A wasu daga cikin jihohin mu na Arewa kamar Jos, Kano da kuma birnin tarayya Abuja.
A Jihar Kano, Ranar alhamis din da ta wuce aka ga wasu dandazon matasa masu gabatar da zanga zanga domin tsadar rayuwa a Najeriya sun fara kira ga shugaban ƙasar Rasha, Vladimir Putin kan neman ya kawo musu agaji, inda wasu kuma suka karkata kan sojoji suyi juyin mulki a ƙasar.
Ranar asabar ma sun ƙara fitowa duk da cewar an sa dokar hana fici da shigi amma sun fito dauke da tutocin ƙasar Rasha inda sukayi rubuce rubucen neman agaji kan sojoji su zo su kifar da Gwamnatin Tinubu.( Thewhistler ne suka ruwaito)
Hakan kuma ta ƙara faruwa a garin Jos na Jihar filato da kuma birnin tarayya Abuja a lokacin gudanar da zanga zangar.
Anji bayani daga majiyar cewa mabiya Shi’a na da manufa wadda ba a sani ba kan wannan sabgar, Saboda a lokacin rikicin ƙasar Nijar suna cikin masu goyon bayan sojojin da sukayi ma Gwamnatin Muhammad Bazoum juyin mulki ranar 26 na watan yuli, shekarar 2024, kamar yanda majiyar to shaida
Mai bada bayanan ya tabbatar da cewa ya jiyo daga majiya mai tushe cikin gidan Gwamnatin Jihar filato cewa an samu wasu ƙungiyoyi da ake daukar nauyin su domin gudanar da zanga zangar inda Gwamnan Jihar wato Caleb Muftwang ya gargadi shugabannin al’umma kan taka tsan-tsan da masu karɓe zanga zangar, daga baya kuma aka sa dokar ta ɓaci na awa 24 a Jos da Bukuru ranar lahadi
Kwamishinan yan sanda na Jihar Kano, Salman Garba da Dattijo Tanko Yakasai sun tabbatar da wasu ne daban ke daukar nauyin wannan zanga zangar da matasa ke yi a ƙasar, ” akwai waɗanda ba sa ƙaunar ƙasar nan, kuma a shirye suke su ribaci duk wata dama da suka samu su yi amfani da wasu domin su rusa ƙasar nan “