Hmm…..
A cikin kowa da akwaishi
Sannan ba ya tsufa
Ba ya Jin rarrashi
Ba ya neman kofa
In zai Shiga ba ka tare shi
Don bashi da wata suffa
Idanu ba su ganin shi
Balle Kayi mai ihsani
So kenan…. Sanadin Labarina
So Kenan…. Sanadin Labarina
Ahh…..
Ba yin kaina ne ba
Kaima ba yin kanka ba
Tsarin Allah ne
Ba mai Iya kauda shi
Ba Wai matsayi ne ba
Sannan ba girma ne ba
Halitta ne, ba mai Iya chanja shi
Bai barni ba
Kaima Bai barka ba
A zuciya, shi ne ke sa rauni
So Kenan…. Hmmmm
So Kenan…… Sanadin Labarina
So Kenan…. Hmmmmm
So Kenan……. Sanadin Labarina
Kuka Bai qare ba…….. Labarina
In ban same ki ba…… Labarina
Ido na ba zai rintsa ba…. Labarina
In Har ban ganki ba….. Labarina
Tallafa mini ki tausaya mini
Daure agaji Kiyi mini
So riqe mini ki adana mini
Kar ki bar ajjali ya cim mini
So Kenan….. Sanadin Labarina
So Kenan….. Sanadin Labarina
Ah…..
Duk rudin zuciya ko kukan idaniya
Mafi akasari duk nasabarsu akan so ne
Mai kyawun kwalliya ko a Kira ki sarauniya
Zauna Kiyi nazari wannan maqasudin so ne
Al’ajabinshi Yana da yawa, gane gaskiyar shi akwai wuya
Sai in ka yo dace kake ajiyar shi da Jan Jane
So Kenan……. Sanadin Labarina
So Kenan……. Sanadin Labarina.