aje wata kunya kin more sauran rayuwarki data rage miki a duniya, in baki saki kiji kinji daɗin mijinki ba yaji daɗinki sai yaushe zaki yi haka.? To wlh ki zama ƙaruwar gidan mijinki ki yi amfani da halittarki, basirarki da kuma kissarki ki sace zuciyarsa yadda zaki yi kane kane koda wata zata shiga wlh kece a sama. Kice mini ma kwanciyar auren ma sake jiki kike yi masa kamar kin mutu baki iya yin komai ya gama sabgarsa ya sauka ko.?
Jalila ta faɗa tana tsureta da ido, Sakina ta sunne kai ta kasa bata amsa, cikin zafi Jalila tace.
Dan ubanki ki daina jin kunyata dan nasan me kike da mijinki nima kinsan me nake yi da nawa, in ba haka ba ta ina muka samu yara, narantse da Allah dole Hamid ma ya tsaneki wannan irin sakarci da kike lafta masa har ina, ba dole yayi sha’awar auren ‘yar boko ba saboda a tunaninsa ita ta waye da sanin komai. Ke sai yanzu ma na tabbatar da dole Hamid ya shanye duk wani rashin kunya da amaryarsa ke yi masa, wataƙila tana bashi can gurin da kyau ta iya sarrafa soyayyarsa a gado, aiko in baki aje kunyar nan ba kina ruwa Sakina.
To anty ki gaya mini ya zanyi tunda na ɗauko hanyar gyara ne, kuma ina son farin cikin mijina da nawa ni kaina.
Kunyar dai zaki aje ki yi rayuwar farin cikin da kike faɗa. Ki iya sarrafa sha’awarki wajen jawo hankalinsa, wlh tun daga kwalliyar daya fara gani a tare dake lokacin ɗaya dawo aiki kwakwalwarsa zata harbo masa jin Sha’awar kasancewa dake, sannan ƙamshin da zai ji yana tashi a jikinki shine zai cigaba da kai saƙo a masarrafar tunaninsa, sannan girkin da kika yi masa mai daɗi shine zai cigaba da aika saƙon da kike muradi, duk wata damuwa daya shigo da ita kin sauke masa shi cikin hikimarki. Babbar garkuwa kuma lokacin barci kin saka kayan barcin da zai fidda jikinki yana hango kayan arziki musamman tudun ƙirjinki da mazaunai, sannan ƙarin abinda zai ƙara rikitashi ki riƙa narkar da idonki cikin nasa kina jifansa da saƙonni wanda daga ke sai shi kuka san ina kuka dosa, sannan ki zauna cikin kissa da yauƙi yanga kusa dashi, ki aro wata murya mai daɗi ba wacce kika saba yi masa magana da shi ba ki furta masa kalma ta soyayya, wannan kuma ƙamshin daya fito a bakinki shine zai sa yaji sha’awar ya yi miki kiss, daga wannan lokacin wlh basai na ƙarasa miki karatun ba kun shiga wata duniya kenan. Sakina ki saki jiki da mijinki ki bashi ragamarki yadda kamar bakya son jikinki, ki koyi sallon kwanciya kuma kina kai masa saƙo wato kina taɓa duk wani weak point ɗinsa kina zaburar da shi abinda yake yi miki, na tabbatar wlh kafin irin wannan moment ɗin ya bar kwanyar Hamid sai dai in kin ƙara yi masa mafiyin wannan, haka kullun zai yini yana tunanin wannan yanayin, baza ki taɓa gundurarsa ba kuma lokuta da dama in ya tuna sai yaji tsantsar farin ciki, in tafiya yayi yana alla alla ya dawo gareki. Bafa wai shan maganin mata kesa miji ya nacewa mace ba Wallahi Summa Tallahi in kika iya sarrfashi a gado to ina kyautata miki zaton duk inda yaje zai dawo gareki yana ɗoki. Sannan kar ki ce sai in ya nimeki ne zaki bashi, ki zama kema kina nuna masa buƙatarki cikin aika saƙonni, ta ido ta cin cingum kina lashe leɓenki cikin salon yanayi, sannan kina sakin surarki wajen girgizasu ko yanayin tafiyarki ya zama na jan hankali, na ƙarshe kinsan weakpoint ɗinsa saiki na aika masa saƙo cikin hira da dubara kina taɓasu da hannunki, to ko shi waye sai ɗankwali yaja hula ba tare da kin furta bama, akwai kuma lokacin da zaki iya furtawan ya zama cikin wasa wanda duk in ya tuna sai yayi dariya. Mijinki ya zama shine babban abokin ki amma fa sai kin iya sarrafa harshenki.
Sakina ta sauke ajiyar zuciya.
To anty kamar me zan dinga amfani dashi wajen saka ƙamshin baki.
Ga mouth wash dana siya miki in kin gama komai zaki tukara ki kuskure baki dashi, sannan a kalla kiyi brush safe da yamma wanka ma haka, sannan zaki iya samun cingum irin masu yaji ɗin nan kamar Obit, ki tafi dashi a baki kina ci, sannan akwai ƙanunfari ki jika shi ki aje shima zaki iya amfani dashi wajen kuskure baki ko kuma ki sirka da ruwan ɗumi ki yi tsarki dashi yana saka ƙamshin HQ, sannan ko ki samu kanunfari guda ɗaya ko biyu ki saka a baki kina taunawa da haƙorin gaba kina haɗiye miyau kamshin zai zauna a bakinki. Sannan hq dinki ya zama da ruwan ɗumi kike tsarki ko shi kaɗai kika riƙe ba zaki riƙa warin hq ba, sannan pant kar ki riƙa barin jiƙaƙƙe a jikinki ko ya daɗe. Sannan akwai turaren baki da ake fesawa na kanti akwai kuma cingum ma na musamman sai dai ni banma taɓa amfani da shi ba, amma ko waɗannan dana faɗa miki kika riƙe su sun ishe ki.
Gaskiya ne nagode Anty Allah ya saka miki a mizani ya biya miki dukkan buƙatunki duniya da lahira.
Ameen ya rabbi, sannan ba ko da yaushe bane ake nacewa oga ana yi ana jan jiki kin gane ai, sannan shigarki ki riƙa yin daban daban karki nacewa ɗaya imma ƙanunan kaya ko manya ki zama dai cikin tsafta da ƙamshi, sannan turaren su zama kamar kala uku ko huɗu masu sanyin ƙamshi, daga Humra har na turara kaya a ka bada ko na fesawa a kaya ko body spray, wanda duk in yaji ƙamshin a wani guri zai tunaki, karki nacewa ƙamshi ɗaya.
Sakina ta saki murmushin farin cikin shawarar da take bata, haka Anty Jalila ta ɓata lokaci tana yi mata bayani musamman na yanayin kwanciyar zamani, Sakina ta riƙe su gam ta haddace a akanta.
*****
Kaduna.
Hamid bayan sun dawo daga siyo ice cream suka yada zango a falo dan shi yanzu sam baya son shiga ɗakin Madina yaga abinda zai ɗaga masa hankali. Da lokacin barci yayi Madina ta miƙe tana hamma.
Beb muje mu kwanta kasan nayi missing ɗinka sosai fa.
Uhum ni kuma gashi bana jin barci kije ki kwanta anjima kaɗan zan biyo bayanki.
Kai Beb ya zaka ce haka? in kuma barci yaci ƙarfina fa, kasan abin bazai yi armashi ba.
To Madinar Hamid gobe ma rana ce ai in yau bai samu ba, kije ki kwanta ina zuwa.
Jim tayi ta tsaya tana kallonsa shima ita yake kallo.
Kodai ka daina marmarina ne har wata ɗayan ya ƙare na gundureka.
Madina meyasa kika fiye ƙorafi ne, kin san fa har yau da sauran gajiyar tafiyar dana yi.
To ni dai ina buƙatar jin ɗuminka.
Ta faɗa tana turo baki, Hamid murmushi yayi kana yace.
Ki yi haƙuri mana Ƙazamar Amaryata ai nace zan zo kuma akwai ma aikin da zanyi yanzu a syatem.
Ummm tace tayi gaba cikin haɗe fuska dan sosai take jin haushin kiranta da yake yi da Ƙazamar Amarya, Hamid yayi dariya yana cewa a ransa.
Duk fushinki sai dai ki yi wlh, amma ba zanje ɗakinki ki tada mini zuciya ba da ƙazantarki, musamman tara yawun nan naki da ya ƙaru, yarinya sai kace mai tsohon ciki.
Sai yaja guntun tsaki ya mayar da idonsa ga tv. Bashi ya miƙe ba sai wajen sha biyu saura yasan ta riga tayi barci, sai ya shige ɗakinsa ya rufe tare da bin lafiyar gado, shi yanzu gaba ɗaya hankalinsa yana ga dawowar Sakina dan ba zai samu natsuwa ba har sai ta dawo gidansa ta kula da shi da yaransa.
Washe gari bayan sun gama karyawa da abincin da yayi musu oder, sai ya ƙara kwanciya bai farka ba sai wajen sha biyu saura yayi wanka ya shirya zai je gidansu ya duba yara, Ya samu Madina a falo cikin shirin fita tana danna waya, tana jin ƙarasowarsa ta ɗago fuska a haɗe.
Beb wai meyasa ka tsiri rufe ƙofa ko dai ka fara guduna ne? Tun ɗazu nake jira ka fito amma shuru har buga maka ƙofar nayi fa.
Madina barci nake yi kuma in ina barci bana so a dameni shiyasa nake rufe ƙofa, amma bagani yanzu na fito ba.
Hmmm sai wani hali kake nuna mini wanda ban sanka da su ba.
Haka dama nake ko Sakina da haka ta saba da halina kema zaki saba. Yanzu ina zaki naga kin yi shirin fita.
Dama nan maƙota zan shiga mu gaisa dan sun shigo, nima ya kamata na shiga mu sada da juna.
A’a ba inda zaki dan ni ba a shiga maƙota hakanan ba tare da dalili ba, ko Sakina haka take dasu sai abu mai ƙarfi kesa ta shiga.
Ni sai wani zancen Sakina kake mini, ko ka manta ni da ita daban, dan haka ni rayuwata daban da nata kuma ina so na saba da maƙota na.
To na hana ba inda zaki je, ke ko tausayin kanki ba kya yi kwata kwata hutun kwana nawa kika yi da aurenmu kika koma aiki? kullum sai kin fita da, to ni bana son tsurfar yawo.
Amma ai kasan ni ba gantali zani ba dan ba a titi ka ganni ka auro ni ba. Kuma wlh tunda nayi niyyar fita sai naje tunda dai na fita haƙƙinka na faɗa maka.
Tana gama faɗar haka ta miƙe fuuu tayi hanyar fita, Hamid ya shiga kwala mata kira amma tana jinsa tayi masa banza har ta fice, girgiza kai kawai yake yana mamakinta tare da tunanin irin hukuncin daya dace yayi mata, dan ya fara gundura da halinta ya kula tana da mugun taurin kai da rashin kunya, kuma ya dace ya sauke mata su dan ba zai jurewa haka ba. Haka ya wuce sashinsu Hajiya, yaga yaran sai wasa suke yi a farfajiya suka gaishe shi kana ya wuce cikin falon bai samu kowa ba sai ya nufi ɗakin Hajiya, ya sameta a kwance tana jan carbi tana ganinsa ta faɗaɗa murmushin ta, ya samu ƙasa kan carpet ya zauna suka gaisa, Hajiya ta dubeshi da kyau tana cewa.
Hamid ko akwai abinda ke damunka ne? naga fuskarka babu walwala.
Ba komai Hajiya yanzu nake tashi barci shiyasa.
Duk da haka ba yadda na saba ganinka ba, ko dai shashashar yarinyar nan tayi maka wani abu ne?
Hajiya ta faɗa tana tsureshi da ido, Hamid kamar yana jira ta tambayeshi ya gyara sama ya koro mata bayanin abinda Madina tayi masa yanzu, ya ƙara da cewa.
Wlh Hajiya gabaɗaya na kasa yadda zan yi maganin yarinyar nan sai ciwon kai take bani.
Kayi mata sakwa sakwa ne shiyasa, amma ina ce Sakina shakkar ka take yi, dan haka wannan ma ka nuna mata kai ne mai gidan ta yadda ko gaba ance tayi maka rashin kunya ba zata kuma yi ba.
Hajiya duk yadda kike tunani Madina ta wuce lissafinki bata jin magana sam.
Hmmm aure dududu wata guda da kwanaki amma matsaloli daga wannan sai wannan, kai tun asali ba a yi bincike ba ne da baka aurenta ba Wlh, dan banga abinda aurenta ya haifar maka ba sai ƙarin damuwa har gwara Sakina, da sai ka cigaba da lallabɓwa da matsalarta tunda bai kai na Madina yawa ba.
Kuskure an riga anyi shi Hajiya yanzu mafita nake nema.
Hakane, sai ka cigaba da addu’a sannan kuma ka tsaya mata tsayin daka kar ka yi mata da wasa.
Allah yasa mu dace, bari na gaishe da Abba ina zuwa.
Hamid ya faɗa yana mikewa, Hajiya tace to sai ya wuce.
[8/13, 7:57 PM] Rahma Kabir: *ƘAZAMAR AMARYA*
Na
©®Rahma Kabir MrsMG.
Wattpad @rahmakabir
Page 34.
Madina bayan ta shiga gidan Maman Murja ta zauna suka shiga yin hira bayan ta turawa mata dubu ɗari da malam yace ta bayar, a cikin hirarsu ne take bata labarin taƙaddamar da tayi da Hamid yanzu kafin ta shigo gidanta, maman Murja ta mele baki tana cewa.
Gwara da kika yi masa haka karki yarda kiyi masa sakwa sakwa ya raina ki, kuma aikin malam ma zaifi tasiri in kika nuna masa kema jan wuya ce.
Ai wlh ni bai isa ya riƙa takura mini ba balle yq yi mini kulle.
Kuma bari ki ga ki koma babu abinda zai iya yi miki sai dai hargagi. Ke Murja sakawa Amarya ɗan wanken in kin gama.
Cewar maman Murja ta ƙare maganar ga ‘yarta, Madina ta washe baki.
Ɗan wake kuka yi? Aiko zanci dan na kwana biyu ban ci ba.
Ai shiyasa nace ta zuba miki saboda ɗan marmari ne ba kowa ke damuwa da yinsa ba.
Cewar maman Murja sai suka cigaba da hira har aka kawowa Madina ɗan wake ta saki ciki taci tana santi, ba ita ta bar gidan ba sai misalin ƙarfe biyu da rabi.
Hamid tunda ya gaishe da Abba bai zauna ba, ya fito ya yiwa Hajiya sallama akan zai fita sai ya dawo gidansa, shuru shuru ba labarin Madina bata dawo ba har aka kira sallar azahar yaje masallaci yayi salla ya dawo, haka ya cigaba da zama a falon yaga lokacin shigowarta. Madina da sallama ta shigo falon tana ganinsa ta wani haɗe fuska tazo taza gotashi ba tare da tayi masa magana.
Madina!
Hamid ya ambaci sunanta cikin kakkausar murya, sai ta ja ta tsaya ba tare da tazo inda yake ba.
Wani irin rashin mutunci ne haka? nayi kama da tsaranki da zaki riƙa kawo mini raini a cikin gidana.
Madina tayi banza dashi bata tanka masa ba, Hamid saboda ɓacin rai a fusace ya miƙe yana nunata da yatsa.
Wlh baki isa ki riƙa taka umarnina son ranki ba, kuma aikin da kike takama dashi idan naso zan hanaki yinsa, ki bar ganin Abbanmu ya saka baki ina da damar da zan yi hukunci a gidana, kuma daga yau idan kika ƙara fita bada izini ba ba ki tabbatar a gidanku zaki kwana, banza mara mutunci! Ai bansan cewa ke ɗin ba kida tarbiyya ba sai yanzu, nayi dana sanin aurenki wlh dan babu abinda ya haifar mini sai damuwa.
Ni kake faɗawa maganganun da ranka yayi maka? wlh kayi kaɗan Hamid, ni ba ‘yarka bace da zata tasa a gaba kana gaya min maganar banza ba, kasan cewa banda aure ƙaddara ce amma nafi ƙarfinka wlh, dana san haka kake da fuska biyu mai zai sa na aureka, kuma wlh aiki yanzu na fara fita inda naga dama yanzu na fara, baka isa ka ja mini layi akan abinda naso ba, ai ba baiwa ka auro ba da zaka juyani son ranka ba…
Wani zabura Hamid yayi ya nufeta cikin ɓacin rai, tana ganin haka ta ruga ɗaki ko kafin ta kai ya cimmata ya figota ya kifa mata kyakkyawar mari tare da ya shaƙo wuyan hijab ɗinta yana zaro mata ido cike da tsantsar ɓacin rai.
Zan nuna miki nike aurenki ba ke kike aure na ba, ki kuskura ki ƙara fita bada izini na ba zan nuna miki cikakken asalina wlh, ƙazamar banza kawai.
Ya ƙare maganar yana sakinta tare da tureta har ta kusa faɗi, ba ƙaramin tsoratata yayi ba, hakan yasa bata iya furta komai ba dan ga dukkan alamu in ta kuma wata magana zata sha dukan banza ne, sai dai tayi aniyar sai ta rama marin da yayi mata koda bata kai hannunta jikinsa ba zata muzguna masa da abinda zai fanshe mata haushinta, tayi ƙofa ta shiga ɗaki, shi kuma tsaki yaja ya koma cushing yaje ya zauna yana mayar da numfashi, sosai ransa ya ɓaci har baya iya controlling kansa, dan da ya biye zuciyarsa dukan tsiya zai yi mata yadai raga mata ne ganin macece ba namiji ba abokin yinsa, amma yana jin dole ya kawo ƙarshen rashin kunyarta dan bazai taɓa ɗauka ba, ko Sakina ba rashin kunya take yi masa ba amma baya ɗaukar rashin kirkinta, dole ne sai ya nuna mata shi ɗin tsayayyen namiji ne a gidansa, daga ƙarshe miƙewa yayi ya bar gidan gabaɗaya bai kuma dawo ba sai wajen sha ɗaya na dare. Ɗakinsa ya shiga t’ya kulle yayi wanka ya shirya ya kwanta dama tun a waje yaci abincinsa, sai dai barci yaƙi ziyartar idanunsa saboda tarin damuwar da yake ciki, Sakina ta tafi taƙi dawowa ga Madina tana shuka masa iskancin data ga dama, haka ya raba dare idonsa biyu, hakan yasa ya sauko daga kan gado ya shiga toilet yayi alwala ya fito ya fara gabatar da Nafila, sai da yayi raka’a shida kafin ya zauna yayi lazumi da addu’a mai tsawo kafin ya miƙe ya hau gado, sosai ya samu natsuwa a zuciyarsa yaji kuma sanyi a ransa daga zafin abinda Madina tayi masa, shi kansa yaji daɗin Nafilar da yayi dan ya mance rabonsa da yayi shi, shima yasan yana da raunin ibada banda sallah biyar baya iya yin wata ibada, wannan nafilar da yayi ya tunatar dashi Allah ya kuma dace ya farga ta ƙara kusantar sa, wataƙila yadda ya bar Allah shiyasa yake ta jarabtarsa, da irin wannan tunanin barcin ya ɗauke shi.
Madina kuwa taci kuka idanunta har sai da suka kumbura saboda takaici, sosai auren Hamid ya fice mata a rai sai dai ba yadda ta iya ƙaddara ta riga fata, dan yanzu abin kunya ne a gareta ace ta kashe aurenta wanda bai fi wata da kwanaki ba da yinsa, sannan ma ga ciki tana da shi bata san ya zata yi da shi, mafitar da take hangowa kanta shine ta dage ta mallaki Hamid dan ta hakane kaɗai zata samu jin daɗin aurensa, da irin wannan tunanin ta samu yin barci.
*****
Kano.
A ranar Lahadi da wuri Anty Jalila ta kira mai ƙunshi tazo har gida ta zane ƙafar Sakina da hannu, jan lalle aka zana mata mai kyau. Bayan an gama tayi wanka ta saka wata atamfa suka fito farfajiyar gidan suka zauna saman tabarma, yau gurasa suka yi da rana dan haka anan suka ci suka ƙoshi Anty Jalila tana dubanta tace.
Sakina ya kamata ki samu abinyi wato ki samu sana’ar da zaki riƙa yi, nasan Hamid ba zai hanaki ba duk da yana wadataki amma kuma buƙatu da yawa, ya dace ace kema kisan yadda ake mayar da biyar ta zama goma, ki buɗe account ki iya harka ta online dan yanzu kasuwar ta kowa nan, nasan kin niya rubutun hausa ki shiga duniyar WhatsApp a dama dake koda ba zaki sauran chart a wasu shafukan ba, wannan yana ɗaya daga abinsa zai sa ki waye kisan ya duniya take ciki, zaki haɗu da mutane zaki koyi mu’amala zaki kuma san yadda zaki yi kasuwanci a sauƙaƙe, kina nan kasarmu Nigeria zaki yi oder ɗin kaya a China, kuma kaya su zo miki har gida ba tare da kin je ƙasar ba. Ko kuma ‘yan kayanmu dake nan ƙasarmu zaki siyar da shi wa saurar Jahohi duk a online, idan ma wannan duk basu samu ba ki siyar a cikin gidanki ki tallatawa maƙota da ‘yan uwa na tabbatar in sana’ar ta amshe ki har gida za azo a siya. Ina so ki sani Hamid ba zai iya ɗaukar ɗawainiyarki duka ba dana ‘yan uwa ki, idan da ya ɗauka to yanzu da kamar wuya domin ba ke kaɗai bace, sannan gidanku da ‘yan uwanki suna buƙatar taimakonki tunda kinsa bashi garemu ba duka, ki kama sana’a koda da ƙaramin jali ne kinga ba komai ne in ya taso miki ba zaki je masa da buƙatarki ba, kuma wlh in dai yasan me yake yi zai ji daɗin hidimar da kika rage masa sannan ma zai iya ƙara miki da jali. Sai dai ina so ki sani kar kuma niman kuɗi yasa ki mance da mutuncin aurenki, ki bawa mijinki lokacinsa sosai da kuma yaranki, duk abinda kike nima na kuɗi idan akazo zancen haƙƙin iyali tofa ya shafe shi, sannan kina sana’a kina sadaka kuma karki bar gidanku ya zama kamar na matattu babu karatun Al-Qur’ani, ki ware lokaci kina karantawa koda ba kullun ba, sannan kina yawan sauraren karatun, In Sha Allah gidanki zai yalwata da farin ciki, kuma duk abinda kike gudanarwa a gidanki babban koyi ne ga yaranki.
Ta ƙare maganar fuskarta cike da murmushi, Sakina ta sauke ajiyar zuciya tana cewa.
Wlh kuma ban taɓa kawowa kaina yin sana’a ba ganin ina cikin sukuni kuma gaskiya Hamid yana ƙoƙarinsa, amma shawarar ki ya zaburar dani zan yi ƙoƙarin niman wani sanawa na fara wanda ba zai takura ni ba, na tabbatar ba zai hana ba tunda ga amaryarsa ma tana aiki.
Sosai ma kuma in kina samun kuɗi daga gumin halak ɗinki wlh da dama damuwar namiji ba zai dameki sosai ba, dan in ya ƙunsa miki kina da yadda zaki rufawa kanki asiri ba tara da kin tambayeshi abu ba yaji daɗin janki a ƙasa ba, kema dai shaida ce kinga yadda nake harkoki na har cikin gida ba tare dana fita ba, dan haka yasa nake tausayawa duk macen da bata sana’ar komai a gidanta mazan zamanin nan ba irin mazan da bane, wani fa in yaga yana baki ci da sha to ya gama miki komai sauran hidima sai dai ki nima kiyiwa kanki, to in baki da sana’a taya in an kira sunanki zaki amsa, koda miji yana yi miki hidima yana da kyau kema ki nima ki yiwa iyayenki da gumin halak ɗinki ki kwashi arbarkansu, sannan ke karan kanki zaki siyawa kanki abinda kike so ki gyara jikinki ki yiwa yaranki ba tare da kinta binsa kina mitar ya baki kuɗi zaki abu kaza ba, sana’a tana ƙara kankaro wa mace mutuncinta a gurin mijin matuƙar baki bari sana’ar ta shiga cikin haƙƙin aurenki ba.
Gaskiya ne anty naji daɗin bayaninki kuma zan fara yi, in ma ya hana zan haɗashi da Abbansa nasan zai goya mini baya.
Yauwa Sakina faɗin baban Hamid da kika yi ya tuna mini wani abu, kina ko kyautata musu da ihisani hakanan matsayinsu na iyayen mijinki?
