fbpx
Wednesday, January 8, 2025
22.1 C
Abuja

Muwaddat by Aysha Bagudo – Complete

💗💗💗💗💗💗

MUWADDAT

💖💖💖💖

💗💗💗💗💗💗

~NA~

*AYSHA  A BAGUDO*

bismillahirrahmanirrahim

….Ayshatul muwaddat kwance take akan lafiyayyen gadonta kiran italy, amman ba bacci take yi ba, kurun dai ta kwanta ne tana tunanin Muhammad auwal ne bisa tsarin zuciyarta.

 cigaba tayi da tunane tunanen zucin data Saba, Wanda ya rigada ya zame mata  jikinta  ,a duk sanda ta ke’be kanta to fa Bata da wani aiki sai na tunaninsa, yayinda zuciyarta zata yita kissama mata yadda sufofinsa jikinsa  suke  had’e da yanayin tsarin rayuwarsa ,komai nashi Yana matukar  burgeta most especial sautin muryarsa  Mai shiga jiki da tsayawa arai  ,da tsarin halittarsa ,  naunayen ajiyar zuciya ta sauke da karfin gaske  had’i  da  lalibo wayarta dake ajiye a saman bedside tashiga neman layinsa .

Kira daya biyu ya d’auka cikin sanyayyiyar muryarsa “hello Aysha nah .. ….

  Tana jin sautin     sanyayyiyar muryarsa mai shiga jiki ta lumshe idanunta,  tana fesar da numfashi saboda wani Abu da taji ya tsarga mata tun daga cikin kwakwaluwar kanta har zuwa kasanta ya dinga yawo a koina a sansar jikinta.

Shiru sukayi gabadaya  batare da kowanensu yayi yunkurin furta wani Abu ga d’an’uwansa ba ,illa numfashi da ajiyar zuciyar da suka dinga saukewa a tare Yana ratsa kowani Shashi na gangar jikinsu .

Jin tayi shiru taki magana yasa yayi karfin halin fixgo magana yace “Aysha  nah kin kirani sannan Kuma kin yi shiru , gashi zuciyata na sanar min da cewar akwai abinda  bakinki yake son fad’i shiyasa Kika kirani ,me ke damunki ?”ki sanar min da damuwarki kinji  ….

Tayi shiru tsabar miskilanci dake cinta ,duk da dai maganar take son yi Amman harshenta yaki sarrafuwa Gurin lankwasa shi ,har sai daya sake yin magana “ki sanar min da damuwarki Aysha nah  , domin sanin haka shi zai sa na samu  natsuwar zuciya, akasin haka  Kuma kin san tashi hankali ne gareni  , Dan haka kiyi hakuri ki sanar min kinji ta hannun damana.

Jin yadda ya wani marairaice mata yasa ta   bud’e bakinta da kyar  tace  “babu komai fa kawai dai na Kira ne mu gaisa  ” kinyi kewata ko ?

“kewarka Kamar ya kenan ?

“Kamar dai yadda Kika Saba ya bata amsa yana buso mata numfashinsa “ta numfasa kana tace “a’a ni ban yi  wani  kewarka ba .

Yayi laulausar  murmushinsa dake k’arawa halitar fuskarsa kyau yace “ban yarda ba akwai dai abinda zuciyarki take ‘boyewa .

tayi shiru taki  yin magana, ya lumshe tsumammun  idanunsa yana tunaninta ,ya santa yasan halinta ba tun yau ba, saboda kusanci dake tsakaninsu, iya shakuwa sun shaku daita fiyye da tunanin Mai karatu ,Amman duk da wannan shakuwar tasu, hakan ba yasa ta sake dashi a waya, har gara ma idan suna chatting ne ta kan saki jikinta dashi  sosai tayita Masa Hira , wani lokacin har mamakin hakan yake, bud’e idanunsa yayi ahankali ya cigaba da magana na tsawon  second biyu  sannan  yace “tunda kin yi magana mu had’u a what’s app  ….ya katse kiran .

