Mahaifiya (Abdul d one)
Ya mamma ya mamma…
Mahaifiyaa……
Soyayyarki mamma….. Ta cika zuciyaa
Tunani na randa Zaki wuce ki barni mahaifiya
Ko ni in wucee… In barki a zaune cikin duniya
Ya Allah Ya Allah, Dubi mahaifiya
Kasa ta cikin aljanna don khairul anbiya
Wasu sun wuce tun kafin zuwan mu duniya
Wasu sunyi haquri na rashin mahaifiya
To ga namu Raye, mai za ya sa baza mu kyautata ba
Hohohohoho… Haba abokai na
Iyaye suna da matuqar Amfani
Ga dukka ma Wanda Ke a raye duniya
Iyaayeeeeeh….
Tun kafin haihuwa suke yawaita dawainiya
Wayyo mamma, mamma, Wayyo mammaah…….
Zauna lafiya mama na mai sani dariya
Zauna lafiya uwa ta mai ban qashin Miya
Zauna lafiya rabin jiki na mama uwa daya
Allah sarki uwa mai dauke damuwa in ba Ke ba lafiya
A rashin uwa wasu Ke rasa shashin jiki gaba daya
A rashin ki ne wasu Ke koma yin Bara su zaga duniya
A rashin ki ne yaro a gida Yake zama maraya
Na ga illar rashin mahaifiya kusa dani Wayyo ni ya
A sanadin hakan nake Kiran uwaye na cikin duniya
Ku daure, komai iyayen mu maza zasu muku ku jure
Fitar ku kubar gida na haifar da babbar hatsaniya
Wayyo Iyaye, ku ne tushen gida da Zaman lafiya
Zaman ku tare da yayanku na qara danqon soyayya
Sannan zasu Samu tarbiyya
Ko ina zasu zauna lafiya
Sabanin hakan, zasu kauce hanya madaidaiciya
Bana wasa da mama na
Kaima Kar Kayi wasa da mamanka
Domin itace farin cikin ka duniya gaba daya
Uwa mai kula da dandanta a ko wani Hali Baza ta barshi ba
Babbar sarauniya da tafi ko wace a duniya
Akan ku ne nake batu Iyaye Mata gaba daya
Ku sanya haquri cikin gida je ku zauna lafiya
Mama mama Wayyo mama
Mama mama Wayyo mamaa…. Hahaha….
Mama mama Wayyo mama