Saturday, September 13, 2025
23.1 C
Abuja

Rarara ya tallafawa sama da mutum dubu goma a kahutu

Rarara ya tallafawa sama da mutum dubu goma a kahutu

SHAHARARREN mawaƙi Alhaji Dauda Adamu Abdullahi (Rarara) ya yi rabon kayan abinci da kuɗi ga mutanen ƙauyen su na Kahutu da ke Ƙaramar Hukumar Ɗanja a Jihar Katsina.

Mawaƙin ya yi rabon kuɗi kimanin miliyan hamsin (N50,000,000) da kayan abinci ga sama da mutum 10,000 a wani gagarumin gangamin jama’a da aka yi a garin a shekaranjiya Asabar, 17 ga Agusta, 2024.

Rarara ya ba kowane mutum ɗaya kayan abinci da kuɗin cefane N5,000.

A wannan karon, mahaifiyar mawaƙin, Hajiya Halima Adamu, ta halarci filin da aka yi taron tare da jikokin ta, inda ta yi amfani da wannan damar ta yi wa jama’a godiya game da irin addu’o’i da gudunmawar da suka ba ta a lokacin da ‘yan bindiga su ka yi garkuwa ita kwanan baya.

Lokacin da ya ke jawabi a wurin rabon, Rarara ya yi kira ga dukkan waɗanda su ka halarci taron da cewa, “Duk wanda ya zo wurin nan zai samu, har da waɗanda ba a gayyata ba. Don haka kowa ya ba da haɗin kai don a yi abin a kan lokaci.”

Haka kuma ya ce al’umma su ƙara haƙuri, nan da wata shida talauci zai zama tarihi a ƙasar in-sha Allahu.

Sannan ya ƙara da cewa, “Duk wanda ka gani a wurin rabon nan, shi ma ba haka ya so ba, domin shi ma ya na so a ce ya bayar ga mabuƙata.”

Mujallar Fim ta ruwaito cewa a cikin wannan shekarar, Rarara ya yi irin wannan rabon aƙalla sau biyar daga watan azumi zuwa yanzu.

Da yawa mutane su na ganin irin wannan taimakon da mawaƙin ya ke yi wa al’umma ya na ɗaya daga cikin abin da ya sa har yanzu ya ke jan zaren sa a harkokin sa ta kowane ɓangare.

Rarara dai ya yi suna wurin taimakon al’umma, ba mutanen ƙauyen su kawai ba, har ma a cikin masana’antar Kannywood da kuma sauran jama’a na wasu jihohin.

Duk da cewa ana cikin wani hali na matsin rayuwa a ƙasar nan, amma mawaƙin bai gaza ba wurin taimako.

A cikin ‘yan siyasar da ya ke hulɗa da su da kuma manyan masu arzikin ƙasar nan, ana iya cewa babu wanda ke kwatanta abin da mawaƙin ke yi.

Hot this week

SEC States That Meme Coins Are Not Securities

On Thursday, the Securities and Exchange Commission (SEC) made...

“NDLEA Destroys 25 Tons of Illicit Drugs in Kogi: A Major Blow to Drug Trafficking”

A Landmark OperationIn a significant move to combat drug...

Tinubu Dismisses NYU VP, Empowers UNIABUJA VC: Leadership Changes in Nigerian Universities

President Bola Ahmed Tinubu has made some bold leadership...

NAHCON Chairman Welcomes NCPC Executive Secretary at Hajj House

In a move aimed at strengthening interfaith cooperation, the...

El-Rufai Joins the Battle: Accuses Ribadu of “Amnesia” in Naja’atu Muhammad Feud

The ongoing war of words between National Security Adviser...

Topics

Eniola Badmus Reaffirms Her Support for President Tinubu, Sparking Reactions

Eniola Badmus, a well-known actress and Special Assistant for...

Rapper Jeriq Explains Why He Has Never Been in a Relationship

Nigerian rapper Jeremiah Chukwuebuka Ani, widely known as Jeriq,...

Album Releases: Ruger and Joeboy Face Off in a Supremacy Battle

The Nigerian music scene is buzzing with excitement and...

“Famous singer NBA YoungBoy has been released from prison.”

Popular American singer Kentrell DeSean Gaulden, better known as...

“My kind of wealth cannot be achieved through investment,” Davido proudly declared.

Nigerian Afrobeats singer David Adeleke, widely known as Davido,...

“I backed Tinubu, but the hardship is becoming unbearable,” said Cynthia Morgan.

Nigerian singer Cynthia Morgan, now known as Madrina, has...
spot_img

Related Articles

Popular Categories

spot_imgspot_img