fbpx
Wednesday, January 8, 2025
22.1 C
Abuja

RUGUNTUSUMI Book 2 Compelet

RUGUNTSUMI

Book 2 part 1

Rubuta labari

Abdul’aziz Sani Madakin Gini

Ɗaukar Nauyi

Mansur Usman Sufi

CEO FOR SUFINOVELS.COM

          Abu na farko da ya fara zuwa zuciyar Jarwal itace wai shin me wannan tsohon Bokan ya ke nema a duniya, alhalin yana da wannan tarin dukiya wacce yai imanin duk duniya ba za’a sami mai rabin ta ba? Wai shin me zai hana ya kwace dukiyar ta zama tasa?T a yaya zaka kwace dukiyar ba tare da ka kashe shi ba? Tabbas ka san takamarka ba ta wuce ta ƙarfi ba, in kuwa haka ne Boka Zarbalu ba zai kasu a hannunka ba, to idan ma ka sami damar kashe shi ɗin, wannan mafarkin da ka yi fa? Wane ne zai iya fassara maka shi? Idan ma an fassara maka ɗin wane ne zai iya tsare ka daga sharrin dake cikin mafarkin? Boka Zarbalu ne kaɗai zai iya warware maka wadannan matsaloli, don haka ya zama wajibi ka bi shi, ka lallaɓa shi har ka sami

damar aiwatar da bukatunka nan gaba.

Wannan shine irin abubuwan da Sarki Jarwal yayi ta sakawa cikin zuciyarsa.

             Bayan Sarki Jarwal da Boka Zarbalu sun isa cikin kogon tsafi har sun ƙule, sai ƙofar ta rufe kai kace tunda aka halicci dutsen a haka yake bai taɓa motsi ba. Shi kuma ruwan nan na fadama wanda ƙasa ta tsotse sai ya sake ɓulɓulowa daga cikin ƙarƙashin ƙasa yaci gaba da gudu kai kace idon teku ne. 

          A wannan lokaci ne bayin nan da suka rako su Jarwal su biyu suka dubi juna, ɗayansu ya dubi ɗan’uwansa ya ce 

“Ya kai Zarkal ka sani cewa yau mun samu shekaru kusan ashirin kenan muna bauta a gidan sarauta har yau bamu mallaki ko da doki guda ba. Gashi yau da idanunmu munga dukiyar da ba mu taɓa gani ba, a cikin kogon can. Me zai hana baza muyiwa kanmu gata ba? Mu je mu kwashi iya abin da zamu iya ɗiba mu kama gabanmu, in yaso sai mu gudu mu bar ƙasar nan, ka san dai duk inda mu kaje a duniya dole a girmama mu, don mu zama attajiran da babu kamarsu. Kaga shike nan sai mu auri zukazukan mata. ko da ‘ya’yan sarakuna ne kuwa, mu zauna mu ci duniyarmu da tsinke. Yayin da Janjamu ya zo nan abayanninsa sai Zarkal yai ajiyar zuciya yace

“Lallai Janjamu sai yau na tabbatar da cewa kai wawa ne, ko da ya ke ban sani ba ko duniya ta ishe ka haka shi yasa kake neman ka kai kanka ga mahallaka, shin ɗazu da me ka rufe kunnuwanka har ka kasa jin kashedin da Boka Zarbalu yai mana? Cewa fa yayi

Kar mu kuskura mu bi su izuwa cikin kogon.

          To idan mun ƙi bin umarnin ta yaya za mu shiga ciki kogon, alhalin gashi kana gani ƙofar ta rufe, fadamar kuma ta sake tare hanyar?”

Wannan mai sauƙi ne in dai ka amince da shawarata, ni na tabbatar da mun faɗi abin da BokaZarbalu ya faɗa ɗazu ƙofar zata sake buɗewa da kanta kuma wannan fadamar zata ɓace

Zarkal yai shi shiru ya kurawa Janjamu idanu,wani abu na ta kai komo a cikin zuciyarsa. Abu biyu neke zarya a zuciya tasa, amincewa da kishiyarta, ma’anayana so yana tsoro.

