Ooooooohh……..
Yanzu na gane Sai Dake
Duniya za na more rayuwa
Eeeeeeeeeh…….
Naji so haduwar jini Sarai
Na amince akan Hakan kwarai
Ni da Ke rayuwa Idan da raii……..
Nayi burin zama Dake
Da’iman abadan a rayuwa
Yau garen kin zamo kamar jini
Ko ko ince idanuwan gani
Dukka Mata basa da kwarjinii…… Aaaaaah
Duk Garin Nan na bincike
Guna Ke daya kin Samu karbuwa
Wanda Bai sonki ni dashi
Babu sauran Shiri a rayuwa
Randa duk nayi Gamo dashi
Allahu yassan me za ya faruwa
Ko da sun Kai yawan tururuwa
Duk su taru su zo da yan uwa
A fagen son ki bani kaduwaaa……
Na sadaukar da rai a Ke
Ko da ni zani rasa rayuwa
Na Kira ki da sarauniya ta
Wacce Ke mulkin zuciya ta
A yanzu babu Wanda ya kaini gata
Tunda kece masoyiyata
Kin Iya kwalliya da tsafta…… Aaaah
Kina da sauqin fahimta…… Oooh
Duk hankalina gunki Nan ya karkata
Da an Kira sunan ki Bana firgita
Sai randa na aureki
Hankalina zai kwantawa
Zuciya ta tana ta damuwa
Kan tunanin Rana ta rabuwa
Babu makawa komai shaquwaa………. Bani Fata dani dakeee