Eh to ban fiye yi ba amma duk salla ƙarama in tazo ina bawa Hajiya atamfa Alhaji kuma ina bashi shadda ko yadi, kuma duk Hamid ne yake siya yace na basu, sannan lokaci zuwa lokaci in nayi girki na sha’awa ina yi dasu na aika musu.
Gaskiya ne kina ƙoƙari sai dai zance ki ƙara a saman na da da kike yi, duk zuciya tana son mai kyautata mata, wataƙila in kika nuna Hajiyarsa matsayin uwa kina kyautata mata sosai zata rage ƙiyayyar da take yi miki, sannan ƙannen Hamid suma ki riƙa yi musu ihisani duk in sun zo garin, kuma zan so yanzu ki fara da guminki ba sai kin jira Hamid ya baki kinyi musu hidima ba, kiyi kar ya sani sai dai yaji a bakinsu, kinga kin jefi tsuntsu biyu da dutse ɗaya, kin kankaro mutuncinki a gurin Hamid zai ƙara darajaki da ƙaunarki, sannan kuma suma kin yi musu abinda zai fara goge ƙiyayyarsu akanki wataƙila su fara sonki domin wannan kyautatawar, sannan ki daina baya baya dasu ki shiga cikinsu in har sun buƙaci haka, ki yi walwala a cikinsu sosai ki nuna musu ke dasu kun zama ɗaya, ina ganin in kika yi haka kin kama hanyar gyara alaƙarki dasu.
Sakina hawaye taji yana sauka a kuncinta na tsantsar farin ciki domin zuwanta gurin anty Jalila ta samu tarin ilimin da zata magance matsalolinta cikin hikima da azanci, saboda tsabar farin ciki faɗawa tayi jikin anty Jalila ta aza kanta a bisa cinyarta tana kuka.
Haba sakina to miye na kuka ni dake abu ɗaya ne dole zan yi iya ƙoƙarina wajen ganin kin samu farin ciki a gidan aurenki. Sannan Sakina babu ruwanki da matarsa kiji da mijinki da kanki, sannan karki riƙa biye mata kuna masa hayaniya a gida sai kace wasu kaji, kinsan aka ce shiru ma magana ce dan haka ki bita da ido, sai dai in ta zabga miki makirci ne sai kema ki nuna mata kin fita iyawa.
Sakina ta saki dariya tana gyaɗa kai, haka suka cigaba da hira sai kiran sallar la’asar ne yasa suka bar gurin.
Washe gari Monday, da wuri suka shirya suka kamo hanyar Kaduna, shatar mota suka yi su biyu akan zai dawo da Jalila dan ba zata kwana ba, suna tafe suna addu’a dan basu bari hira ta cinye musu falalar yin addu’ar matafiyi ba, har suka ƙaraso cikin Kaduna Sakina ta shaƙi iska taji wani daɗi a cikin ranta, musamman yadda zata yi zolali da yaranta da take matuƙar kewa, dauriya kawai take yi amma a ranta ita kaɗai tasan yadda take ji na rashin yaranta kusa da ita, har gate ɗin gidan Hamid suka isa driver yayi parking suka sauka ya zauna jiran Jalila dan tace ba zata zauna ba yanzu zata fito su wuce gidansu, daga can ta leka gidan baba malam sannan ta biya ta gidan Umma kafin su wuce.
[8/15, 7:16 PM] Rahma Kabir: *ƘAZAMAR AMARYA*
Na
©®Rahma Kabir MrsMG.
Wattpad @rahmakabir
Page 35.
Bayan su Sakina sun shiga gidan suka tsaya ta saka key ɗinta ta buɗe ƙofar falo dan da farko ta murɗa ta jishi a rufe, suka shiga ciki ba laifi tsaf yake, har bedroom ɗinta Jalila ta rakata suka tsaya ta dafa kafaɗarta tana cewa.
To Sakina ni na gama nawa saura ke ya rage miki ki samarwa gidanki farin ciki, ina fatan duk shawarwarin dana faɗa miki kiyi amfani da su koda ba duka ba, Allah ya ƙara miki haƙuri da juriya yasa kinci jarabawanki.
Ameen anty nagode Allah ya saka miki da mifificin alkhairi, Allah ya sauke ku lafiya ya huta gajiya.
Ameen Sakina ni zan wuce sai ki fara fafatawa daga yau.
Jalila ta faɗa fuskarta da murmushi sai ta juya ta soma tafiya Sakina tabi bayanta tana cigaba da zuba mata godiya, har mota ta rakata suka wuce kana ta juya ta koma ciki. Kitchen ta shiga taga komai tsaf ta buɗe freezer taga akwai komai da Hamid ya saba aje musu, dan haka ta koma ɗaki ta sauya shigarta zuwa doguwar riga na aiki kana ta fito ta ɗaura sanwar tafashen kaza dan so take tayi musu pepe chicken. Data gama ɗaura tafashe sai ta ɗiba tattasai da tarugu sai albasa ta wanke ta niƙa kamar jajjage, ta aje abinta a gefe sai ta wanke shinkafa ta sakashi a matsami shima ta aje a gefe danya tsane, so take yi tayi musu fried rice da pepper chicken haɗe da drink ɗin kankana da abarba. Sakina tun misalin sha ɗaya da rabi ta fara aikin bata gama ba sai wajen ƙarfe biyu ta kwashe tukwanen abincin duka ta kai ɗakinta ta aje kana drinks ɗin ta zuba shi a manya gora biyu ta saka a frigde can ƙasa inda ba za a gani ba, da yake da ƙanƙara ta haɗashi bata buƙatar dole saita saka shi a guri mai sanyi, kuma suna da wuta sosai area ɗinsu ba su da matsalar nepa in ma sun ɗauke invata zata cigaba da aiki, ta wanke komai ta mayar inda suke ta gyara kitchen ɗin tamkar ba a yi aikin komai ba, sai ta koma ɗaki ta rufe da key ta yi alwala ta gabatar da sallar azahar, data idar ne ta zuba abinci ta ci sai ta bi lafiyan gado dan ta huta, ta kira anty Jalila ta tambayeta hanya tace basu daɗe da kama hanya ba tayi musu addu’ar sauka lafiya kana suka yi sallama ta kashe wayar, da yake tasan yaran ko sun dawo makaranta gidan Hajiya zasu je kuma Hamid sai yamma ko magrib zai dawo hakan yasa ta ke son yin barci ta rage gajiya, ba jimawa kuwa barci ya ɗauketa.
Hamid da sassafe ya shirya ta fito bai bari sun haɗu da Madina ba ya aje mata kuɗin mota daya saba sai ya wuce abinsa gurin aiki, a can ya samu abun karyawa yaci kana ya tsunduma aiki a company kasantuwar ranar monday ce tushen aiki. Madina kuwa da wani irin kasala ta tashi ji tayi kamar ba zata iya fita aiki ba, amma da yake sun matsa mata da kira yasa ta miƙe ba shiri tayi kwaskwarima dan ji tayi bata ƙaunar saka ruwa a jikinta, ta fito ta shirya cikin doguwar rigar leshi ta feshe jikinta da turare ta shirya babu wanda zaice bata yi wanka ba, dan haka ta ɗauki mayafi ta saka da jaka ta saka takalmi ta fito bata bi ta kan Hamid ba dan tayi tunanin bai fita ba, kuɗin data gani kan center table ne yasa ta gane ita ya ajewa dan haka ta ja guntun tsaki ta ɗauka tana cewa.
Wlh duk randa ka shigo hannuna Hamid sai na murzaka kamar fulawa, dani kake zancen.
Ta ƙare maganar da jan tsaki ta wuce fuuu kamar guguwa. Ba ita ta bar gurin aiki ba sai wajen ƙarfe uku, da farko taso zuwa gidansu ta faɗawa momy abinda Hamid yayi mata sai dai kuma ta tuna momy ba tada sauƙi zata iya kiran Hamid ɗin tayi masa rashin mutunci, ita kuma bata so a fara yin haka tun yanzu gwara dai ta dage da niman maganin mallaka har ta shawo kan matsalarta dan haka gidan maman Murja ta sauka, nan taci abincin rana shinkafa da wake da mai da yaji, suka kafa hira wanda duk rabi na zagin mazajensu ne da irin matakin da suke burin ɗauka akansu, maman Murja ta tabbatar mata da ta aika da kuɗin aikinta wa malam kuma ta zuba ido taga yadda aikin zai kama Hamid ta kwantar da hankalinta, haka Madina ta rashe ƙafa sai wajen ƙarfe biyar da rabi ta koma gida, tun a falo ta fara kurɓan ruwan mamaki ganin an saka turaren wuta a falon sai tashin ƙamshi yake gashi kamar an ƙara goge ko ina yayi haske, ta wuce kitchen shima ta leƙa nan ma fes yake babu kuma alamar anyi girki tasan dai ba kowa dan mai aikinta ma yau sunyi ba zata zo ba, tunaninta ya bata ko Hamid ne ya dawo sai dai kuma bata ga motarsa daya saba fita ba, sannan ƙarin mamakinta a buɗe ta samu ƙofar falon kuma itace ta rufe da key, ganin babu motsin kowa sai tunaninta ya bata ƙila Hamid ya dawo da rana shine ya saka turaren ya barshi a wuta, da wannan lissafin ta wuce ɗaki ta aje jaka da mayafi tabi lafiyar gado dan ta ƙara hutawa kafin ta tashi tayi wanka.
Sakina kuwa kiran sallar la’asar ne ya farkar da ita daga barci ta tashi ta ɗauro alwala ta fara gabatar da sallah, data idar ta fito ta yi moping ɗin falon kana ta saka turaren wuta ta koma ciki ta haɗawa kanta ruwan wanka tayi, ta fito ta fesa kwalliya cikin shigar atamfa riga da siket, ita kanta sai ta koma tana jin kunyar ganin kwalliyar da tayi bata san ya kuma gogan zai fassarata ba in ya gani, tabbas tayi kyau duk da ba cika kwalliyar tayi ba ta fesa turare guda biyu bayan humra data shafe jikinta da shi sai ƙamshi take zubawa ta saka ɗan kunne da sarka ta saka warwaro da manyan abin hannu guda biyu ta saka zobe a yatsarta na kusa da ƙaramin, nan take ta sauya daga Sakinar da zuwa sabuwa, ta zauna tana duban wayarta a lokacin ƙarfe biyar da mintuna shigowar Madina yasa ta miƙe amma jin motsin buɗe ɗakin bana Hamid bane yasa ta koma ta zauna, a lokacin ta kira anty Jalila ta ɗaga tayi mata sannu da hanya dan har sun sauka daga bisani suka yi sallama ta cigaba da latsa wayarta har misalin ƙarfe shida da minti goma a lokacin ne taji dirar motar Hamid, da sauri ta miƙe ta isa madubi ta ƙara duban kanta tabbas tayi kyauta daidai gwargwado, dan haka ta ƙara goga sosan powder a fuskarta kafin ta ɗauki sabon mayafinta ta yafa a kafaɗa gefe ɗaya, ita dai gabanta faɗuwa kawai yake yi saboda rashin sabo da abinda take shirin yi, tasan zata samu tarba a gunsa saboda yana ɗokin ganinta sai dai kuma jikinta har ɗan rawa yake yi saboda bata saba da irin wannan shigar ba, ta saka takalmi mai tsini ta aje wayarta tare da karanto addu’ar samun natsuwa kana ta nufi ƙofa ta buɗe ta shiga takawa a hankali saboda rashin sabo da tafiya da takalmi mai tsawo, a haka harta isa ƙofar fita farfajiya ta ɗan tsaya ta sauke ajiyar zuciya ta sauke numfashi mai ɗumi kafin ta kama handle ta murɗa ta buɗe ta fita.
Hamid tunda yayi parking bai fito ba saboda wayar da ya tsaya yi da wani abokin kasuwancinsa, yana wayar amma da ɗayan hannunsa yana buɗe ma’ajiyar motar tare da duba wasu takardu, kamar an ce masa ya ɗaga kai sai ya hango Sakina tana tawo wa cikin shiga mai kayatar da zuciya, sakin baki yayi yana dubanta dan gabaɗaya hankalinsa ya koma gunta gani yake kamar gizo take yi masa saboda kwanakin nan ya sakata sosai a zuciyarsa, can dai yayi sallama da wanda suke waya akan zai kirashi in ya duba takardun motar, ya rufe ido ya kuma buɗewa domin ya farka daga mafarkin da ya shiga yi a farke dan zuciyarsa ce kawai take niman yaudararsa, amma baya tunanin Sakina zata dawo a kurkusa haka, koda ya buɗe ido tana gabda isowa gareshi ya cigaba da kallonta tana sakin murmushi harta ƙaraso motar, Hamid mutuwar zaune yayi ya kasa kwakkwaran motsi, Sakina ta kama hannun motar ta buɗe ta ɗaura hannunta ɗaya a kan marfin motar tana cewa cikin fara’a.
Sanmu da zuwa Alhaji Hamid.
Wai Sakina dama dagaske kece nake gani? ashe kin dawo?
Na dawo ɗazun da safe misalin ƙarfe sha ɗaya, anty Jalila ta rakoni yanzu haka itama tana gidanta.
Ikon Allah sannu da zuwa ya hanya da fatan kina lafiya.
Hamid ya samu kansa da jero mata bayani baki cike da dariyar farin cikin sake ganinta, tace.
Lafiya lau Alhamdulillahi gajiya ma tabi lafiya, dan na samu barci ɗazun na huta sosai. Muje ciki ko.
Tace tana sauke hannunta daga marfin motar ta gyara zaman mayafinta da yake niman sauka ƙasa, ta matsa gefe Hamid ba musu ya fito ya rufe motar suka jera suna tafiya gwanin ban sha’awa, har suka ƙarasa falo ya samu guri ya zauna Sakina tace.
Ai da ka shiga ciki ka watsa ruwa kafin a kira sallar magriba dan an kusa.
Eh eh hakane fa, to bari na yi na fito.
Ya miƙe ya wuce ɗakinsa da sauri itama tabi bayansa, da suka shiga ita toilet ta wuce ta haɗa masa ruwan wanka kana shi kuma ya rage kayan jikinsa, data fito ya shiga bayi yana mamakin sauyawarta lokaci guda, gani yake tafiyarta Kano tamkar an sauya masa ita ne yadda yaga tasha ado tana zuba ƙamshi mai dadi, gashi ta ƙara yi masa kyau, bai taɓa kawowa a ransa zai ganta a irin wannan shigar ta zamani ba, haka yayi wanka cike da farin ciki da mamakin sauyawarta, ko da ya fito ya samu ta fito masa da farin jallabiya da ƙaramin wando da singilet a gefe tana kuma zaune har ya fito ɗin, murmushi ta sakar masa.
Sannu da fitowa.
Yauwa Sakina ashe ma kin fito mini da kayan da zansa, kamar kinsan su zan saka dan bana son saka masu nauyi.
Saninka da haka yasa na fiddo maka su.
Ta faɗa tana wasa da tsayunta, Murmushi Hamid yayi bai ce komai ba ya isa wajen madubi ya shafa mai ya dawo ya saka kayan ya fesa turare kana yace.
Kinji ana kiran sallar Magrib bari na tafi masallaci sai anyi sallar isha’i zan dawo, amma daga can zan wuce na nima mana abincin da zamu ci.
A’a kuɗinka su huta dan nayi mana girki in ka dawo sai muci.
Masha Allah.
Ya faɗa yana faɗaɗa fara’arsa kana ya nufi ƙofa ya fita itama tabi shi a baya ta shiga ɗakinta shi kuma ya wuce masallaci.
Bayan sallar Isha’i, Hamid gida ya nufo da saurinsa dan yunwa yake ji kuma ba ƙaramin ɗokin cin abincin Sakina yake yi ba, yana shiga falo ya tadda dinning an gama shirya shi dan haka can ya nufa ya zauna, ya kira Sakina a waya bata ɗaga ba ta fito dan taji motsin shigowarsa, itama gurin abincin ta nufa ta fara zuba masa kafin ta saka nata ta samu guri ta zauna suka fara ci. Madina da tun dawowarsa take tunanin zai shigo ya ganta tare da lallashinta akan abinda yayi mata jiya amma shuru, hakan yasa ta ƙara ƙuluwa saita ƙi fitowa ta cigaba sa kwanciya, koda aka kira sallah da kyar ta miƙe tayi shi wankan ma cewa tayi ba zata yi shi ba dan sanyi sanyi take ji, kayan jikinta ne ta ciye ta saka ƙananun kaya riga da siket, tunda taji fitarsa tayi zaton ba zai dawo ba sai tayi barci irin na jiya, duk da tana ta jin motsin ƙofa da takun mutum sai ta bayar ko ‘yarsa Mufeeda ce ta shigo gidan, sai dai jin an shigo bayan sallar isha’i ya bata Hamid ne dan haka cikin ɓacin rai ta yunƙura ta sauko ta zo ta buɗe ƙofa ta fito kai ko ɗankwali babu, ganin bata ga kowa a falon ba yasa ta isa ɗakinsa ta ga baya ciki, sai ta juya ta nufi wajen kitchen jin alamun kamar ana cin abinci saboda tsokali yana dukan plate, tana isa ta gansu suna cin abinci Madina sai da gabanta yayi mummunar faɗuwa, numfashinta ya yanke na wucin gadi da kyar ta iya laluboshi ta shiga fidda shi mai zafi, ƙugunta ta riƙe tana kallonsu wanda suma ita suke kallo, ba ƙaramin firgita tayi da ganin Sakina ba amma haka ta shanye ta soma magana.
Ya zan ga haka kuma?
Kamar ya fa?
Cewar Hamid yana ɗan haɗe rai, Madina ta saki riƙon da ta yiwa ƙugunta ta ƙara matsowa dinning ɗin ta dafa da hannu bibbiyu.
Amma kasan matarka zata dawo shine baka sanar dani nasan cewa kwana ya fita a guna ba? to wlh yau kwanana ne tunda baka sanar dani ba gobe in yaso sai ta amsa girki dan wannan cin amana ce.
Ta ƙare maganar cike da zafin kishin data ji yana turnuƙeta, Hamid yayi guntun murmushi.
To me miji, ita duk tsawon wata ɗayan data baki har da ƙarin kwanaki bata yi ƙorafi ba sai ke, to baki isa ba girki ya dawo hannunta ki jira zuwan jibi da yamma saiki amsa.
Wlh ban yarda ba.
Madina ta faɗa tana gyara tsayuwarta har da tafa hannu, Sai a lokacin Sakina ta saki murmushi tana duban Hamid.
Abban Mufeeda ina ganin wannan ba wani abin tashin hankali bane, ka bari ku kwanan in yaso gobe In Allah ya kaimu sai na amsa dan yau da gobe duk ɗaya ne a gurin Allah, kuma tabbas ban kyauta ba tunda bata san da dawowa na ba kaima baka sani ba sai da ka ganni, kaga kuwa kwana nata ne.
A to ga gaskiya sai a taketa, dama munafurci yasa baki faɗi zaki dawo ba dan ki rabawa mutane hankali.
Madina ta faɗa tana danƙara mata harara, murmushi Sakina tayi ta cigaba da cin abincinta, Hamid ya miƙe yana cewa.
Ki ɓacewa mutane da gani kafin ranki ya ɓaci bana son sakarci, kuma idan kika ƙara kiran matata da munafuka wlh saina fasa miki baki mara ɗa’a kawai.
Raina na nawa ka ɓata mini, ba shakka Hamid matarka ta dawo zaka soma wulaƙantani ko saboda kaci moriyar ganga ai dole ka yada korenta.
Zaki wuce kosai na tattakaki a nan shashasha.
Hamid ya faɗa tare da zabura zai kai mata hannu, da sauri Madina ta wuce dan tasan ba mutunci ne da shi ba tsaf sai ya mareta a gaban Sakina tunda takula halinsa kenan, Sakina ce tace cikin sanyin murya.
Kai Abba Mufeeda meyasa zaka yi mata haka tafa mufi gaskiya, dan dai kwanan yau kawai ka yi mata adalci, kuma dan Allah ka daina biye mata Madina yarinya ce da kuruciya a tare da ita wataƙila ni in kayi mini na shanye ita ba lallai ta ɗauka ba, saboda akwai ɗanyan kai a tare da ita.
Wlh bazan ɗauka ba Sakina bana son shirme da sakarci.
Ka dai yi haƙuri maganar ta wuce.
Sakina ta faɗa, Hamid yayi ƙofa ya cigaba da cin abincinsa ransa duk babu daɗi, dan ya so ace yau ya keɓe da Sakina dan yana cike da kewarta.
[8/17, 6:42 PM] Rahma Kabir: *ƘAZAMAR AMARYA*
Na
©®Rahma Kabir MrsMG.
Wattpad @rahmakabir
Page 36.
Hamid bayan ya kammala cin Abinci ya miƙe domin zuwa falo sai Sakina ta tare shi da cewa.
Ya batun yara zaka ɗauko su ne yanzu ko sai gobe?
Ko zaki shirya muje tare yanzu daga nan kya gaisa dasu Hajiya, in yaran basu yi barci ba sai mu tawo dasu.
To tace masa kana ya wuce falon ita kuma ta ƙarasa cinye sauran abincin daya rage a plate sai ta miƙe ta haɗe kayan ta soma kaiwa kitchen, data gama ta wuce ɗaki ta ɗauki mayafi ta fito falo Hamid ya miƙe ya fara gaba ta bishi a baya, a lokacin ne Madina ta sake fitowa daga ɗaki, ganin fita zasu yi yasa tayi sauri dakatar da su da kiran sunan Hamid ga miyau cike da bakinta.
Sakina ce ta fara juyowa ta tsaya kafin Hamid ya juyo shima yana kallonta, Madina matsawa tayi jikin bangon falon zata tsirtar da miyau Hamid ya buɗe murya cikin daka uwar tsawa.
Karki kuskura ki fetsar da miyau jikin bangon falon nan, ki tafi can ɗakin ki da kika saba ƙazantar, dan wlh zanyi matuƙar saɓa miki.
Madina ta gumtse miyau ta juyo fuska haɗe ba damar magana saboda miyan ya cika mata baki, ganin ta tsaya ɓata musu lokaci Hamid ya juya.
Sakina mu je kinji.
Madina da sauri ta fetsar da miyau jikin bangon tana cewa cike da gatsali.
Ina zaku je tare? naga dai kwanana ne ko.
Kika zubar da miyau a bangon ko? na rantse da rabbin ka’abati sai kinsan kin yi haka, bazan ɗauki ƙazantarki ba ki je ki samu tsumma ki goge gurin nan kafin mu dawo, dan in har yayi jirwayi abin da zanyi miki sai yayi miki matuƙar muni.
Hamid ya faɗa cike da tsantsar ɓacin rai, Madina ta turo baki.
Kayi duk abinda zaka yi ɗin ai lalura ce yasa ni tara miyau, sannan ina son yin magana da kai naga dole ne sai na zubar kafin inyi.
Bai ce komai ba ya buɗe kofar falon ya fita Sakina ta bi bayansa, sai Madina ta buɗe murya.
Allah ya isa ban yafe ba tunda kuka fita tare a ranar kwanana.
Babu wanda ya tanka mata suka wuce Sakina tana mamakin halin Madina na rashin kunya ace har shi Hamid bata ragawa ba, abin nata yayi yawa haka suka wuce zugum zugum kamar marasa lafiya tsabar tunanin abinda Madina tayi, shi dai Hamid tunanin matakin da zai ɗauka ne a kanta yake yi wanda yana jin da wuya ya jure wannan ƙazantar, dole ne ya kai ƙararta gida ko za a ja mata kunne. Da suka isa falo sun tadda Hajiya da Alhaji suna kallon labarun ƙarfe tara da aka fara yanzu, da idanu suka bisu bayan sun amsa musu sallama har suka samawa kansu gurin zama a kan capet suka shiga gaisawa, Abba cikin tsokana yana cewa Sakina.
Na ɗauka ko sai ni da kaina nazo bikon ɗiyata ashe dai zaki dawo, da fatan zaki ƙara haƙuri da Hamid ki yafe masa komai ya wuce.
Haba Abba ai ba sai kazo ba zuwan Hamid ma ya wadatar, dama ‘yan shirye shirye ne yasa ban biyoshi ba a ranar sai ɗazun muka zo yaya Jalila ta rakoni. Da fatan na sameku lafiya.
Lafiya lau Alhamdulillahi Allah ya kauda shaiɗan a cikin zamanku ya wanzan da zaman lafiya.
Duk suka amsa da amin kana Hajiya ta ɗaura da cewa.