 batare da ‘bata lokaci ba,kai tsaye  ta kunna datanta sannan ta shiga contact dinsa inda

cikin  sanyayiyar muryarta tasoma  masa voice …

 “auwal  kanina ya kake? “ya karatu hope komai na tafiya daidai ?

ba kamar yadda ni na tsinci kaina ba, gabad’aya bana jin dadin rayuwata   saboda rashinka kusa dani,  ta tura masa sakon  ta koma ta jingina da abun gadon tana Mai  runtse idanunwata kad’an, zuciyarta na wani irin harbawa da sauri sauri .

can kmr minti biyu sai ga sakonshi yashigo ,da sauri ta zabura  ta gyara  zuwa kwanciya, sannan ta kunna vioce din daya turo mata , tare da manne earpiece a kunneta saboda tsaro ,ahankali ta soma sauraron sakon daya turo mata.

jin zazzakar muryarsa yasa take ta sake shiga cikin wani yanayi na daban .

“Muwaddat kenan daman nasan akwai abinda ke cin ranki ,nima wallahi bakiji yadda nake jin kaina adalilin nisan danayi dake ba, ji nake tmkr bani tare da wani kuzari a bangaren rayuwata   , dan Allah ki fad’a min yadda kike ji akaina ina son sani ..?

tayi shiru taki cewa komai illa zuciyarta da gangar jikinta da suka sake shiga cikin  shaukinsa …..

“kinyi shiru hope kina cikin koshin lfy dan banason jin yanayinki irin haka plz talk to me my muwaddat?

amadadin tayi masa voice kmr yadda suka saba sai tayi masa typing “uhmmmmm, share kawai  kanina  nagode sosai da kulawarka sannan babu abinda ke damuna   .. ..

“nidai a’a ban yarda ba , sai kin fad’a min ko nayi miki kuka ya turo mata sako tare da alamar yar bbyn nan mai zanen kuka.. 😭😭

Hot this week

Kazar Kwanci By Rufaida Omar

Kazar Kwanci By Rufaida Omar *1)*  " Mairamu! Mairamu!!" Matar dake zaune...

KAZAMAR AMARYA Na Rahama Kabir Mrs Msg

KAZAMAR AMARYA Na Rahama Kabir Mrs Msg Rahma Kabir:...

RUGUNTUSUMI Book 2 Compelet

RUGUNTSUMI Book 2 part 1 Rubuta labari Abdul’aziz Sani Madakin Gini Ɗaukar Nauyi Mansur...

GUDUN KADDARA NA HUGUMA BOOK 2

GUDUN KADDARA NA HUGUMA BOOK 2            ".............ya fada soyayya?,yana...

Gudun Kaddara na Huguma Book 1

Gudun Kaddara na Huguma Book 1 🏃🏽‍♀️ GUDUN ƘADDARA🏃🏽‍♀️ H U...

Topics

“Candace Owens expresses, ‘I wish I were Nigerian.'”

Famous American media personality Candace Owens has openly shared...

“I regret supporting the exhumation of Mohbad,” says Iyabo Ojo.

Iyabo Ojo, a prominent figure in the Nigerian entertainment...

Actress Chioma Akpotha responds to the announcement of the arrival of her baby boy.

Actress Chioma Akpotha has shared her heartfelt reaction to...

Foreign Direct Investment

Foreign Direct Investment (FDI) continues to be a crucial...

Intensified Crackdown on Oil Theft

Nigeria has ramped up its efforts to tackle oil...

Telecom Companies Warn of Service Cuts Due to Rising Costs

Telecom companies in Nigeria are raising alarms about potential...

Jeniks and Qatar’s $20 Billion Deal to Boost Africa’s Gas Wealth

Africa, home to over 620 trillion cubic feet of...
spot_img

Related Articles

Popular Categories

spot_imgspot_img