- Wani alkali yayi alkawarin zai biyawa Salele sadakin Naira N100,000 dan auren masoyiyarsa Bilkisu
- Mahaifiyar Bilkisu, Rahila Lawal tayi karar Salisu Salele kan cewa ya kyale mata yarta kar ya lalata mata ita ko kuma ya fito a daura masu aure.
- Salele a bangarensa ya fadawa kotu cewa bashi da sadakin aure saboda haryanzu agidan iyayensa yake kuma shi dalibin Jami’ane.
Alkalin kotun sharia a Kaduna malam Salisu abubakar tureta a ranar laraba ya amince zaibada tallafin naira 100,000 Dan biyawa wani saurayi Salisu salele sadaki dan ya auri bilkisu sahibarsa.
Alkalin ya fadawa Salisu ya tafi yayi nazari kan tayin da yamasa sannan ya dawo ya fadawa mai sharia abinda ya yanke a ranar 6 ga watan Satunba da za a cigaba da sauraren shariar.
Rahila Lawal mahaifiyar Bilkisu tayi karar Salisu Salele tana nema akan atilastashi ya nemi auran yarta ko kuma ya bar mata yarta idan bai tashi yin aure ba .
Mahaifiyar bilkisu tace:
“A layi daya muke zaune dashi kuma yana zuwa wajan ‘yata a sace ba tare da izininmu ba matsayin iyayenta.”
“Nasamu mahaifiyar sa dan tasan abinda ke faruwa sai tasanar dani cewa danta Salisu bai tashi yin aure ba.”
Salisu ya canza shawara na daina zuwa gurin yata, amma kuma yana kiranta a waya dan haduwa a gurare ma banbanta .
Banasan Salele ya lalatamin tarbiyar yata na shekaru, shiyasa na kai kararsa kotu.
Mahaifiyar Bilkisu ta jadda cewa idan Salele ya shirya ta amince zata bashi auren yarta.
Salisu Salele a bangarensa ya fadawa kotu cewa yanasan yarinyar , amma bashida shirin yin aure sai nan da shekaru biyu.
Salisu ya shedawa mai sharia cewa:
“Ni dalibine a daya daga cikin jami’um gwamnatin tarayya ,kuma bazanso aure ya hanani maida hankali ba.” Kuma ya kara da cewa “Banida sadaki, hasalima haryanzu a tare da iyayena nake zaune.”
A bisa wannan dalilin ne shi alkali mai shari’a ya yanke hukuncin biya ma Salisu sadakin Naira dubu dari (N100,000) dan ya auri masoyiyar tasa Bilkisu.