Lamba……. Lamba, lamba
Lamba…… Lamba
Lamba
Lamba….. Lamba raina Ke ce lamba ta daya, cikin raina, soyayya ta ki na qara yin girma
Lamba….. Lamba raina Kaine lamba ta daya, cikin raina, soyayya ta ka na qara yin girma
Zuciyar ki kin sa ni
Farin ciki kike ba ni
Kin sa ni na kece raini, cikin abokai…
Babu abinda nike shakka
Kin mini shimfidar fuska
Tuwo na girma kun tuqa da miyar sarakai….
Kin ce ba rabuwa
Mun zama tamkar da da uwa
Shaquwa ta Kai shaquwa ko da ba mu tare muna ganin juna
Kai zan yi wa kalamaina
Kai zan baiwa muqamaina
Ungo makullaina ka riqe….
Ni ban furta da wasa ba
Samari dukka basu Kai ba
Kana Nan ban ganin kowa da ido basu ishe ni kallo ba
Kai za ka bani gurin kwana
Kullum ka zauna a dama na
Shi ne fassarar mafarki na da nake kullum cikin barci
Bani da aiki Sai na ki
Ako dayaushe tunaninki
Da na yi kwance mafarkinki nake…..
Mutum da ba ya boyuwa
Da Ke nake son rayuwa
Ba na son rabuwa Dake….
Zuciya ta Ke kin mallake….
In ba Ke ba akwai sa Ke
Mata ba zan Kalle su ba
Dani dakai Allahu yayi hadawa
Wa ne Mutum ya yo rabawa
Muna kama ake ta cewa da anganka ni ake tunawa
So ne silar hakan baby
Sai godiya gurin rabbi
So shi yasa cikin qalbi
Suna in ce dakai hubby
Liman, Kai ne gaba mai martaba
Baza su Kai ka ba Kai ne lamba ta daya
Lamba…. Lamba raina Ke ce lamba ta daya, cikin raina, soyayya ta ki na qara yin girma
Lamba……. Lamba
Lamba
Lamba…. Lamba
Lamba
Lamba…. Lamba
Lamba
Lamba…… Lamba
Lamba.