Jaruma Rahama Sadau ta sha alwashin za ta cire wa mutum 100 kebura domin saukaka wa jama’a a daidai wannan lokaci da ake fama da tsadar rayuwa da yunwa da matsin tattalin arziki,
Tuni dai jarumar ta buƙaci jama’a su ajiye akawunt lambarsu wato asusun banki za ta zaɓi mutum 100 da za ta gwangwaje su da kyautar kuɗaɗe a matsayin nata gudunmawar a daidai wannan lokaci na halin ƙaƙa nikayi,
Read Also: Masu Zanga-Zanga Sunyi Watsi da Maganar Lauyansu Sun Ce Za Su Cigaba da Fitowa Zanga-Zanga
Jaridar A Yau ta ruwaito a cikin sa’o’i huɗu an samu sama da mutum 24 da suka yi comment da account dinsu kuma jarumar ta duƙufa cika alƙawarin da ta dauka din inda ta riƙa tura masu kuɗi adadi daban-daban,
“To jama’a hannu na ya gaji, burina in turawa mutum 100 amma zan huta kafin zuwa can anjima in cigaba da turawa, amma wanda ya ga alert (sakon kyautar kudin) da na tura masa yayi magana, nima idan na natsa zan yi posting din receipt (takardar shaidar) tura kudi na banki” inji Jaruma Rahama Sadau