Daga Shafin Dandali.com.ng Masu jagorantar zanga zangar lumana wadda suke yi domin kawo karshen yunwa da tsadar rayuwa sun bude asusu a qarqashin shafin neman taimako na duniya da ake kira GoFundMe domin samun tallafin kudin da zasu ci gaba da gudanar da zanga zangar su mai taken #EndbadGovernance# da ake yi a Najeria.
Shafin Dandali.com.ng ya binciko cewar masu bude asusun sun bude asusu har guda uku ne domin karbar gudummuwa ta kudin kasashen waje kamar su dalar Amurka da Euro na qasar Ingila da sauran kudade na mabanbantan qasashe
Read Also: Muhimman Abubuwa cikin bayanin Tinubu a kasa da shekara 1
Burin su shi ne su tara aqalla Naira Biliyan Arba’in da daya saboda su iya tunkarar Gwamnatin Najeria cikin kwanaki goman da suka sa na zanga zangar #EndbadGovernanceInNigeriaProtest#
Bincike ya tabbatar da gudanarwar asusun ba a qasar Najeri ake yin ta ba ana yi ne a qasashen Amurka da Canada