fbpx
Wednesday, January 8, 2025
30.1 C
Abuja

Tsutsar Nama Book 3 Na billyn Abdul

Tsutsar Nama Book 3 Na billyn Abdul

__________

…….Suna shiga cikin headquter ɗin Lawyers nashi na isowa shima. Sai dai kafin su ƙarasa gareshi an shige dashi wani ɗakin bincike. Table ne kawai da kujeru biyu masu facing juna. Sai da ya gama ƙarema ɗakin kallo fuskarsa a yamutse kafin yaja kujerar ya zauna. Yana zama cikin jami’an wani shigo, da girmamawa yake tambayarsa ko yana buƙatar wani abu kamar su tea haka. Ɗan jimm yay yana kallon ma’aikacin, sai kuma ya murmusa kaɗan alamar a’a. Fita Jam’i yayi, shi kuma ya jingina bayansa da kujerar sosai ya lumshe idanunsa kawai. Kusan mintuna fin ashirin sannan aka sake buɗe ƙofar. Bai motsa ba bai kuma buɗe idanunsa ba har jami’in ya kai zaune. Kaɗan ya ɗan buga table ɗin, sai dai a hakan ma Maash ɗin ƙin motsawa yayi. Sai da ya mula dan kansa sannan ya buɗe idanunsa ya zubama jami’in batare daya tashi ba. Ji Jami’in yay bazai iya jure kallon ba, sai ya kauda idanunsa cike da basarwa yana furta, “Sir bamu da isashen lokaci. Idan ba damuwa ka amsa mana wasu ƴan tambayoyi mana”.

       “Jeka maganarka kai tsaye” Maash ya faɗa a daƙile.

     Ran jami’in ne ya sosu, sai dai baice komai ba ya cigaba da faɗin, “Akwai containers ɗinka da suka tashi daga Lagos a shekaran jiya da dare zuwa ƙasar Ghana. An samu yara ƴammata a cikin ɗaya da muke da tabbacin safararsu aka shirya yi. Still dai a cikin container ɗin anyima yaran makwanci, a ƙasan shi mun samu kayan laifi”.

       “Kamar……?”

Maash ya faɗa cike da rainin hankali. Yanzu kam a fusace jami’in ya kallesa. Sai dai kuma bai iya cewa komai ba ya cigaba da faɗin, “Drivers ɗin sun tabbatar mana da cewar sun fito daga companyn ka ne”. Ya ƙare maganar da tura masa hotuna gabansa. Batare da Maash ya ɗauki hotunan ba ya zuba musu ido kawai. Kansa ya ɗan girgiza cike da rashin damuwa ya furta, “A staff ɗina bana tunanin nasan waɗan nan fuskokin”.

       “Ba zamu tabbatar da hakan ba, dan zaka iya hiding nasu. Sai dai kuma su containers ɗin ai bazai yiwu kace ba naka bane ba”.

Shiru babu alamar Maash ɗin zai tanka, sai da ya mula dan kansa sannan ya saki ɗan gajeren murmushi da kai hannu ya shafi kwantaccen gashin fuskarsa. Zamansa ya gyara da ƙyau gaba ɗaya hannayensa akan table ɗin ya zubama jami’in ido. “Mr Man kamar ya dace ka tuna kai jam’i ne ba alƙali ba. Damar samuwar amsar tambayoyinka kuwa zaka same su ne kaɗai a bakin lawyers ɗina”. Daga haka ya gyara zamansa ya sake lumshe idanunsa duka hannuwansa harɗe a ƙirjinsa.

     Iya ɓacin rai Jam’in nan ya shiga. Dan haka ya miƙe a fusace ya fice abinsa. Murmushi Maash ya saki mai ɗan sauti batare da ya buɗe idanunsa ba.

         Har yamma Lawyers na Maash na fafatawa a station ɗin, shi dai yana a inda aka kaisa har yanzu. Sai da lokacin Sallah yayi ya buƙaci yin alwala. Basu da damar hanashi. Abincin da Hayatu ya kawo masa kuwa ko kallonsa baiyi ba. Dan shi fa sam bawai cakwakiyar station ɗin ma bace damuwarsa. Hankalinsa ma gaba ɗaya baya a wajen.

     Gab da magrib Baba prof… Ya iso, da ga airport kai tsaye shima station ɗin yayo, anan ya samu kusan duk ahalin gidan. Paah, Uncle Abdullahi, Hajiya Mammah, Maman Maleeka (Matar Uncle Abdullahi) sai Hayatu dake kai kawo tsakanin asibiti da aka kwantar da Samraah zuwa nan. Ko bayan isowar Baba prof.. ɗin shima ya kai awanni uku a station ɗin kafin su samu bell ɗin Maash ɗin bisa wasu sharuɗɗa masu tsauri.

         Ƙarfe tara da wasu mintuna aka fiddo Maash da ga ɗakin nan. Kallo ɗaya yay ma ahalin nasa ya ɗan kauda idanunsa. Sai kuma ya cigaba da takowa a nutsensa har inda suke. Baba prof.. ne ya riƙosa ya rungume yana faman ambaton Alhamdullah. Shi dai Maash baice komai ba. Bayan ya sakesa kuma ya koma tattaɓashi da jera masa tambayoyi. “Kana jin yunwa? Akwai inda ke maka ciwo? Sun maka wani abu ne?…..”

       “Grandpa! I’m not small boy now”.

Hot this week

Kazar Kwanci By Rufaida Omar

Kazar Kwanci By Rufaida Omar *1)*  " Mairamu! Mairamu!!" Matar dake zaune...

KAZAMAR AMARYA Na Rahama Kabir Mrs Msg

KAZAMAR AMARYA Na Rahama Kabir Mrs Msg Rahma Kabir:...

RUGUNTUSUMI Book 2 Compelet

RUGUNTSUMI Book 2 part 1 Rubuta labari Abdul’aziz Sani Madakin Gini Ɗaukar Nauyi Mansur...

GUDUN KADDARA NA HUGUMA BOOK 2

GUDUN KADDARA NA HUGUMA BOOK 2            ".............ya fada soyayya?,yana...

Gudun Kaddara na Huguma Book 1

Gudun Kaddara na Huguma Book 1 🏃🏽‍♀️ GUDUN ƘADDARA🏃🏽‍♀️ H U...

Topics

Honeywell Reloaded: Flour Mills of Nigeria Revives Its Iconic Brand

Flour Mills of Nigeria Plc (FMN), the leading food...

Fintech in Nigeria: Breaking Barriers and Driving Inclusion

Nigeria’s fintech industry continues to break barriers, driving financial...

Nigeria to Host Africa’s Largest Tech Expo

In a major boost to its tech credentials, Nigeria...

Edtech Revolution: Nigerian Startups Transforming Education

Nigeria’s edtech sector is witnessing unprecedented growth, with startups...

Telegram Sees A Rise In User Data Sharing With Law Enforcement

Recently published information from the messaging platform Telegram indicates...

BMW’s Latest User Interface Displays Widgets on the Windshield at CES 2025.

BMW is completely overhauling its in-car user interface, beginning...

Lagos Tech Summit Focuses on AI and Blockchain

The annual Lagos Tech Summit returned in 2025 with...
spot_img

Related Articles

Popular Categories

spot_imgspot_img