Lokaci ne….. *2
Lokaci ne, gashi namu ya zo auren mu za a daura, yau mun cimma burinmu a qauna
Eeeeeeeeeh…….
Lokaci ne, gashi namu ya zo auren mu za a daura, yau mun cimma burinmu a qauna
Ke na hango, jiki a take ya hau dari
Sai na rugo, qafafuwa na cikin sauri
Ungo Ungo, kyauta gare ki mai alkhairi
Bude ki duba, zuciya ta ta kamu da qauna
Nai mafarkin Gamo da Kai a sa’in bacci
Ka taho guna Don nufin ka kore qunci
Ni ka zabo Hakan gare ni ka yi karamci
Nagode Allah, shi ya bani Wanda nike qauna
Ku dau girma ku bata, ta Zama malama
Kun San ya kamata, gwara ku sallama
Don na Bata tuta, ta Zama jaruma
Kun bani dama, wacce nakkaso ita ta Soni Kwai alama, zamu more soyayya da qauna
Eeeeeeeeeh…..
Lokaci ne gashi namu ya zo auren mu za a daura, yau mun cimma burinmu a qauna…..
Baqo in zai mutunci, yayo sallama
Tuwon girma da nama, shine Karrama
A so na bar madaci, na dau Zuma
Ba husuma, dukka Inda zanje hannunka za ni kama, tunda Kai kake da Dada Raina
Kyakykyawa son kowa, yar budurwa ta
Kida ya sani rawa, ni da matata
Farin ciki ku ka gani cikin idanuna
Ranar biki zani Kira dukkan abokaina
Su Taya murna, tunda na Riga na samo
Farin ciki na, damuwa tana nesa da guna
Gasa da za ayo shi na San ba a kada mu ba
Ko da za a kaimu, na San ba a zarce mu ba
Mu ne Kan gaba ku Kira mu na daya a lamba
Muna qololuwa tafiya ba a tadda mu ba
Jini da hanta, rabuwar mu zaiyi wuya
Kar da ma ku tanka, Nan gani ku bar ni da mai sona
Lokaci ne gashi namu ya zo auren mu za a daura, yau mun cimma burinmu a qauna
Eeeeeeeeeh……
Lokaci ne gashi namu ya zo auren mu za a daura, yau mun cimma burinmu a qauna.