Banda abinki Sakina, ko wace mace haƙuri take yi a gidan mijinta ko ba dan ke ba zaki zauna domin yaranki tunda kin tara zuri’a, tafiya ki barsu ba shine mafita ba, in ma wani abun Hamid ya yi miki ki zo ki faɗa mana kinsan dole zamu tsawatar masa, dole ne duk ku haɗu kuyi haƙuri da juna tunda zamane na har abada muke fata sai randa mai duka in yayi ikonsa aka ce ba ɗaya.
Hakane In Sha Allah hakan ba zai sake faruwa ba, kuyi haƙuri.
Cewar Sakina tana sunne kai ƙasa, Hajiya ta taɓe baki.
Haƙuri ai ke zamu bawa shi tunda ke aka ɓatawa rai, Allah ya huci zuciyarki ya kuma ƙara muku zaman lafiya.
Sakina ta kasa amsawa da amin banda wasa da yatsunta da take yi, ta san da biyu Hajiyar ta faɗi haka dan dama ba ƙaunarta take yi ba, Hamid ne ya amsa da sauri.
Ameen Ameen ai komai ya wuce. Hajiya yara fa suna ina?
Suna ɗakin Jidda ban daɗe da tasa ƙeyarsu ba nace suje can suyi hirarsu su barmu muyi kallon labarai, duk idonsu biyu har Rauda, Jidda! jidda!.
Hajiya ta ƙare maganar tana buɗe murya tana kiran Jidda, da sauri ta fito ganin su Hamid yasa ta ƙaraso da sauri ta gaishesu tana cewa Hajiya.
Gani.
Je ki kira su Mufeeda ga Mamansu ta dawo.
To tace mata kana ta miƙe ta koma ciki ba jimawa sai gasu sun fito da gudunsu, suna ganin Sakina suka isa gunta suka gewayeta har Mufeeda ta kasa ɓoye farin cikinta, Rauda kuwa cinyarta ta yiwa kanta masauki tana narke ido zata yi kukan shagwaɓa wa maman, Ita kanta Sakina farin cikin ganinsu ba zata iya misaltashi ba, nan suka shiga tambayarta ina taje taƙi dawowa, Sakina tana kallonsu cike da kauna.
To ba gani na dawo ba ku tashi muje can gida kar mu hana su Abba sauraren labarai.
Nan duk yaran suka miƙe cike da murnansu, Hajiya ta kallesu tana ‘yar dariya.
Wato uwa daɗi daga ganinta za kuyi mana ƙaura ku gudu ko, to Allah ya bamu alkhairi
Ai zamu zo in mun dawo makaranta ki bamu kwakumeti.
Cewar Baba ƙarami, Hajiya tayi dariya tana cewa.
Sarkin kwaɗayi zan saka a yo muku da yawa kuyi ta ci amma kasan kun cinye wanda ke hannuna ko. Jidda zata biyosu da kayan makarantarsu in yaso da safe zai a kawo sauran.
Sakina tace to tare da zuba godiya, Nan dai suka yi sallama da juna suka tasa ƙeyar yaran suka wuce gidansu, Alhaji bayan fitarsu yace.
Kin gansu gwanin sha’awa Allah ya tabbatar musu da zaman lafiya ya kaɗe fitina, duk da na kula AbdulHamid ya shiga hankalinsa da tafiyar Sakina, wataƙila ya sauya akalar zaman nasu yayi kyau.
Itama Sakinar tafiyarta zai sa ta gane Hamid ɗin yana da muhimmanci a rayuwarta, duk dai su haɗu su gyara zaman nasu ake fata.
Hajiyaaa! Kin fiye son kanki da yawa wlh, ba dama nayi magana sai kin san yadda kika kare Hamid, kin san Allah yadda kika riƙe sarakuwarki haka suma ‘ya’yanki mata sai kiga sun dace da surukai, abinda kayi fa duk sai anyi maka walau khairan ko shairen.
Hmmm ai dama Sakina tafi yaranka muhimmanci a gurinka, ni bari na rage mara dan in na niye ta taka mun dinga musu kenan har rai yazo ya ɓaci.
Gaskiya ce dai bakya so.
Abba ya faɗa yana murmushi, itama murmusawa tayi ta miƙe ta wuce ɗaki.
***
Madina lokacin da su Hamid suka fita kitchen tayi sauri ta shiga ta samu plate ta ɗiba sauran abincin da Sakina ta bari har da naman ta ɗiba ma’ishinta, kana ta ɗiba juice ɗin a kofi ta fito ta shiga ɗaki da sauri tasa key, ta zauna ta cika cikinta tana santin girki tana kaɗa kai.
Shegiyar mata ta iya girki, ko wannan zaisa Hamid yayi farin cikin dawowarki, kai nima dai ya kamata nayi zuciya naje makarantar koyan girki na iya, ko dan na burge Hamid tunda naga mayen abinci ne, ko tanan ai ta riƙa yi masa barbaɗe ta mallake shi ni ina nan baki sake.
Ta ƙare maganar tana jan tsaki tare da yatsine fuska, haka ta gama cin abincin har sai da ta haɗa da mugun ci ta dafe hannu biyunta ta baya ta daga kai sama tana mayar da numfashi, ta jima a zaune a haka, wanda a lokacin ne su Hamid suka dawo dan taji ihun yara, kamar zata fito sai kuma ta fasa dan bata san karonta da Hamid ba ya jizgata a gaban su, sai dai ta bayar da yau sai ta kwana a ɗakinsa saboda hakanan taji tana kewarsa, da alama kamar cikin jikinta irin mai sa buƙatuwa ne sai dai bata fahimci hakanta tunda na farko ne sannan ba sanin ciwon kanta tayi ba.
A falo su Hamid suka yada zango yaran sai surutu suke yi musu, haka suka ɓata lokaci har misalin ƙarfe goma da minti shida, a lokacin ne Sakina ta tasa ƙeyarsu akan suje su kwanta zasu makaranta da safe karsu makara, sai da ta tabbatar da duk sun kwanta kafin ta fito falon ta samu Hamid a zaune yana kallo ta zauna tana cewa.
Yallaɓai nima zanje na kwanta sai da safe in kuma da akwai abinda kake buƙata to ka faɗa mini yanzu na yi maka kafin na shiga ɗaki.
A yanzu banda buƙatar komai saboda kin cika mini ciki da abincinki mai daɗi, abu ɗaya nake buƙata sai dai na san bazan samu yau ba.
Sakina ta fahimce shi amma da yake bata waye da harkan sakin layi ba ta sunne kai tana cewa.
Me kenan?
Kin fini sanin me nake buƙata Sakina, saboda kin san ai ina cike da kewarki.
Murmushi ta saki tana miƙewa.
Allah ya kaimu gobe lafiya yau dai ranar Ƙanwata ce.
Sakina hakama zaki ce? Ya kamata ki fita batun Madina ki amsa girki yau tunda kece kika ciyar dani abinci.
Duk da haka kayi haƙuri muyi mata abinda take so, bana so mu riƙa samun saɓani akan haka.
Shikenan Allah ya kaimu goben.
Ameen Abban Mufeeda, me za muyi abincin safe?
Ki dafa komiye zanci banda zaɓi.
Gyaɗa kai tayi tare da lumshe ido ta buɗe alamar to cike da murmushi a fuskarta kana ta juya ta wuce, da kallo Hamid ya bita harta shige ciki, gani yayi har wani ƙiba ta ƙara mazaunenta ras Masha Allah, nan ya haɗiye miyau cike da buƙatuwa amma babu abinda ya bar gobe in dai da rai da lafiya, haka ya ɓata lokaci a gurin har wajen sha ɗaya da kwata kafin ya miƙe ya kashe kayan kallo ya wuce ɗakinsa, wanke baki yayi ya ɗauki wani tomtom daya siya ɗazun yana jin alamar mura yasa a baki ya kwanta ya soma danna waya, sai ya tuna lokacin da yake zuba soyayya da Madina a irin wannan yanayin lokacin da tana gidansu, murmushin takaici ya saki yana cewa.
Ashe soyayyar aure itace ta gaskiya, duk faɗin da take yi tana so na a baki ne kawai, ga tarin ƙazanta da ban san tana da ita ba, wato rayuwar aure ta gaskiya da gaskiya ce duk wani mugun halin mutum a nan sai ya fito.
Ya ƙare maganar da ajiyar zuciya, jin motsin ana taɓa ƙofarsa yasa shi kallon ƙofar da sauri, sai yaga Madina ta shigo, shaf ya manta ma bai rufe ƙofa ba, cikin haɗe girar sama dana ƙasa yace.
Me ya kawoki ɗakina? Ki fita tun kafin raina ya gama ɓaci da ke.
Amma kasan rabon da mu kasance a guri ɗaya an kwana biyu, ya kamata tunda matarka ta dawo mu kwana yau tare, gobe da jini kai ba nawa bane.
Hamid yaja guntun tsaki yana dubanta dan ya kasa yi mata magana saboda tsantsar rainin wayonta, wato harta manta da rashin kunyar data yi masa ɗazun, Madina ta zo ta zauna a gefen gadonsa nan take warin hamamin jikinta ya naushi hancinsa, duk da tana ƙamshin turare amma sai da yaji wani hamami na daban, cikin tsananin ɓacin rai ya sauko daga gadon ya isa ƙofa ya buɗe mata.
Tashi ki fita mini daga ɗaki kafin ki saka na amayar da abincin dana ci.
Madina miƙewa tsaye tayi tana duban jikinta tare da baje hanci dan jin ko tana wari, amma bata ji komai ba duk da tasan yau bata yi wanka ba.
Hamid wulaƙancinka ya kai har kayi mini haka, Madina ce fa wacce kake rawar ƙafa akanta lokacin ina gida, kwata kwata wata ɗaya da kwanaki har na cacanci irin wannan tsanar.
Zo ki fita nace miki domin bani da lokacin ɓatawa da jin ƙorafinki, dan na kula kullun ba kya rasa abin faɗa na ƙorafi.
Shuru tayi tama kasa yin wani magana saboda tsabar takaici sai kawai ta wuce ta fita tana jin tuƙuƙin baƙin ciki yana turnuƙota, yanzu ta tabbatar da lallai Sakina da shirinta ta dawo dan gashi lokaci ɗaya ta kasa gane kan Hamid ya ƙara rikice mata, koda ta fice Hamid ya bita da cewa.
Kuma ban manta da iskancin da kika yi mini ba ɗazun, dole saina ɗauki mataki akan ki.
Ya ƙare maganar yana banko ƙofar da mugun ƙarfi ya rufe da key, Madina da zubar hawaye ta wuce ɗaki jikinta har rawa rake yi saboda ɓacin rai, wayarta ta ɗauka taga ƙarfe sha ɗaya da kusan rabi, duk da dare yayi bai hana ta kira Maman Murja ba a waya wacce ita kuma tana turakar oga, tana ganin kiran Madina ta miƙe tana cewa mijinta tana zuwa sai ta fice, ta isa ɗakinta lokacin har kiran ya katse tana ƙoƙarin kira sai ga Madina ta kuma kira ta ɗaga da sauri, sai taji Madina ta fashe mata da kuka cikin tsantsar kulawa ta soma tambayar ta meke faruwa, Madina cikin kuka ta soma cewa.
Sakina ta yi nasarar shiga tsananina da Hamid wlh korata yayi daga ɗakinsa, wai karna saka shi yayi amai.
Ikon Allah ko dai warin jaɓa ta saka miki dan kin san ana jifar mace da irin wannan sihirin. Amma ta dawo ne da kike maganar Sakina.?
Eh mana ta dawo ɗazun kwatsam na ganta har girki tayi masa fa yaci ya koshi, da kafewa yayi wai dole kwanan Sakina ce sai da ta saka baki kafin ya yarda kwana nane.
Tafɗi ai ko shikenan ta riga ta gama asirce shi tunda har tayi masa girki yaci to ta gama barbaɗe a ciki, dan haka ki yi haƙuri zuwa da safe zan kira malam duk yadda muka yi dashi zan faɗa miki yanzu ki daina kukan haka dan ba zaiyi miki maganin komai ba, za muyi maganinta duk kullin data dawo dashi sai ya warware.
Nagode.
Madina ta faɗa tana matsar kwalla, sai suka yi sallama suka aje wayar, Maman murja ta riƙe haɓa tana cewa.
Wato Sakina sai da ta gama shiri ta dawo da ƙarfinta, aiko Madina kina ruwa dan wannan matar kafin Allah ce.
Data ƙare maganar ta mayar da wayarta silent ta nufi ɗakin mijinta, dan yau so take ta tatiƙe aljuhunsa wato ban gishiri in baka manda.
[8/18, 7:27 PM] Rahma Kabir: *ƘAZAMAR AMARYA*
Na
©®Rahma Kabir MrsMG.
Wattpad @rahmakabir
Page 37.
Da safe da wuri Sakina ta tashi ta yi musu abin karyawa ta sallami ‘yan makaranta da shi kansa Hamid ya tafi aiki kafin ta samu damar yin waya da yaya umma, nan ta dinga mata faɗar yin gaban kanta data tafi, Sakin ta bata haƙuri kana umma ta ɗaura da cewa.
Da kin zo kin sanar dani zaki tafi Kano ni mai mara miki baya ne, domin muyi maganin matsalarki tunda Hamid ya kasa sauya hali, amna kika yi gaban kanki kika saka mu cikin damuwa, madadin da kika kwana biyu a can ko ni kya nima ko kisa anty Jalila ta sanar dani kina gunta, kin san ni mai rufa miki asiri ne kodan hankalina ya kwanta.
Kiyi haƙuri yaya umma wlh lamarin ne naga kamar ku ba zaku yarda da hukuncin dana yanke ba shiyasa, amma bazan sake yin haka ba In Sha Allah.
To Allah ya amince ya kuma kyauta na gaba amma ba wata matsala ko?
Lafiya lau Alhamdulillahi.
To Masha Allah haka ake so kuma In Sha Allah Hamid yanzu zai yi miki riƙon mutunci dan ba ƙaramin damuwa ya shiga ba da bakya nan, kema kuma ki ƙara riƙe shi da muhimmanci Allah ya kauda fitina, in an kwana biyu ina nan zan zo.
In Sha Allah kafin ki zo nima zan zo ki raka ni gida dan ina tsoron haɗuwata da baba malam.
Ja’ira kema kinsan kinyi ba daidai ba amma bana tunanin zaiyi miki faɗa sosai, tunda su yaya Ali sunyi masa bayani duk bayanki suke bi, ko zai yi faɗa bai wuce yadda kika ɓoye ba’a san inda kike je ba, ko jiya faɗan da baba ya yiwa Jalila kenan.
Har naji hankalina ya kwanta to zan zo ranar juma’a In Sha Allah daga nan sai mu yini a gidan da yara.
Hakan yayi kyau Allah ya kaimu.
Sakina tace amin kana suka yi sallama ta aje wayar ta kwanta dan ta huta, Rauda kuma tana zaune a gefenta tana wasa.
….
Hamid ko da ya fita aiki bayan ya ɗan rage abubuwan da suke gabanta sai ya kira Anty Aisha yayar Madina, bayan sun gaisa sai yake sanar da ita dalilin kiransa akan matsalolin Madina, kaf babu wanda ya ɓoye mata ya ɗaura da cewa.
Ni babban damuwata shine yadda take da ƙazanta hatta wanka bason yinsa take yi ba, Fisabilillahi taya za ayi rayuwa mai daɗi da ita, shiyasa na kira ki ko da yadda za ayi magana da ita ta gyara, dan gaskiya ta fara kaini bango duk haƙurina yana niman ƙarewa.
Subhanallahi abu bai yi daɗi ba amma kayi haƙuri In Sha Allah zanyi magana da momynmu za a tsawatar mata.
Cewar Aisha, nan Hamid yayi mata godiya kana suka yi sallama ya aje kiran ya cigaba da aikinsa. Aisha kuwa nan take ta kira momy ta zayyane mata komai yadda suka yi da Hamid, momy ta ɗaura da cewa.
Ai dana aura masa ita ba bautar wahalar gidansa nace tayi masa ba, mai aiki ya kamata ya samar mata da mai girki ko ke kina aiki ne a gidanki?
Haba mom ni bana komai sai dai ayi mini wlh, nima nayi mamaki wlh tunda a zatona masu aiki sune za suyi mata hidima tunda yasan daga gidan gata ya aureta, kuma arzikinsa ya kai yayi wa Madina haka.
In baiyi haka ba ai bai nuna shi ƙanƙamo bane, tsabar mugunta ce da maƙo, dan haka zan kirasu duka su biyun nayi magana dasu.
Ya kamata dai dan wlh Hamid sai a hankali hatta motar daya yi mata alƙawari fa yaƙi bata.
Dama can makaryaci ne ya yaudareta da daɗin baki, ita kuma ta rufta tunda ba wayo ne da ita ba tabi daɗin soyayya.
Cewar momy cike da masifa, haka sukai ta ririta maganar daga nisani suka yi sallama. Momy ta kira Madina koda ta ɗaga ce mata tayi ta sanar da Hamid tana son ganinsu ita dashi anjima, to tace mata suka yi sallama, dan bata kawo tunanin komai ba tunda bai nuna alamar zai kai maganarta gida ba, sannan ma da safe kafin ya fita aiki har ɗaki ya sameta ya sallameta kuɗin mota kamar wani abu bai faru tsakaninsu jiya ba. Ko da ta fita aiki gidan maman murja taje suka yi magana akan tayi waya da malam ya tabbatar mata da yana aiki mai zafi akan lamarinta ta kwantar da hankali, haka suka rabu ta wuce aiki cike da damuwa.
Wajen ƙarfe biyu da mintuna Madina ta kira Hamid akan yazo ya ɗauketa suje gidansu momy tana son ganinsu dan lokacin ta tashi daga aiki, Hamid yace ta wuce daga nan zai sameta a can, bata yi mamaki ba dan tasan an sauya mata Hamid ɗinta dan in da dane jikinsa yana rawa zai ce to dan yasha ɗaukota daga gurin aiki ya mayar da ita gida lokacin da suke soyayya kafin suyi aure, amma kamar kiftawar ido komai yana niman zama tarihi, tayi ƙofa ta miƙe ta gyara fuskarta da powder kana ta yi sallama da mutanen office ɗinsu ta wuce gida. Koda ta isa minti bai fi goma sha uku ba da isarta shima Hamid yazo, bai tsaya kiranta ba ya shiga gidan kaitsaye tunda ya zama ɗan gida shima, sannan ma an san da zuwansa tunda momy ce tayi kiransu, daya isa ƙofar falo ya buga tare da buɗe murya yayi sallama, Ladi mai aiki ita ce ta zo ta buɗe masa da yi masa iso ciki ya samu guri ya zauna suka gaisa kana ta shiga kitchen ta kawo masa ruwa da lemun gora da kofi a tire ta aje a center table ta wuce, ba jimawa sai ga momy ta fito tare da Madina duk suka zauna Hamid cikin girmamawa ya gaisheta kana suka ɗanyi shuru, Madina dai bata ce masa komai ba sai cika take yi tana batsewa akan ƙararta daya kawo, dan sun fara maganar a ɗakin momy kafin zuwansa, daga bisani momy tayi gyaran murya ta soma da cewa.
Na samu saƙon ka a gurin Aisha akan Madina, shiyasa nace kuzo tun kafin abin ya ɗauki lokaci.
Ta ƙare maganar tana jan fasali, Hamid ya ɗan sunkuyar da kai yana cewa.
Hakane, kuma abin yaci tura ne yasa har na faɗa wa Anty Aishan.
To dama baka san cewa Madina ‘yar gata ka aura ba?
Na sani.
Hamid ya bata amsa yana mamakin tambayarta, sai yaji momyn ta cigaba da cewa.
To gaskiya in har Madina tana ƙazanta ko kai ne kaso haka saboda bata saba da wahalar aikin gida ba, anan gidan kafin tayi aure masu aikinmu mutum biyu ne suke yi mata duk hidimar da take so, dan haka in har bata iya girki da gyaran gida ba karka ga laifinta domin bata saba da su ba, sannan kuma duk yadda kake da arziki ai abin kunya ne ace matanka suke yin hidimar gidanka, kamata yayi masu aiki keyin komai dan kana da kuɗin, dan haka abinda zan faɗa maka bana aura maka ita bane dan taje ta yi wahala ba, a’a gidan aurenta so nake yafi nan gidan jin daɗi, batun kuma wanka wannan duk zanyi mata faɗa zata bari dama anan mai aiki ce take haɗa mata ruwan da komai iyaka nata tayi ne ta fito, kaga kuma kana sama mata masu yi ba zaka ƙara ƙorafin ƙazantarta ba.
Momy data kawo nan a maganarta tayi shuru tana dubansa dan fuskarta ma a haɗe yake saboda haushin daya bata, Hamid dai sunkuyar da kai yayi ƙasa kamar ruwa ya cinyeshi bai taɓa zaton haka daga momyn Madina ba, kenan duk iskancin data ke yi masa ɗaurin gidi ne daga gun mahaifiyarta, yanzu ya tabbatar da maganar Habib na cewar ya auri ‘yar mace, momy jin bazai yi magana ba sai ta daura da cewam
Shiyasa na kiraku kuzo domin in faɗa maka haka dan Madina kam bata san duk wannan wahalar ba, in dai zaka riƙeta amana to zaka ɗaura daga kulawar da muke yi mata ne ka ƙara akan namu. Sannan ina so in baka shawara ka raba mata gida da uwargidanka, dan gaskiya wannan gidan naka yayi kaɗan da aje mata biyu, nasan ba wannan ne kaɗai gidanka ba, ga kuma alƙawarin mota daka yi mata tace har yanzu baka bata ba, Hamid ya kamata ka zama mai cika alkawari ka faɗa ka cika, Ke kuma ban sanki da rashin kunya ba, ki daina yi masa rashin kunya tunda ba haka na tarbiyyantar dake ba, dan haka zaka iya tafiya ita kuma zan ƙara yi mata faɗa.
To nagode Hajiya sai anjima.
Hamid ya faɗa yana miƙewa tare da zaro dubu goma daya waresu a aljihunsa tun kafin ya shigo gidan ya aje akan center table yana cewa.
A Kara cefane ba yawa.
Mai yawan kenan angode ka gaida gida.
Cewar momy, Madina ta miƙe tabi bayansa har ya kusa fita gate kafin ta dakatar dashi da cewa.
Hamid ka ƙara mini kuɗin mota sai anjima zan dawo.
Tsayawa yayi ya zaro kuɗi a aljuhunsa ya cire dubu biyu ya bata ta amsa ba tare da yace mata komai ba ya juya ya fita, bata damu da yanayinsa ba ta koma cikin gida dan sosai taji daɗin maganganun da momy tayi masa, ƙila zata samu sassauci daga abinda yake yi mata.
Hamid da kyar ya iya tuƙa kansa yana tafe yana tunanin abinda momy tace masa, gabaɗaya jikinsa babu ƙarfi dan ba ƙaramin sare masa guiwa tayi ba, dana sani sosai ya samu kansa a ciki na auren Madina, yana jin da wuya aurensu yaje ko ina dan baya jin zaiyi abu ɗaya daga cikin maganar momy, dan aiki dai ya ji zai iya barinta kuma yace ta kawo mai aikin gyaran sashinta, banda wannan baya jin zai iya yi mata wani abu dan itama ba kyautata masa take yi ba kuma duk zuciya tana son mai kyautata masa, sannan ma in har mota ce to a yanzu Sakina ce ta cancanci ya bata mota dan ya tabbatar itace matar rufin asirinsa wacce take bashi dukkan kulawa da ƙauna ta gaskiya, hawaye yaji ya cika masa ido tunawa da wasu abubuwan da yayi mata a lokacin da zai auro Madina, tabbas ya kamata ya sakawa Sakina da alkhairi bisa haƙurin zama dashi da tayi na wulaƙancin da yayi mata, haka ya koma gurin aiki jiki a sanyaye dan baya jin da akwai wanda zai sanar dashi wannan abin da maman Madina tayi masa, dan yasan ba za a faɗa masa shawara mai daɗi ba akan haka, addu’a kawai zai dage dayi Allah daya ƙaddara masa aurenta shine kaɗai zai kawo masa mafita.
****
Sakina.
