- An gurfanar da Kazeem Bamidele a gaban wani alkali inda ake tuhumarsu akan satar wayoyin hannu da sukayi a yankin Ajegule da shi da abokan satar shi da suka gudu.
- Har wayau kuma ana zargin wannan mutumi mai shekaru 50 a duniya da siyan wata waya kirar iPhone 12 pro max akan kudi N520,000 inda shi kuma ya musa wannan zargin.
- An kuma shigar da karar wani mutum mai suna Wasi’u Adele a wata kotun majistare dake yankin Ogba a Jihar Legas inda ake tuhumarsa akan ya saci kaya yana kuma yawo da jabun kudi tare dashi.
Karanta: Wani Alkali yayi Alkawarin zai Biyawa Saurayi Sadakin Naira 100,000
Jaridar punch ta ranar Laraba 24 ga watan Agusta 2022 ta rawaito cewa ana tuhumar Kazeem Bamidele da laifin satar wayoyin hannu.
Ana zargin wasu mutane da ba a samu nasarar kamawa ba tare da wani mutum Bamidele da aikata laifukan da suka Kai guda biyar, ciki akwai daukar kayan da ba mallakinsu ba.
A wata karamar kotu ta majistare, rahoto ya bayyana yadda lauyoyi suka bada sanarwar rashin samun sauran abokan aikin Bamidele.
Siyan Wayar Sata Kirar iPhone 12 Pro Max
Kazeem Bamidele da aka fi sani da suna Elewura da shi da wasu mutane da ba a gani ba sun sayi waya a hannun wani mutum mai suna Ojaburo Michael mai kirar iPhone 12 Pro max Akan kudi N520,000
Harkallar ta faru ne a yankin Ajeromi a cikin dare misalin karfe 10:30, tara ga watan Yuli 2022 cikin Jihar Legas
Sauran Laifukan da ake Tuhumar Kazeem Bamidele da su.
Zargin da ake mishi Akan daukar wayoyin hannu da suka Kai guda 76 na mutane dashi da sauran abokan aikin shi da ba a kama ba.
Har wayau kuma ana zargin shi da siyan wayar iPhone 12 pro max Akan N520,000
An bada belin wanda ake zargin akan N500,000 sakamakon musa zargin da yayi kuma an sauya lokacin da za a ci gaba da gudanar da shari’ar.
A wannan lokacin ne kuma shari’a ta barke da wani mutum Wasi’u Adele mai shekaru 42 wanda ke amfani da kudin bogi da ya sa ci kayan N4.8m anan kotun majistare da ke Garin Ogba.