“Kai Janjamu dakata tukunna, na san ba mutaba samun dama ba a rayuwarmu irin wannan, kuma natabbatar idan ta suбuce mana, ta tafi kenan har abada.To amma fa ka sani a biyu ne, ko mu yi nasara ko murasa rayuwarmu”

“Ni dadina da kai kenan, to tsaya kaji masu iyamagana sunce matsoraci ba shi zama gwani, kawai kazo mu jarraba sa’armu. Ni fa dama tun shekaran jiya nafara mafarkai na alherai, ina ganin samun wannandukiyar ne akai tayi min nuni.’

Zarkal yai ajiyar numfashi sannan ya fago kaiya dubi Janjamu yace “Yi hakuri na fan yi guntuntunan

Wannan shi ne abin da ya faru tsakaninSarki Jarwal, Zarkal da Janjamu wadanda su kairakiya a izuwa kogon tsafin Bóka zarbalu

*** ***

    Al’amarin Sarki Jarwal da Boka Zarbalu kuwalokacin da suka wuce inda tarin dukiyar nan take tuniahankalin Jarwal ya soma jirkita, saboda tunanin dukiyarda suka wuce a baya, har sai da Boka Zarbalu ya dafakafaɗarsa sannan ya dawo cikin haiyacinsa.

“Na san zuciyarka cike take da tunani, abin da nake so da kai shi ne ka yi hakuri har na gama bincikenaakan abin da ya kawo mu, nayi alkawarin zan sanar dakai komai na dangane da ni da kuma wannan kogo.”

        Boka Zarbalu ne yai wannan jawabi, ba tare da yakara fadin komai ba sai ya kama hannun sarki Jarwal.suka tashi sama sai ga su suna tafiya a cikin iska kamartakardu. Sannu-sannu suka iso wata kayatacciyar fadawadda akai mata kawa matuka, sai dai wani abinmamaki babu komai a cikinta sai wani katon gunkinbil’adama guda faya, wanda a gabansa an ajiye watashimfida mai laushi ta musamman.Kafin mutum yakai ga inda wannan shimfida takeya hau watamatattakalar bene mai hawa ashirin da shida, wadda akaginata da tubalin yakutu.

       Zarbalu yai sujjada ga wannan katon gunkia sake kama hannun Jarwal suka hau kaalar nan su kai ta hawa sama har suka isa indafidar nan take, maimakon su zauna akan shimfifaruka zauna a kas a bangaren hagun shimfifaransu ke da wuya wani farin hayaki ya baiyana aisakiyar kan shimfidar wadda a ka yi da jan kilishicikin abin da bai wuce dakika biyar ba, farin hayakin valrikida ya zama wani tsohon mutum mai dogon faringemu. Saboda tsananin tsufa fatar jikinsa ta yankwanegaba daya, akalla dai shekarun tsohon za su kai fari da doriya.Boka ya bude baki zaice wani abu sai tsohon yadaga masa hannu, alamar yai shiru.”Nasan abin dake tafe da ku, kun zo ne don kuji fassarar mafarkinSarki Jarwal yayi, ko ba haka bane?”

             Boka Zarbalu yace “Haka ne ya shugabana”

Tsohon ya bushe da dariya, sannan yace “Ya kaiSarki Jarwal ka saurara da kyau ka ji abin da zan gayamaka, ka kiyaye da sharadan da zan fafa maka idan harkana so ka tsira da rayuwarka, ka jima akan karagarmulki. Ina mai sanar da kai cewa ka kashe maciji ammabaka sare masa kai ba, a iya tunaninka kana ganin kagama da dukkan iyalan sarki Salmanu, to da saura. Alhalin yanzu akwai wata matarsa mai suna Humairahawadda ta dade da tafiya ganin gida can wani gari mai nisan gaske daga nan kasar, cikin wani kauyc mai suMadawal. Humairah na fauke da ciki wata bakwzhakika nan da wata biyu zata haifi da namiji, wanna:da shi ne itaciyar da ka gani a cikin mafarkinka.Tabbas idan ba ka nemo Humairah ka farke cikinta kaciro jaririn ba, sai ya zama a jalinka, kamar yadda kaimafarkin an faure ka a tsakiyar fada, jama’a sun je fekato haka zai yi maka”

          Ko da tsohon ya zo nan a zancensa sai idanunSarki Jarwal suka zazzaro, jikinsa ya hau kyarma yadurkusa bisa guiwoyinsa yace

“Ya shugabana yanzu ya za’a yi na je wannanagari na Madawal har na kama Humairah na farkacikinta na fiddo jaririn?”