Wajen ƙarfe huɗu ta fito tsakar gida ta aika Iro ya siyo mata kuɓewa ɗanya da man shanu, ta koma ciki ta ɗaura sanwar tuwon Masara, sai sauran pepper chicken fin nan ta ƙara gyara shi ta adana. Koda Iro ya kawo mata cefanen har ta yi talge tana shirin tuƙa tuwo, nan ta shiga aikin ɗaura miya ta kuma soya man shanun ta adana man sai ta ɗiba kaɗan tasa a sanwar miya, ta zuba ƙashi a ciki ya shiga dahuwa, sai wajen ƙarfe shida da rabi da gama komai ta jera su a dinning kana ta koma ɗaki tayi wanka, fitowarta an soma kiran sallar magrib dan haka sai da ta fito tasa yaran suka shiga ɗaki dan yin Sallah kana ta zo ta gabatar da nata sallar. Data idar ta zo madubi ta shiga shiryawa, kwalliya ta yiwa fuskarta ɗan daidai kana ta ciro ɗaya daga cikin kayan da suka siya da Jalila, riga da siket ‘yan kanti, rigar fara ce kuma ‘yar daidai ta kama jikinta kuma in ta daga hannunta sama cibiyarta zata fito saboda ‘yar ƙarama ce, sannan siket ɗin iya guiwa mai faɗi da baza pink color ne kuma da ratsin baƙi baƙi a jiki, ita kanta data saka kayan sun zauna a jikinta ba ƙaramin kyau suka yi mata ba, ta ɗauki ƙaramin baƙin gyalenta na abaya ta ɗaura tare da baɗeshi tayi ɗauri mai kyau, sai ta feshe jikinta da turare ta tsaya tana kallon kanta a madubi sai taga kamar ba ita bace, sai kuma ta soma kunyar fita da kayan har yaranta su gani balle kuma Hamid ya ganta da su, to abu ne da basu saɓa gani ba tasan sai ta zame musu abin kallo, to wannan kallon nasu ne zai sa taji kunyar, haka ta gama ta adana komai ta dawo bakin fado ta zauna ta shiga taraddadin yadda zata fita, a haka ne har aka kira sallar isha’i sai ta miƙe ta ɗaura zanin sallarta ta saka hijab ta gabatar, koda ta idar tana zaune a dadduma tana lazumi, a lokacin ne taji shigowar motar Hamid, ta yi saurin yin addu’a ta miƙe ta naɗe kayan sallar ta adanasu ta koma jikin madubi ta gyara fuskarta da soson powder kana ta ƙara fesa wani turare ta juya ta nufi ƙofar fita sai da ta tsaya jim tana lissafi, wanda a lokacin har Hamid ya shigo yaran suna yi masa sannu da zuwa Rauda kuma ta isa gareshi da gudu ta rungume shi, ya duƙa dan ya ɗauketa a lokacin ne Sakina tayi shahada ta fito, ta tsaya jikin ƙofa ta kasa tafiya tana kallonsu, dai dai lokacin Hamid ke ɗagowa da Rauda ya ɗauketa sai kuma ya sauke kallonsa ga Sakina da take tsaye tana sakin murmushi, mutuwar tsaye yayi ya shiga kallonta kamar wanda ya warke cutar makanta, gani yake kamar zigo take yi masa a wani shiga da bai taɓa ganinta dashi ba, yadda ya buga fosta yana kallonta baki buɗe yasa yaran suma duk suka waiga suga me Abbansu yake kallo, ganin Mamansu da wannan kayan yasa suma suka zuba mata idanu, Mufeeda kuwa tsintar kanta tayi tana murmushi tare da gimtse bakinta dan kar dariyarta ta fito, Baba ƙarami ya miƙe ya nufi Sakina.
Laaaa Mama kinsa kayan yara.
Daƙuwa tayi masa da hannu.
Kaci gidanku na ce.
Sai duk suka tuntsire da dariya, Hamid shima ya kasa riƙeta ya shiga yi, ya aje Rauda ya ƙaraso gaban Sakina.
Wai Sakinata ce haka ko wata ce aka sauya mini, wannan irin bazata haka, gabaɗaya tunda kika dawo kike bani mamaki fa, meye wannan sirrin da kika samo ne a Kano matar Hamid? Kin ganki kuwa, kinyi matuƙar yin kyau sosai bana wasa ba, gaskiya na siya wannan wanka ki saka masa farashi ko nawa ne zan biyashi.
Ya ƙare maganar yana ciro wayarsa daga aljihu ya shiga wajen ɗaukar hoto ya seta camera ya soma ɗaukarta a wayarsa, ita kuwa banda murmushi ba abinda take yi bakinta ya ma kasa rufuwa, idanunta har wasu ruwa ruwa suka yi na hawayen farin ciki, daga bisani Hamid matsowa yayi kusa da ita ya shiga ɗaukar su salfie, yaran sai dariya suke yi suna cewa sunyi kyau, a dai dai wannan lokacin Madina ta fito daga ɗakinta dan hayaniyarsu taji yayi yawa, dama tunda ta shigo gidan ta lafe a gado ta kasa motsin kirki, yadda taga suna hoto gwanin burgewa yasa taji wani tuƙuƙin baƙin ciki ya turnuƙota, sai taja dogon tsaki ta juya a fusace ta shiga ɗaki tare da banko ƙofa, wanda hakan yasa Hamid ya juya ya kalli ƙofar ya dawo da kallonsa ga Sakina suka haɗa ido sai suka sakarwa juna murmushi, Sakina tana cewa.
Muje kayi wanka sai muci abinci.
Gaskiya abinci zan fara ci dan yau babu wani abincin kirki a cikina bayan na safe, da yunwa na shigo gidan.
Muje to mu ci.
Ta faɗa tare da kama hannun Rauda data matso kusa da ita, suka yi gaba Hamid ya bita da kallo zuciyarsa cike da farin cikin ganinta a haka, duk wani ɓacin rai da ƙuncin da momyn Madina ta saka shi a ciki, ji yayi ya tafi sai farin cikin ganin Sakina, ji yayi da tun farko haka matarsa ke yi ƙila da bai kalli kyale kyalen Madina ba balle ya auro ta, ya tabbatar zuwanta Kano Anty Jalila ta yi mata sabon karatu, kuma ga dukkan alamu ta ɗauki darasin kamar yadda ta ɗaurata akai, babu abinda zai cewa Jalila sai addu’a da fatan gamawa lafiya.
[8/19, 6:54 PM] Rahma Kabir: *ƘAZAMAR AMARYA*
Na
©®Rahma Kabir MrsMG.
Wattpad @rahmakabir
Page 38.
Koda suka kammala cin abincin a falo suka yada zango suka cigaba da kallo, wajen ƙarfe tara Sakina ta sallami yara duk suka shiga ɗakinsu suka kwanta, dan yanzu Rauda ta fara yarda ta kwana da Mufeeda hakan yasa falon ya rage sai su kaɗai, Sakina ta muskuta tana dubansa.
Ya kamata kaje ka watsa ruwa naga lokaci ya tafi.
Hmmm kinsan kuwa na sha’afa, gabaɗaya yau ɗin nai kin rikita mini kai ba ga kwalliyarki ba ba ga abinci ba, komai yayi Masha Allah, wai in tambayeki mana.
Ina jinka Abban Mufeeda.
Yauwa! menene sirrin ne naga gabaɗaya duk kin sauya? Jalila ina ga ta baki wani maganin daya sauya ki ba kika dawo ‘yar caras dake ko? wai dama haka kike duk tsawon lokacin nan kika nima mayar da kanki tsohuwa.
Ya ƙare maganar yana ‘yar dariya, itama dariyar tayi bata ce komai ba dan ba tada amsar da zata bashi saboda basu saba hira irin haka ba, Hamid ya ɗaura da cewa.
Da tun farko nasan zaki iya sauyawa da tuntuni na turaki Kano kin ƙaro cos a gun Jalila, ƙila da babu abinda zaisa na ƙara ma aure wlh.
A’a fa ka daina wannan maganar dan bazan mance irin giyar soyayyar amaryarka daka sha ba, ka dinga amayar mini da ɗokin zuwanta a gidan nan, dan haka kayi shuru kawai.
Hmmm Sakina kenan, ba zaki ganne bane amma ina mai ƙara baki hakuri akan faruwar wasu abubuwan, Allah ya huci zuciyarki yanzu muje nayi wanka sai ki haɗo mini cofee nasha kafin mu kwanta.
To tace masa tana murmushi ta miƙe tayi gaba ya bita a baya, sai da ta fara haɗa masa ruwan wanka kafin ta fito ta wuce ɗakinta ta fara kuskure bakinta da mouth wash, ta wanke kwalliyar fuskarta ta fito ta shafa mai a fuskar da man baki, sai ta ciro kayan da zata saka, sai dai tsayawa tayi tana tunanin saka su dan bata taɓa saka irin su ba bata so Hamid ya gano ta zaƙe da yawa, dan haka ta mayar da kayan masu shara shara ta ɗauki wasu masu kyau riga zuwa rabin cinya da dogon wando, ta saka su tare da shafe jikinta da humra mai sauƙin ƙamshi ta saka turaren data ware na barci a jikin kayan ta zura hijab da nufin fitowa, ta isa kitchen dan haɗa masa cofee.
Madina tunda taji sun bar falon sai ta fito da sauri ta wuce kitchen dan ta ɗiba abincin da suka rage taci kamar dai jiya, ta buɗe taga tuwo nan take ta haɗiye miyau dan sosai cikin jikinta ya saka mata ƙaunar tuwo, ta buɗe miyar taga miyar yauƙi ne nan ma taji daɗi sosai dan haka cikin sauri ta ɗauki plate ta saka tuwon da miya ta ja kujera ta zauna ta soma saka loma tamkar tana cin nama saboda mugun daɗin da yayi mata, a wannan yanayin ne Sakina ta shigo kitchen ɗin, Madina tayi saurin aje plate a gefenta ta miƙe tare da ɓoye hannunta baya tana wani cin magani da zazzare ido kamar mage a kwali, sosai ta bawa Sakina dariya dan sarai taga yadda ta zura lomon tuwo a bakinta lokacin da ta shigo, sai ta gimtse dariyar tayi kamar bata ganta ba ta isa gefen inda kayan kitchen ɗinta yake, nan ta shiga haɗawa Hamid cofee ɗinsa harta gama Madina tana nan a tsaye kamar fosta ita bata cigaba da abinda take yi ba bata kuma fita ba, Sakina ta yi kamar ta fita sai Madina ta koma ta zauna ta ɗauko plate ɗinta ta zabtari ƙaton loma, takai bakinta kenan Sakina ta ƙara shigowa zata ɗauki cokali kuma da gangan ta ki ɗauka dan dai ta ƙara kama Madina, ai Madina tsayawa tayi ga lomar tuwo takai baki bata ƙarasa ci ba ga kuma plate a hannunta, wani sabon fosta ta kuma yi, a wannan lokacin Sakina sai da tayi dariya mai sauti.
Daɗi na da gobe saurin zuwa. Allah na gode maka.
Ta faɗa tare da ficewa tana dariya, Madina wani haɗe rai tayi tana cin magani, sai dai duk rashin kunyarta sai da taji nauyin ganinta da Sakina tayi da abincinta tana ci, tunawa tayi da lokacin da tayi mata rashin mutunci kan an ɗibar mata dambun da Hajiya ta kawo mata, maganar Sakina yana nufin habaici ta sakar mata kenan, taja guntun tsaki ta kai loman bakinta tana cewa a ranta.
Ko meye ma ki faɗa sai na ci dan uban mutum, ai Hamid ne ya kawo abincin ba ke ce kika siya ba, dan dai kin dafa naci…
Ta ƙare da sake jan tsaki, haka ta tura tuwon ta cinye tas kana ta miƙe tana sakin gatsa, ta isa sink ta wanke hannu kana ta aje plate ɗin a gurin ta dawo itama ta haɗawa kanta tea mai kauri yaji madara mai yawa, anan taye tana kurɓa harta shanye shi tas ta koma kuma ta shiga ɗibar madara a tafin hannu tana hambuɗa a baki sai kace wata ƙaramar yarinya, nan take kuwa cikinta ya murɗa mata taji zuciyarta ta fara tashi saboda man shanun dake miyar ya fara taso mata, da alama cikin jikinta baya sonshi ga kuma mugun haɗe haɗe, ansha tea mai kauri bai isa ba ta koma hambuɗar madara, sai ta zauna a kujera dan ta huta ganin kamar dagaske amai ke yunƙuro mata, ta miƙe da sauri amma ina ya riga yazo nan ta sake shi a tsakar kitchen ɗin, sai da ta amayar da abincin data ci tas kana ta fara aman ruwa da majina, data gama haka ta tsallake shi ta fito falo nan ma aman yana turnuƙota tana tafiya tana sakin aman ruwa da majina duk ta yaryaɗa a tiles har ta isa ɗakinta, ta faɗa bayi tayi yunƙuri iya yunƙuri daga bisani ya lafa mata ta dawo gado ta kwanta rubda ciki tana mayar da mumfashi.
Sakina koda ta fita ɗakin Hamid ta shiga ta aje masa cofee ɗin kana ta cire hijab ɗin data saka ta ninke ta koma gefen gado ta zauna tana danna waya, a haka ya fito daga wanka ya sameta zaune sai ya shiga kallonta yana jin wani farin ciki musamman yadda yaga sumar kanta ya kwanta luf sai sheƙi yake yi gashi baƙi tayi parking ɗinsa da ribom, ba laifi tana da suma dama rashi gyara ne amma data saka rilaxer sai ya yi tsawo ya ƙara kyau ya daina curewa guri ɗaya, ɗago da kai tayi taga ita yake kallo ta sakar masa murmushi shima ya mayar mata, kana bai ce komai ba ya isa gurinta yasa hannu ya shafa kan sannan ya cire rebom ya baje sumar, nan take ya sauka kan gadon bayanta. Ya koma jikin madubi ya soma shafa mai yana cewa.
Daga yanzu in dai kanki a tsefe yake to haka nake son ganinsa ki sake shi ya sauka a bayanki, dan yafi yi mini kyau musamman in mun zo barci.
An gama ranka yadaɗe duk abinda kake so shi za ayi.
Ta bashi amsa, murmushi yayi ya isa wajen kayansa ya ɗauki singilet ya saka yana cewa.
Yau za muyi barci da wuri domin ina son fita da sassafe akwai mutanen da zan gani a office, dan haka abin kari ba sai kinyi dani ba.
To Allah ya kaimu. Ga coffe ɗin nan karya huce.
Ya zauna gefenta ya ɗauka ya fara kurɓa suna hira, yana bata labarin company da irin nasarar da suke samu, dama In suna zaman lafiya in hirar tazo masa yana faɗa mata cigabansa, ita kuma ta bishi da addu’a, haka suka kai wajen goma da rabi kafin suka kwanta suka kashe haske, Hamid yace ta ɗan matsa masa ƙafarsa saboda takalmin daya saka yau cover shoe sun matse masa ƙafar baya jin daɗinsa, tace to kana ta soma matsa masa daga nan kuma karatu ya sauya, dan Sakina tun tuna matsa ƙafa har ta koma tana shafa ƙafar tare da ɗan tsigo sumar dake jikin fatar ƙaurinsa, nan Hamid ya ɗauki hanya tun suna basarwa har dai suka bada kai bori ya hau.
Da asubahi Hamid ya farka dan lokacin har an idar da sallah, ya jingina bayansa da gado ya kurawa Sakina ido dake fegensa wanda gashinta ya bazu akan gado barcinta kawai take sha cike da natsuwa, hakanan yaji Hawaye nabin kuncinsa na tsantsar farin cikin da bazai iya misaltashi ba, bai taɓa zato ba bai taɓa tsammanin sake jin Sakina a nayi irin na baya ba lokacin da take asalin ƙuruciyarta, yasan dai budurci baya dawowa amma kuma wannan karan lamarin yazo masa a bazata bai taɓa zaton Sakina zatayi ɗanɗano mai gamsarwa da kuma bashi haɗin kai yadda ya kamata ba irin jiya, tun dawowarta take shayar dashi ruwan mamaki, sai dai kuma na daren jiya yafi ko wanne abin mamaki da ɗaure kai, tabbas ba Sakinarsa bace ta da yanzu wata ce sabuwa a gabansa yake kallo, daren jiya yana ɗaya daga cikin tarihin da zai iya kafashi a rayuwarsa, wani irin sabon so da ƙaunar Sakina yaji yana bin dukkanin wani ɓargon jiiinsa wanda ya sa shi kasa tsaida hawayensa na tsantsar tausayinta da dana sani akan irin tarin abubuwan da yayi mata a baya na muzgunawa, idan har Sakina tana da laifi gurin bashi kulawa shima yanada laifi tunda baya zama da ita ya fito mata da matsalolinta domin ta gyara, ya tabbatar Jalila itace tsaunin sauya Sakina zuwa sabuwa, tabbas tayi dogon hange da nazarin sanin asalin inda matsalar aurensu ya dosa kuma ta ɗaura Sakina akan gyaransu, yana jin dole ne ya yiwa Jalila baban kyauta domin bajintar da tayi wajen gyara masa rayuwar gidansa. Haka ya ɓata lokaci yana tunanin abubuwa sai da Sakina ta motsa zata sauya gefen kwanciyarta yasa shi saurin goge hawayensa ya sauko ya shiga toilet. Koda ya fito ya saka jallabiya ya tayar da sallah, wanda kabbarar daya yi yasa Sakina ta farka a gajiya ji tayi itama abinda ya faru jiya kamar a mafarki, bata taɓa zaton haka auratayya yake da daɗi har haka ba sai a jiyan, lallai tasan tana da tarin laifi sosai a rugujewar jin daɗin aurensu, ba tada abinda zata cewa anty Jalila sai fatan gamawa lafiya da samun aljanna maɗaukakiya, ta fito da ita duhu zuwa haske ta wanzar mata da wani jin daɗin da bata taɓa zato ba. Yau ta tabbatar da kyawun kayan BOJUWA HERBAL’S, in dai ko hakane itama zata yi amfani da wannan damar wajen ceto rayuwar ma’aurata ta fara oder ɗin kayan tana sayar dasu a cikin gidanta, tana jin wannan business ɗin zata fara tana amsowa daga gurin BOJUWA HERBAL’S BY SURAYYA. Saiwowi ne da basu da illa daga saiwowin sanyi, da maganin sanyi. Saiwowin dahuwar kaza, dafaffiyar gimbiyar kaza. Silky kola na musamman. Tsumin sababi. Hakkin daka gangariya. Gumba special. Gaban ayu. Dukkan Saiwowi da kayan daga Chad suke zuwa.
Ga mai buƙatar kayan ku tuntuɓi wannan number 08032773332. Surayya HALIN YAU.
Haka Sakina ta yi zurfi a cikin tunaninta har saida taji Hamid ya sallame kafin ta buɗe ido tana dubansa, wanda shima a daidai lokacin idonsa yana kanta, nan take suka yi ido huɗu sai suka sakarwa juna murmushi, ta miƙe ta mayar da rigar barcin ta sauko ta shiga bayi, bata fito ba sai da ta tsaftace jikinta tayi wanka kana ta fito ta zura hijab, lokacin Hamid ya saka takalmin silifas ɗinsa zai je mota ya ɗauki wasu takardu daya aje yace.
Kivje ki shirya bari in ɗauko wasu takardu ina zuwa.
To tace masa sai ya sa kai ya fito, sai dai lokacin daya ɗaura ƙafa kan aman Madina ga santsin tiles, nan take ya zamar dashi ji kake suuuuu sai tim ya faɗi a ƙasa, da sauri Sakina ta fito, ganinsa zaune dirshen a ƙasa ta rafka salati.
Lafiya ka faɗi.?
Wlh zamewa nayi, kamar ruwa ne a gurin.
Hamid ya faɗa yana duba ƙasan tiles ɗin sai ya kunna hasken touchligt ɗin wayarsa nan ya shiga haskawa, ya miƙe da sauri yana bin duk inda yaga ruwa ruwan mai haɗe da majina, ya ɗago yana kallon Sakina.
Kinga ruwqn majina ne da kamar miyau.
Ya faɗa yana cigaba da haskawa dabin gurin, sune har suka dangana da kitchen ganinsa a buɗe, nan take ƙarnin aman Madina ya fara ziyartarsu, Hamid yana gani yayi baya yana koro salati tare da kawar da kai, Sakina itama salatin tayi.
Abban Mufeeda amai akayi fa.
Duk yadda aka yi Madina ce dan nasan ita ce uwar ƙazanta, amma dama taci tuwo ne.?
Nan saki ta saki murmushi tunawa da tayi jiya ta kamata tana cin tuwon, ta bashi labari bata ma kai aya ba yace.
Habawa wlh itace zata yi wannan aikin, in banda iskanci tayi amai ta barshi a gurin sannan a cikin kitchen, innalillahi wa inna ilaihir raji’un! wannan ƙazantar har ina. Ina zuwa wlh sai ta kwashe shi.
Ya faɗa tare da fita a fusace zuwa ɗakin Madina, Sakina itama fitowa tayi ta shiga ɗakinta dan ba kaya daga ita sai towel, ta zauna ta shafa mai kana ta saka jallabiya ta zura hijab da nufin tayar da sallah, amma hayaniyar Hamid da ta ji yasa ta fito da sauri.
Hamid koda ya shiga ɗakin Madina ya sameta a kwance cikin bargo sai kwasar barci take yi, tsabar yadda yake cike da haushinta bai tsaya ya tasheta cikin mutunci ba, sai yaye bargon yayi ya figzo hannunta, sai ta farka a firgice, ganin Hamid ne yasa ta ƙara lafewa.
Meye haka kuma dan Allah.
Tashi maza muje ki goge iskancin da kika yi mana a kitchen ƙazamar banza kawai.
Ya faɗa yana figota daga gado ya kama hannunta, Madina ta fashe masa da kuka tana tirjewa amma haka ya jawota suka nufi kitchen yana surfa uban masifa, a lokacin ne Sakina ta fito tana cewa.
Haba Abban Mufeeda ka bita a hankali mana kar yara su fito suga haka.
Bar ni da ita Sakina, wlh yarinyar nan tayi masifar raina wa mutane hankali ta rasa inda zata yi amai sai a kitchen, sannan ta shure ƙafa ta barshi a haka bata gyara ba, ace tsabar ƙazanta har falo tabi ta ɓata, wannan ai masfa take son saukar mana dashi, ta ja kwalera duk ta kama mu.
Sakina ta kasa magana sai ta matsa gurin da ya tsaya ta kama hannunsa ta na son kwace Madina, nan taji jikinta rau yayi zafi sosai ta kalli Hamid.
Da alama ba tada lafiya ko baki yadda jikinta yayi zafi ba, dan Allah ka cikata ka fita waje ka kira Iro yazo da tsumma ya kwashe sai ya gyara gurin, nima zan yi nawa mopoing ɗin, dan dai bana son amai ne amma da ni ce zan kwashe.
Sakina ta ƙare maganar tana kwace hannun Madina daga na Hamid, yaja gutun tsaki ya yi hanyar waje dan kam baya jin zai cigaba sa musu da Sakina tunda ta saka baki dole Madina taci albarkacin ta, sai a lokacin Madina ta buɗe murya tana ce masa.
Allah sai ya saka mini wlh, kuma ka cigaba da wulaƙantani akwai ranar ƙin dillanci.
Bari na dawo zaki maimaita abinda kika faɗa.
Hamid ya faɗa tare da ficewa waje, Sakina kam ganin abin na Madina ba mutunci sai ta juya da nufin shiga ɗaki, Madina ta tareta da cewa.
Ke kuma munafuka In Sha Allah sharrinki zai kome miki, nafi ƙarfinki jahila kawai.
Sakina jin zaginta data yi na jahila yasa ta rumtse ido ta buɗe tsabar ɓacin rai, girgiza kai kawai tayi ta shiga ɗaki bata kulata ba, sai dai kuma tayi da ‘yar halak, Hamid ko yanka namanta zai yi ba zata sake saka baki ba In Sha Allah zata gwada mata aikin ilimi.
[8/20, 7:21 PM] Rahma Kabir: *ƘAZAMAR AMARYA*
Na
©®Rahma Kabir MrsMG.
Wattpad @rahmakabir
Page 39.
Iro ne ya gyara gurin aman kana ya fita, sai Sakina ta fito tayi mopping ɗin kitchen kana ta ɗaura musu abin kari, Hamid kuma shiryawa yayi sai yayi sallama da Sakina ya fice abinsa bai sake bi ta kan Madina ba. Haka ta gama shirya ‘yan makaranta suka tafi kana itama ta samu damar hutawa da nufin anjima zata yi sauran aikinta.
