Na shiga so…. X2
Na shiga so, zurfi kamar rijiya.
Ni Na fadi, sanki nake Zahiri
So nake ki rike mani alkawari
Kina jina, kece zan yiwa albishiri
Kudin aure, nake tarawa daga fam dari
Dake nake kalle ni kamar wani almajiri
Bida nake a kanki nake kokari
Akan sanki, zan jure a ce mani ko makiri
Madubi na idan ba ke to zan bar gari
Kin zama ni na zama ke mu bayyana so zahiri
Mu kau da maza a zuciya sai ni kadai
So so soyayya mai sona. So soyayya ina sonki
So so so soyayya soyayya . So soyayya.
Sanki ya mini tsiro a jikina ni
Yayi niyyar ya tsaya ya kurumtani
In Akan soyayyarki bana Ji gani
Nabi hanya dodar shin ina zani
Ke ce wacce nasan Zaki ma fahimtar ni
Me kike so ki fadan za na kama ni
Dubi Yadda nake sonki za ya zauta ni
Tausayinki nake so kawai ki kama ni
Tunda dai sonki a zuci ya yimin rauni
Ko da a soyayya Taki za a kulle ni
Baza na barki ba mun zamma yan uwa na Jini
Ke daya nake kallo zuciya tamin sanyi
Kinga so soyayya na shigo
So da so soyayya
Girman ki a zuciya ya wuce in yi misali
Mai kyau na Ido Sai ma in kin sa kwalli
Na kulle kofar har na Yada makulli
A gida na wataran za ki Shiga lalle
In so ya Kai so ni da ke ba zan yi fushi Sam ba
Mata dayawa ke bi na ko daya ba zan dakko ba
Daga ke na kulle kofa ta ba zancen qarya ba
A madubi in na Duba ke ce ko ban Wai go ba
Kallon ki nike yi zahirin ba Wai a mafarki ba
Zaben da na yo zabene Bai canza gani na ba
So so so soyayya, mai sona
So soyayya ina sonki
So so soyayya, soyayya
So soyayya…..