Autar Mata Lyrics by Auta Waziri

    0
    474

    Auta waziri kuke ji malam

    Kuzo kuji ga autar mata
    Kar ku taba mini yar gata
    Ku barni kawai nayi mata rawa
    Babu irinki cikin mata

    Kuzo kuji ga auta na maza
    Kar ku taba mini dan gata
    Ku barni kawai nayi masa rawa
    Babu irinsa cikin su maza

    Autar mata……..heeeeey
    Autar mata……haaaaaah
    Autar mata……
    Kuzo kuji ga autar mata

    Zaqi na zuma ba ya illa,naji tun farko
    Bara na zube muku labarin, da na dan dauko
    Da na tsunduma kogin soyayya,nayi ninqaya na hadu da ya mai alkunya a daren farko
    Mun shaqu da ita a soyayya ba ja baya
    Abinda take so ta nuna, kuma na dauko
    Ku barni kawai ni nai nisa
    Sonta jikina yayi rassa
    Ku bar maganar ma nayi bacci
    A mafarkina naga mun aure

    Kuzo kuji ga auta na maza
    Kar ku taba mini dan gata
    kubarni kawai nayi masa rawa
    Babu irrin sa cikin su maza

    Autar Mata…. *3

    Abinda nike so ka bani, ba ka min qarya
    Gare ni ka zama cikon buri……..autar mata
    Ka riqe matakan soyayya kai ba ka zarya ,to dole a saka a tarihi…….autar mata
    A rai ka dasa min soyayya,kai daya ne da wuri
    Gare ka nake dada tambihi……..autar mata
    Gare ni ka zamto alkhairi. Da bai manta uwa
    Abarni da kai muyi soyayyaa….kar muyo rabuwa

    Kuzo kuji ga autar mata
    Kar ku taba mini yar gata
    Ku barni kawai nayi mata rawa, babu irinta cikin mata

    Kuzo kuji ga auta na maza,kar ku taba mini dan gata
    Ku barni kawai nayi masa rawa .babu irinsa cikin su maza

    Sabo da maza akace jari,na san kin gano ke zaki qure su a labari …..
    Samun mace ince tamkar ki alkhairi ne ma
    Ki kauda dukan wani mai sharri……
    Kowa ya fada miki zai so ki, sam bai kai wa ni
    Haka din yake ba wani inkaari……
    Na bar magana in ba hujja ,so baya tabuwa
    Mai yinsa yake masa linzami don kar ayi rabuwa

    Kuzo kuji ga auta na maza
    Kar ku taba mini dan gata
    Ku barni kawai nayi masa rawa
    Babu irinsa cikin su maza

    Autar mata….*3

    Kace mani zamuyi soyayya tun haduwar farko
    Amsa maka nayi ba jayayya…….autar mata
    Qawaye na sunyi mamaki yadda na dan sakko
    Ta yadda na amsa na shirya……autar mata
    Abinda yasa naji zan soka,kayi zubin natsuwa
    Na bincika kyawun halayya…….autar mata
    Bara na rufe maka labari sai da mukayi shaquwa
    Na gane ana gina soyayya har tayi daduwa

    Kuzo kuji ga autar mata
    Kar ku taba mini yar gata
    Ku barni kawai nayi mata rawa
    Babu irinta cikin mata

    Kuzo kuji ga auta na maza
    Kar ku taba mini dan gata
    Ku barni kawai nayi masa rawa
    Babu irinsa cikin su maza

    Autar mata…….autar mata…..autar mata…..