Na yarda da kai farin ciki na
Na yarda da ke masoyiya ta
Na yarda da kai ne farin ciki naa…..
Kin bani abinda na baki
Kinso ni a sanda na soki
Kika bani kujerar mulki
Kika yi mini kyautar doki
Samunki na yi dubara
Barinki zanyi asara
Na roqi rabbi tabara da ya ban ke zani jira
Ni kika martabaaa…
Baki bugeni baaaa…
Bazan auri waninki baa…
Ai tunda banga kamarki baaa…. A soyayyaa
Baka buqatar in ma tuni
Mai sonka ni ce ka sani
Na gaishe ka Ina wuni
Soyayyar ka na a cikin jini
Da kai na sa ba tun farko
Da kai na yarda a mini baiko
Farin ciki na kai ne
In nayi kuka kai ne
Ko ban so ka baa….
Ba zan qi kabaaa…
Ja ni muje gabaa…
Don banga kamar ka baa… Hahahaaaaaa…..
Kin riqe amana ta kin boye ta kinqi nuna ta
Zancen rabuwa ku daina ta
Ko mun saba za mu sasanta
Tsakaninmu mu daidaita
Jini da jijiya
Komai dadi wuya
Mun dauki alqawari
Zamuyi zaman hakuri
Kin ce ba yani
Na ce ba yake
Kin kula dani
Zan kula dakeee….
Masoyi na gangariya
Tauraron duniya
Soyayya ka iya
Agurinka a kwaikwaya
Kai ke koren haushi in ka ga ina acikin halin damuwa
Kayi mini rarrashi kasa naji babu yani cikin duniya
Rabin jiki na kaine
Idon gani na kaine
Sanyin zuciyaaaa….
Ka sani na zaman sarauniyaaa…… A soyayya
Naa yarda da kai ne farin ciki naa….
Naa yarda dake masoyiya taa….
Na yarda da kai ne farin ciki naaaa