Tsoho ya sake bushewa da dariya yace “Kafinka samu wannan nasara sai kayi abu guda uku, abu nafarko shi ne, daga nan zuwa garin Madawal tafiyar watashida ce, amma idan Zarbalu ya ha daka da aljaniZambanu zai iya kai ka a cikin wata biyu. Abu na biyushi ne jama’ar da ke cikin garin Madawal gaba dayansuma’abota addinin musulunci ne, garin yana bisa kanwani karamin tsibiri ne wanda ke tsakiyar wanimakeken kogi. Ka sani duk aljanin da ya doshi wannankogi koncwa ya ke yi, saboda tsabar sihirin mutanengarin, kuma in ba aljanin ba babu wani mahaluki da zaiiya shiga cikin gogin yai tafiya da kai bare har kuaketarc, sai dai ka samu musulmin aljani ya haye ruwan

             Abu na uku wanda shi ne na karshe kuma shiwanne wahala da hafari, dole ne kaje ka faukosarki Imhatul Las, domin ita ce kadfai ce wufaata iva farke cikin Humairah har ka fiddo jaririn doiki. Asalin wukar an samo ta ne daga irin kirarafunan da bil’adama ya fara sarrafawa a duniya. Kalsani sato wannan wuka daga hanun sarki Imhatul Idaidai ya ke da neman jaki mai kaho domin ba taganuwa da idanu haka kawai, sai da cikakken sihiriAmmasani duk wadannan abubuwa guda uku dolelne ka gama da su kafin nan kafin kwana sittin, watokafin ranar haihuwar Humairah. Idan ka sake kwanakinsuka cika daidai ba ka yi nasara ba, taka ta Rare. Akarshe na ke ba ka shawarar ka hada kai da wannanjikannawa wato Zarbalu domin shi kadai ne zai iyataimaka maka, sai dai ban sani ba ko zai amince yataimaka makan.”

             Tsohon na gama wannan jawabi,ya bace, awannan lokaci tuni sarki Jarwal ya gama jikcwa dagumi sharkaf, saboda tsananin firgita. Tun da yake arayuwarsa hankalinsa bai taбa tashi ba irin na wannanrana. Jikinsa na karkarwa ya dubi boka Zarbalu yace

           “Ya kai sarkin matsafan duniya ka taimake ni, nikuma nai maka sakaiya da duk irin bukatar da kake so.”.

Ko da Zarbalu ya ji wannan batu sai yayiamurmushi, maimakon yace wani abu, sai ya sake kama

hannun sarki Jarwal ya tashi suka sake kutsawa cıwanan kogo mai tsananin zurfi,

               Al’amarin Zarkal da Janjamu kuwa, bayan Zarkal

ya gama tunani sai ya dubi Janjamu yace”Hakika na amince da shawararka saboda hakaina ganin kawai mu je mu nemi sa’a.”

                Nan take suka karasa daf da fadamar nan daidaiwajcn da suka ga su boka Zarbalu sun tsaya su ma sukatsaya, Janjamu har sai da ya saita sawayensa bisa daidaikan na boka Zarbalu, sannan ya runtse idanuwansa, yagama tafin hannayensa biyu waje guda, ya daga sama

sannan yace”Bude mana kofa ya Zanzamanu! Samar dahanya garemu ya Zamzamanu! Yau muna da manyanbaki.”