Madina jin ƙarar fitar motar Hamid yasa ta soma kukan baƙin ciki akan yadda ya nuna ko in kula da rashin lafiyar ta, hakan yasa ta ɗaga waya ta kira momy tana kuka ta faɗa mata bata jin daɗi kuma Hamid ya sani amma ya fice abinsa, momy ranta ya ɓaci sosai sai kawai tace ta shirya zata zo ta ɗauketa suje asibiti, haka suka rabu a wayar Madina ta gyara kwanciya dan yadda take jin jikinta ko wanka ma ba zata iya ba. Koda momy ta zo a bakin gate tayi parking ta kira Madina a waya akan ta fito su wuce, da kyar ta iya miƙewa ta saka hijab ta fito ta shiga motar suka kama hanya.
Binciken farko da likita yayi ya tabbatar da tana da maleria ne sannan kuma da laulayin ciki, nan ya ɗaurata akan magani daga bisani ya sallamesu, Momy gida ta wuce da Madina sai da ta tabbatar da ta samu natsuwa taci abinci da magani sannan tayi wanka kafin tasa Madina ta kira mata Hamid a waya, sai da tayi masa kira uku ana huɗu ne ya ɗauka a fusace dan ya manna mata masifa, amma jin ba muryanta bace tayi sallama ya sashi sausauta fushinsa, momy cikin haɗe rai tace.
Da Momyn Madina kake magana, yanzu Hamid duk bayanin da nayi maka akan yadda Madina take rayuwa bai gamshe ka ba, ace yarinya tana rashin lafiya amma ka shure ƙafa ka barta cikin wani hali, to gaskiya idan kasan ba zata iya riƙe ta ba to ka dawo mini da ita bazan jure ka wulaƙanta mini ‘ya ba wlh.
Ayi haƙuri momy babban uzuri ne ya fitar dani, kuma dama na bari inna dawo gida zamu je asibiti.
Na riga naje na ɗauketa munvje asibiti taga likitanmu, dan haka in ka gama abinda kake yi ka zo ka ɗauketa a gida, amma gaskiya bana so daga aure a fara samun matsala da kai, dan ba haka muka yi zato ba a gunka.
In Sha Allah za a gyara ayi haƙuri.
Abinda ya faɗa kenan sai ta kashe wayar, Hamid yasa duka hannunsa ya tallafe kuncinsa, shi dai kam yasan ya saka ƙafarsa a cikin damuwa, tsabar sakarci da rashin wayon Madina yake gani, a madadin ta kirashi sai ta kira mahaifiyarta dan kawai aga rashin kyautawarsa, abinda yasan Sakina bata taɓa yi masa ba kenan, hasalima bata taɓa kai kararsa gurin danginta ba shine ma yake faɗa musu matsalolinta, yanzu ne ya ƙara tabbatar da tarbiyyar Sakina da kuma haƙurinta, haka ya yini a office yana tunanin yadda makomar aurensu zai kasance da Madina, dan hanyar da ta ɗauko baya tunanin mai ɓullewa ce.
Yau da wuri ya dawo aiki dan bayan sallar La’asar ya shigo ya samu Sakina tana ta aikin girki a kitchen, duk da ba tayi wanka ba amma tana cikin kyakkyawar shiga wanda tayi tun tashinta barci ɗazu. Yayi wanka ya fito ya shirya ya sameta a falo tana aikin yanka ganyen latas, yana gyara karin hularsa yace mata.
Madam yau salad za muci kenan?
Eh shinkafa da miya nayi mana kuma kasan zaka so a haɗa da salad harma da cream salad ɗinsa.
Gaskiya ne shiyasa kike matuƙar burgeni, in dai a abinci ne ko ban baki zaɓi ba kinsan me zaki yi naci yayi mini daɗi.
Abban Mufeeda yau da gobe akace ƙaryata boka, zama ne da an jima kaga ya dace ace nasan wasu abubuwa dan gane da kai ba sai an faɗa mini ba.
Wannan gaskiya ne, ni zan je gidan su Madina ashe ɗazun mahaifiyarta ta kira wai ba tada lafiya maimakon ta kirani, shine yanzu zan je da ɗaukota, gabaɗaya na rasa ina yarinyar nan hankalinta yake sam ba tada lissafi, ɗazun fa zo kiga maganganun da maman faɗa mini, raina ya baci sosai amma haka na danne tunda ni na jawa kaina, auren nan matsala kawai ya jawo mini ya zame mini ciwon ido.
Allah ya bata lafiya, kasan sha’aninmu mata sai haƙuri kowa da irin lissafinsa. Amma kasan me nake so da kai.
Ya saka hula yana gyara zamansa sai ya zauna a cushing yana dubanta, ganin bazai ce komai ba yasa ta soma magana.
Hamid zan fi so ka riƙa riƙe maganar matsalar matarka ka daina faɗa mini domin hakan bai dace ba, nima bazan so kana faɗa mata abinda ya shafe ni ba, ya kamata matsayinka na babba ka zama mai kamanta adalci a fannin magana a tsakaninmu domin gujewa matsala nan gaba. Zanso ko faɗa ne zaka yiwa ɗayanmu to ka yi shi a sirri.
Ta ƙare maganar tana jan fasali tare da duban fuskarsa, jim yayi yana nazarin maganarta dan gaskiya ta faɗa saboda ya kasance baya riƙe sirrin nan, kuwa da duk matsalar Sakina yasha faɗawa Madina lokacin tana gida, hakan yasa Madina data shigo ta rainata har take jifarta da maganganun da Hamid ke faɗa mata, ya sauke ajiyar zuciya.
In Sha Allah zan gyara kuma nagode da tunatarwa, Allah ya bani ikon yin adalci a tsakaninku.
Ameen ya rabbi. Kaga ba dan ina aiki a kitchen ba da nayi maka rakiya mun je mun dawo.
Ta faɗa tana murmushi, Hamid ma murmushin yayi yana cewa.
Kuma fa, sai dai zan so ki gama girkin da wuri na dawo na ganki irin ba sauƙi ɗin nan, yadda zaki ƙara rikitani in susuce akanki, dan fa ban mance da jiya ba yana cikin kundun tarihina.
Dariya sosai Sakina tayi shima yana tayata a haka suka rabu ya wuce, Sakina ta samu kanta cikin tsantsar farin cikin da baya misaltuwa, gani take yi tamkar an sauya mata Hamid, wai shine yanzu suke hira har yake yi mata barkwanci, lallai giwa tayi lafiya, sai ta ɗaga hannunta duka biyu tana cewa.
Allah nagode maka daka sauya mini mijina ka ƙara mana zanan lafiya da kwanciyar hankali.
Sai ta sauke hannu tana cewa amin a ranta ta cigaba da aikin da take yi.
Hamid koda ya fita wajen abokinsa ya nufa inda suka saba haɗuwa suyi hira, shine ma dai bai damu da zuwa sosai ba amma kusan kullun suna haɗuwa sai dai su bashi labarin abinda suka tattauna in sun haɗu. Sai bayan sallar magrib yaje ɗauko Madina ya ki shiga ya kirata a waya akan ta fito su wuce, ta fito falo tana turo baki.
Ni wlh dama kin ce masa kwana zanyi tunda ba nice da girki ba, sannan ma ai bani da lafiya.
Maza ki wuce ki tafi bana son shirme, ai da yake yasan baiyi mutuncin ba sai ya tsoge a waje ya ki shigowa, gaskiya Madina ba kiyi dacen miji ba, haka zaki ta lallaɓawa tunda kin riga kin shiga, Allah ya kyauta kawai zan ce.
Kai mom Hamid fa yada da daɗin sha’ani matarsa ce kawai ta juya masa kai da asirinta.
To ta Allah ba tata ba, duk da ni bana son shiga hurin malamai amma ya zama dole na shiga na fita dan na sama miki farin ciki, ban yarda ki zama mara galihu ba a gidansa.
Cewar momy ta faɗa tare da miƙewa ta kama hannunta ta rakata tsakar gida, anan suka yi sallama ta fita ta same shi ya buɗe mata gefensa ta shiga ta zauna ba tare da tace masa komai ba, ya kunna mota suka wuce. A hanya sai da ya tsaya yayi musu siyayya dangin kayan fruits da kuma biscuit na ‘yan makaranta, Madina tace zata sha youghot sai ya siya mata haɗe da ice cream gabaɗaya gidan kana suka wuce gida.
Kamar yadda Hamid ya more a daren jiya yau ba bai yi ƙasa a guiwa ba ya gwangwaje, itama Sakina ta bada haɗin kai yadda ya kamata, haka suka wayi gari cikin farin ciki da kaunar juna. Tun daga wannan ranar ya zamana Hamid yana ɗokin girki yazo hannu Sakina dan kullun ƙara rikita masa lissafi take yi da sabon salonta, Madina kuwa sai da ta shafe sati na jinya daga bisani ta warke, sai yawan kwaɗayi da ƙarin kazanta, sauƙinsu mai aikinta Ladi tana zuwa kullun tana yi mata aiki harma da Sakina, dan yanzu Hamid yace mai aikin ta riƙa share falo da ɗakunansu da mopping, nashi ɗakin ne dai yace bai yarda ba sai Sakina ce ke gyara masa, sannan kuma wanke wanke duka take haɗawa ta yiwa Sakina sannan dana Madina, abinci kuma Sakina take girma nata da yara in tana da miji ta yi dashi, in kuma Madina ce da girki to mai aikinta ke girka mata nata shi dai Hamid maƙewa yake gurin Sakina yaci ko ya je gidansu yaci a gun Hajiya ko yaci a waje. Madina saboda wauta har lokacin bata sanar da Hamid tana da ciki ba, ta bari sai aikin da Malam ke yi mata ya kama shi kafin ta faɗa mishi yadda ƙila zata samu kyauta a gurinsa ko ya bata motar da yayi mata alƙawari. Kusan duk bayan kwana biyu sai ta shiga gidan maman murja, wanda sun yi mugun sabo sosai kuma Sakina bata san da haka ba, dan bata shiga sabgar kowa sai hidimar gidanta. A haka aka shafe wata ɗaya da sati biyu, wanda yayi dai dai da wata uku da auren Hamid da Madina, cikinta kuma wata biyu da sati uku, da yake ba tada tumbi bai nuna ba sai ƙiba data yi da fari sosai, Sakina ta gane ciki gareta sai dai kuma tunda Hamid bai faɗa mata ba itama tayi shuru da bakinta, kuma shi sam bai sani ba dan bai fiye shiga sabgar Madina ba saboda rashin kunyarta da take zabga masa dan ba fasawa tayi ba, ita kuma da yake shashsha ce bata faɗa masa ba har lokacin.
A ranar Asabar Salim ƙarnin su Hamid ya dawo daga Sokoto ya kammala karatunsa, a washe gari kuma su Asma suka zo garin domin bikin wani ɗan kanin Hajiya da za ayi, sunta saka rana zasu zo akan su duba jikin Hajiya tun sadda tayi fama da gudawa ita da Hamid amma basu samu zuwa ba har dai Hajiya ta dakatar dasu akan su bari sai bikin su zo gabaɗaya, to da cikin Madina suka sauka dan sunyi alwashin sai sun haifeta akan rashin mutuncin data yiwa Hajiya dan basu mance ba. Sakina kuwa tun jiya Hamid ya faɗa mata da zancen zasu zo hakan yasa ta wayi gari da shirya musu gurasa da rana, saboda bata mance da huɗubar Anty Jalila ba akan ta kyautata musu wata ƙila wannan yasa ta samu sassaucin ƙiyayyar da suke yi mata. Bayan ta sallami yara masu zuwa hadda, Hamid kuma yana barci a ɗakinsa dan ranar baya fita sai da rana, hakan yasa ta samu damar yin gashin gurasa, mai yawa tayi dan suma shi zasu ci da ranar, Allah yasa ba ita ce da girki ba dan haka zuwa ƙarfe sha biyu ta gama, ta haɗa musu shi a babban kwanon samira da haɗinsa gabaɗaya yaji ƙulu da mai da kayan miya data yanka, data gama ta shiga ɗaki tayi wanka ta shirya cikin rigarta ready made cikin wanda ta siya a kano, ta yi kwalliya daidai misali kana ta gabatar da sallar azahar, data idar sai tayi rollin da ɗan kwalin kayanta ta fito ta shiga ɗakin Hamid ta samu ya fita masallaci, kitchen ta wuce ta ɗauki wannan samira data haɗa gurasa ta fito zuwa sashin Hajiya.
A falo ta samesu suna ta zuba hira, ta shiga da sallama ta zauna a carpet kamar yadda ta gansu zaune, ta dire musu kwanan a gabansu tana cewa.
Maraba da baƙin Abuja da Zaria fatan kun iso lafiya.
Ta ƙare maganar fuskarta ɗauke da fara’a, suma da dariyarsu suka amsa mata nan suka shiga gaisawa, Hajiya tace.
Ashe kin samu labarin zuwansu.?
Eh tun jiya Hamid ya sanar dani zasu zo, nasan kuma sunfi zuwan wuri shiyasa nayi tunanin sun ƙaraso, nace bari nazo mu gaisa gama gurasa nayi ta marmari nasan Kubura kina sonsa sosai.
Ta ƙare maganar tana buɗe musu samirar, ai basu Asma ba hatta Hajiya sai da ta haɗiye miyau tana cewa.
Sannu da aiki, ashe kin iya yin gurasa ko aiki kika bayar ayi miki?
A’a nice nayi, zuwana Kano na koya a gurin anty Jalila.
Gaskiya kuwa gashi tayi kyau kinyi ƙoƙari Allah yayi albarka, dama bamu gama abinci ba kinga sai muci wannan, ke Jidda jeki ɗauko kula a zubawa Alhaji dan nasan zaici in dai girkin Sakina ce.
Hajiya ta ƙare maganar da Jidda, nan fa aka shiga rabon gurasa Sakina tana zaune suna hira a haka Hamid ya shigo ya same su, yaji daɗin ganin Sakina tare da ‘yan uwansa ya zauna yana cewa.
Hajiya ina kuka samu gurasa?
Au ashe kaima baka san da ita ba, to Sakina ce tayowa ƙannenka gashi kowa zai ci na marmari.
Aiko banda labari, Madam irin wannan kayan arziki ba zaki sanar dani ba, to ina nawa.?
Yayi maganar yana duban Sakina yana dariya, ta bashi amsa tana murmushi.
Naka yana gida na aje maka.
To kuwa ki sani yau shine abincin rana na dana dare.
A’a fa na ranar dai, dan girkin dare yana gurin Amarya.
Ta faɗa tana dariya. Ya muskuta ya saka hannu a plate ɗin Asma da aka zuba mata ya ɗauki ɗaya yakai bakinsa, sai da ya tauna yaji daɗinsa kana ya kalli Sakina.
Wai dama kin iya wannan abun shine bakiyi mana, aiko wlh yau ko kinƙi dole ki aje mini shi da dare dan shine abinci na.
Ya faɗa cike da santi, Kubura ta sa dariya.
Yaya ko dai ayi maka waigi ne dan na kula kamar santi ya ɗibeka.
Nan dai suka dinga barkwanci wa juna suna dariya, haka Sakina ta kai har aka gama girkin nan gidan aka saka mata ta zauna taci ta ƙoshi, dan ita tunda tayi gurasar taji ya hau kanta ta bari da dare zata ci tunda tayi mata auki zai kaisu suci da dare. Wajen ƙarfe uku tabar gidan suka rabu cike da mutunci, bayan fitarta ne Hajiya tace.
Wlh naji daɗin sauyawar Sakina da haka take yi ina ma Hamid zai ƙara aure, koda ya kara ai da muna tare da ita.
Wlh nima dai naji daɗin karramamu data yi Allah yasa ta ɗaure, kinsan wasu matan basa dawowa hayyacinsu sai anyi musu kishiya, kuma karin abun burgewa ba kuga tayi shiga mai kyau ba da kwalliya, gaskiya kam ta sauya sosai.
Hmmmm ni ne zan gaya muku Sakina ta dawo Asalin sunanta, wato ta zame mini Natsuwa a gidana.
Cewar Hamid, Hajiya kam ba ƙaramin jin daɗin furucinsa taji ba, haka suka cigaba da hirar zumunci.
_Gobe In Allah ya kaimu ba zan samu typing ba an yi mini haihuwa zani suna sai jibi In Sha Allah_
[8/22, 7:45 PM] Rahma Kabir: *ƘAZAMAR AMARYA*
Na
©®Rahma Kabir MrsMG.
Wattpad @rahmakabir
Page 40.
Bayan sallar la’asar Sakina ta shirya ta shiga gidan Maman Murja dan su gaisa dan tunda ta dawo take son shiga bata samu hali ba, hakan yasa ta kira Hamid ta sanar dashi zata shiga maƙota yace sai ta dawo amma karta jima, a haka suka rabu ta saka hijab ta fice ita kaɗai dan Rauda tana gidan Hajiya tun ɗazu. Koda ta shiga gidan Maman Murja da fara’a ta tarbeta nan suka yada zango a falo suka shiga gaisawa, daga bisani suka shiga yin hira har maman Murja tana cewa.
Sakina kin zama Hajiya ganinki sai an cika form, kwanaki na samu labarin kin bar gidanki nayi ta nemanki a waya ban samu ba, haba Madam yanzu an wuce lokacin yaji kodan yaranki zaki zauna, sannan na zo miki da hanya mai ɓullewa amma kinki amsar tayina.
Maman Murja kenan, ni dai wlh bazan saɓi Allah ba saboda Namiji in gyara duniyata in ɓata lahirata, sisina bazan kashe akan Hamid ba, na kai ƙararsa gurin Allah kuma Alhamdulillahi ina kan samun nasara, dan haka ki aje wannan maganar ni na shigo ne mu gaisa dan mun jima bamu haɗu ba.
To ai shikenan na rabu dake amma ki sani ance in kana da kyau ka ƙara da wanka, sannan ke in bakya niman maganin da zai share miki hawaye ba to ita amaryanki ba zata zauna ba dan na ganta idonta a feƙe yake, anya ma kina yin zaman lafiya da ita kuwa?
Lafiya lau Alhamdulillahi muke zamanmu, babu mai shiga harkan wani tunda girkinmu ba ɗaya ba kowa da nashi.
Amma ace falo guda komai naku ɗaya a raba girki, lallai Hamid yana ƙoƙari da aikin cefane. Ai da nice ke hatta amaryar zan mallaketa sai abinda naso tayi a gidan, wlh sai na mayar da ita ‘yar aiki tayi ta mini bauta tunda harta aure mini miji, koda yake ni No kishiya a gidana dan bazan bari ba.
In kuma Allah ya ƙaddara miki baki isa ki sauya ba, kedai ki nima zaɓin Allah da fatan alkhairi, sannan ni bazan biyewa son zuciya na saɓawa Allah saboda wani jin daɗin duniya da ba zai tabbata har abada ba. Mutuwa kaɗai ta isa bawa wa’azi. Ni nazo ne ma dan in tallata miki hajata dan ina so na fara sayar da kayan mata dan tayar da komaɗa, nasan ke me mutane ce ki tayavni talla in har kika kawo mini customers kema kina da kasonki.
Kai Sakina! kice da zafinki kika dawo gidan Hamid, aiko na tayaki murna dan zama haka ba daɗi, ga kuma kishiyarki tana aikinta kinyi wa kanki farar dabara.
Cewar maman Muryar cike da murna a fuskarta, nan dai Sakina ta shiga yi mata bayanin kayanta dan har tayi oder ɗinsu q gurin Surayya daga Kano jibi za a aiko mata dasu, dan Hamid ne ma ya bata jali mai tsoka, shima yaji daɗin business ɗin da zata yi hakan ya tabbatar masa da Sakinarsa ta fara wayewa da rayuwa, nan dai sukai ta hirar kasuwancin suka aje zancen malamai, dan in Maman Murja zata kwana tana yiwa Sakina zancen ba ɗauka zata yi ba.
….
Madina da yake yau ba tada aiki tana kwance a gado mai aikinta kuma ta shiga kitchen dan ta ɗaura mata abincin dare inta gama sai ta wuce gida. A lokacin ne su Asma suka shigo falon suka yi sallama, Ladi ta leƙo daga kitchen tana amsa musu, ganin su Asma ne ƙannen Hamid yasa ta gaishesu dan ta ganesu tun lokacin biki, suka tambaye ta Madina tace tana ɗaki bari ta kira musu ita, Kubura tace barta zamu sameta a can, Ladi tana jin haka ta koma kitchen ta cigaba da aikinta. Asma ce ta fara yin gaba zuwa ɗakin Madina dan basu bi takan Sakina ba saboda ba gunta suka zo ba, falonta suka fara buɗewa suka shiga nan suka yi sa’ar taddata kwance kan doguwar kujera ga popcorn a kusa da ita tana ci wanda momy tayi mata aikensa, tana ganinsu ta miƙe ta zauna suna kallon juna, a yadda taga fuskokinsu ya tabbatar mata da ba alkhairi ya kawo su ba dan haka ta yatsine fuska.
Lafiya zaku shigo babu ko sallama?
Kema kinsan lafiya ba zata kawo mu ba dan baki isa muzo inda kike ba hakanan, ashe dama ke matsiyaciya ce ba kida mutunci bamu sani ba, muna yi miki kallon salaha mai tarbiyya ashe ‘yar mace ce ke ba kwaɓa, ki rasa wacce zaki raina ki ciwa mutunci sai Hajiyarmu, to mun zo mu muna miki cewa Hajiya tana da ‘ya’yan da zasu ɗauki mataki akan duk ‘yar iskan data nima takata.
Cewar Asma tana nunata da yatsa, Madina ta miƙe tana ‘yar dariya tare da tafa hannu.
Ku koma ku kira Hajiyar ni da ita zanyi ba kuba cikon benci, ashe ma tsorona take ji data aiko mini ku. To bari kuji wlh duk wanda yayi mini kan kara sai nayi masa na itace, rashin mutunci na iya shi kala kala kuma ina dai dai daku, kai inma akwai waɗanda suka fiku ina daidai dasu, ni ba Sakina bace da zasu laftawa rashin mutunci ku zauna lafiya.
Haka kika ce? Kaji ‘yar iska Hajiyar tamu zaki yiwa raini.
Cewar Kubura tare da isa inda Madina take a zafafe ta koɗa mata mari, aiko bata sauke hannunta ba Madina ta rama, nan fa dambe ya kaure, Asma tana gefe sai girgiza jikinta take yi tana kiran number din ƙaminsu Salim, yana ɗagawa tace.
Ka zo gidan yaya Hamid amaryarsa ta zagi su Hajiya.
Kutumar kaza kaza, ai wlh gani nan zuwa dama tunda na dawo Hajiya take bani labarinta, ashe ba tada mutunci.
Asma ta kashe wayar bata amsa masa ba, ganin faɗar nasu kamar na kaji suke yi yasa ta cire gyale ta aje ta rufar musu, wato suka haɗu ita da Kubura suna dukan Madina, tun tana kai musu hannu danta rama harta kasa ta shiga kare kanta, dama da niyyar suyi mata dukan tsiya suka zo gidan, dan sunce koda Yayansu zai rama mata sai sunyi maganin iskancinta ko gaba ba zata sake yiwa Hajiyarsu rashin kunya ba. Madina ganin fa sun tarar mata gata dama ba kwari ba nan ta fara kuka tana zaginsu, amma basu fasa dukanta ba hakan yasa ta nufi ƙofa da mugun sauri ta buɗe ta fita falo, a lokacin ne Ladi ta fito tana tambayar lafiya? dan tun ɗazu take jin hayaniya bata ɗauka daga ɗakin Madina bane, ganin Madina yarkace yarkace yasa ta gane ba lafiya ba, su Asma suka fito suna haki a lokacin Salim ya shigo yana cewa ina take? ya ƙaraso ciki Kubura ta nuna masa ita, dama bai santa ba dan ya jima baya Kaduna har aka yi auren bai dawo ba, Salim ya zo tsakiyar falon ya shiga ƙunduma mata ashar yana zaginta, Madina da yake akwai baki bai mutu ba ta shiga ramawa, hakan ya tunzura Salim yayo kanta gadan gadan Madina tana ganin haka ta ɓoye bayan Ladi, da yake Ladin ba ƙiba nan ya finciketa ya cafki hannun Madina ya shiga kai mata naushi a baki dan so yake ko bai zubar mata da haƙora ba to ya sasu suyi girgiɗi yadda zai yi maganin rashin kunyarta, Madina ta shiga kwarma ihu Ladi tana kama hannu Salim amma ina ta kasa hana shi kasantuwarsa namiji ne mai karfi da gwanji, nan fa ya haɗa mata jini da majina, madina ganin fa dagaske zai nakasata yasa ta kwasa a guje tayi hanyar kitchen, a lokacin ne Sakina ta shigo falon ganin su a ƙofar kitchen suna ta bugawa da dukan ƙofar yasa ta ƙarasa ciki da sauri.
