Ga tamburan masoya
Ga baitukan masoya
Ku fito Rawa masoya
Baya da babu manya
Shi so ya Tara gayyaa, Kuma so ya watsa gayya
Soyayya ruwan Zuma ce, in ka sha ka ba masoyi
Soyayya farar Zuma ce, wacce a yau ake ta yayi
Soyayya farin ciki ce, mai yaye bakin ciki ce
In dai da so da kauna, ai komai Daren dadewa
Ita duniyar masoya, ai filin ta Bai matsewa
Komai duniya tabawa, soyayya Ana dadewa
Saqon zuciya da Lura, an aika Yana isarwa
Ku tambayi zuciyar masoya, Tai saqar da Bai katsewa
Ga tamburan masoya, mai jita Yana bugawa
Soyayya ruwan Zuma ce, in ka sha ka ba masoyiiii
Salam Salam Alaikum, magana ta da sallama ce
A cikin salo na waqa, Kuma in Sanya dan kwatance
Ni na San hali na kauna, soyayya ruwan Zuma ce
Wasu sun sani da baki, wasu a karance ko rubuce
Su dai Tambura na jita, ba kashe kunnuwa sukee ba
Ga tamburan masoya, mai jita Yana bugawa
Ga Saqo gurin masoya, kuyi haquri wajen riqon ta
Kada ku damu Don magauta, Don wasu masu shirya qeta
A kula riqon Amana, tabaraka jalla ya rubuta
Ina mafita gurin masoya, zaku Ji ga Aliyu jita
Soyayya tana da dadi, ba qarya nike fadi ba
Ga tamburan masoya, mai jita Yana bugawa
Ruwa, iska gami da sanyi, alqawari bazai gusa ba
Wani zai soka ne da rana, da daddare Bai qi ka mace ba
Wani zai soka Don Amana, ko Bai baka ko kwabo ba
Idan Allah ya ma masoya, bakai kuka a duniya ba
Bude idon ka Dubi nawa, bazan sakaci da addu’a ba
Ga tamburan masoya, mai jita Yana bugawa
Mai son ruwa a gora, shine za ya rabi tulu
Tilon cikin mazaje, wannan an Kira ta delu
Soyayya tana da tsari, ba ta rarrabe qabilu
Na Saka hausa nai misali, Idan magana kawai ta bullu
Ni Dan hausa mai azanci, ba gaza maggana nake ba
Ga tamburan masoya, mai jita Yana bugawa
Ya Allah ka kauda sharri, sharrin aljani mutane
Da Yan hassada da qeta, sun gaza zaune ko tsugunne
To tunda jalla yayi, ya ya zasu yi da rai ne
Kuyi haquri kawai ku barmu, komai kunga qaddara ne
Sunyi kadan su canza wannan, ba sa canza qaddara ba
Ga tamburan masoya, mai jita Yana bugawa
Soyayya ruwan Zuma ce, in ka sha ka ba masoyii