                  A lokacin da Janjamu ke wannan furuci tuni subiyun sun jike sharkaf da gumin tsoro, ko’ina ajikinsukarkarwa ya ke kamar sun kamu da mugun zazza i.Bisa mamaki sai suka ji karar tsagewar dutsen kogon.Cikin sauri suka buɗe idanuwansu, sai suka ga kofa tabude, ruwan fadamar nan kuwa take ya tsotse cikinRasa, tamkar ba’a ta a samun danshi ba a wajen. Cikintsananin murna da zumudi Zarkal da Janjamu suka rugaizuwa cikin kogon. Da shiga suka fara kokarin

par akwati guda na lu’u lu’u, amma sai abu yaa saboda tsabar nauyi. Zarkal ya dubi Janiamu

“Na rantse da girman sarki wannan akwatun tafilarfin daukar karti ashirin, sai dai arba’in

“To yanzu yaya za mu yi?” Janjamu ya tambaya”Kaga kawai kowa ya jidi iya abin da ya ga zailiya diba, mu kama gabanmu tun da wuri.”Ai kuwa nan ake yenta, kowannansuya kwancel jakarsa suka yi ta dura dukiya a ciki, sai da suka cikajakunkunan nasu, suka ji da kyar suke iya dagawa sama,.sannan suka juya baya da nufin fita daga cikin kogon..Anan ne fa ido ya raina fata, sakamakon abin da sukagani kuru-kuru. Kofar da suka shigo ta cikinta ta shafe,babu ita babu alamarta. Nan take jikin Janjamu ya farakarkarwa cikin tsananin tsoro, ya ji kamar ba zai iyatsayuwa ba akan digadigansa. Shi kuwa Zarkal ji yayizuciyarsa na bugawa da karfi kamar wani abu na shirinfasata ya fito waje. Janjamu ya rufe idanunsa ya sakekiran sunan aljani Zamzamanu don ya sake buɗe masuRofafita. Maimakon hakan ta faru, sai suka ji ankyalkyale da mahaukaciyar dariya wadda tasa cikinsuya hautsine, take suka ji gudawa na shirin dakako masuasallama. Yayin da suka yi arba kuwa da mummunarkatuwar halittar sai Zarkal ya yanke jiki ya fadi kasasumamme, shi kuwa Janjamu sai ya kame, komai nasaya daina aiki tamkar gunki don tsananin firgita.

Mu hadu a RUGUNTUSUMIN RUGUNTUSUMI Cigaban Ruguntusumi

Daga 

Abdul’aziz Sani Madakin Gini 

Hot this week

Kazar Kwanci By Rufaida Omar

Kazar Kwanci By Rufaida Omar *1)*  " Mairamu! Mairamu!!" Matar dake zaune...

KAZAMAR AMARYA Na Rahama Kabir Mrs Msg

KAZAMAR AMARYA Na Rahama Kabir Mrs Msg Rahma Kabir:...

GUDUN KADDARA NA HUGUMA BOOK 2

GUDUN KADDARA NA HUGUMA BOOK 2            ".............ya fada soyayya?,yana...

Gudun Kaddara na Huguma Book 1

Gudun Kaddara na Huguma Book 1 🏃🏽‍♀️ GUDUN ƘADDARA🏃🏽‍♀️ H U...

Innocent Girl Na Nameerah and Nainarh

Innocent Girl Na Nameerah and Nainarh بسم الله الرحمن الرحيم Ep....

Topics

“Candace Owens expresses, ‘I wish I were Nigerian.'”

Famous American media personality Candace Owens has openly shared...

“I regret supporting the exhumation of Mohbad,” says Iyabo Ojo.

Iyabo Ojo, a prominent figure in the Nigerian entertainment...

Actress Chioma Akpotha responds to the announcement of the arrival of her baby boy.

Actress Chioma Akpotha has shared her heartfelt reaction to...

Foreign Direct Investment

Foreign Direct Investment (FDI) continues to be a crucial...

Intensified Crackdown on Oil Theft

Nigeria has ramped up its efforts to tackle oil...

Telecom Companies Warn of Service Cuts Due to Rising Costs

Telecom companies in Nigeria are raising alarms about potential...

Jeniks and Qatar’s $20 Billion Deal to Boost Africa’s Gas Wealth

Africa, home to over 620 trillion cubic feet of...
spot_img

Related Articles

Popular Categories

spot_imgspot_img