Sallama nake gunki
Gimbiya a soyayya
Gamo da katar ga ki
Na gama da soyayya
Ja ni Ja ni kin Ja ni
Kin ka bani soyayya
Bari mu wuce, lambu
Ni Dake mu hau, doki
Tunda na ciyo kambu
Zo Taya ni muyi shauqi
Gaskiyar zance nayi Miki so Ke ma ki gwadan naki
Ki kula dani….
Zan kula da Kai a gidan aure daina magiya
Ki kula dani….
Zan kula da Kai yayinda kake rashin lafiya
Ki kula dani…
Zan kula da Kai Har yan uwanka gaske zan tsaya
Ki kula dani….
In babu tallafawa a cikin so to baida amfaaniii
Gani Nan tafeeee….
Me kike bida da da….
Fadi fadi yanzun zan Iya kiga ko huda da da….
A boye ki a ajiye basawa zan Budaaa….
Ke ce maganin jarumta ta ki Kira ni da actor
A taba ki in gwada nagarta ta bani tsoron qato
A soyayya ba abinda bazanyi ba indai na ganki
Ki kula dani…
Zan kula da Kai a gidan aure daina magiya
Ki kula dani…
Zan kula da Kai yayinda kake rashin lafiya
Ki kula dani….
Zan kula da Kai Har yan uwanka gaske zan Iya
Ki kula dani….
In babu tallafawa a cikin so to baida amfaanii
Ina suke na tabo yan maza Kai daya ne ban Kira da Rago
Musamman in Ana ingiza a cikin yan wasan ta bugo
Ko ko langa in ka bi ruwa da gudu Sai ka fizge Rago
Wannan shi ne Yake mini nuni Baza ka barni da yunwa ba
Ko ina Kaine kake mini gata Baza ka Bari in ta be ba
Na zabe ka abokin rayuwa Kai kadai ne ka kula daniiiii……