Auta waziri kukeji maaaalam
Na ji na gani, zan baki lokaci na
Tunda kinka nuna qauna, dare da rana
Baki nuna so, domin arzikina
Kikan tsare mutunci ko ba kya gaba na
Ke nake gani
Ke nake gani
Ke nake gani to bani kula kowa
Kai nake gani, kai nake gani
Kai nake gani to bani kula kowa
Ke nake gani, ke nake gani
Ke nake gani, ya mai farin jini *2
In ka yi sansani, kayi kwarjini
Kayi kyan gani tauraron zuciya ta
Hannuwa na miqo
Riqesu suyi karko
Ayi mana baiko, musha biki na aure
Kai nake gani, kai nake gani, kai nake gani to bani kula kowa
Ke nake gani, ke nake gani, ke nake gani ya mai farin jini
Ke nake gani, ke nake gani, ke nake gani to banikula kowa
Ni na san so yana da zaqi, kuma yana dadaci
Ana farin ciki cikinsa har da qunci
In damuwa yazo, ka kasa cin abinci
Yasa ka laulayin jiki, har ka kasa bacci
Na ga damuwa
Na qi shan ruwa
Kin zamo jinin jikina yar uwata
Ke nake gani, ke nake gani,
Ke nake gani ba zan kula kowa ba
Kai nake gani, kai nake gani
Kai nake gani to bani kula kowa
Ke nake gani, ke nake gani,
Ke nake gani ya mai farin jini*2
Bugun zuciya, shi yake sa kewayar jini
A so na riqe ka na sani baka yadani
Alamunka sun gwada hakan zaka je dani
Ko an lura ni fa Kan ka to nifa na gani
Don ka yi mini gata, ba ka kula Mata
Ko na shige cikin duhu kana cire ni haske
Ke nake gani, Ke nake gani
Ke nake gani, ya mai farin jini
Kai nake gani, Kai nake gani
Kai nake gani to bani kula kowa
Akan ki nake misali, Ke kika ban kula
Kin maida so dalili, kika zamo sila
Da wayau na zo gare ki, Sai na zamo dila
Na Zama mallakinki, baki da matsala
Kinyi haquri, Kinyi qoqari
Kin jure masu qi, kin tsaya guri na
Ke nake gani, Ke nake gani
Ke nake gani, ya mai farin jini
Kai nake gani, Kai nake gani
Kai nake gani, to bani kula kowa
Ke nake gani, Ke nake gani
Ke nake gani, ya mai farin jini.