Inda so Yake (Salim Smart)
Ki tallafi raina, ce in zauna dake
Furta kina so, na muyi aure dake
Gaggawa soyayya tayi wa zuciya ta
Ta kama ni a sa’in da ban zata ba
Soyayyaaa…….
Gaggawa soyayya tayi wa zuciyaa…
Ta kama ni a sa’in da ban zata ba
Inda zuciya take
Soyayya ma Nan take
Don haka Kema Nan kike
Kinji gimbiyaa..
Na dimautu a bani Ke
Ni don Ke zan naniqe
Kama hannu na riqe
Zo mu zagayaa….
Kyakyawa kike
Sannan son kowa kike
Mai hankali kike
Mai kyan tarbiyyaa…
Na haddace, kalaman so a saboda Ke
Na firgice, dalilin son da nake ga Ke
Zan tsaftace harshe don magana dake
In fadi kalmomi masu Sosa zuciyaa
Soyayyaaa……
Babu gadar zare, dagaske nake qaunar ki ni
Kafin so ya zubar dani bani magani
Ni na ankare, har wasu na kishi dani
Don na furta inai dake sun dau gaba dani
Na ci qafar Kare, nayi nisan tafiya gari
Zan ga masoyiya daf dani, so ya Ja ni ni
Kyakyawa mai adon gari, mai kyawu in tayi adon yari
Ke kin yi daban ko a cikin aayari
Sunan ki nike wa kirarin gimbiyaa
Yeeeh…..
Tsakar dare mai ban tsoroo
Masoyi ba a mai qeta
Don Allah Kar Kiyi min horoo
Na durqusa Kan gwiwata
Ina da burin ai taroo
Auran mu ayyo daurawa.