Saturday, September 13, 2025
26.7 C
Abuja

Kuskuren Baya by Aysha Bagudo – Complete

*In the name of Allah the most gracious the most merciful*

🅿️01

Zara-zaran yatsun hannunta   wanda suke sanye  da zobina masu matukar  kyan gaske da d’aukar hankali  ,idona ya soma  hangowa sanadiyyar motsa hannun da take tana   juya stearing   tana  ɗan kad’asu lokaci-lokaci saboda   wak’ar dake tashi a cikin Motar, tare da fitar sautin siriryar muryarta me dadin saurara.
       ‘I don’t care who you are, where you from what you did as long as you love me’. sautin  dake tashi kenan a cikin motar na Back Street Boys wanda take marming  kamar ita tayi shi.
      yayinda a hankali take  motsa  lips  dinta  kamar batason motsasu,  gefe guda   kuma  zuciyarta ke bugawa da matsanancin karfin gaske  wanda  ta rasa dalili faruwar haka  tun safe  ta tsinci kanta cikin tsanani faduwar gaba ..

Shiru motar baka jin sautin komai sai na qarar sautin wakar dake tashi a hankali  ta ɗauki hanyar  TANWER HOSPITAL  dake Ikeja in side  …

Kyakkyawar yarinya ce ajikin farko siririya mara kiba  mai  kyakkyawar  fuska  dake ɗauke da  siririn hancin   Kamar an zana mata shi ,mai dara daran idanu dake zagaye da gashin ido da gira , ba’a iya   ganin  kwayar idannunta  saboda Black sunglass dake sanye a face dinta ita ba fara bace haka Kuma ba za’a kirata da baka ba chocolate colour  ce me kyan gaske kamar ita tayi kanta  dan  rashin kibarta  qara mata  kyau yayi adalilin dukiyar fulaninta dake cike bam da qirjinta ,yanayin fatar jikinta kawai  zaka kalla kasan daga  irin gidan  data fito dan  asalin kamala  ta ya’yan masu arziki sun zauna mata ajiki babu karya ,kayan jikinta kuwa tun daga kan  rigar jikinta takalminta handbag   har zuwa kan  agogon dake d’aure a tsintsiyar hannunta tsadaddun gaske ne  ..

Lokaci guda sautin Motar ya sauya ‘Cardi! Cardi!……wooo Leave a bitch alone….’ da sauri ta dannah receive batare data kallah wanda ke calling d’in nata ba.

“Tan Baby”. Da sauri jin me kiran nata yasa ta kalla inda wayar ke ajiye tare da yatsina fuskarta sannan ta kai hannu ta ɗauki  bluetooth ta manna  a kunneta ta cigaba da tuki batare da tayi magana ba .
        “Kina ina? “Ya tambaya cikin low voice kamar yana ganinta.
        Tabe ‘yan kananun lips d’inta tayi tana yatsina fuska sannan tace “Why?”. Ta tambaya cike da jin haushin tambayar daya mata tana  kara tsura ma wayar  ido , ya sauke ajiyar zuciya kamar yana kallonta.
  
Batare data ankara ba steary d’in hannunta ya kubce  mata sai ji tayi Motar ta yi wani irin juyi , kasa  controlling d’in steary din tayi take motar tayi kan wani matashi wanda yake shirin tsallakawa. “Move aside move aside!”. Abunda take iya nanatawa kenan tuni  glasses din dake manne da idannunta ya cire batare data ankare ba.
        Idannunta ya firfito waje shima ita yake kallo  yana kokarin janyewa yana daga mata hannu alamun ta kauce cikin rashin sa’a saida ta dan goge shi sannan ta tafi ta bugi wani gini dake gefe.
     
“Innalillahi!”. Kalmar daya furta kenan yana kallonta   wacce tuni kanta ya bugu da steary din  tare da samun makwanci akai.
         da sauri yayi kanta ya bude murfin dake gefenta. “Baiwar Allah baiwar Allah! Ya fada cikin rude’wa ganin jinin dake diga daga goshinta tana kallonshi tana lumshe ido alamun tana so ta mishi magana, amma ina tuni idannunta suka rufe ta kasa aiwatar da komai , tunda yake bai taba ganin  macen data mishi kyau ba irin ta, kallonta kawai yake baya ko kifta idanunshi  yana jin zallar bacin rai na ratsashi “ko tunanin me take da har take  ƙoƙarin ganganci da rayuwata da tashi rayuwar ?  a hankali ya ja tsaki yana furzar da iska mai zafi  .
        “Hello! Hello!! Hello Tan!!! Talk to me baby me yasa kikai shiru? Are you alright?”. Duk na cikin wayar ke wannan surutan kyakywan matashin dake tsugune  gefenta ne yaji wadan nan tambayoyin bai bada amsa ba inda  yasa hannu ya shiga kiciniyar cire seat belt  din dake zagaye a jikinta dan a samu a bata taimakon gaggawa.

Hot this week

Kazar Kwanci By Rufaida Omar

Kazar Kwanci By Rufaida Omar *1)*  " Mairamu! Mairamu!!" Matar dake zaune...

KAZAMAR AMARYA Na Rahama Kabir Mrs Msg

KAZAMAR AMARYA Na Rahama Kabir Mrs Msg Rahma Kabir:...

RUGUNTUSUMI Book 2 Compelet

RUGUNTSUMI Book 2 part 1 Rubuta labari Abdul’aziz Sani Madakin Gini Ɗaukar Nauyi Mansur...

GUDUN KADDARA NA HUGUMA BOOK 2

GUDUN KADDARA NA HUGUMA BOOK 2            ".............ya fada soyayya?,yana...

Gudun Kaddara na Huguma Book 1

Gudun Kaddara na Huguma Book 1 🏃🏽‍♀️ GUDUN ƘADDARA🏃🏽‍♀️ H U...

Topics

Eniola Badmus Reaffirms Her Support for President Tinubu, Sparking Reactions

Eniola Badmus, a well-known actress and Special Assistant for...

Rapper Jeriq Explains Why He Has Never Been in a Relationship

Nigerian rapper Jeremiah Chukwuebuka Ani, widely known as Jeriq,...

Album Releases: Ruger and Joeboy Face Off in a Supremacy Battle

The Nigerian music scene is buzzing with excitement and...

“Famous singer NBA YoungBoy has been released from prison.”

Popular American singer Kentrell DeSean Gaulden, better known as...

“My kind of wealth cannot be achieved through investment,” Davido proudly declared.

Nigerian Afrobeats singer David Adeleke, widely known as Davido,...

“I backed Tinubu, but the hardship is becoming unbearable,” said Cynthia Morgan.

Nigerian singer Cynthia Morgan, now known as Madrina, has...
spot_img

Related Articles

Popular Categories

spot_imgspot_img