Kamanni mun yo (Umar m Shareef)
Kamanni.. Mun yo Har a halayyaa
Shiyasaa….. Muka dace da tarayya
Kamanni…… Munyo Har a halayyaa
Shiyasa….. Muka dace da tarayya
Kin dana tarkon soyayya, gashinan ya kama ni
A yanzu ban Miki jayayya, tunda ba mai fidda ni
Zaman ciki nasa na shirya, masoyiyata ki kyale ni
Wa yafi sonki da soyayya, a tambaye ki ki Nuna ni
Soyayyaa…… Ta toshe kunnuwa na
Ta sanya.. Ban so inji laifinki
Inda abinda ya zarce qauna, zan ba ka
Inda abinda ya zarce raina, na ba ka
Bani da buri kullum Sai in ganni a damanka
Ko a ina Naji anyi maganarka Sai na tanka
Soyayyaa…. Ta kulle idanu na
Ta sanya.. Ba na ganin laifinka
Hahaha hahaha………..
Zuciya ta hana mini Kar da in so wata Sai Dai Ke
Ga kwakwalwa Bata tuna komai a cikin ta Sai Dai Ke
So dubu tambaya ayi min wa nafi so amsar Dai Ke
Rayuwata in za na sadaukar ga wata Ke ce Ke
Soyayyaa…. Ta zarce lissafi
Kwakwalwa… Ba ta kwatanta qaunar ki
Bani da kowa, bani da komai cikin soyayya Sai Kai
Bani Jin kowa, ban ganin komai ko a duhu Sai Kai haske
Kai ne farin ciki, da Kai zanje Har gidan biki
Aboki na arziki, wata ran zan zama mallaki
Du’aii…… Kullum nake kanka
Ka zamto ango na ni ko matarka.