Quianna Hudson, mai shekaru 8, ta kawo bindigar mahaifinta makaranta, inda tayi amfani da ita wajen harbe malaminta mai shekaru 56, Jim Turner, a makarantar firamare ta Ford da ke Detroit, Michigan, Amurka.
Rahotanni sun nuna, Turner ya gayyaci Quianna zuwa ofishinsa, a lokacin da ake karatun motsa jiki, kuma jim kadan bayan haka, sai aka jiyo karar harbe-harbe guda biyu, lamarin da ya tsorata sauran dalibai suka tsere cikin firgici,
Jami’an tsaron makarantar sun garzaya wurin da lamarin ya faru, inda suka iske Turner ya rasu, tare da harbin bindiga a cinyarsa da kuma kirjinsa.
Nan take ’Yan sanda suka kama Quianna kuma a cen ne Quianna ta bayyana wa yan sandan cewa Malamin nata Mista Turner yana shafa ta a inda bata so kuma ya yi barazanar cutar da ita idan ta kai rahoton cin zarafin da yake yi mata.
Read Also: Da Dumi-dumi: Wasu Matasa Sun Yiwa DPO Yan Sanda Dukan Tsiya a Kano
Tsoron abunda zai faru ya sa, ta dauko bindigar mahaifinta daga karkashin katifa ta zo da ita makaranta domin kare kanta,
Hotunan CCTV sun tabbatar da bayanan da Quianna ta faɗi, inda aka ga bidiyon Turner yana kai ta ofishinsa akai-akai. Sai dai duk da haka ana sa ran iyayen Quianna za su fuskanci tuhume-tuhume da suka shafi mutuwar Mista Turner.
Al’ummar yankin sun samu rarrabuwar kawuna kan lamarin, inda wasu ke nuna shakku game da labarin Quianna, ciki har da malami Lorraine Jacobs, wanda ya shaida abin da ya faru.
“Na san Jim shekaru da yawa. Ba irin wannan mutumin ba ne mai mummunan hali,” in ji shi.
Sai dai wasu sun goyi bayan maganganun yarinya Quianna kuma suka ce ta kare kanta ne