Asma Lafiya meke faruwa.?
Hajiya dukan Madina suka yi duk sun yi mata jina jina.
Cewar Ladi cike da tashin hankali dan jikinta har rawa yake yi, Sakina ta shiga koro salati tana tafa hannu.
Haba haba me tayi muku data cancanci haka, ina ce Hamid wanku ne, kome ta muku ba sai ku faɗa masa ba ya ɗauki mataki da kansa, gaskiya bai dace ba haka.
Sakina babu ruwanki ki barmu da ita mu nuna mata Hajiya tana da gatan ‘ya’yanta, ita ɗin banzanta zata yiwa Hajiyarmu rashin kunya ta zauna lafiya, wlh ba a haifi ‘ya ba.
Cewar Asma, Sakina kasa magana tayi ta wuce zuwa ɗakinta ta cire hijab tare da kiran Hamid a waya, sai dai tayi ta kiransa bai ɗauka ba hakan yasa ta yanke shawarar kiran Abba, tayi sa’a kira ɗaya ya ɗauka ko damar gaisheshi bata yi ba ta soma da cewa.
Abba ka zo gida ba lafiya Su Asma ce suke yin rikici da Madina, nima yanzu na shigo gidan na tadda suna yi.
Salati ya saki tare da kashe wayar ya fito daga ɗakinsa yana riƙe da charbi, Hajiya ganinsa cikin sauri yasa ta shiga tambayarsa lafiya? Bai bata amsa ba ya fita, itama da saurinta tabiyo shi ganin ya shiga gidan Hamid yasa taji gabanta ya faɗi, tasan dama su Asma suna can kuma sun sanar da ita zasu jawa Madina kunne ita bata san da rikici suka je ba, haka suka shigo falon su Asma da suke surfa masifa ganin Abba duk suka yi tsit ko wanne yasha jinin jikinsa, shikam tsayawa yayi tana binsu da kallo ɗaya bayan ɗaya bai ce komai ba, lokacin Sakina ta fito itama ta tsaya Hajiya ce ta katse shurun.
Kuyi mana bayanin meke faruwa a nan?
Dukan Madina suka yi suka haɗa mata jini da majina shine ta gudu kitchen ta kulle.
Cewar Ladi tana matsar kwalla dan sam bata ƙaunar tashin hankali, shiyasa ta fita waje ta kira momyn Madina ta faɗa mata dan taga abin nasu ba zai ƙare ba, karsu kashe Madina su jawo mata matsala ace a gabanta aka yi, Abba shuru yayi saboda tsabar baƙin ciki Hajiya ce ta fara yi musu faɗan famau, wani irin tsawa Alhaji ya daka mata wanda yasa ta yin shuru yana nuna ta da yatsa.
Ki yiwa mutane shuru na tabbatar da saninki suka zo gidan nan, yanzu fisabillahi har da kai Saleem ina yi maka kallon mai hankali, ashe Hamid ne kaɗai yaro nagari a cikinku, na tabbatar shi bazai taɓa yin wannan ta’asar ba, to wlh gabaɗayanku sai kunsan kunyi wannan rashin tarbiyyar, mutanen banza kun girma amma kullun cin ƙasa kuke yi.
Abba zagin Hajiya tayi fa tanayi mata rashin mutunci, ai duk ɗan halak shike kare mutuncin iyayensa.
Cewar Salim yana wani fuzga, Abba ya ce cikin ɓacin rai.
Bazaka yi mini shuru ba sai na tattakaka anan shashasha kuma…
Bai ƙarasa me zai ce ba suka ji jiniyar motar ‘yan sanda a gate ɗin gidan, Momy ce ta ɗaukosu da yake akwai wani station a unguwarsu nan kusa dasu, ba ɓata lokaci ta koro musu bayani tare da basu kuɗi mai coka akan azo a tafi da ƙannen Hamid, tayi alƙawarin yau sai ta nuna musu gatan da Madina take da shi, babu wanda ya isa ya taɓata ya kwana lafiya koda kuwa Hamid ne da kansa, shigowar momy a fusace yasa duk suka zuba mata ido, ta kalli Ladi.
Ina ‘yata take?
Tana cikin kitchen.
Madina! Madina!! Fito ga ni nazo tafiya dake, Ladi su waye suka duketa.
Ta ƙare maganarta ga ladi, nan Ladi ta shiga nuna su Asma, ‘yan sanda da suka shigo momy ta nuna su Kubura.
Gasu nan ku tafi dasu.
Haba Hajiya taya zaki ce a tafi dasu, kamata yayi ki tsaya ayi magana ta fahimta.
Cewar Hajiya da hankalinta yayi mugun tashi za a tafi mata da yara, Abba ya ɗaura da cewa.
Dan Allah kiyi haƙuri laifi kam mun san anyi miki amma bai dace lamarin ya tafi a haka ba, ni zan ɗauki mataki mai tsauri akansu In Sha Allah, yallaɓai ina ganin zaku iya tafiya za muyi sulhu dan abin da family ne.
Alhaji wlh sai antafi dasu dan ko Hamid ne ya taɓa mini yarinya sai na ɗaura shi balle su, ai itama ‘ya ce da zasu kama su duketa, bazan taɓa yin uzuri ba a wannan maganar dan ‘yata Madina tana da gata nice Uwa da kuma ubanta. Koda mahaifinta ya faɗi ya mutu ban bari tayi kukan maraici ba, dan haka oficer ku tafi dasu sai kun kwatarwa ‘yata ‘yanci daga na har kotun ƙoli.
Alhaji ya shiga girgiza kai cike da tsantsar ɓacin rai yama kasa yin magana, a lokacin Madina ta buɗe ƙofar kitchen ta fito tana ganin momy ta ƙaraso da gudu ta rungumeta, wanda ga jini yana bin ƙafarta momy ta kamata tana bubbuga bayanta alamun lallashi. Madina ta ɗago kai tana cewa cikin kuka.
Momy kasheni suka so suyi cikina ciwo yake mini kinga jini ke zuba, gashi sun fasa mini baki da hanci.
Ai wlh sai sun biya bashin abinda suka yi miki. Officer sai kun tawo.
Momy ta faɗa tana jan Madina suwa farfajiya dan bata bari ma Madina ta ɗauki ko ɗankwali ta rufe kanta ba dan so take ta kaita asibiti a duba lafiyarta. Su Asma ido ya raina fata Abba fita tsakar gida yayi ya tsaya yana kiran Hamid a waya, haka ‘yan sandan suka tasa ƙeyar su Kubura zuwa motarsu dake ƙofar gida, Hajiya da Sakina suka bi bayansu suna basu haƙuri amma kamar ƙara zugasu suke yi har suka tafi dasu, su Amsa suna kuka dan basu taɓa ɗaukar lamarin zai kai ga haka ba, wannan abu ba ƙaramin zubar da ƙimar gidansu yayi ba dan mutanen unguwar duk sun fito waje jin jiniyar motar ‘yan sanda, Abba koda ya sanar da Hamid guri ya samu ya zauna a wani dakali da yake na filawa, ya dafe kansa saboda chajin da yayi masa tsabar ɓacin rai, Hajiya ma tsayawa suka yi cirko cirko a tsakar gidan sun kasa magana ko wanne da irin tashin hankalin da yake ciki, Ladi kuwa tana ɗakin Madina tana haɗa mata kayan sawanta a trolley kamar yadda momy tabata umarni a waya, koda ta gama haka ta koma kitchen ta sauke sanwar abincin data ɗaura ta kashe gas kana ta koma ɗakin Madina ta fito da kayan ta shiga falo ta ɗauki mayafinta da jaka kana ta fito, haka ta wuce su momy ba tare da ce musu komai ba ta fita ta samu abin hawa ta wuce gida.
Momy kuwa asibiti ta kai Madina likita ya dubata wanda ya tabbatar da firgici ne yasata zubar jini amma cikinta yana nan sai dai kuma yana cikin barazanar fita, nan suka bata gado momy tace ba zasu kwanta ba su basu magani likita ya riƙa zuwa gida yana dubata bata son zaman asibiti, sai gabda magrib suka bar asibiti suka wuce gida.
Hamid koda ya ƙaraso ya samu labarin komai, tsabar baƙin ciki kasa magana yayi ya tsaya yayi shuru, Abba yana dubansa yace.
Yanzu meye abinyi?
Abba wlh ban sani ba tunda sune suka jawa kansu matsala, ko meye Madina tayi musu ai ya dace su sanar dani na ɗauki mataki, kuma wlh Mahaifiyarta zata iya komai dan ganin ta wulaƙantasu tunda ba mutunci ne da ita ba hatta ni ban cira a gunta ba in dai akan Madina ce, dan haka a barsu su kwana in jikinsu ya gaya musu gaba ko ance su duki wani ba zasu yi ba.
Haba Hamid ya zaka ce haka? laifi dai sunyi amma ya kamata kayi wani abu kodan kare martaban gidan nan.
Cewar Sakina cike da damuwa, Hajiya dai ta kasa magana dan duk abinda zata faɗa goyon bayan yaranta zata yi kuma tasan hakan ba zasu kwashe da Abba ta daɗi ba, Alhaji ya da girgiza kai.
Duk tsuntsu da ya ja ruwa shi ruwa kan duka, dan haka sai gobe In Allah ya kaimu zamu je station ɗin muyi belinsu, muje masallaci an kira sallah.
Ya ƙare maganar yana miƙewa yayi hanyar fita gate, Hamid ya rufa masa baya ba tare da yace komai ba amma har cikin ransa baya jin daɗin ƙannensa zasu kwana a sation, Hajiya kuwa fashewa tayi da kuka ta koma gurin da Abba ya tashi ta zauna tana share kwalla, Sakina ta matsa tana bata haƙuri da cewa.
In Sha Allah a zasu kwana a gurin ‘yan sanda ba zanyi magana da Hamid ɗin.
Hajiya dai matsar kwalla kawai take yi ta kasa magana dan baƙin ciki.
[8/23, 6:25 PM] Rahma Kabir: *ƘAZAMAR AMARYA*
Na
©®Rahma Kabir MrsMG.
Wattpad @rahmakabir
Page 41.
Da kyar Hajiya ta miƙe ta wuce sashinsu Sakina ma ta shiga ɗakinta ta gabatar da Sallah, tasan Hamid baya shigowa gida har sai anyi sallar Isha’i amma saboda abinda ya faru tana son yin magana dashi yasa ta kira shi a waya sai dai kuma bai ɗaga ba hakan yasa ta haƙura akan har ya dawo dan bai dace abar su Asma a wajen ‘yan sanda ba tunda da aurensu. Hamid kuwa ana isar da sallar magrib suka wuce gurin ‘yan sanda shida Abba dan dama da suka fita sunyi maganar zasu je duk da Abba yaso abarsu su kwana jikinsu ya gaya musu Hamid ne ya dage akan gwara aje ɗin, Hamid drivern gidansa ya kira ya fito masa da motar kai yara makaranta da ita suka je gurin ‘yan sandan, cikin ikon Allah DPO yana ganin Hamid ya gane shi dan ya taɓa siyan mota a gurinsa, kuma a lokacin yayi masa mutunci wannan yasa suka zauna suka tattauna maganar har dpo ya bada belinsu akan da safe zasu dawo domin ayi case ɗin domin a kashe shi anan, suka yi masa godiya bisa karamcin da yayi musu ko sisinsu basu amsa ba kana suka baro station ɗin suka dawo gida, sai dai Hamid da Abba an sauke su a masallaci dan gabatar da sallar Isha’i, su Asma aka ƙarasa dasu gidan Hajiya kana driver ya dawo yayi parking mota a gidan Hamid.
Bayan sun yi sallah Hamid gida ya shigo ya samu guri ya zauna a falo, yara yadda suka ganshi yasa suka bnatsu bayan sunyi masa sannu da zuwa, a lokacin Sakina ta fito ta zauna tana dubansa cikin kulawa.
Barka da shigowa.
Yauwa, akwai sauran Gurasar nan ne?
Eh gashi can na haɗa maka yana dining haɗe da zoɓo.
Kin kyauta kuwa, ku kunci naku ne?
Eh tun bayan magrib yara suka ci, ni na kasa ma ci wlh kasan tashin hankali hanani sukuni yake yi.
To sai ki tashi muje kici dama tunda naga kiranki ɗazun nasan zancen su Asma za kiyi mini, to ki kwantar da hankalinki munje da Abba sun dawo suna can gida.
To Alhamdulillah Allah ya kyauta na gaba.
Ta ambata tana miƙewa Hamid ya amsa da Amin sai ya miƙe suka wuce dinning, nan ta zuba musu suka fara cin abincin, Hamid yana yi mata hirar abinda ya faru a gurin ‘yan sanda, sai wayar Hamid ya shiga ruri yana dubawa yaga Madina ce sai ya basar ya cigaba da abinda yake yi, har ya katse ta kuma kira bai ɗauka ba Sakina ta dubeshi.
Hamid ka ɗauka mana wataƙila mai kiran yana cikin uzuri ne.
Madina ce fa bana son damuwa sam.
Haba dai ai ya dace ka ɗaga kaji uzurin ta tunda ɗazun naji mahaifiyarta tace asibiti zasu tunda tanata zubar jini.
Guntun tsaki yayi ya ɗaga wayar lokacin da kira na uku ya shigo yana ɗauka ta fara da cewa.
Hamid ka nuna mini iya son da kake mini, yanzu na tabbatar da ba sona kake yi ba jikina kawai ya ruɗeka ka aureni, to ka sani sai Allah ya saka mini wlh, amma kasan yau nice da girki ga kuma abinda ƙannenka suka yi mini amma ka kira kaji halin da nake ciki ya gagareka, gashi har cikin jikina suka nima zubar mini har zuwa yanzu zubar jini nake yi.
Madina yaushe kike da ciki? Sannan da wanne kike so naji? Bayan Mahifiyarki ta ɗauki matakin da taga shine daidai, dan haka ni babu wata magana da zan yi dake iyaka in baki haƙuri sai kuma gobe in munje gurin ‘yan sanda sun yanke hukunci, tunda daga ke har Momy baku ɗauki aurena a bakin komai ba.
Haka ma zaka ce? to Allah ya isa ban yafe ba ka cuceni ka rusa mini rayuwata, nayi dana sanin saninka wlh Hamid kuma ina ɗauke da cikinka ban…
Bata ƙarasa ba ya kashe wayar ya dafe kansa saboda ɓacin rai, kusan duk Sakina taji komai da suka tattauna batace masa komai ba ta cigaba da cin abincin, Hamid sai dai ya ɗauki kusan minti goma a haka kafin ya iya saita kansa ya ja guntun tsaki ya cigaba da cin abincin, idanunsa har ja suja yi tsabar ɓacin rai, haka dai ya tusa abincin badan yana jin daɗinsa ba sai dan ya gusar da yunwar da yake ji. Bayan sun gama Sakina ta tura yara ɗakinsu su kwanta ita kuma ta rage kayan jikinta ta saka doguwar rigar barci ta saka hula ta zo falo ta zauna kusa da Hamid, dan ya kishingiɗa ne a doguwar kujera ya rufe idonsa, haka ta ɗaura ƙararsa a cinyarta ta shiga matsa masa.
Abban Mufeeda dukkan tsanani yana tare da sauƙi, kuma ko wani abu in ya faru ƙaddara ce kuma rubutacce ne daga Allah, ka sassautawa zuciyarta domin damuwa ko tunani bazai yi maka maganin matsalarka ba face addu’a da mayarda komai ga Allah, In Sha Allah sai ka ga ya warware maka komai cikin ikonsa.
Buɗe ido Hamid yayi ya zuba mata ido itama shi take kallo fuskarsa cike da murmushi, ganin bazai yi magana ba yasa ta ɗaura da cewa.
Koda ace Madina ce ba tada gaskiya to su Asma sun take dokar Shari’a bai dace su biyota har gidanta ba su duketa, dan haka kar zuciya ko fushi yasa ka yanke mata hukuncin da bai kamata ba kayi mata adalci kamar yadda suma kayi musu uzuri, sannan kaga ba tada lafiya ko yaya in ka nuna kulawa a gareta zata ji daɗi zata gane ka damu da ita, dan haka ita aka yiwa laifi ya kamata a rarrasheta a bata haƙuri. Kayi mini afuwa bisa wannan maganar da nayi maka nasan ba hurumina bana sai dai ciwon ‘ya mace na ‘ya mace ne, bazan so nima haka ya faru dani ba duk da tana matsayin kishiyata.
Na fahimceki domin gaskiya kika faɗa sannan ita gaskiya ɗaci gareta, koda hakan bai mini daɗi ba dole in yarda da zancenki domin daga ƙin gaskiya sai ɓata.
Nagode daka fahimce ni Allah ya daidaita lamarin yasa iyakarta kenan.
Ya amsa da amin kana suka cigaba da kallo, lokacin barci daya yi suka miƙe zuwa ciki.
****
Madina.
Tunda Hamid ya kashe mata waya ta dinga rusa kukan baƙin ciki, sai duk taji ma ta gaji da aurensa dan babu abinda ya kawo mata face baƙin ciki da ɓacin rai, ta kashe kuɗin ta domin biyan buƙatarta duk a banza, sannan ace ƙannensa suzo har ɗaki su duketa amma ya rasa abinda zai saka mata sai maganganu mara sa daɗi har yana kashe mata waya, a haka momy ta zo ta sameta tana kukan, ta zauna cike da ɓacin rai tana cewa.
Kiyi ƙoƙari ki kashe kanka abanza saboda namiji, tun farko wannan nake ta guje miki kika ce Hamid yana sonki bai da matsala ya yaudareki da daɗin baki, dan haka ni da zaki ji ta tawa da kin haƙura da wannan auren har Allah ya baki na gari, Madina kina da kyau da ƙuruciya zaki samu namijin daya fishi komai ƙilama ki auri saurayi mai gata da kuɗi, cikin nan ma cireshi za muyi dan ba zan yarda na haɗa zuria da su ba gayyar tsiya.
Jin furucin momy na zancen cire ciki yasa Madina gimtse kukanta ta ɗago tana duban momy.
Ni dai ba za a cire mini ba dan ina so.
To ai wannan cikin shi zai hana rabuwarki da Hamid, dan haka ki zauna kiyi wa kanki tunani amma in kince zaki zauna dashi bazan hana ba sai dai jiki magayi.
Tana kai maganarta anan ta miƙe ta fita, da ido Madina ta rakata tare da curewa ƙofar data fita ido, itama a yanzu ji take bata son sake zama da Hamid in ma zata cigaba da zama dashi to dole ne sai ya cike duk wani sharuɗɗa da zata gindaya masa, sannan kuma ita tana son cikinta koda ba zata zauna da Hamid ba zata so ganin gudan jininta, haka ta raba dare tana tunani ta hana kanta sukuni a haka barci ya ɗauketa. Da safe momy ta shigo dan ta tasheta amma me sai ta ganta cikin jini male male, ciki dai ya fita, da salati ta haura gadon ta taɓa jikin Madina taji yayi mugun zafi cikin tashin hankali ta fito ta kira Ladi, ita ce ta tayata yiwa Madina wanka suka shirya ta kana momy ta wuce da ita asibiti. Koda suka je likita ya duba ciki ya fita akwai kuma sauran datti da dole sai anyi mata wankin ciki, ya ɗaura da cewa.
Allah ya ƙaddara dole sai ya fita amma naso ace kun kwana anan domun ta samu kulawa mai kyau.
To likita ya za ayi ni gwarama da ya fita dama shine nake tunanin zai kawo min cikas, yanzu a yi mata komai daya dace.
Muna buƙatar saka hannun mijinta, in yana gari a kirashi yazo.
Likita kayi mata komai ni zan saka hannu bana son damuwa wlh.
Haƙƙinsa ne ya kamata yazo ɗin.
Likita ya faɗa yana cigaba da rubuce rubuce, momy badan ranta yaso ba haka ta fito ta isa ɗakin da aka kwantar da Madina, tace mata ta kira Hamid ta faɗa masa za ayi mata wankin ciki yazo likita yana son ganinsa.
Yanzu momy shikenan sunyi sanadin zubewar cikina, wlh bazan taɓa yafe musu ba.
Ta ƙare maganar cikin kuka, momy fuska ɗaure tace.
Ai ni naji daɗin fitar cikin meye amfanin haɗa zuri’a da Hamid, kuma wlh ba zasu sha ba sai sun san sun zubar miki da ciki.
Ta ƙare maganar tana ƙofa da girgiza kai, ta zauna a kujerar kusa da gadon Madina, Ita kuma Madina text kawai ta tura masa ta aje wayar a gefen ta.
Hamid dama ya wayi gari da nufin zaije gidansu Madina ya duba jikinta kafin suje station dan sosai maganar da Sakina tayi masa jiya ya zauna a zuciyarsa, ya gama shiryawa Sakina ta fito daga kitchen ta sameshi a tsaye yana saka maɓallin rigar sa.
Sai gurin ‘yan sanda kenan?
A’a zanje duba Madina tukuna daga can sai mu ƙarasa nasan, Abba zai tasa ƙeyarsu Asma.
To Allah ya sa a daidaita ya kyauta na gaba.
Ya amsa da amin kana suka yi sallama ta rakashi har ƙofar falo ya tafi kana ta koma ciki dan ta ƙarasa aikinta taje gidan Hajiya dan yin jajen abinda ya faru. Hamid ya tada mota kenan saƙon Madina ya shigo koda ya duba bai kirata ba ya tuƙa mota ya wuce asibitin dan yasan asibitin da gidansu suke zuwa. Koda ya isa wajen likita direct ya wuce nan yayi masa bayanin komai yace ba damuwa ayi mata duk abinda ya dace, ya bashi takarda yasa hannu kana yace duk wani abu da aka kashe shi zan biya kar su karɓi kuɗin mahaifiyarta, sannan ya fito ya nufi ɗakin da likita yace sun kwantar da ita, Hamid da sallama ya shiga sai dai daga momy har Madina ba wanda ya amsa masa, ya tsuguna ya gaishe da momy amma ta kawar da kai bata amsa ba, ƙarshe miƙewa tayi ta fice faga ɗakin, Hamid jiki a sanyaye ya miƙe ya isa jikin gadon Madina ya tsaya.
Ya ƙarfin jikin Allah ya baki lafiya yasa kaffara ce.
Hamid bana son ganinka dan Allah ka fita ka bani guri. Kuma ka sani zamanmu ya ƙare dan bazan cigaba da zama da kai ba na tsaneka.
Yadda take maganar a zafafe take yinsa dan har cikin zuciyarta tana nufin rabuwarsu, Hamid ya haɗiye malolon baƙin ciki ya dubeta da kyau.
Madina kin san bazan taɓa goyon bayan ƙannena ba in barki matsayinki na matata ba, nima zanso hukuma suyi musu duk hukuncin daya dace domin sun taka Shari’a, dan haka kiyi haƙuri dan Allah, kuma kin san ina sonki bazan iya rabuwa da ke ba kima daina wannan maganar.
Ƙarya kake yi wlh baka sona, ka fita bana son ganinka wlh, azzalumi macuci gashi nan sun zubar mini da ciki kuma wlh sai sun biya abinda suka yi mini.
Amma Madina dama kina da ciki baki sanar dani ba? Ban san ya kika ɗauki aurenmu ba sam.
Ka damu dani ne da har zaka sani, ina ce amai nayi ka ci mini mutunci ka tafi ka barni ina rashin lafiya har sai da momy tazo ta ɗaukeni ta kawoni asibiti, ka tsaya ka tambayi meke damuna?
Ta ƙare maganar tana tsure shi da ido, zai yi magana likita ya shigo tare da wasu nurses yace za a kaita ɗakin da za ayi mata wankin ciki, Hamid yace ba damuwa nan suka ɗauketa a wani gado suka wuce da ita ya fito farfajiyar asibitin ya kira Abba a waya ya sanar dashi, Abba yayi salati yace.
To ka tabbatar da ka zauna ayi mata komai har a gama, ya kamata ka muna kulawarka zasu ji daɗi.
Eh dama na aje komai zan jira, yanzu ma zan kira dpo na sanar dashi in yaso gobe in Allah ya kaimu sai muje a kashe case ɗin.
A haka suka aje maganar, Abba dama yana falo nan ya kira su Asma ya dinga surfa musu faɗa kamar zai ari baki, nan yake sanar dasu Madina tayi ɓari, ba ƙaramin nadamar abinda suka aikata suka yi ba, sai bawa Abba haƙuri suke yi Hajiya dai bakinta gum dan taƙi yarda tasa baki a maganar faɗar ya dawo gunta, dan tasan halin Abba tas zai wanke ta. Cikin hukuncin Allah anyi wa Madina wankin ciki an gama lafiya har ta samu barci, hakan yasa Hamid ya bar asibiti yaje ya jido mata kayan ciye ciye dan dai ya ƙara wanke kansa, duk kuwa abinda yayi bai burge momy ba dan alla alla take yi a gama komai su koma gida ya sakar mata yarinya.
Madina sai da ta kwana biyu a asibiti kafin aka sallameta ta warke sarai sai sauran samun ƙarfin jiki, su Abba dasu Hajiya harma dasu Asma sun zo dubiya, Sakina ma sun zo da Hamid sai dai kam basu ga fuskar arziki ba dan momy kamar zata rufesu da duka, Madina kam juya musu baya tayi dan bata amsa musu sannun da suka yi mata ba.
Sai ranar Alhamis suka je station nan fa aka yi danbarwa dan momy ƙeƙeshe ido tayi akan bata yarda ba lallai sai an turasu kotu an amsarwa ‘yarta ‘yancinta, a ranar da ɓacin rai aka rabu, ganin fa Momy ta ɗauka da zafi hakan yasa Abba da Hamid suka je suka samu yayyin Madina mazan wanda sune suka basu aurenta suka tattauna, to a washe garin juma’a da suka koma station yayyin Madina sune suka yiwa momy fin ƙarfi akan a rufe case ɗin, aka saka su Asma suka bada haƙuri momy har kuka tayi dan baƙin ciki yadda suka nuna mana fin ƙarfi akan ‘yarta. To bayan an sasanta an bawa juna haƙuri a nan ne Madina tace tana da magana, aka ce an bata dama tayi tace.
Ni ina da sharaɗi akan zamana da Hamid, in har kana son na cigaba da zama da kai to dole ne ka sauya mini gida, sannan ka sama mini masu yi mini hidima mutum biyu zuwa uku, sannan kuma dole ne ka bani motar da kayi mini alƙawari lokacin aurenmu. In kuma ba haka ba to sai dai ja sakeni.
Ta ƙare maganar tana kallonsa ido cikin ido, Hamid kasa magana yayi yana dubanta, nan yayyinta suka rufeta da faɗa momy ta saka baki, a takaice tsiya tsiya yayyinta suka bar gurin suka ce sun bar maganar in momy ta kashe mata aure wannan ruwansu, suka bawa Hamid haƙuri kana suka tafi. Hamid ma baice komai ba yace zai yi tunani akai, a haka dai aka ƙare maganar akan zasu ƙarasa a tsakaninsu, an dai riga an rufe case ɗin su Asma, kuma Hamid dama shine ya ɗauki hidimar asibitin Madina harma da karin kyautata mata, dan duk abinda take son ci shi yake siya ya kai mata gida, to haka suka dawo gida, Abba da Hamid suka tafi Masallacin Juma’a, su Asma kuwa shiryawa suka yi zuwa gidan biki tare da Sakina dan ranar ne ɗaurin aure.
[8/25, 8:32 PM] Rahma Kabir: *ƘAZAMAR AMARYA*
Na
©®Rahma Kabir MrsMG.
Wattpad @rahmakabir
Page 42.
Bayan sallar isha’i Abba ya haɗa yaran duka a falo harda Hamid, yayi musu faɗa sosai akan abinda su Asma suka aikatawa Madina, ya ɗaura da cewa.
Ban san ya akayi kuka sauya tarbiyyar da muka yi muku ba, kunyi aure madadin kuyi hankali sai kuma ku ƙara lalacewa, idan Mahaifiyarku ya faɗa muku magana son ranta akan matan Hamid sai ku hau ku zauna ba tare da bincike ba, ko ance ita bata laifi ne? da bata shiga harkan matansa na tabbatar da basu raina girmanta ba, ko ku sirikanku sun takura muku ne? Dan haka baku bullo hanyar da zai ɓulle muku ba ku gyara rayuwarku matsawar kuna son ganin daidai. Kai kuma Hamid ina ganin ka samawa Madina ɗaya daga cikin gidanka ta koma can dan ina ganin raba matanka shine zai kawo maslaha a tsakinsu, sannan kuma batun ‘yan aiki ka sama mata guda ɗaya wacce zata ɗauke duk hidimarta, haka ma Sakina dole ne ka sama mata ɗaya wacce zata tayata aiki, batun mota kuma ka tabbatar in har zaka bawa Madina to Sakina ce farko ka fara bata kafin ita amayar, ina ganin in kayi haka ka samawa kanka maslaha, kuma bana son daga aure a fara da zancen saki kayi mata abinda take so matsawar bai sabawa addini ba ko kuma bai takuraka ba sai a zauna lafiya.
Abba wlh bana sha’awar raba gidan nan saboda ina fatan kan yarana su tashi a haɗe, amma tunda kace a raba zanyi hakan sai dai batun mota ne ko zan basu sai nan gaba, zanje na sameta da maganar in hakan yayi mata shikenan.
To madalla Allah ya muku albarka zaka iya tafiya gidanka na sallameku.
Hamid ya miƙe yayi musu sallama ya wuce gida, suma su Asma ɗakin da suka sauka suka wuce sai Salim daya wuce nashi ɗakin, falon ya rage daga Abba sai Hajiya, itama bai barta ba sai da yayi mata faɗa sosai akan abinda ya faru ya ɗaura laifin kacokan ya ɗaura akanta.
Bai dace matsayinki na uwa a garesu ki riƙa faɗa musu duk abinda ya faru anan ba, suna gidajen Aurensu ki barsu suyi zaman natsuwa, amma kome aka yi miki ki kira ki faɗa musu hankalinsu kullun yana nan ba zasu mayar da hankali suyi zaman auren daya dace ba, sannan ke da kike babba in baki hana tashin hankali ba bai dace ki haɗa ayi ba, ki riƙa riƙe magana a cikinki kina haƙuri da kawaici ki daina sakawa surukanki ido, ki barsu suyi rayuwarsu, tunda kema babu wanda ya takura miki, dan Allah ki gyara zuciyarki ki ɗauki yaran nan ɗaya suke da naki domun suma ‘yapyan wasu ne ba wanda zai so yaga ana ƙuntatawa nashi.
Ya ƙare maganar yana jan fasali, Hajiya ta sauke ajiyar zuciya.
In Sha Allah zan gyara dan abinda ya faru ya zama izina sosai a gareni, Allah ya yafe mana kurarenmu Nagode Alhaji Allah ya ƙara girma yasa albarka a dukkan zaman auren yaran nan.
Ameen ya ambata kana ya ɗauki remote ya sauya tashar da yake son kallo.
****
Bayan kwana biyu abubuwa sun daidaita hankula sun kwanta, Hamid ya samu zuwa ya tattauna da Madina akan ya yarda zai sauya mata gida batun mota kuma tayi mishi haƙuri sai nan gaba kaɗan, ‘yar aiki ma ta tafi da wacce ta fara yi mata nan gaba inda yuwuwar ya ƙara mata wasu zai yi, sosai hakan ya faranta ran Madina bata taɓa zaton Hamid zai sauya mata gida cikin sauƙi haka ba, hakan yasa ta sauko daga dokin fushin da tayi dashi tace ba zata koma gidansa ba har sai an gyara mata gidanta dan yace ta jira za ayi mata sabon fenti da gyare gyare, hakan yasa ta cigaba da zama a gidansu tana zuwa aikinta. Ranar Laraba daga aiki Madina ta wuce gidan Maman Murja, koda ta shiga falon bata sameta ba ga yaran duk suna makaranta, ta samu guri ta zauna jin shuru ba wanda ya fito yasa ta nufi bedroom ɗinta anan taji maman Murja tana yin waya kamar zata shiga sai taji tana cewa.
Ke ƙawata ai harka da Malam ba ƙaramin kuɗi yake kawo mini ba, bana baki labarin wata amarya nan maƙociyarmu ba yanzu a jikinta muke tasha muyi kashe mu raba da malam, shiyasa bazan iya jure sana’a ba saboda wannan yafi kawo mini kuɗi cikin sauƙi ba tare da wahala ba.
Sai taji maman Murja tayi shuru, alamun wancen da suke wayar tana magana can sai taji tana kyalkyakewa da dariya.
Ke ai wlh yarinyar kamar mai wayo amma tuni na dulmiyar da tunaninta, kuma kinsan kishiyarta Sakina na fara yiwa tallar malam amma taƙi yarda tace ba zata yi asarar kuɗinta kan namiji ba, sai kuma Allah ya haɗani da amaryar mara lissafi, da farko malam ya fara aikin kwarai kishiyar tana ta karyawa ai sai muka cigaba da business da ita, yanzu haka munyi magana da malam yace na kirata ta turo da dubu hamsin za a cigaba da aiki, dan yanzu haka tana gidansu sun samu matsala da dangin mijinta.
Madina kasa haƙuri tayi jikinta yana rawa ta banko ƙofar ɗakin ta shiga tana duban maman Murja cikin ƙanƙance idonta, da sauri ta kashe wayar tana dubanta da yage baki.
Amarya yanzu nake zancen zan kiraki akan na faɗa miki saƙon malam, ashe kina hanya sannu da zuwa.
Munafuka azzaluma to wlh naji duk abinda kika ce a kaina, na baki nan da gobe ki haɗo mini duk kuɗin da kuka damfareni zan zo na amsa in kuma ba haka ba zaki sha mamakin matakin da zan ɗauka akanki.
Wlh baki isa ba tunda aiki kika sa ayi miki, dan haka kuɗi suna gurin malam ya gama aiki dasu baki isa kizo kice a biyaki ba.
Wani shu’umin murmushi Madina ta saki.
Gobe In Allah ya kaimu na baki zanzo da yamma, kuɗina ya zama suna a haɗe.
Muzuba mu gani kaji mini yarinya kin bada kuɗi ayi miki aiki kizo kina cewa a baki, aiko uban kuturu yai kaɗan.
Cewar maman Murja tana fuffuka, Madina bata ƙara magana ba ta wuce ta fita, gida ta wuce cike da lissafin matakin daya dace ta ɗauka akan Maman Murja dan ba zata taɓa ɗaukar asara ba, ashe cutarta suka yi ba aikin gaske suka yi mata ba shiyasa komai yaƙi yi mata daidai ashe ba aikin da suka yi, gashi faruwar rikicinta dasu Asma ya zama silar biyan buƙatarta tunda har zai sauya mata gida, hakan yasa tace ba zata ƙara ɓata kuɗinta ba akan wani mallam ba, makaminta shine tsiwa da tsaurin idonta ya ishe ta tayi maganin Hamid, har ta isa gida tana lissafin zuci wanda bata sanar da momy komai ba dan bata so tayi mata faɗa akan biyewa maman Murja da tayi, amma kuma ya zama wajibi ta ɗauki mataki da kanta ta kashe case ɗin ba tare da wani yaji ba.
Washe gari Madina ta gama duk abinda zata yiwa Maman murja dan ta tabbatar sai sun kai ruwa rana dan ta kula matar ba tada tsoro balle kunya, hakan yasa tana barin gurin aiki ta nufi unguwarsu ta tsaya a gurin ‘yan sandan unguwar ta shigar da ƙara akan damfararta da maman Murja suka yi, hakan yasa aka bata ‘yan sanda uku da mota suka tafi gidan maman murja, koda suka isa basu tsaya ɓata lokaci ba suka kutsa kai cikin gidan, tuni yara suka isa da gudu suka sanar da ita ‘yan sanda sun zo, cikin Maman murja ya ɗuri ruwa, da saurinta ta saka hijab ta fito, ganinsu tare da Madina yasa ta yi mugun mamaki bata taɓa zaton hlamarin zai kaisu ga haka ba, ta tsaya tana duban Madina.
Yanzu Madina haka za muyi da ke? na ɗauka zaki zo mu sasanta ba tare sa kowa yaji ba.
Cewar maman Murja dafe da ƙirji, Madina tayi murmushi tana cewa.
Ai jiya naga baki biyo ta hanyar da za muyi sulhu ba dan haka ga ‘yan sanda nan zasu kwatar mini haƙƙina ta ƙarfin cin tuwo, yallaɓai ga matar data damfareni nan ku kamata har sai ta fito mini da kuɗina.
Madina ta ƙare maganarta ga ‘yan sanda, ba ɓata lokaci suka tasa ƙeyar maman Murja wacce take tayi musu magiya da ban haƙuri akan karsu tona mata asiri zasu yi sulhu, basu saurareta ba suka sakata a motarsu a baya dake buɗe tamkar sun kamo ɓarauniya, suka tafi gabaɗaya station, nan dai aka matse maman murja ta faɗi gaskiya dan saida tasha mari da duka da kulki, nan aka ƙara tura wasu ‘yan sanda tare da Madina suka tafi ɗauko malam, haka suka taso ƙeyarsa tare da saka shi a bayan kanta, duk yadda suka yi musu magiya akan zasu yi belin kansu sannan suyi sulhu a tsakaninsu abu yaci tura, dan Madina kuɗi ta sake musu akan su riƙe su na tsawon kwanaki, in suka ji wuya babu gardama zasu biyata kuɗinta kuma horon da suka sha zaisa ba zasu ƙara sha’awar cutar da wani ba, sai bayan sallar magrib Madina ta koma gida.
***
Hamid.
Sosai ya mayar da hankali kan gyaran gidan Madina, dama tunda ya gina gidan bai ƙarasa aikin ba ganin ba wai amfani da shi zai yi ba sayarwa zai yi ya samu riba, amma dawowar Madina gidan yasa shi ware kuɗi akan a saka duk abunda babu, musamman ya je *MG Funitures Company* yayi magana da CEO ɗin akan yana so a saka masa ƙofofi da kitchen cabinet da kuma kujerun Cushing na falo set da na gado set na ɗakinsa, haka suka tattauna bayan ya biya kuɗin kaya, ya basu adreshinsa domin zuwa buga masa aikinsa na ƙofofi na kitchen cabinet, sunyi masa sauƙi kasantuwarsa customer ɗinsu ne dan duk wasu kayan gidansa a gurinsu yake oder, sqi yayi sallama dasu ya wuce.
_Kayanmu tamkar daga turai suke ga kyau ga sauƙi, muna tura kayanmu ko ina a faɗin Nageria, ina mutanen Niger kuma ku matso kusa domin muna da manyan customers ɗinmu daga ƙasarku. Munayin kayan Funitures ko wani iri dangin kaya gida set. Cushings, Gado set, Kitchen cabinets, Dinning table, Kayan Office da company, Interior decoration etc. Zaku samemu a No.3 Ali Akilu Road, Freetime House, Daura Da Giwa Hospital, Kaduna. Ko a tuntuɓemu a wannan number 09034940106. Dan Allah serious magana in kun shirya._
Cikin kwana huɗu an fara aikin gidan har an kusa kammalashi, hakan yasa Hamid ya kira Madina ya sanar da ita fara shirin tarewa a gidanta, sosai taji daɗi da farin ciki a ranar Hamid yaje ya ɗauketa ya kaita taga gidan, ba ƙaramin kyau yayi mata ba dan komai yazo mata a tsarin da take so, farfajiyar gidan data ga ba fulawa tace a saka mata masu kyau harda faɗar waɗanda take so a zuba mata. Daga gidan sai da suka tsaya cin abinci wani rastuarant yayi mata siyayyar kayan ciye ciye kana ya sauketa a gida, Madina sosai take farin ciki da yanayin da ta samu kanta na kulawar Hamid, dan dama abinda take so kenan ya riƙa yi mata duk abinda take muradi.
***
Ranar Monday Hamid yana aiki a office masinger ɗinsa ya shigo ya sanar dashi yayi baƙo, Hamid ya bashi izinin shigowa kana masinger yaje ya isar da saƙonsa ga baƙon, mijin Maman Murja ya tura ƙofa ya shiga, Hamid yana ganinsa ya miƙe dan ya wayeshi sosai musamman a masallaci sukan dawo gida tare in sunyi sallah, ya bashi hannu suka gaisa kana suka zauna, Hamid yana cewa.
Alhaji Tanimu yau kaine da kanka a office ɗinmu, da fatan lafiya.
Lafiyar kenan Alhamdulillahi, dama nazo neman wata alfarma ne, ina so ka saka baki matarka ta janye ƙarar matata data kai gurin ‘yan sanda yau kusan kwana duɗu kenan a cel anƙi bada belinta.
Cike da tsantsar mamaki Hamid ke dubansa yace.
Ban gane matata ba? ni bani da alaƙa da ‘yan sanda kuma duk matana bansan wacce take rikici da matarka ba, anya ba kuskuren hanya kayi ba.
Kwarai banyi kuskuren hanya ba domin matarka itace ta kai ƙarar matata aka zo har gida aka kamata.
Hamid shuru yayi kana ya ɗanyi nazari kafin ya ƙara dubansa.
Wacce daga cikin matan nawa tace maka suna rikicin.?
Amaryar ce.
Hamid nan take ya gusar da mamakinsa dan yasan ko miye Madina zata aikata tunda suma basu tsallake ba sun kai ƙennansa gurin ‘yan sanda, dan haka cikin sanyin jiki ya miƙe yace suje station ɗin yaji ƙarin bayani, Baban Murja ya miƙe suka fito daga office din kowanne ya hau motarsa suka wuce Hamid dai a baya ya bishi zuciyarsa cike da tunanin meya haɗa Madina da maƙotansu.
Koda suka isa ya ƙara tabbatar da Madina ce, dan station ɗin da suka kai su Kubura nan ɗin ne, har gun DPO suka je suka gaisa kana mijin maman Murja ya koro bayani, DPO yasa aka fito dasu maman Murja aka kaisu office ɗin, nan aka sasu suka tsuguna kan guwarsu malam sai rarraba ido yake yi cike da jin kunyar abinda ya faru dashi, DPO ya koro musu bayanin takardar ƙarar da Madina ta yi kana ya kalli malam ya tambaye shi ya faɗi asalin meya haɗa su, malam ya gyara tsuguno ya zauna dan ranar wanka ba ɓoyon cibi ya shiga zayyano duk abinda ya faru tsakaninsu tun farkon zuwansu Madina gunsa babu abinda ya rufe, Hamid kam gumar mamaki ne ya karya masa duk garguwar jikinsa bai taɓa zato ko tsammani lamarin Madina ya kai har haka ba, dududu yaushe suka yi aure da har zata yi tunanin rabashi da matarsa ta mallake shi, yanzu ne ya tabbatar da yayi zaɓen tumun dare, ya ɗauka a iya sakarci da wauta da rashin kunya rayuwarta ya tsaya ashe har ya kai ga shirka, haka ya cigaba da baza kunne yana sauraren bayanin maman Murja wacce itama bata rufe komai ba, hatta tayin data dinga yiwa Sakina taƙi yarda saida ta faɗa, Hamid yasha mamaki har ya kasa magana. DPO shima bai zaci wannan ne damfarar da suka yiwa Madina ba tasa aka rufe su, da tun farko yayi bincike bazai riƙesu haka ba tunsa itace takai kanta gunsu domin a cutar da wasu, nan yace dole su saka hannu su biyata kuɗinta sannan ya bada belinsu ya kuma yi musu kyakkyawar gargaɗi akan in har ya kuma ganinsu an kawosu akan irin wannan to kotu zai kaisu domin a yanke musu hukunci daidai da abinda suka aikata, suka ce sun tuba ba zasu ƙara ba, Baban murja shima bai zaci wannan ne ƙarar ba da tun farko ya sani bazai yi ta zarya akan a sake masa mata ba, sosai yaji zafin lamarin dama ya jima yana zargin matarsa da rashin natsuwa gashi ba yida wani say sai abinda ta faɗa, yanzu ne ma ya dawo hayyacinsa, haka suka yi sallama da DPO ya tabbatar musu da zai kira Madina suyi maganar dan dama tace so take a riƙesu na kwanaki kafin a sakesu lokacin ta tabbatar da kuɗinta zai fita. Mijin maman Murja suna fita ya tsaya yana dubanta maman Murja ta sunne kai ƙasa dan tasan asirinta ya gama tonuwa, da kyar ya shanye malolon baƙin cikinsa ya buɗe baki yana cewa.
Daga nan ki wuce gidanku na sakeki saki biyu. Allah ya isa tsakanina dake.
Yana kaiwa nan a maganarsa ya buɗe motarsa ya shiga yaja, maman Murja tabi motar da gudu tana ɗaura hannu akai da ambaton ta shiga uku tana kuka wiwi, haka ya barta a gurin tana kukan baƙin ciki da dana sani tare da tsinewa Madina. Malam dama tuni ya cikawa bujensa iska bai ɓata lokaci ba.
[8/26, 6:48 PM] Rahma Kabir: *ƘAZAMAR AMARYA*
Na
©®Rahma Kabir MrsMG.
Wattpad @rahmakabir
Page 43.
Hamid office ɗinsa ya wuce ransa in yayi dubu to a dagule yake, koda ya isa yasa key ta ciki ya rufe ya zauna ya dafe kansa da hannu bibbiyu, damuwa da baƙin cikin auren Madina kawai ya samu kansa a ciki, yayi dana sani fiye da cikin masaki bai taɓa zaton yadda ya aurota zai samu matsala da ita ba duba da yana mata kallon mai ilimi da wayewa, ashe kallon kishe yake yiwa rogo matarsa Sakina itace dai rufin asirinsa wacce ta haɗa kyawawan halayya amma son zuciyarsa ya kasa fahimtar da shi haka sai a yanzu, ya tabbatar alhakinta ma dole Allah ya jarabceshi da Madina, haka ya ɓata lokaci shi kaɗai yana nazarin meye mafitarsa, yasa wayarsa a silent yaki fita masallaci hatta sallah ma anan cikin office yayi shi, shine a har ƙarfe takwas na dare yana zaune ya kasa miƙewa balle ya kama hanyar gida. Sakina kuwa tun bayan fitarsa da safe ta dinga kiransa akan zata sanar masa da zata fita tambayo registration ɗin islamiyar da take son shiga na layinsu, amma bai ɗauka ba hakan ba ƙaramin tada mata hankali yayi ba dan ko yaya Hamid baya yi mata haka, ko da ace bai ɗaga ba daga baya yakan tura mata saƙo ko kuma ya kira suyi magana amma yau tun safe har dare ba amo ba labari, bata san tana ƙaunar mijinta ba sai a irin wannan ranar dan shaiɗan yaita hasasho mata matsalolin daya samu Hamid, hakan ya sa ta burkice ta rasa sukuni ko abincin kirki ta kasa shi, yaran ma ganin rashin walwala a tare da ita yasa su natsuwa.
Da kyar Hamid ya iya seta kansa ya samu wata takarya yayi rubutun da zai yi kana ya miƙe ya ɗauki waya da key motarsa ya fito, mota ya shiga ya zauna kana ya koro addu’ar daya saba yi duk in ya shiga mota, ya kunna ya nufi gidansu Madina. Koda ya isa a gate yayi parking ya ɗaga waya ya kirata akan ta fito yana ƙofar gida. Cikin zumuɗi ta fito dan dama ta rubuta lis ɗin kayan masarufi da take buƙata ya zuba mata a gidanta akan in yazo zata bashi ya siyo mata su, tana fitowa ta buɗe gefensa ta shiga ta zauna ta gaishe shi, bai amsa ba sai bin fuskarta da kallo da yake yi, yana san son Madina amma a wannan gaɓar son ya ragu ba kuma zai rufe masa ido ba ya hanashi ai watar da abinda yayi niyya ba.
Beb sai kallo na kake yi hala kayi kewata sosai, wlh nima duk na ƙosa mu tare mu huta da wannan yawon a hanya, dama kai nake jira kazo ga list ɗin dana rubuta na abubuwan dana ke buƙata a gidana. Sannan muje ka siya mini shawarma shi nake jin ci.
Kallonta kawai yake yi har ta kai aya a maganarta kana yaja fasali ya sauke guntun ajiyar zuciya, baice komai ba sai ya buɗe inda ya aje takardar nan ya ciro ya miƙa mata.
Ki shiga gida ki karanta, list ɗin ma ki riƙe tukuna, ina da uzuri zan je gida.
Jikin Madina a matuƙar sanyaye ta amsa takardar tana dubansa, yadda taga yanayinsa babu walwala yasa bata ce komai ba ta buɗe motar akan maybe wasu sun ɓata masa rai, ta fito tana yi masa sai da safe kana ta juya cikin gida da sauri domin taga meke cikin takardar, bata kawo saki ba domin tasan daga ita harshi suna ɗokin komawarsu sabon gida, tafi bayar da wani saƙon ne daban ko ƙila takardan motarta ce ya kawo mata dan yayi mata ba zata, tana shiga falo ta zauna a cushing ta buɗe takardar a hankali ta soma karantawa, koda tazo gurin sakin a zabure ta miƙe tana ɗaura hannu akai sai ta kwarma ihu tana ta shiga uku Hamid ya tona mata asiri, a gigice momy ta fito daga ɗakinta suma masu aiki da saurinsu suka fito dan jin meke faruwa, momy tazo ta kamata tana ambaton.
Ke lafiyarki kuwa? meya sameki? ina Hamid ɗin?
Madina takardar data yar a ƙasa ta shiga nuna mata.
Mom shikenan Hamid ya sakeni ya rabu dani.
Da sauri momy ta cikata ta duƙa ta ɗauki takardar, ta karanta saki ɗaya yayi mata bisa dalilin kamata da yayi da laifin bin koka na aikata shirka, Momy ta dubeta tare tamke fuska.
Ya akayi yasan da wannan maganar? ina ce tun lokacin da kika zo muka yi maganar naje gun wancen matar muka shafe babin zancen, to ma in ya sake ki sai me akanki aka fara, Alhamdulillahi da babu ma yaro a tsakaninku, In Sha Allah a cikin kwanakin nan da kin fita idda zaki samu wanda ya fishi dama tuni na sakawa aurenku iyaka nasan ba lallai ya jima ba.
Mom wlh ina son mijina ina son Hamid fiye da yadda kike tsammani, ace sai da na samu kansa ina farin ciki da zan yi mulki a gidana ni kaɗai sannan zai sake ni. Maman Murja kin cuceni Allah ya isa tsakani na dake.
Da wani irin kallon tuhuma momy kebin Madina da shi, ‘yan aiki kuma suka kalli juna cike da gulma a cikinsu, momy ce taja hannu Madina zuwa ɗakinta tasa key ta rufe ta zaunar da ita gefen gado tana cewa.
Wacece maman Murja me tayi miki? Karki ɓoye mini komai dan ina buƙatar ƙarin bayani.
Madina kuka take yi sosai mai cike da nadama da dana sani, kaico da haushin kanta take ji dan a yanzu ne taji tana mugun son zama da Hamid, musammam yadda ta samu kansa cikin sauƙi yana yi mata duk abinda take so, ta ɗago fuska shaɓe shaɓe da hawaye cikin kuka tace.
Mom na kashe aurena da kaina ki taimakeni Hamid ya mayar da aurenmu ina sonsa wlh.
Madina ki faɗa mini me kika aikata sai naji ta ina zan iya taimakonki.
Momy ta faɗa tana tsureta da ido, Madina cikin kuka ta soma korowa momy bayanin haɗuwarta da maman Murja da duk abinda ya faru a tsakaninsu, sodai ran Momy ya ɓaci ta shiga nunata da tsaya.
Tayaya zaki aikata irin wannan abun ba tare da kin nima shawarata ba, na gaya miki bana son harkan malaman nan dan ni ban saba yinsa ba, ko wancen matar da kika ji naje gunta domin kawai ba nida hanyar sama miki mafita ne dole sai tanan, sannan daga kanta ban sake tunanin zuwa wani guri ba, to ki sani babu abinda zanyi miki ki koma gidan Hamid dama ba son zamanku nake yi ba, haka za kiyi haƙuri ki yi jinyar zuciyarki ki manta da shi domin baku dace da juna ba, rayuwarki daban naki daban.
Mom saina koma gidan mijina bana son kowa sama dashi a yanzu, tunda ba zaki taimaka mini ba shikenan dama kinfi son Anty Aisha akaina.
Ta ƙare maganar tana rusa kuka, Momy tsayawa tayi tana kallonta cike da takaici tama kasa ce mata komai daga ƙarshe ta fice daga ɗakin ta barta a nan zaune, Madina cikin azama ta miƙe ta shiga kiran Hamid a wayarta sai dai ta yi masa kiya fiye da shida bai ɗaga ba, kuka ta zauna ta cigaba da yi da tunanin ta wani hanya ne zata bi don ganin Hamid ya mayar da aurensu, bata taɓa sanin tana mugun son kasancewa dashi ba sai yanzu, bata jin zata iya rayuwa da wani namiji bayan Hamid sosai take jinsa a cikin zuciyarta.
****
Hamid.
Ji yayi har wani zazzaɓi yake ji a jikinsa domin yana matuƙar son Madina, amma rabuwarsu shine kamar abinda yafi zama masa mafi Alkhairi a yanzu, yasan dole sai yayi jinyar zuciyarsa amma na dan lokaci ne zai warware ya dawo yadda yake da, baya jin zai iya mata afuwa ya dawo da ita dan zai iya zama da ita da ƙazantarta amma banda shirka da bin malamai, yana ganin kiranta bai ɗaga ba dan wayar har lokacin a silent yake haka ya isa gida, Sakina tana jin dirar motarsa da saurinta tayi waje kamar zata kifa dan ba ƙaramin shiga damuwa tayi ba na rashin ji daga gareshi, yayi parking ya fito riƙe da key da waya, da sassarfa Sakina ta isa ta rungumeshi tsam a ƙirjinta dan niman kunya da mance inda suke tayi, ta shiga sauke ajiyar zuciya tana jin wani kwallar farin ciki yana barazanar saukowa daga idonta, Hamid ne yayi ƙoƙarin raba ta da jikinta suka tsaya kallon juna cike da yanayi na musamman, ko wanne da tunanin da zuciyarsa ke zuwa masa, shi dai Hamid tsantsar tausayin Sakinan yake ji daga cikin ransa, ita kuma tsantsar damuwa da ganinsa cikin rashin kuzari take yi, itace ta katse shurunsu da cewa.
Lafiya tun safe ina kira baka ɗaga ba wlh na shiga cikin yanayin damuwa mara misaltuwa.
Ki kwantar da hankalinki Sakinar Hamid gani a gaban na dawo, ko baki faɗa ba yanayin da kika tarbeni ya gamsar dani damuwar da kika yi dani, bana jin daɗin jikina ne kuma nayi busy sosai yau a office da fatan keda yarana duk kuna lafiya.
Yayi maganar yana murmushin yaƙe, itama murmushin ta mayar masa kana ta tuna da abinda ta aikata na rungumeshi a farfajiyar gidan da tayi saita sunne kai tana cewa.
To Alhamdulillahi tunda Allah ya kawo mini kai gida lafiya, muje ciki ka watsa ruwa sannan kaci abinci kasha magani, amma meke damunka haka?
Baya wuce Maleria, me kika dafa mana.
Tuwon shinkafa miyar agushi yaji gamda da naman kai.
Tana faɗa cike da farra a fuskarta, hannunta ya kamo suka fara tafiya.
Shiyasa nake matuƙar sonki saboda kin san duk abinda nake muradi, na tabbatar yanzu zanji na warke daga yanayin da nake ji na sabbin salonki, gashi kinyi kyau Masha Allah kin zama ɗaya tamkar da dubu Sakina.
Ka daina koɗani haka mana aikina ne dana kula da kai tamkar kwai.
Dakatawa yayi da tafiyar da yake yi itama dole ta tsaya dan ya kama hannunta, suka kalli juna Hamid ji yake tamkar ya haɗiyeta.
Wai dama haka nake a gunki amma a baya kika barni ina ta garari, dan Allah Sakina ki cigaba da bani irin wannan kulawar karki gaji dani domin ke ce farin cikina, In Sha Allah ni kuma zan mayar dake sarauniyata sai abinda kike so zanyi.
Sakina ji tayi kamar ta shige jikinsa ta rungume shi amma ganin a waje suke yasata jansa suka wuce ciki ba tare da tace masa komai ba, shima bai mata musu ba suka shiga ciki, yara duk suna ɗakinsu dan da wuri suka kwanta saboda yadda suka ga mamansu ba walwala, Sakina saida ta kai ɗakin Hamid ta buɗe ta shiga dashi ciki ta jingina shi jikin ƙofar ta shiga cire masa maɓallin rigarsa suna kallon juna cike da tsantsar shauƙi, Hamid kasa haƙuri yayi ya tallabo kuncinta ya haɗe bakinsu guri ɗaya ya shiga aika mata da zazzafar saƙo itama tana mayar masa, a takaice a wannan daren sun shayar da kansu wani irin danyan zuma mai tsananin zaƙi da wuyar misali, dan duk da Hamid yana cikin alhinin rabuwa da Madina amma fa Sakina ta rage kaso saba’in a cikin ɗari na damuwarsa, dan ya tabbatar Sakina ce cikon addininsa kuma yasan a hankali in tana bashi irin wannan zazzafar ƙaunar zai manta da rayuwar da yayi da Madina.
**
Washe gari Hamid kafin ya fita aiki sai da ya fara zuwa gidansu ya samu Abba a ɗakinsa, bayan sun gaisa sai yayi jim yana tunanin ta yadda zai faɗawa Abba ya saki Madina, Abba ya kalleshi da kyau.
Akwai magana a bakinka meke faruwa.?
Abba jiya na saki Madina saki ɗaya, bisa laifin daya cancanta ace na rabu da ita.
Da ido Abba yake binsa bai iya ce masa komai ba bisa ga yana son gamsasshiyar bayani, Hamid baiyi ƙasa a guiwa ba ya cigaba da koro masa bayanin dalilinsa na sakin har ya kai ƙarshe, Abba ya sauke ajiyar zuciya.
Allah yasa hakan shine mafi alkhairi a tsakaninku, na gamsu da bayaninka domin Allah ba abin wasa bane duk wanda ya ce Allah bai isar masa ba to tabbas tun a duniya zai ga sakamako. Gaskiya lamarin yarinyar ya girma sosai tunda har ta iya aikata haka wanda tsantsar rashin tarbiyya ce da kuma rashin jagora na kwarai, dan haka na goyi da bayanka akan wannan hukunci sai dai ina mai ƙara jan hankalinka akan wannan ya zama izina a gareka da masu tunani irin naka, Sakinar daka raina gashi itace alkhairi a gareka, ni bazan taɓa hanaka ka ƙara aure ba amma kasan a ina zaka nima auren, wacece yarinyar? ya gidansu yake? wani tarbiya gareta? kayi kyakkwar bincike akanta kafin a kaiga auren.
Gaskiya ne Abba kuma In Sha Allah na ɗauki darasi sosai akan aurena da Madina, wanda kuma ya zama izina a gareni kuma na ɗauki hanyar yin gyara koda a nan gaba.
To Alhamdulillahi daka fahimci haka, Allah yayi muku albarka.
Cewar Abba yana murmushi, Hamid ya amsa da amin kana yayi sallama da shi ya fito ya wuce aiki, dama saida ya fara gaisawa da Hajiya kafin ya isa ɗakin Abba. Koda Hajiya ta samu labarin sakin Madina a bakin Abba ba ƙaramin farin ciki tayi ba sai dai ta ɓoye hakan a gaban Abban, tace ai Hamid ma ya haƙura da ƙara wani auren tunda Sakina ta yi hankali.
[8/27, 4:28 PM] Rahma Kabir: *ƘAZAMAR AMARYA*
Na
©®Rahma Kabir MrsMG.
Wattpad @rahmakabir
Page 44.
Sai da aka yi mako guda kafin Hamid ya sanar da Sakina ya rabu da Madina, sai dai bai gaya mata dalilin ba rabuwarsu ba itama bata nima ta sani ba face addu’a da fatan Alkhairi data yi musu. Haka suka cigaba da rayuwarsu cikin natsuwa da kwanciyar hankali.
Madina kuwa har office take binsa akan ya yafe mata amma Hamid yayi buris da ita, tasan Hajiyarsa ce kaɗai zata iya saka baki ya mayar da ita amma kuma ta lalata alaƙarsu da kanta, da ace ta riƙe Hajiyarsa da muhimmanci kamar yadda suka nuna mata soyayya tun farko to da tabbas in tabi ta hannunta Hamid sai ya maida aurensu. Abbansu kuma bai bata fuska ba balle taje gunsa, yanzu ne ta gane Momynta ta taka rawa sosai akan alalacewar aurenta, dan da bata bi wasu huɗubobinta ba da tabbas tana zaman lafiya a gidanta, yanzu ne ta gane ba gata tayi mata ba face ta cutar da ita ne, wannan ne ya haifar da rashin jituwa a tsakaninsu, wanda Madina gabaɗaya ta ɗaura laifi mutuwar aurenta akan momy, ita kuma Momy tana ƙoƙarin son fahimtar da ita aurenta da Hamid ba alkhairi bane, hakan yasa Madina ta samu kanta a cikin damuwa wanda hakan ya shafi aikinta bata iya mayar da hankali shiyasa aka bata hutun gargaɗi, ita kuma ganin haka yasa ta shirya ta koma gurin yayarta Aisha dake Abuja. Tun tana lissafin Hamid zai maida aurensu kafin ta fita idda har tazo ta fita idda ba labarinsa, hakan yasa ta sadaƙar da cewa ta rasashi kenan har abada, saboda tabi duk hanyar da zata bi bata samu nasara ba, hatta abokinsa Habib yayi mata ƙoƙari amma Hamid ya kafe yaki saurarenta, Kausar ƙawarta ko tana nan da tsohon cikinta tana zaman lafiya da mijinta saboda ta saka aure ibada ne a cikin ranta, Madina tayi dana sani sosai da cizon yatsa dan tasan ta yiwa kanta illa na barin nagartaccen miji. A nan Abuja manema sun fara damunta sai dai har yanzu ba wanda ya kwanta mata domin har gobe Hamid ne a zuciyarta.
Su Asma sun samu labarin mutuwar auren Madina, ita kam bata yi wani murna ba bisaga halin da take ciki a yanzu, domin mijinta yanata shirye shiryen ƙara aure har an kai sadaki, bata taɓa zaton duk wata mace haka take ji ba in za a ƙara mata kishiya ba sai yanzu, haƙiƙa ta jinjinawa Sakina da irin juriya da haƙurin dabta yi da ɗumbin cin kashin da suka yi mata, lallai aka ce ciwon ‘ya mace na ‘ya mace ne sai yanzu ta gane haka, dan sosai auren mijinta ya gama karya garkuwar jikinta ya kashe mata baki duk wannan rashin mutuncin da masifa ta nimeshi ta rasa, Hajiya ma bata ji daɗin auren mijin Asma ba dan abun da ciwo amma haka ta dinga bata haƙuri tana bata misali da Sakina, akan haƙurin data yi gashi ya zame mata riba, Kubura kam tunda taji mijin Asma zai ƙara aure ta ƙara shiga hankalinta.
****
Sakina tana zaune ita da yara a falo Hamid ya fito daga ɗakinsa ya ƙaraso falon ya miƙa mata takardar visa da komai ta amsa tana dubansa, fuskarsa cike da murmushi yake cewa.
Sati mai zuwa In Sha Allah zamu tafi Umara tare.
Wani irin tsalle Sakina tayi ta rungume shi ta shiga zuba masa godiya, Hamid ya jayeta daga jikinsa yana dubanta.
Kin cancanci fiye da haka Sakina domin kece hasketa, haƙurinki ne ya jawo haka.
Allah ya saka da alkhairi yasa kafi haka ya ƙara maka buɗi na alkhairi, ya kare ka daga sharrin masu sharri ina alfahari da kai Hamid nagode.
Sakina ta faɗa tana matsar kwallar farin ciki, Hamid lakace hawayenta yayi yana cewa.
Jeki shirya muje mu yiwa yara siyayya dan a gidan Hajiya zamu barsu, saboda zamu yi kusan wata a can mu huta sosai.
Da sauri ta koma ɗaki dan Hamid bai taɓa fita da ita ba irin haka suyi siyayya a tare. Sakina shiga tayi na musamman na kece raini, koda ta fito sai da ta sha hotuna gurin Hamid kafin suka tafi da yake yanzu Rauda itama sun sakata makarantar su Mufeeda. A babban super market suka yada zango wanda suka fito suka jera sai suba ƙamshi suke yi gwanin sha’awa, suka shiga suka fara ɗiban duk abinda suke so, Sakina ta isa gurin kayan kwalliyar mata taga wani tabarau nan ta ɗauka ta saka a idonta sai ta juya tana cewa Hamid.
Ya ka ganni?
Kinyi kyau irin sosai ɗin nan.
Yayi maganar yana haɗe babban yatsarsa da manuniya, ta saki murmushi ta cire gilas ɗin ta saka cikin siyayyarta taji a ranta daga ranar zata fara amfani da glass, lokacin da Hamid ya nufi ɓengaren kayansu na maza yana dubawa ita kuma tana ɗibar nata danasu Mufeeda, sai kawai taji anyi mata sallama a bayanta, da sauri ta juya dan muryar ba zata manta me ita ba, Madina ce cikin shigar atamfa da gyale tayi kyau sosai sai dai ta ɗanyi rama, cikin sakin fuska Sakina tace.
Hajiya Madina ya gida.
Lafiya lau Alhamdulillahi, dama ina son haɗuwa dake na baki haƙuri akan abubuwan da suka faru a tsakaninmu.
Haba ai babu komai ya wuce.
Nagode ki gaida yaran.
Zasu ji ta bata amsa kana suka yi sallama ta cigaba da siyayyarta Madina ma ta ɗiba wasu turaren da take so, koda taje biya aka ce mata anbiya mata tasan Hamid ne dan taga lokacin da yayi magana da mutanen, suka saka mata a leda ta amsa ta nufi titi ta tari napep ta wuce gida, satinta ɗaya kenan da dawowa daga Abuja domin cigaba da zuwa aikinta, dan hutun da suka bata ya ƙare harta ƙara da nata, ganin suna ta yi mata barazanar zasu koreta gabaɗaya yasa ta dawo tare da karɓar ƙaddararta na rashin Hamid. A hanya Sakina take cewa Hamid taga Madina a cikin super market yace shima ya ganta basu dai yi magana ba.
Abban Mufeeda, Madina tayi sanyi sosai har ce mini tayi wai nayi haƙuri akan abinda tayi mini.
Dole ta nina gafararki dan ta cutar dake ai, Allah yasa mu dace.
Daga haka suka yi shuru. Sakina dai tun haɗuwarta da Madina abin ya tsaya mata a rai take ganin koda Hamid bai mayar da ita ba gaba zai iya ƙara aure, kuma bata san waye zai ɗauko mata ba ita dai dazai mayar da Ƙazamar Amaryarsa da yafi mata, ko ba komai kowa yasan matsayinsa duk da tana kishinsa sosai amma ba zai rufe mata ido ta hanashi aikata abinda Allah ya bashi damar yi ba, yanada kuɗi da komai kuma yasan daɗin mata biyu nan gaba zai iya ƙara auren, hakan yasa Sakina ta samu Hamid da maganar, amma ƙiri ƙiri ya nuna baya ra’ayi duk da bawai baya son Madina bane kawai halinta ya tsana, tunda kuma ya gwasale Sakina bata ƙara kawo masa maganar ba har suka bar ƙasar zuwa ƙasa mai tsarki. Sabon amarci suka fara kamar ba zasu dawo ba, a taƙaice sai da suka samo ɗan Saudiya dan da ƙaramin shigar ciki Sakina ta dawo gida. Anan ne ta soma laulayi ga rashin bawa Hamid haɗin kai a gado, wannan ne dalilin daya saka shi fara tunanin wani auren dan shi mutum ne mabuƙaci kuma bai yarda da zina ba, hakan yasa shi fara tunanin Madina dan yasan ƙila zuwa yanzu ta dawo hayyacinta tasan tayi ba daidai ba, bai yi ƙasa a guiwa ba yaje ya samu Abba da maganar ya nuna masa yana son mayar da ita ne duba da ya fahimci ta yi nadama, Abba ya goya masa baya yace Allah ma muna yi masa laifi ya yafe mana balle a tsakaninmu ‘yan Adam, kuma daya je a auro wacce bai sani ba gwara Madina daya tabbatar ba zata kuma aikata kuskuren data yi a baya ba, bayanin Abba shine ya ƙarawa Hamid ƙarfin guiwa, baibi takan Hajiya ba dan yasan ba zata taɓa yarda ba ya barta taji labarin a bakin Abba. Hamid bai ɓoyewa Sakina ba kuma ta nuna amincewarta duk da a cikin ranta tana tsananin jin kishinsa, musamman yanzu da tasan mihimmancin sa a rayuwarta ga aurensu a yanzu yafi na baya daɗi, amma haka ta zage ta mara masa baya dan daya ɗauko mata wata tazo ta farraƙa musu zaman lafiyarsu gwara ya auro ƙazantarsa ta san darajar raƙumi yayi nesa da ƙasa, a yanzu Madina ba zata gwada mata komai ba dan ta fita nesa ba kusa ba a gurin Hamid.
A cikin wata guda aka yi maganar aka sake ɗaura auren Hamid da Madina ya biya sadaki, Madina kamar zata yi hauka dan murna. A washe gari ta tare a sabon gidanta da tuntuni Hamid ya gama gyaransa ya rufe. Ta soma rayuwa ita kaɗai ba zancen ‘yar aiki dan tayi alƙawarin koyan komai da kanta hatta girki ta mayar da hankali ta koya duk da har lokacin bata iya ba, Hamid da kansa yace ta samu mai aiki tace ita ba zata samu ba zata koya aiki da kanta sannan ma in ya yarda zata riƙa zuwa Sakina tana koya mata girki dan tana so ta iya, Hamid yace ta dai nima wani gurin da ake girki ta koya baya son damuwa, bata yi masa musu ba haka ta samu online class na girki ta shiga sannan tana yawan kiran Kausar ko taje gidanta ta faɗa mata yadda ake yin girki da gyaran gida, ƙazanta dai tana taɓawa sai dai ba kamar na da ba, in tayi kuskure Hamid yana faɗa mata tana ƙoƙarin gyarawa, kuma a yanzu tana ƙoƙarin gyara alaƙarta da Hajiyarsq duk da har gobe bata sake mata ba, tsakaninta dasu Aama ba mai zuwa gun wani kadaran kadahan, a gurin Sakina ce kawai take samun tarba mai kyau dan sosai take so su zauna lafiya tana yawan zuwa gunta suyi zumunci, ita Sakina bai fi sau biyu taje gidanta tare da yara ba amma ita ko yafi a ƙirga.
Lokacin da Sakina ta ƙara haihuwar Namiji mai suna Salihu, to da Madina aka yi shagalin suna har tana gayyatar abokan aikinta, sunyi komai cikin girma da karamci duk da bata samu sakin fuska a gun su Kubura ba amma hakan bai dameta ba tunda a yanzu ba tada matsala dasu. Sannan itama tana da ƙaramin cikinta wanda take fatan ta haifeshi taga jinin Hamid a tare da ita, tana mugun jin zafin kishin Sakina sai dai a yanzu tana controlling da daidaita tunaninta, kuma ta daina kaiwa momy ƙorafin Hamid dan bata son wata matsala, abokiyar shawarta a yanzu Kausar ce ƙwarya, wacce kuma tana bata shawarar kwarai kuma tana ganin nasara akan duk shawarar data bata.
Hamid ya samu kwanciyar hankali sosai ga iyalinsa har wani ƙiba yayi, kuma a tsakanin matansa yana ƙoƙarin yi musu adalci, duk da Madina tana taɓa ƙazanta amma haka yake haƙuri da ita ganin tana ƙoƙarin gyarawa, babu yadda ya iya tunda Allah ya jarabceshi da auren ƘAZAMAR AMARYA yasan hakan zai zama labari watarana.
Ƙarshe.
Alhamdulillah!
Alhamdulillahi da Allah ya bani ikon kammala wannan littafi lafiya, Allah yasa za muyi amfani da darasin da ke ciki ya bamu ladansa, kuskure dake ciki Allah ya yafe mana yasa mu gama da duniya lafiya.
Ina mai miƙa ɗumbin godiya a gareku masoya wannan littafi daga mutanen WhatsApp, Wattpad, Facebook dama sauran kafar sada zumunta inda littafin nan yakai, haƙiƙa nasha addu’o’i da ɗumbin yabo a gareku, Allah ya saka muku da alkhairi ya haɗamu a Aljanna maɗaukakiya. Ina matuƙar ƙaunarku Allah ya bar zumunci.
Ina mai ƙara mika gaisuwar ta’aziyar mijin ɗaya daga cikin member ɗin group ɗina Aisha Mahmood wacce aka fi sani da maman Hayat, Allah ya ya ƙara miki haƙurin rashi ya jikansa da Rahma yasa Aljanna ta zama makomarsa, ya raya abinda ya bari Amin.
Ni Rahma Kabir matar MG Ummu Sultan da Samha nake yiwa masoyana fatan alkhairi sai mun haɗu a sabon littafina da zai zo cikin kwanakin nan In Sha Allah. Nagode.